Showing 18001 words to 21000 words out of 166068 words
tana yake duk a lokaci guda saboda yanda zuciyarta ta jagule.
A falo suke zaune kusan duk dangi ne a kewaye da ita anata raha da kokarin kwantar mata da hankali.
Ta sha kwalliya cikin wani shudin leshi mai ado da fulawowi ruwan gwal ta yafa karamin mayafin nan da ake kira Chantilly a kanta. Hannuwanta da kafufunta sun dauki kunshi ga fatarta sai sheki takeyi. Kunshin yayi matukar kyau a kan fatar tata duk da ita din ba fara bace, fuskarta babu yabo babu fallasa domin ta ki bari ayi mata kwalliya; sai dai hakan bai hanata yin kyau ba.
Tana zaune a tsakiyar danginta amma kamar ace kyat! ta ruga da gudu.
Farha ce ta shigo da gudu itama ta sha kwalliya, da murnarta ta tsallake mutane ta fada jikin Aishan tana fadin
‘Mama Baba Abba ya zo, da Anti Bushra da Anti Rakiya harda ma Sultan da Hajiya karama. Bari ma naje na shigo da su na manta.’
Kafin a bata amsa ta mike ta sake fita da gudu cikin murna da farin ciki tana ta tsalle-tsalle.
Take jikin Aisha ya kara sanyi, ta dubi Zahida wadda take gefenta suka hada ido Zahidan tana kokarin kara mata kwarin gwiwa da idonta; nan da nan hawaye ya kwace mata ta mike da gudu tayi dakinta. Kafin ayi magana Zahida ta mike ta bi bayanta Anti Uwani tana fadin
‘Ke ki dinga tashi a hankali saboda cikin jikinki.’
Ko saurarenta bata yi ba ta rufa mata baya suka turo kofar. Ta kusa kaiwa bandaki Zahida tace
‘Ya Aisha.’
Ta juyo ta tsaya, yayinda Zahidan ta kara matsowa. Ta fada jikin Zahida suka rungume juna; duka su biyun kowacce tana fitar da hawaye, sai da suka dauki lokaci a haka sannan Zahida tayi kokari ta banbare Zainab daga jikinta saboda yanda take ji yaron dake cikinta ya fara takura yana zullo. Suka rike hannun juna suna kallon juna suna hawaye, Zahida ta jasu suka karasa suka zauna a bakin gado. Aisha ta matse hannun Zahida ta bude baki cikin rawar murya tace
‘Hida zan iya kuwa? Hida Mustafa ya tafi da rabin zauciyata, ya za ayi na iya sallamawa wani mutumin ruhi na?’
Ta kifa kai a cinyar Zahida ta cigaba da kuka Zahida tana shafa kanta tana share nata hawayen. Da kyar ta lalubo bakinta tace
‘Ki yi hakuri Yaya Aisha, ki cigaba da yi masa addu’a. You will be fine in sha Allah kuma wannan auren da zakuyi shine zai tabbatar da cewa kin karbi hukuncin Allah a kanki, ki cigaba da addu’a.’
Motsin bude kofa ya sa Zahidan ta waigo yayinda Aishan ta dago kanta fuskarta duk hawaye. Bushra ce ta turo kofar a hankali ta shigo da sallama ta mayar ta rufe kofar.
Aisha ta kalleta tayi mata murmushi da fuskarta me hawaye a hankali ta kirawo sunanta
‘Anti Bushra.’
Ta karasa ta tsuguna a gaban gwiwoyin Aisha ta dafata tana dariya
‘Bari na tari hawayen amarya.’
Sukayi dariya gaba daya, su Aisha suna share hawayensu.
Zahida tace
‘Kiyi hakuri Anti Aisha kin ji, wannan shine hukuncin Allah. Allah ya sa miki albarka a rayuwarki. Hajiya tana gaisheki, kuma don karta sakaki kuka ne taki zuwa amma duk da haka sai da kikayi kukan.’
Tayi murmushi ta share sabon hawayen da ya zubo mata.
Bushra ta kalli Zahida tace
‘Anti Hida kin barta zata latse mana hancin yaro saboda kukan amarci.’
