Showing 3001 words to 6000 words out of 166068 words
‘Principal?’
Ta tambayi kanta.
Ta dan saita fuskarta daga murtukewar da tayi, ta nufi motar tana tafiya a hankali tana tunani kala-kala; Allah ya sa dai ba wata matsala aka samu a wajen aikin ba da principal zai taso da kansa har gidansu.
Tana tsayawa a kusa da motar ya bude kofar motar ya fito yana ta faman murmushi kamar wanda yaga wata sabuwar amarya, dariya murmushin nasa ya bata amma sai ta waske da murmushi tana fadin
‘Yallabai sannu da zuwa. Kai da kanka? Ai da kirawo nima kayi yallabai da ba sai ka taso ba.’
Ya kara fadada murmushinsa
‘Haba Malama Aisha, ai zancen mai mahimmancine shi yasa gara na taso dai na zo.’
Suka gaisa tana ta mamakin wannan zance da ya kawo shi. Suka yi shiru tana sauraronsa, yayi dan gyaran murya yace
‘Um ai gara mu sami wajen zama ko? Ko nan cikin motar ma sai mu zauna kya fi fahimtar abinda na zo da shi.’
‘Uhm, hakane. Shigo daga ciki sai mu zauna a nan.’
Ta wuce gaba ya bita a baya suka shiga cikin gida; suna shigowa akwai gareji wajen ajiye mota daya wanda motar mahaifinsu ake ajiyewa a da amma tunda ya rasu sai wajen ya zama babu motar. Ta zaro kujerun roba guda biyu daga cikin kujerun da suke ajiye a garejin ta gyara musu zama ta nuna masa daya tace
‘Bismillah.’
Ya zauna itama ta zauna a dayar. Suka sake yin shiru na dan lokaci, principal yayi gyaran murya
‘Uhmm! Wato Malama Aisha na san dai kin yi mamakin ganina to amma kamar yanda na gaya miki maganar mai mahimmanci ce sosai.’
Ya dan numfasa sannan ya cigaba da yaji bata ce komai ba.
‘Wato ina so ne ki bani dama na shiga cikin manemanki, tunda shi aure nufi ne na Allah. Kuma na san dai duk wani bayani da zaki so ki ji a kaina kin riga kin san shi, sai dai ina fatan ki yiwa zancen nawa kyakkyawar fahimta.’
Tuni murmushin fuskarta ya gushe, sai dai bata daure fuskar sosai ba. Ta kalleshi suka hada ido ta kawar da nata idon yayinda shi kuma yake ta kara fadada murmushin da yake fuskarsa. Ta gyara zama kadan tayi gyaran murya
‘Hmmm! Uhhm! Ban ki zancenka ba, amma dai ina bukatar karin lokaci don a yanzu bana ma jin sha’awar sake wani auren. Don haka ina ga mu bar wannan maganar kawai yallabai.’
‘Wannan babu wata damuwa, ni dinma ba sauri nake ba. Tunda dai kin san da zamana babu wata damuwa Allah ya sa dai ni din ne mai rabo, kuma Allah ya ji kan babansu Abdul din.’
Ta ji mamaki da ya san sunan yaranta ko da yake ta san dan sa ido ne na gaske.
‘Amin.’
Ta amsa a gajarce. Ta mike tsaye ta koma ta tsaya a bayan kujerar da ta tashi tana wasa da kujerar tana fadin
‘Bari na shiga gida don dama kokarin dora abinci nake aka kirawoni.’
Shima ya mike.
‘Allah sarki, to ai babu damuwa. Akwai ‘yar tsaraba da na zowa da su Abdul ita a mota bari na dauko sai ki shigar musu da ita.’
Kafin ta bashi amsa ya juya ya nufi gate. Tana nan tsaye ya shigo da leda a hannunsa ya mika mata.
‘Yar alewa ce ta yara, kya shafa min kansu tunda naga kamar kina sauri balle nace ki kirawosu mu gaisa.’
Ta karba tana murmushi
‘Ai da yake ma basa nan, suna gidan kanwata amma in sha Allah da sun dawo zan basu. An gode Allah ya saka da alkhairi.’
