Showing 126001 words to 129000 words out of 166068 words

Chapter 43 - UWAR SADIKU COMPLT BY SAKINA YAZID.txt

11 Jul 2024

25394

san ko yana gida ko baya nan ba. Ta juyo cikin sanyin jiki ta koma kan gadon ta zauna ta zuba fuskarta a tafukan hannunta ta sake fashewa da kuka. Bata da wata mafita illa ta kirawo Abban Saddiku ta sanar da shi domin idan ma taje asibitin ita kadai a halin yanzu komai zai iya faruwa.

Ta kama gefen hijabin da yake jikinta ta goge hawayenta, tayi ajiyar zuciya ta laluba jakarta ta dauko wayarta. Ta lalubo lambar Abban Saddiku ta danna kira ta kara a kunnenta zuciyarta na dakan uku-uku.
…………

Fitowarsu kenan daga gidan Hajiya shi da Yaya Bello, suka shiga motar Abban suka kama hanyar gidan Yaya Bello inda a can zasu ci abincin rana. Yana zura mukullin motar kira ya shigo wayarsa wadda ajiyeta kenan a kusa da giyar motar; ya fasa tayar da motar ya amsa wayar ya kara a kunnensa. Ba tare da ta amsa sallamarsa tace

‘Abba Saddiku bashi da lafiya yana asibitin Malam a emergency, yanzu Yayan abokinsa da suke tare ya kirawoni ya sanar da ni.’

‘Subhanallah! Accident yayi ko me?’

‘Nima dai ban gane bayanin ba amma dai ba accident bane, nima yanzu zan sami motar haya na wuce asibitin idan kuma kana unguwar sai na shirya mu tafi.’

‘Ina gidan Yaya kiyi zamanki zan je na gani in ya so mayi waya.’

Ya ajiye wayar ba tare da ya saurari amsarta ba.
Ya dubi Yaya Bello da yake gefensa ya sanar da shi abinda ta gaya masa, nan yace su wuce asibitin kawai. Don haka Abban ya tayar da motar suka kama hanya.

Ita kuwa Zahra yana ajiye wayar ta dora hannu aka ta sake rushewa da kuka; shikenan a gaban Yaya Bello za a yi mata wannan tonon asirin, ya sami dalilin da zai shiga rayuwarsu ita da yaranta ya hanasu jin dadi.

Sai da tayi mai isarta sannan ta dauki wayarta ta kirawo Yaya Murja ta sanar da ita halin da ake ciki, duk da bata gaya mata cewa kwaya Saddikun ya sha ba.


Sukayi sallama a kan idan taji abinda ake ciki ta sanar da ita.
…………

Har suka isa asibitin Malam Aminu Kano babu wanda yace wa dan uwansa wani abu; shi Abba yana ta mamakin to Saddikun da aka ce masa dazu ya fita meye zai sameshi har a kaishi emergency kuma ace ba accident ba yayinda shi kuma Yaya Bello yake kallon hanya yana nashi nazarin.

A kusa da emergency din yayi parking suka fito suka shiga, sai dai suna shiga kuma ya rasa wanda zai kama. Don haka ya janyo Yaya Bello suka dawo waje ya kirawo Zahra ya tambayeta wanda zasu nema; bayan ta sanar da shi ya ajiye wayar ya kirawo lambar Saddikun sanna suka nufi komawa cikin emergency din.

Yana shiga ya hango wanda yake waya da shi; yaro ne matashi wanda ba zai wuce shekaru ashirin da biyar ba zuwa da shida. Da hanzari ya karaso wajen su Abban,bayan sun gaisa ya mikawa Abban wayar Saddiku yana fadin

‘Ga wayar Sadik din.’