Sukayi dariya gaba daya, Aishan ta mike tana dariya ta shige bandaki tana fadin
‘Bari na wankon fuska.’
Sai da tayi da gaske sannan ta iya tsayar da hawayenta ta fito ta gyara fuska, suka fito aka cigaba da bikin wanda dama amaryar da kanta tace bata son kida.
Ana saukowa daga sallar Juma’a aka daura auren Yusuf da Aisha.
Kafin ayi sallar magriba matar Yaya Abubakar ta tattara yaranta ta hada da Abdallah da Farha da kuma yaran Zahida suka wuce gidanta; haka Hajiya ta sakata saboda yanda take ganin idan an zo daukar amarya zasu sata kuka.
Ana idar da sallar magriba Anti Uwani ta leka dakin Aisha tacewa Zahida su shirya ‘yan daukar amarya sun taho. Nan take hawaye ya sake ballewa a idon Aisha, haka Zahida da Zainab suka sakanta a gaba suka tayata shiryawa.
Atamfa ta saka dinkin riga da siket, rigar fitted ce shi kuma siket din dogo ne mai tattara a baya. Ta nade jikinta da farar laffaya wadda Sajida ‘yar kanwar Hajiya ta aiko mata ita daga Switzerland; inda take zaune da mijinta. Kana ganin laffayar nan ka san an kashe kudi, fara ce kal da zanen shudayen fulawowi a kasanta ga duwatsu sai kyalli take. Tunda aka ware laffayar kamshi ya cika dakin saboda yanda Zahida ta dauki lokaci tana yiwa laffayar nan turaren wuta.
Tayi matukar kyau musamman da yake an samu ta daina kukan, sai kwalla kawai wadda da zarar ta fito take gogewa da tissue din da yake hannunta.
Wajen karfe takwas na dare masu daukan amarya sukayi sallama a gidan, ba tare da wani bata lokaci ba aka basu amarya. Anti Uwani da kuma Inna wato kanwar mahaifinsu tare da su Zahida sune suka tafi rakiya.
Sai bayan sun kama hanya sannan Yaya Bello ya kirawo Yaya Saratu ya sanar da ita idan sun dauko amaryar su fara kaita gidan Zahra sannan su kaita dakinta. Shi kuma Yusuf Zahida ya kirawo ya sanar da ita domin da sun gama maganar gidanta za a kaita.
Ba tare da wata damuwa ba suka kama hanyar unguwar Sokoto road inda nan ne za a kai amarya.
UWAR SADDIKU
Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)
9
An riga an bawa ango hutun aiki na ‘yan kwanaki don haka ranar Juma’a ma sai wajen sha daya ya tashi daga bacci. Bayan ya gama karin kumallo ya shirya abokinsa Alhaji Safiyanu yazo suka fice, sai da suka karbi kayan da ango zai sa daga wajen guga sannan suka wuce guest house din Alhaji Safiyanu inda daga nan zasu shirya su wuce daurin auren.
Yana fita itama Zahra ta hau shiri, nan da nan aka gyare gida aka sa turare ya dauki kamshi. Zuwa azahar aminiyarta wato Hajiya Amina ta karaso da abincin da baki zasu ci domin ita aka bawa kwangilar, bayan sun kule a daki suna zaune a gefen gadon Zahra Amina ta dubeta tace
‘Baki da matsala kawata, sai wani sheki kikeyi kamar ba wadda za ayiwa kishiya ba.’
Tayi dariya suka tafa
‘To me yafi raina kawata, auren dare daya ai ba zai daga min hankali ba.’
‘Hakane.’
Suka gama shirya yanda za ayi sannan suka sauko falon aka cigaba da hidima inda ‘yan uwan Zahra suka zo aka hadu.
Daga baya wajen la’asar kuma Hajiya Karima matar Yaya Bello ta iso tare da Maimuna matar Musa kanin Yusuf din da yaransu.
……..
