Showing 33001 words to 36000 words out of 166068 words
yayi mata fada amma ya rasa me ya hanashi.
Cikin sanyin murya ta shafe kwalla daga idonta tace
‘Kayi hakuri idan rabon da nayi bai yi maka ba, ka kwashi naman gashi can a falo ka kai mata ta raba in ya so ta aiko mana da kason mu.’
Ta sake share hawaye tana shirin kwantawa, yace
‘Wannan duk ba abun kuka bane, shikenan a barshi haka. Allah ya maimaita mana. Ni na tafi sai da safe.’
Kafin ta amsa ya tashi ya fice daga dakin, ta bi bayansa da kallo tana mamaki don ta zata fada zai yi kuma sai taga ya fice. Tayi murmushi da ta tuno da aikin da Hajja tayi mata; tabbas aikin ne ya fara ci da ta san baran-baran zasuyi don ba zata bashi naman ba.
Dama tana sane tace a nan za su soya naman don kawai Aishan tayi mata aiki ne don bata isa taci kamar rabonta ba.
UWAR SADDIKU
Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)
13
Tunda ya shigo gidan ta gane bashi da nutsuwa, bai yi mata maganar naman ba don haka itama sai kawai ta kyaleshi. A nan kan dining table a nan kwanukan da aka kawo naman suka kwana, har ta saka musu abincin safe suna nan bata dauke ba.
Kwai kawai ta soya suka hada da shayi da burodi suke karyawa, suna yi suna hirarsu cikin walwala. Ya dubi kwanon yace
‘Naman nan inaga in na fita zan bawa Malam Sule danyen nama ya kawo miki, sai ki soya ki barshi a nan kya yi amfani da shi tunda ko babu komai naman sallah ai ka bawa baki.’
Da mamaki ta dubeshi
‘Nama kuma, haba dai! Me yayi zafi?’
‘To duk sun rabe wancan naman, akwai dai danyen nama a babbar freezer a can idan zaki yi miya ki dinga turawa a karbo miki. Wanda za a kawo din kuma sai ki soya.’
‘Hakan ma yayi, amma ba sai an kawo wani danyen nama ba. Kasan na gaya maka nayi layya a gidan Umma ko? To wallahi ta ajiye min nama danye da soyayye, don nice ma nace su barshi a can idan naje na taho da shi da tuni an kawo shi.’
‘Zaki dai kwashewa Umma nama, bayan ga naki a nan.’
‘Ba haka bane, ka san fa raguna hudu aka yankawa Umma naman ma ai ya yi mata yawa; ga na Yaya Abubakar, ga nawa ga kuma na mijin Zahida sannan daga gidan Baffa ma cinyar sa aka kawo.’
Haka dai ya hakura da batun naman.
Sai bayan azahar ta shirya sukaje tare ya ajiyeta a gidan Umman, nan yara suka hadu akayi ta murna. Tayi matukar kewarsu don haka ta sanar da Umma duk ranar Juma’a zata dinga daukarsu daga makaranta su dinga yin weekend a wajenta, in ya so ranar Lahadi da yamma sai ta dawo da su.
_
Kamar yanda ta daukarwa kanta alkawarin ana sallacewa taje aka cire mata abun family planning din da ta saka, don haka ko al’ada batayi ba bayan an cire ta sami ciki. Shi kanshi Abban Sadik din bata sanar da shi da cikin ba ta bari sai ya kai kamar wata hudu; saboda bata so ta gaya masa ya gayawa Aisha kada ta cutar mata da ciki.
Duk wata tambaya da zata yiwa Rukayya a kan alamun ciki a tattare da Aishan Rukayyan ta tabbatar mata ba haka bane. Sai dai bata yarda da hakan ba; gani takeyi kamar Rukayyan ce bata gane ba. Don haka har saida cikin nan yayi wata uku sannan ta sanar da Abban Sadik wanda daman ya riga ya gane kyaleta kawai yayi.
Tunda ta san ta sanar da shi cikin nan kuma bata ji ya ce Aisha ma tana da ciki ba sai ta tsiri fitna; kullum akwai abinda zatace ya sa Aishan ta dafa mata daga karshe kuma idan an dafa bata ci sai ta san abinda tace bai yi mata ba. Da kanshi ya gane hakan ya daina biye mata.
Namiji take so ta haifa don haka sosai ta dage da addu’a Allah ya sa namiji ne a cikinta, sai da cikin ya kai wata biyar sannan taje aka yi mata hoto wato scanning inda aka tabbatar mata namijin ne.