Ya karba yana fadin

‘Wai me ya samesu ne?’
Cikin damuwa yace

‘To ni dai abokinsu ne ya kirawoni kuma a hotel na samesu wai party sukeyi shine suke competition aka wanda yafi shan kwaya da yawa zasu bashi kudi 250k. Su ukun da suke kwance a nan su suke shan kwayar shine da sauran suka ga sun sume duk suka gudu sai abokinsu daya ya kirawo ni ya gaya min don harda kanina a cikinsu. Shima yana gaya min ya gudu, don yanzu ma likitocin tambayar da suke shine a gaya musu sunan kwayar da suka sha don su san irin abun da ya dace suyi musu amma ni ban sani ba; abokan nasu kuma duk sun kashe waya. Gasu can dai su uku a kwance a sume an dai musu allura.’

Yaya Bello yace

‘Subhanallah!’

Matashin da yake yi musu bayani yace

‘Likitan da yake duba su yana wancan office din, ku zo mu karasa sai kuji daga bakinsa.’

Yaya Bello yaja hannun Abban Saddiku wanda ya kasa wani katabus suka bi bayan yaron.

Bayan ya gabatar da su a wajen likitan shima likitan irin bayanan da yayi musu ya sake basu, ya dora da

‘Matsalar itace bamu san irin kwayar da suka sha ba. Shi daya yaron da ya farfado yace sunan kwayar flash dayar kuma rod, a lussafinsa shi kwaya uku ya sha yayinda su kuma suka sha biyar ko shida. Muna bincike kuma muna jira su farfado mu sami ainahin sunan kwayar domin shine zamu san irin abinda ya dace muyi musu.’

Suka yiwa likitan sallama bayan ya sanar dasu idan sun farka za a mayar da su sashen kula da kwakwalwa.

Bayan sun fito daga ofishin suka karasa inda Saddikun yake; yana nan a kwance babu alamar wani motsi a tare da shi idan banda numfashi da yake futarwa a hankali. Suka kare masa kallo Yaya Bello yace

‘Allah ya kyauta.’

Ya janyo hannun Abban Sadik wanda yake binsa kamar mutum-mutumi suka fito bayan sun yiwa yaron godiya sun sanar dashi cewa suna nan a farfajiyar asibitin idan an bukaci wani abu.

Akwai dan waje daga gefen emergency din da kujerun siminti na zama, nan suka je suka zauna. Suna zama Abban ya zuba fuskarsa a tafukan hannunsa yayinda shi kuma Yaya Bellon ya zauna kusa da shi yana nashi nazarin ba tare da yace komai ba.

Sun dauki kusan minti goma haka kafin Abban Sadik ya sauke hannuwansa ya dubi Yaya nasa cike tsananin damuwa yace

‘Allah ya sauwake.’

‘Amin ya Allah.’

‘Wallahi Yaya ban san yanda aka yi Saddiku ya zama haka ba. Kusan mutum uku ne suka yi min magana a kan na binciki yaron nan, don malaminsu na secondary school ma kai tsaye ya gaya min cewa yana shaye-shaye. Amma duk yanda naso na dauki mataki a kai uwarsa ba zata bari ba domin wasu lokutan ko bari na ganshi ma bata yi. Gashi ko an kama shi da laifi ta iya kare shi, wasu lokutan ma kamar shashantar dani take ta mantar dani al’amarinsa. Yanzu ka ga abinda ya faru ko Yaya? Da anyi mata magana sai tace wai ana so a hadani da shi.’

Yaya Bello yace

‘Sha’anin mata ne sai hakuri. Yanzu jira zamuyi ya farfado muji daga bakin likitocin yanda za ayi a taimaka masa don ba zamu barshi haka ba.’

Cikin kunan rai ya cigaba


‘Ka ga tunda har ya kai ya shiga gasar shan kwaya kenan ya dade yana yi har ta bi jikinsa, kuma ma kudi har naira dubu dari biyu ina suka samo su? Ni dai ban taba bawa Saddiku naira dubu goma ba ma ba balle dubu dari biyu ko fiye. Ina ya sami wadannan abokanma?’

Suka cigaba da tattaunawa Yaya Bello yana kwantarwa da Abban hankali yana gaya masa za a samu ya bari in Sha Allahu.

Wajen karfe biyu suka jiyo kiran Sallah daga nesa, Yaya Bello ya dafa Abban yace

‘Ba muyi Sallah ba ai gara mu lekashi sai mu nemi masallaci muyi Sallah ko.’