Ana cikin kiran sallar magriba Hajiya Amina ta mike ta yiwo alwala a dakin baki da yake kasa, ta tsaya a falon ta dubi Karima tace
‘Yaya Karima kuyi alwala sai ayi Sallah a dakin don a samu a share falon a gyara tunda ance da anyi sallar magriba za a kawo amaryar.'
Nan da nan kuwa aka mike, aka fara alwala ana Sallah.
Jummaice ta share wajen tsaf ta gyara kafin a gama Sallah.
Kana shigowa falon kujerar zaman mutum uku ce ta bawa kofar baya, don haka idan mutum ya shigo akwai waje tsakanin kujerar zaman mutum uku da Kuma ta mutum daya inda ta nan ne mutum zai karasa tsakiyar falon ga zauna. Duk wanda ya shigo ta nan wajen yake wucewa don haka Zahra da Amina suka yanke shawarar a nan za a ajiye ‘yar layar da Malam ya ce a saka inda amarya zata tsallaka.
Da fari Amina ta so a saka a kasan dan carpet din da yake bakin kofa amma Zahra ta sanar da ita shi ana yawan dagashi saboda yawan wucewa, idan aka saka a nan akwai yiwuwar wani ya gani. Wannan babban center carpet din kuwa tunda kafar doguwar kujera a kansa suke ba a dagashi, gara su saka a nan tunda dole ta nan za a wuce da ita.
Ana gama shara Hajiya Amina ta faki ido ta daga carpet din ta ajiye layar ba tare da kowa ya kula ba, daga baya suka idar da sallah suka fito aka zauna aka cigaba da hirarraki. Daga baya makota suma suka shisshigo aka hadu ga yara sunata guje-guje don haka aka cika falon.
Tunda ‘yan kawo amarya suka daukota suka kamo hanya Yaya Saratu ta kirawo Zahra ta sanar da ita sun taho kamar yanda ta nema; a cewarta don su kintsa. Karfe takwas da kwata motocin amarya suka tsaya a kofar gidan Zahra.
Sai da kowa ya fita daga mota sannan aka bude motar amarya, Inna ce ta fara fita sannan amaryar ta fito yayinda Goggon Yusuf din ta fita ta daya gefen suka saka amarya a tsakiya Goggo na rike da hannunta. Duk matan da suka fito daga motocin su suka wuce gaba don haka amarya ce a karshe da su Goggo, sai Anti Karima matar Yaya Bello wadda itace a karshe ta dafe musu baya.
Suna shiga falon aka fara zabga guda, nan da nan wasu daga cikin matan dake falon suka mike.
An shigo da amarya sai kuma aka dan sami tsaiko mutane sun dan yi yawa ana ta magana su gafara a karasa a zaunar da amarya. Kafin su gama budawa Anti Karima ta tabo Goggo ta nuna musu daya gefen tace
‘Goggo ku zaga ta nan mana, yara sun cushe nan din yanzu sai na fitar da su.’
Don haka Goggo ta ja amarya suka kewaye kujerar mutum biyu suka shigo ta daya gefen tsakanin kujera da TV, nan amarya ta kwabe takalminta fuskarta lullube da mayafi aka karasa da ita aka zaunar da ita kusa da Zahra bayan an tashi matar da take zaune a wajen.
Nan take zuciyar Zahra ta cushe, suka kalli juna ita da Amina dake gefenta Amina tayi mata alama ta nutsu don haka ta hadiye takaicin da ya taso mata ta waske.
Nan su Goggo suka saka su a gaba da nasiha a kan su zauna lafiya, bayan sun gama akayi addu’a. Duk yanda Amina taso ta canzawa layar nan waje bai yiwu ba domin yarane ma a daidai wajen a tsattsaye suna kallon amarya suna surutunsu.
Bayan an Shafa addu’a Amina ta mikawa Zahra canjinta naira dubu goma ta dorawa amarya a cinyarta tana fadin
‘Ga wannan amarya babu yawa.’
Zahida ta sa hannu ta dauke suka yi godiya amarya ta mike, daidai lokacin Amina ta mike ta wuce musu gaba tana kokarin su bi ta daya gefen inda ta saka layar dai-dai lokacin Inna tabi ta daya gefen tana fadin
‘Ga takalman mu nan, ku biyo ta nan.’