Sukayi sallama ya fice ita kuma ta nufi cikin gida tana mamaki da takaici a lokaci guda. Gaba daya ma dariya abun yake bata; duk da dai principal mutumin kirkine amma gaskiya ko zata yi aure ba zata aureshi ba balle ma da yake gaba daya auren ma yanzu baya gabanta. Bayan Mustafa ba taga wani namiji a duniya da zata iya sallamawa zuciyarta da jikinta gaba daya ba, ba zata iya ba gara tayi zamanta ta kula da yaranta.
Tana shiga gidan ta wuce daki ta sami Hajiya a zaune a gefen gado, ta karasa ta zauna tare da ajiye ledar a gabanta tana dariya.
Hajiya ta dubeta tana murmushi
‘Ikon Allah! Har kun daidaita kenan da bazawarin kenan?’
Ta kara tsananta dariyarta tana fadin
‘Hajiya, wai bazawari!’
Ta bita da harara
‘Bana son shakiyanci fa.’
‘Hajiya principal dinmu ne fa na makarantar da nake koyarwa, wai ni zai zo yace yana so.’
Hajiya ta dan bata rai
‘Ikon Allah! To bai kai ba kenan ko me?’
‘A’a Hajiya, nifa ban ce komai ba. Kawai dai ba zan aureshi ba kuma na gaya masa don bana son ma na bata masa lokaci. Makarantar tasa ma na san zuwa sati mai zuwa transfer dina zata fito don tun da na koma na nema a dawo dani nan Sabontiti don tafi kusa. Yaje dai yaji da ‘yar matarsa nima naji da kaina.’
Ta karasa tana dariya.
Hajiya tace
‘Amma dai kin san ba zamu zuba miki ido haka babu aure ba ko? Idan ma so kike kice ba zaki sake aure ba to ki bari, ba ki kai shekarun da za a zuba miki ido babu aure ba sai dai idan Allah bai fito da mijin ba.’
Ta sunkuyar da kai tana wasa da ledar da ta shigo da ita. Hajiya ta gyara zama ta dafa hannunta
‘Hakuri zakiyi kinji Aisha, ki fawwalawa Allah lamarinki shi ya hadaki da Mustafa kuma shi zai hadaki da wanda ya fi shi cikin bayinsa nagari. Ki cire komai daga ranki ki sawa ranki idan Allah ya kawo miji zakiyi aure kin ji ko?’
‘Um.’
‘Yauwa. Allah ya kara miki hakuri.’
Ta amsa sannan ta yiwa Hajiya bayanin alewar ta tashi ta fice ta nufi dakinta.
Tana shiga ta turo kofar ta fada kan gado, hawayen da ta tare ya kwace; ba zata iya auren wani mutum ba bayan Mustafa, ita din tashi ce shi kadai in sha Allah. Duk ma rigimar da za ayi sai dai ayi amma babu wanda zata aura a duniya, sai dai su gaji su barta.
……..
Tunda aka canza mata makaranta ta toshe duk wata hanyar da ta san principal zai sameta, haka ya gaji da zuwa gidansu bata fita ya hakura.
Ta kula da yanda Hajiya take matukar so tayi aure, don haka duk wani wanda ya nuna yana so ta da wuri take dakatar da shi kafin ma Hajiya ta ji zancen. A haka har aka shekara uku da rasuwar Mustafa, lokacin Abdallah yana da shekaru bakwai Farha tana da shekaru biyar.
UWAR SADDIKU
Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)
3
Ranar asabar ce yau, don haka gidan Yaya Zainab suka wuni ita da su Abdallah, sai da sukayi sallar la’asar suka fito suka kamo hanya. Suna karyo kwanar gida ta hango motar Yaya Abubakar, ta san yana gidan.
A dakin Hajiya suka sameshi yana zaune a kan dadduma Hajiya tana zaune a gefen gado suna hira. Bayan sun gaisheshi su Abdallah suka fito falo da gudu suka barsu, itama Aisha ta mike zata fita ta koma dakinta, Hajiya ta dakatar da ita
‘Dawo ki zauna ai maganarkice dama ta kawo Yayan naki, duk da na san babu wata matsala.’