Suka mike gaba daya.


UWAR SADDIKU


Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)


38

A nan asibitin suka zauna, sai waya Yaya Bello yayi gida ya sanar da su Asma’u taje ta bawa Hajiya abinci.

Tun shigowarsu abokin Sadik din ya bawa Abban mukullin motar Sadik din ya sanar da shi hotel din da sukayi party din inda a nan motar take. Don haka suna nan zaune ya kirawo wani yaronsa Shamsu yace ya zo ya sameshi a asibitin. Da yake lokacin da suke wayar Shamsun yana court road ba tare da bata lokaci ba ya hawo Babur ya karaso ya samesu. Mukullin motar Mommy din ya bashi ya sanar da shi inda motar take, yace yaje ya dauki motar ya ajiye masa ita a wajensa zai nemeshi. Sukayi sallama ya hau babur dinsa ya kama hanya.

Bayan an idar da sallar la’asar su Abba suka koma inda Saddiku yake kwance. Zuwa lokacin daya yaron wanda ya rigasu farfadowa har an canza masa daki yana tare da iyayensa. Shi kuma daya yaron kanin saurayin da su Abban suka tarar mahaifiyarsu ta riga ta zo inda ta yiwa likitan bayanin tana so su sallameshi zuwa gobe don ita da yaran zasu bi jirgi zuwa Lagos daga can zasu wuce Dubai hutu; tana so likitan ya rubuta mata medical report idan sun je can likitocin zasu sake duba yaronta.

Bayan ta gama bayanin suka gaisa da Abba suka jajantawa juna, likitan yayiwa su Abban bayanin cewa su Saddikun ma yanzu sun farka don haka ana bukatar a samo madara su sha sannan za a canza musu daki inda za a cigaba da kula da lafiyarsu.

Ba tare da bata lokaci ba Abba ya fita ya siyo madarar ya kawo, da taimakon ma’aikaciyar jinya Yaya Bello ya daga Saddikun wanda har zuwa lokacin idonsa yake a rufe ya dura masa madarar aka samu ya sha kadan.

Zuwa karfe biyar da rabi sun dan kara farfadowa domin shi Saddiku har yana kiran Mommy yana wasu zantuka da ba a gane me yake fada. Nan aka turashi a gadon jinya aka mayar dashi wani dakin a sashen kula da kwakwalwa. Aka saka mishi drip kuma aka sake yi masa allurai.


Bayan likitan ya fita Abba ya zauna a kujerar dake ajiye a dakin yayinda Yaya Bello ya tsaya a daidai kan Saddikun yana tofa masa addu’oi.

A hankali yayi shiru ya daina surutun, Yaya Bello ya dawo ya zauna a kujerar dake kusa da wadda Abban yake kai. Ya dubi Abban yace

‘Ko Zahran za a sanarwa saboda a sami wanda zai zo ya kwana da shi mu samu muje gida zuwa safiya ko?’

Cikin sanyin murya yace

‘Eh ba zan ma kirawota ba don bana jin zan iya saurarenta yanzu. Namiji dai ya kamata a samu ko kuma ni din in an jima sai na dawo zuwa safiyar mu gani.’

Yaya Bello yace

‘Ba za ayi haka ba, gamu da samari a dangi. Ko wajen su Jamilun Inna ai za a sami mai kwana da shi ko kwana nawa za ayi. Kuma ma yanzu ina ga Muhammadu zan kirawo ya taho musu da kayan bukata ya zo su kwana da shi tunda ba abu ne da ake so ya baza dangi ba ayi ta faman cewa yana shaye-shaye.’

Kafin Abban ya bashi amsa ya kirawo Karima ya sanar da ita halin da ake ciki, yace ta bawa Muhammadu kudin mota kuma ta zubo musu abincin dare ta bashi abun shimfida suna jiransa idan ya zo sai su tafi.

Muhammadu shine yaron Yaya Bello na farko wanda zai bawa Saddiku kamar shekaru hudu, don a halin yanzu shi yana ajin karshe a Jami’a inda yake karantar aikin jarida.