Don haka suka bi ta inda suka shigo ana ta zabga guda, suka fice amarya ta bar falon yana kamshinta.
Makotan Zahra duka sukayi mata sallama suka wuce don suna son su ga gidan amarya, nan da nan zugar yara suka bisu harda ‘yan uwan Zahra ma don babu wanda yaga gidan sai yanzu kowa yake so yaje ya gani.
Aka barsu daga ita sai Amina da Yaya Murja sai Yusra wadda itama take taya uwarta kishi.
Suna ficewa Yusra ta shige dakinsu ta turo kofa, Yaya Murja ta dubi Zahra da Amina tace
‘Kowa ya tafi ganin gidan amarya, to Allah ya baku zaman lafiya. Bari na dauko wayata a dakinki Zahra can na sa chaji.’
Tana hayewa sama Zahra ta dubi Amina rai a bace harda kwalla a idonta
‘Kin gani ko Aminoni, kin gani ko! Na gaya miki Karima bata kaunata tun tuni, tunda aka fara maganar auren nan ita da mijinta suke rawar kai da shisshigi. Ita ta hana ayi mata kishiya amma don iskanci duk wadda za ayiwa itace a gaba wai ita nan matar Babba a dangi. Wallahi sai na gyarawa matar man zama ko da wa take yawo.’
Amina ta dafa cinyarta
‘Ki bar wannan maganar, yanzu zan dauke miki layar tunda na san gobe da safe zai kawo miki ita in ya so sai kiyi amfani da wannan damar kinga daga ku sai ku.’
Tayi kwafa ta share kwalla
‘Aminoni ban so matar nan ta wuce gobe a gidan nan ba, amma bari Allah ya kai mu goben zan yi maganinta.’
‘Kada ki damu kawata ai sai mun…'
Motsin saukowar Yaya Murja ne ya dakatar da ita, take kuma ta sauya zancen
‘Ai hakuri ne naki, kece babba idan baki bada wata kafa ba babu abinda zai faru.’
Yaya Murja tace
‘Gara dai ki gaya mata, ki rike girmanki babu matar da zata fiki a wajen miji. Kuma gashi ma ke danginsa duk suna sonki ai ke idan tace zata ja dake ma sune zasuyi miki fadan.’
Ta jijjiga kai tana murmushin yake.
A hankali mutane suka fara dawowa gidan kuma suna yi mata sallama domin wucewa gidajensu. Daga baya Aminan ma tayi mata sallama bayan ta bata ‘yar karamar layar wadda ta saka a aljihun doguwar rigar da take jikinta, ta rakata kofar falon sukayi sallama ta fice.
……..
Sai wajen sha daya na dare saura sannan Alhaji Safiyanu ya kawo ango gida da ledojinsa guda biyu; daya na Zahra, daya kuma na Aisha.
Gidan Zahra ya fara shiga, lokacin duk yara sunyi barci don haka babu kowa a falo. Kai tsaye ya wuce sama.
Dakinsa ya wuce kai tsaye, kamar yanda yayi tsammani Zahra bata ciki. Don haka ya ajiye kayansa ya dauki ledar da ya shigo da ita ya wuce dakinta.
Tana kwance a kan gado sanye da kayan bacci an kashe fitila da alama bacci takeyi, ya kunna fitlar tare da yin gyaran murya ya karasa ciki da sallama. Ta juyo ta dubeshi sannan ta tashi zaune a tsakiyar gadon, yayinda shi kuma ya zauna a gefen gadon.
‘Sannu da zuwa.’
Ta fada murya kasa-kasa.
Da murmushi ya amsa
‘Sannu. Ya gajiya? Ya taro?’
‘Alhamdulillah, kowa ya tafi makwancinsa.’
Yanayinta da kuma yanda take bashi amsa ya fahimci bata da walwala kuma idan yaja hirar zasuyi rigima, don haka ya ajiye ledar a kan durowar gefen gadonta yana fadin
‘Ga wannan ke da yara, sai dai naga duk kunyi bacci sai ki saka a fridge kwayi breakfast da shi.’