Ta koma ta zauna a gefen gado kusa da Hajiya cikin sanyin jiki don ko ba a gaya mata ba ta san ba zai wuce maganar aure wadda kwana biyu da taga babu wanda yayi zancen ta zata an hakura.
Yaya Abubakar yayi gyaran murya yace
‘Ai kin san Musbahu abokina ko?’
Ta daga kai alamar ‘e’.
‘Yauwa to shine yayi min magana a kan yana so ya zo neman aurenki, idan kin amince.’
Hajiya tace
‘Ai ba za a sami matsala ba ma, mutumin da ba bako bane a gidan nan.’
Ta sunkuyar da kai don bata san me zata ce musu ba, kamar ma dai sun gama yin na’am da maganar Musbahun.
Yaya Abubakar yace
‘Baki ce komai ba.’
Ta danne damuwar da take ciki tayi murmushi tace
‘To Yaya sai ya zo din, Allah ya tabbatar mana da alkhairi.’
‘Amin ya Allah. Ai in sha Allah ba zaku sami matsala ba.’
Ta fice daga dakin ta barsu suna tattaunawa.
Tana shiga daki ta jefa jakarta da hijabinta kan gado, ta dora hannu a ka; so take ta rusa ihu amma ta san dole sai an jiyo ta. Ta karasa gaban mudubi ta tsaya tana kallon fuskarta tana fitar da kwalla; kamar dai kowa ya manta da Mustafa ita kadai ce bata manta da shi ba. Tana aikinta tana kula da kanta kuma yara iyayensu suna yi musu komai amma an dameta da wani aure.
‘Musbahu.’
Ta fada a fili tana jijjiga kai, ta juyo daga mudubin ta zauna a gefen gado ta dafe goshinta da hannuta.
Ya za ayi ta auri wani Musbahu, ta san shi sosai tunda abokin Yayan ne tun suna yara kuma dama can ita Allah bai hada jininta da shi ba tana dai girmamashi saboda abokin Yaya ne. Ta san matarsa daya da ‘yayansa, kuma ta san shi din dan kasuwa ne don haka take ganin idan ta aureshi zata rasa damammaki da yawa kamar aiki da takeyi da sauransu.
Ta share kwallar ta mike ta shige bandaki.
Haka ta karasa wunin nan a daki ita kadai, Hajiya tana kula da yanda yanayinta ya canza saboda anyi maganar aure amma tayi burus da ita, don babu yanda za ayi a kyaleta babu aure.
……..
Suna zaune a falo bayan sallar isha’i ta jiyo karar wayarta daga daki, kafin ta motsa Farha ta zura da gudu ta dauko wayar. Bakuwar lambar ce don haka babu suna, tayi sauri ta amsa kiran ta kara wayar a kunnenta kafin ta tsinke.
Tunda yayi sallama ta gane muryarsa, ta mike ta koma dakinta. Kafin yace wani abu saida ya gabatar mata da kansa
‘Sunana Musbahu Ahmad Tudunwada.’
Ta dan yi yake ta juya kwayar idonta tace
‘Hm, ai na gane.’
Suka gaisa suka dan taba hira yana tambayarta yaranta. Daga baya ya sanar da ita gobe zai zo bayan sallar isha’i, sukayi sallama suka ajiye wayar.
Ta janyo kujerar gaban mudubi ta zauna tare da ajiya wayar a kan mudubin, ta zuba tagumi; gaskiya bata son mutumin nan, ba zata iya aurensa ba don kwata-kwata baya cikin irin mazan da take jin zata iya rayuwa da su. Gashi taga Yaya da Hajiya duk sunyi na’am da shi, ta san yanzu tana yin magana Hajiya zata ce bata son aure.
Ta daga hannu tana addu’a
‘Allah ka kawo min mafita.’
Ana yin sallar isha’i kuwa sai ga Musbahu, ba yaro ya turo ba da kansa ya shiga bayan ya buga kofa an bude. Har falo ya shiga ya gaida Hajiya, tayi ta sa masa albarka tana fatan Allah ya tabbatar da alkhairi. Bayan sun gama gaisawa ya koma gareji don jiran Aisha wadda Hajiya tace masa yanzu za a turo ta.