Nan suka zauna har zuwa lokacin da Muhammadu ya iso sannan sukayi masa sallama suka tafi.
-----------

Tunda Abban Saddiku ya fita ya sanar da ita gasu a asibiti kuma shima bai san me ya sami Saddikun ba don baya cikin hayyacinsa take cikin matsananciyar damuwa. Gashi Abban ya ce kada ta sake ta zo asibitin sannan kuma ya ce ta daina damunsa da waya idan ana bukatar wani abu a wajenta zai nemeta. Haka ta kasa sukuni kuma ta rasa me zata cewa yaran da suke ta faman tamabayarta ko bata da lafiya; don haka kawai sai ta biye musu a kan bata da lafiya sannan kuma Yaya Sadik ma bashi da lafiya yana asibiti Abba ya kai shi.

Har la’asar tana rike da waya tana jiran shigowar kiran Abba ko kuma ta ji shigowarsa gidan amma shiru. Hankalinta ya kara tashi don haka ta sake kiran Yaya Murja ta rushe da kuka. Cikin firgici Yaya Murja tace
‘Subhanallahi! Zahra Saddikun mutuwa yayi ne kike kuka haka? Ki gaya min me ya faru.’

Cikin shesshekar kuka tace

‘Yaya nima ban sani ba Abbanshi yana can tare da shi kuma yaki yayi min bayani har yanzu shiru, cewa ma yayi kada na sake yi masa waya sai ya dawo.’

‘Ikon Allah! To kiyi hakuri mana, na san tabbas da mutuwa Saddiku yayi da yanzu kin ji labari ai lafiya ce take buya akasinta baya buya. Kiyi hakuri zuwa lokacin da zai dawo gidan sai mu ji.’

Suka ajiye waya.

Jimawa kadan kuma Yaya Murja itama ta kasa nutsuwa saboda yanda Zahran take kuka, don haka nan da nan ta barwa abokiyar zamanta girkin da yake nata ta kama haryar gidan Zahra.

A dakin ta sami Zahran suka zauna tana ta bata baki; sai dai har zuwa lokacin Zahran bata gaya mata gaskiyar abinda ya samu Saddikun ba. Ta dai sanar da ita cewa lafiya kalau ya fita abokinsa ya kirawota yace bashi da lafiya har sun kai shi emergency. Don haka suka zauna suna jiran Abban ya dawo ko ya bugo waya.
Har Magriba ta kawo jiki bai dawo ba don haka Yaya Murja tayi mata sallama ta tafi nata gidan a kan duk abinda taji ta sanar da ita, sannan kuma idan dare ya kara yi Abban bai dawo ma ta sanar da ita sai ta gayawa Yaya Muhammad ya nemeshi.

Ta tafi ta barta zuciyarta fal damuwa.
---------

Suna fita daga asibitin suka sami masallaci sukayi Sallar Magriba sannan suka wuce ya sauke Yaya Bello a gidansa.


Ya ji dadi matuka da Allah ya sa ba a gidan Zahra zai kwana ba don yanda zuciyarsa take tafasa baya jin zai iya saurara mata; domin duk halin da Saddiku ya shiga laifinta ne.

Ba zai kirawo wannan abun da jarrabawa ba domin sakaci ne kuma ya san da laifinsa a ciki; to amma me yasa Zahra take katangeshi daga yiwa dansa tarbiyya? Shi din me ya rufe masa ido yaki ya jajirce? Tabbas Zahra itace ta san kulle-kullen da ta dade tana yi a kansa kuma baya jin zai iya yafe mata idan ta lalata masa yara.

Kai tsaye gidan Aisha ya wuce; ta gama abincin dare ta jera a table gidan yana ta kamshin turare.


Kallo daya tayi masa ta san cewa akwai damuwa a tare da shi. Bayan ya amsa sannu da zuwanta ya dubi dining table yace

‘Kin gama abinci ko? Yunwa nake ji.’

‘Na gama, zaka sake kayan ko sai ka ci abincin?’

‘Hakane, bari ma na fara yin wanka.’