--------
Kwanci tashi cikin Zahra har ya kai wata bakwai, ya riga ya fito sosai gashi da alama yaron da yake cikin nata yana da nauyi sosai. Dole yasa take hakura da kusantar Abban Sadik kamar yanda take so, ya zama sau daya a mafi yawancin dare wasu lokutan ma kuma idan yaga yanayinta haka yake lallabata suyi bacci ba ayi komai ba.
Babu abinda yake bata mata rai a rayuwarta kamar ta tuna cewa Yusuf yana da wata matar da zai iya biyan wannan bukatar da ita. Ta fiso ace ita kadai Yusuf zai iya kusanta, idan kuma ta kama dole sai an hada da wata to ta zama itace a sama.
Yanzu da bata iya yi masa yanda take so tabbas ta san ranar kwanan Zahra kwana sukeyi suna faranta ran juna, watakila ma shi yasa a mafi yawancin kwanta yake lallabata suyi ta bacci kawai; duk da tayi masa bayani sau babu iyaka cewa zata iya don babu inda yake mata ciwo amma ya ki ya saurareta.
……..
Ita da Jummai ne kawai a gidan saboda yara duk sun tafi makaranta, maigidan kuma daman ba a wajenta yake ba. Jummai tana kasa tana ayyukanta yayinda ita kuma take zaune a falon sama tana kallon TV.
Jummai ce ta kwankwasa mata kofa ta sanar da ita zuwan Hajiya Amina, nan da nan ta bayar da umarni ta hawo sama. A nan fridge din saman ta samar mata ruwa da lemo suka zauna sun hirarrakinsu.
‘Kinyi nauyi kawata, kin rike wuta sosai fa.’
Amina ta fada tana dariya.
Itama dariyar tayi sannan ta bada amsa
‘To ke kuwa ya za ayi a zo gidana kuma a fini iyawa? Ai ba zai ma yiwu ba. Kin san cikin ma da na dauka tana da shi ashe babu komai in gaya miki.’
‘Ke kawata?’
‘Allah kuwa, kuma kin san nayi scanning an tabbatar min namiji ne a ciki na.’
Ta zaro ido tana murmushi
‘Kai amma na miki murna kawata, finally. Ina ma biyu ne maza.’
‘Kada ki damu dayan ma yana tafe in sha Allah. Yanzu kawai damuwata na san a ranar kwananta kashe dare suke suna harka tunda in ya zo nan sai yayi ta wani faman nuna min tausayi na yake ji wallahi duk jarabata haka nake kyale mutumin nan saboda takaici. Ko da yake na san dama haka yake idan ina da ciki da ya fara girma yake rage wannan bukatar, to amma yanzu kin ga ai ba kamar da ba da nake ni kadai.’
Amina ta harareta tana fadin
‘Kai kawata, kina faman motsi da kyar ki dinga tausayin kanki mana. Ki barshi kawai wallahi damarsu ce, amma da kin haihu ki nemi Hajja ta hadaki da kyau sai ki koma aiki.’
Haka suka cigaba da hirarrakinsu har wajen azahar sannan Aminan tayi mata sallama ta tafi.
Ta kula Amina ba zata taimaka mata wajen karkato Abban Sadik ya rage kusantar Aisha ba don haka ta barta da zancen, amma bata fasa tunanin mafita ba don tayi lissafi ta ga daga yanzu zuwa tayi arba’in akwai wajen wata biyar kenan da zai je yayi ta kusantar Aisha tana nan tana kallo.
Gashi ba gidansu daya ba balle ta gane me yake faruwa idan ya shiga dakin Aishan. ‘Yan kwankin nan idan yayi mata sallama ya tafi haka take kasa bacci saboda takaici. Da haka ta yanke shawarar zata nemi Hajja ko da akwai abinda zata iya bata tunda dai ta san tana da abubuwan da idan aka sakawa mutum a abinci za a tayar masa da sha’awa don haka ta san na kashe sha’awar ma ba zai gagara ba.
Bayan ta gama yiwa Hajja bayanin duk wata damuwarta tace
‘Hajiya kenan, Uwar Saddiku baki da wasa. Kada ki damu akwai abinda zan taho miki da shi kawai ki tanadi dubu goma da kuma kudin montana shikenan.’
Sukayi sallama da alkawarin da yamma zata zo.
Yamma tana yi kuwa sai ga Hajja. Nan suka zauna a falonta, bayan sun gaisa tace
‘Hajja, kin san me nake so? Wallahi so nake idan kina da wani abu wanda kika san baya cutarwa amma dai ya zama ko da ya je wajen matarsa ba zai iya komai ba, a kalla zuwa lokacin da zan haihu na dawo normal sai mu cigaba da karawa.’