Yana ficewa itama ta fito daga daki ta kama hanyar fita daga falon, sauri takeyi don kada Hajiya tace wani abu don a halin yanzu haushin yanda Hajiyan ta dinga wage masa baki take tana faman sa albarka kamar wadda yayiwa alfarma. Tana daf da isa bakin kofa Hajiya tace
‘Haba Aisha, ai ko ruwa kya dauka ki bawa bakon naki ko, tunda dai bakonka annabinka.’
Ba tare da ta juyo ba ta bata amsa
‘Hajiya zan dawo na dauka.’
Ta fice da sauri kafin Hajiyan tace wani abu.
Haka ta daure zuciyarta suka dan taba hira babu yabo babu fallasa, sai dai zuciyar Aisha a cunkushe take bata jin zata iya bashi waje a cikinta. Haka dai har ya gaji da surutu yayi mata sallama ya tafi.
Daga wannan lokacin ya zama duk juma’a sai Musbahu ya zo, duk da ya fuskanci bata saki jiki dashi ba sai dai yana ganin kamar idan ya bata lokaci zata dawo ta saki jiki.
Yanda Hajiya take kara sakankancewa da maganar Musbahu yasa ta kasa gaya mata bata sonshi. Tayi kokarin gayawa Yaya Abubakar shima ta ga kamar ba zai fahimceta ba, don haka ta hakura. Ta dai yiwa kanta alkawarin babu yanda za ayi ta aureshi.
___
Tunda mahaifinsu Aisha ya rasu duk ranar Juma’a sai Baffa Aminu ya zo gidan, shi ya zama kamar ubansu. Yau din ma ana saukowa daga masallaci ya wuto gidan danuwansa. Nan ya zauna a falon Hajiya, Aisha ta kawo masa abinci ya sa su Abdallah a gaba suka ci tare. Sai da aka kusa la’asar ya fara shirin tafiya. Ya dubi Hajiya wadda take zaune a kujerar zaman mutum uku yace
‘Ina Shatun ne, kirawota. Gara muyi zancen nan a gabanta mu ji yanda za ayi.’
Ta dubi su Abdallah tace
‘Ku je ku cewa Mamanku tazo inji Baffa, sai ku zauna a can kuyi game a tab ko.’
Suka tashi da gudu suka tafi dakin Aishan. Basu dade da shiga dakin ba ta fito, ta zauna a kan kafet daga gefen Hajiya tace
‘Baffa gani.’
Yayi gyaran murya yace
‘Yauwa Shatu, da magana na zo. Akwai wani mutum; ni kaina ban san wa ya nuna masa ni ba amma dai ya ce sunansa Yusuf Muhammad Bala, kuma darakta ne shi a ma’aikatar ilimi ta jiha. Yana so na bashi izini ya zo neman aurenki. To kwanaki na san Yayanki yace min akwai abokinsa, sai dai ban san ina zancen ya kwana ba don haka nace ya bari na zo muyi magana da ke da mahaifiyarku tukunna.’
Ya dubi Hajiya yace
‘Ko ba haka ba?’
Ta gyara zama
‘Gaskiya ne Baffa, wancan din ne dai har yanzu yake zuwa kuma a yanda yake nunawa yayannasu shi a shirye yake itace bata bashi dama ba.’
Ya dubi Aisha
‘Shatu hakane? Ko bai yi miki bane abokin Yayan?’
Kafin ta bada amsa Hajiya ta tari numfashinsu
‘Babu wani yi mata da bai yi ba fa, ta dai sakawa ranta ba zata yi aure ba tunda Allah ya kashe uban ‘yayanta.’
Baffa ya dubeta yace
‘Subhanallah! Haba Shatu, rayuwar ai sai hakuri kinji, duk yanda Allah yayi da bawa kuma dai-dai ne. Da kuruciyarki baki kai ki zauna babu aure ba tunda dai akwai maneman, kiyi hakuri in sha Allah zaki dace kin ji Shatu. Kada ma na sake ji kince ba zakiyi aure ba kin ji ko?’