Yana fitowa daga wankan ta zuba masa abincin wanda tuwo ta dafa da miyar agushi, ya ci ya koshi ba tare da yace mata komai ba. Bayan ya gama ya taso daga table ya dawo gaban TV, ta kwashe kwanukan sanna ta hado shayi ta ajiye masa. Ya dauki remote ya kunna TV a daidai lokacin da ta zauna a kusa da shi tana kallonsa.

Ya kalleta yayi gajeren murmushi yace

‘Ya ake ta kallon fuskata kamar ana karanta littafi?’

Ta mayar masa da murmushin tana wasa da gashin kansa tace

‘Na ga kamar ka shigo da damuwa ne shine tunda ba a gaya min ba nake kokarin karantawa, tunda ka san an ce labarin zuciya a tambayi fuska.’

Yayi murmushi.

Nan ya bata labarin abinda ake ciki, sosai ta jajanta masa sannan tace

‘Kuma ka ga maganar Yaya gaskiya ne, idan aka samu ya farfado gaba daya akwai rehabilitation centers inda idan ka biya zasu ajiye shi tsawon wani lokaci a dorashi a kan magunguna da therapy har a samu ya rabu da shan kwayar. Sai dai fa su yawanci gaskiya a can ake kwana kamar boarding school.’

Ya kalleta cike da damuwa

‘To ya za ayi, ai dole a kaishi tunda idan na barshi a gida uwarsa ba zata bari a yi masa abun da zai bata masa rai ba.’

‘Amma fa babu uwar da zata so ace danta yana shaye-shaye, ita din ma na san idan kayi mata bayani zata gane kuma zata so a rabashi da mugun abu. Ka dai yi mata bayanin tunda ko babu komai yana bukatar addu’arta.’

‘Hmmm!’

Ya mayar da hankalinsa ga kallon TV din yana shan shayinsa.

Bayan ya kurbe shayin ya ajiye kofin, ya dauki kafafunsa ya dora a kan cinyar Aishan tare da gyara zama. Ta muskuta ta fara matsa masa kafafunsa tana yi masa tausa domin ta san idan yayi mata haka abinda yake bukata kenan.
Sai wajen karfe tara da rabi sannan ya tashi yayi sallar isha’i wadda bai samu yayi a masallaci ba saboda gajiya. Bayan ya idar ya dauki mukullansa yayi mata sallama a kan zai je gidan Zahra ya dawo.

Yana fita itama ta tayar da Sallah.
---------

Tana kwance a dakinta ta jiyo shigowarsa gidan, nan da nan ta taso ta fito falon sama don ta tareshi.

Yaran duka sun yi bacci sai Rukayya da Yusra wadanda suke zaune a falon kasa suna jiran suji halin da Yayansu yake ciki kafin su kwanta. Bayan ya amsa sannu da zuwansu ya nufi saman.


Suka biyoshi a baya Rukayya tana fadin

‘Abba kwantar da Yayan aka yi?’

Yace

‘Eh, sai zuwa gobe zasu sallameshi watakila.’


Yusra tace

‘Abba wai me ya sameshi?’

Baya son ya amsa wanna tambayar don yana ganin bai dace ya ce musu dan uwansa shaye-shaye yayi ba. Ya kada kai yace

‘Zuwa yayi gidansu abokinsa suka sha lemo wanda yayi expiring ba tare da sun sani ba shine suka sami food poisoning shi da abokansa biyu.’

Yana cikin bayanin suka shiga falon saman don haka Mommy taji lokacin da yake maganar food poisoning, sai da tayi ajiyar zuciya saboda yanda ta dan sami nutsuwa; to da me yasa bai yi mata bayani ba ya barta cikin damuwa?

Suna karasa shiga cikin falon ya cewa su Rukayyan

‘To tunda an ji inda Yaya yake sai aje a kwanta ko?’

Suka yi masa sai da safe itama Mommy din suka yi mata sai da safe suka shige dakinsu na na saman domin kwanciya bacci.

Suna shigewa ta mike ta bi bayan Abban wanda ya nufi dakinsa tana yi masa sannu da zuwa. Bata sani

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login