‘Mungode.’
Suka dan taba hira tana ta faman cijewa saboda kada tayi kuka a gabansa, shi din ma da yake yana sauri ya tafi wajen amarya kafin Zahran ta fara wata fitnar sai kawai yayi mata sallama yace ta rufe musu gidan.
Ta biyoshi a baya har suka zo bakin kofa sannan ta rufe musu kofar shi kuma ya wuce, ya dauki ledarsa a mota ya nufi gidan amarya.
……….
Kamshin da ya cika gidan shi ya fara yi masa maraba, ya riga ya san ita kadai ce a gidan don haka yana shiga ya mayar da kofar ya kulle. Ya karasa ya ajiye ledar hannusa a kan dining table, ya juyo ya karewa falon kallo yana murmushi.
Ya shige dakin yana rike da Babbar rigarsa, tun kafin ya karasa ciki ya hangota a kan gadon nade da laffayarta ta kashingide daga zaune a gefen gadon. Ya karasa ciki da sallama wadda ta farko da ita daga gyangyadin da takeyi, ta gyara zama tana amsa sallamar.
Ya karasa ya zauna a kusa da ita yana kallon fuskarta yana murmushi yayinda ta mayar masa da murmushinsa tana kokarin boye kwallar da take makale a idonta. Ya kama hannunta na hagu yana kallon lallenta, ta bi hannunsa da kallo yanda ya rike hannunta. A take hawayen da take boyewa ya kwace; Mustafa; ta kasa cire shi daga kwakwalwarta tunda aka ce an daura mata aure.
Ya matsa kusa da ita ya janyota jikinsa ya kwantar da kanta a kirjinsa; ya fahimci abinda yake saka ta kuka, ko bata gaya masa ya san tunanin tsohon mijinta takeyi. Yayiwa kansa alkawarin tabbas sai ya jiyar da ita dadi a rayuwarsu, sai ya so ta ya nuna mata soyayya fiye da yanda tsohon mijinta ya nuna mata. Sai ya jiyar da ita dadin da zata manta da duk wani namiji idan ba shi ba; domin shima yana sonta kuma ya tabbatar yana sonta fiye da yanda Mustafa ya sota.
Sai da ya dauki lokaci yana lallashinta sannan ta iya samu ta tsayar da hawayenta. Ya tayata ta warware laffayarta suka ci abinci sannan sukayi alwala sukayi Sallah.
Sai da yayi da gaske da ita sannan ta iya canza kayanta ta saka kayan bacci, yana ta yi mata dariya kamar wata budurwa saboda kunyar da take ji. Bayan sun gama ya kashe musu fitila suka kwanta, rungumeta kawai yayi saboda ya kula da yanda take cikin damuwa kuma ga bacci da take ji. Ya danne duk wata bukata tasa ya kyaleta zuwa gobe, kafin nan ta kara sakewa ta sami nutsuwa.
……
Kusan lokaci guda suka tashi da asuba, nan da nan sukayi wanka suka yi Sallah. Yayi zaton zata koma bacci don haka ya fice daga dakin ya komo falo ya fara kokarin hada TV. Bai jima da fitowa ba itama ta fito, suka zauna yana hada TV din suna hira, har ya gama suka zauna suna kallo.
Karfe takwas ta dan gota ta dubeshi tace
‘Nifa yunwa nake ji, bari na duba ko ruwan shayi na sama mana.’
Ta mike ta nufi kicin, yayinda shima ya nufi dining table inda ya ajiye ledar da ya shigo da ita jiya. Ya zazzage kayan shayin da burodin da ya siyo ya kwasa ya kai mata kicin din.
Yayi tunanin Zahra zata basu breakfast amma baya so yayi maganar don bai san yanda za su dauki abun ba. Nan da nan Aisha ta hada musu shayi da burodi ta dumama ragowar naman jiya suka zauna suna kallon TV suna cci
____
Tana zaune a falonsa ita kadai tana shan shayi, shayin kawai zata iya sha a halin yanzu domin kanta ciwo yake yi saboda yanda bata samu tayi bacci