Ta daga kai alamar ‘to’
Ya dubi Hajiya yace
‘Ai al’amuran sai hakuri Hajiya, kin san rabuwa da masoyi sai an yi jinyar zuciya amma in sha Allah za a dace.’
Sukayi shiru na dan lokaci, Baffa ya dubi Hajiya yace
‘To yanzu wannan din a dakatar dashi kenan koko shima a bashi dama yazo tunda wancan din ma babu wata tsayayyiyar magana?’
‘To ai gata nan sai ta bada amsa.’
Ta fada tana nuna Aishan, don haka Baffa ya mayar da hankalinsa kanta yace
‘Shatu ke nake sauraro, wannan din yazo ko kuwa kun daidaita da abokin Yayan?’
Ta sake sunkuyar da kai tana fakon idon Hajiya wadda ta dauke kai
‘Baffa gara dai wannan din yazo.’
Hajiya ta bita da kallo mai cike da tambayoyi yayinda shi kuma Baffa yace
‘To babu laifi in sha Allah. Ki kwantar da hankalinki ki duba a hankali; kin riga kinyi aure kin san menene rayuwar aure don haka ba zamu yi miki auren dole ba. Idan ya zo wannan din idan baku daidaita ba shima kada kiji komai sai a cigaba da addu’a.’
Ta daga kai cikin gamsuwa da bayanin Baffa.
Yayi musu sallama ya fice.
Aisha ta mike zata bar wajen Hajiya ta dakatar da ita
‘Zo nan.’
Ta dawo ta zauna a inda ta tashi ta sunkuyar da kai, Hajiya ta harareta tace
‘Shi Musbahun me yayi miki da kuka kasa daidaitawa?’
Ta yi shiru na dan lokaci sannan ta bada amsa
‘Hajiya babu abinda yayi min, kawai dai bana sonshi ne.’
Hajiya ta bude baki tana mamaki, kafin tace wani abu Aishan ta cigaba
‘Kuma kinga daga maganganusa yana nuna min shi zai fi so na daina aiki sannan kuma gida daya zamu zauna da matarsa, gaskiya ba zan ji dadin hakan ba shi yasa naga gara mu hakura kada a bata goma daya bata gyaru ba.’
‘Ai shikenan, Allah ya sa hakane ya fi alkhairi. Bari Yayan naki yazo sai a dakatar da shi ya daina zuwa yana batawa kansa lokaci.’
Ta tashi ta koma dakinta.
Hajiya ta bi bayanta da kallo tana mamaki yanda za ace namiji kamar Musbahu wai ba a sonshi saboda dai fitna irin ta Aisha.
Tana shiga dakin ta koro su Abdallah wajen Hajiya ta fada kan gado ta kwanta ranta a bace; bata son aure amma ta rasa dalilin da yasa aure yake sonta. Ta fuskanci lallai idan batayi da gaske ba za su fara samun matsala da Hajiya don babu wanda ya kai Hajiya son ganin tayi aure, yanzu kuma ga Baffa. Wannan mutumin ma da Baffan yace zai zo bata jin zasu daidaita, za dai ta saurareshi ne kawai saboda kada ace taki kula mutane; amma gaskiya yanzu aure baya gabanta.
____
Ranar asabar da yamma sai ga kira daga Alhaji Yusuf M. B. Haka ta shirya ta fita ba don ta so ba suka zauna a gareji.
Hirar tasu babu yabo babu fallasa; ya gabatar mata da kansa, kamar yanda Baffa ya gaya mata shima ya tabbatar mata cewa shi ma’aikacin gwamnatin jiha ne kuma yana da mata daya da yara biyar; daya namiji, hudu mata.
Duk da bai wani burgeta sosai ba amma dai ta san akwai yiwuwar su daidaita don kamar shi din yana da saukin hali. Haka suka taba hira kafin suyi sallama ta koma gida.
……..
A hankali Aisha ta fara sakewa da Alhaji Yusuf M B, ba wani tsananin so shi take ba kuma zata fi so ace an barta da auren nan amma dai ta san a yanzu idan an tashi zata iya aurensa. Sun gama maganar aiki ya gaya mata bashi da matsala da aikinta, uwargidansa ma iya secondary school tayi