Tayi dariya tace
‘Uwar Sadiku kenan, kin san kan tsiya. To akwai abinda zan baki, shayi kawai zaki dafa dashi ko zobo idan dai ya sha babu abinda zai iya komai kokarinta sai bayan akalla awa goma Sha biyu. Ke wasu ma har awa ashirin da hudu. Kedai aikin da zakiyi kawai shine ki san yanda zakiyi duk ranar kwanta ya sha wannan hadin musamman bayan magriba.’
Ta karbi kullin da Hajja ta miko mata tana dariya tace
‘Yauwa ta wajena, bashi dai da illa ko?’
‘Babu wata illa, da zarar ya dauki lokaci zai fita daga jikinsa ya cigaba da harkarsa normal.’
Nan suka gama magana ta kawo kudi ta sallameta.
Cikin walwala ta karasa wunin ranar; ko babu komai ta san abinda yake hanata bacci ya kau don haka yau akwai bacci harda minshari.
…….
Wajen karfe tara saura ta ji shigowarsa, nan da nan ta kintsa.
Yaran su kadai ya samu a falon kasa don haka bayan sun yi masa sannu da zuwa ya basu ledojin da suke hannunsa wadanda kazar Yahuza suya ce a ciki.
Nana ce ta dauke ledojin yayinda Abban yace
‘A kaiwa Mommy ta dauki nata tukunna, kafin kurar gidan taga menene a ledar.’
Cikin shagwaba Rukayya wadda ta tabbatar da ita yake tace
‘Abbaaa!’
‘Na’am, ni ai ban kama suna ba ko?’
Sukayi dariya gaba daya suka nufi saman, shima Abban ya bisu a baya.
Tana zaune a falonsa a kan kafet ta mike kafafun ta dorasu a kan filo saboda yanda suke dan kumbura. Daga gefen damanta jug ne cike da zobo yana gumi saboda sanyi yayinda take rike da karamin kofi mai dauke da zobon da alamu sha takeyi.
Suna shiga suka zube a gabanta suna yi mata bayanin naman da Abba ya siyo yayinda Abban ya wuce ya zauna a kan kujerar bayanta. Ta bude ledojin ta dauki nata, ta mikawa Yusra sauran tana fadin
‘Gashi nan kowa ya dau daya sai a sakawa Ummi nata a fridge tunda tayi bacci.’
Nan da nan suka kwasa sukayi kasa.
Ta sake yiwa Abban sannu da zuwa, bayan ya amsa ya dubi kofin hannunta yace
‘Yau kuma zobo kike sha ke kadai abunki?’
Tayi ‘yar dariya tace
‘Zobo kam ai na mu duka ne, suma yaran duk sun sha da rana. Bari na dauko kofi na difara maka don ma kada na cika maka ciki ka kasa cin abincin amarya.’
Ta kurbe ragowar wanda yake kofin hannunta tana kokarin mikewa, ya dafe kafadarta yana fadin
‘Ba sai kin dauko wani ba, zuba min a wannan tunda kin shanye. Kadan zan sha na wuce sai ki cigaba da jin dadin ki.’
Ta zuba masa zobon a kofin da ta shanye, ya dauka yana zuka a hankali suna hira.
Sai da shanye kofi guda ya kara rabi sannan yayi mata sallama ya fice.
Tabi bayansa da kallo tana murmushin mugunta; ta san duk daren da ya siyo kaji irin wanna to hirar dare yake so ayi, yanda ya sha zobon nan kuwa ta san wannan hirar ta yau babu abinda zai iya.
-------
Tun da yamma ya sanar da ita kada tayi abincin dare don zai siyo abinci. Shayi kawai ta dafa mai kayan kamshi suka baje a falo suka gama ciye-ciyensu suna hirarrakinsu.
Sai da suka gama komai suka kwanta a nan labarin ya canza, duk yanda ya kai ga sha’awarta da son ya kusanceta abun bai yiwu ba. Yayi iya kokarinsa itama tana taimaka masa amma abu yaki, daga karshe itace ta koma tana bashi baki saboda yanda ya shiga tsananin damuwa. A tunaninsa bashi da lafiya, amma kuma babu wani rashin jin dadi da yake ji, haka ya kwana cikin damuwa da tashin hankali.
Da asuba bayan ya dawo masallaci ya sake kokarin gwadawa amma shiru, nan ma haka ta dinga nuna masa ita bata damu ba yayi kokari kawai ya je asibiti a duba shi.
Da gari ya waye ya shirya ya fice office da niyyar idan ya rage aiki zai nemi likitanshi ya ji yanda za ayi. Yanayin aiki da kuma kasancewar babu wani abu da yake masa ciwo sai ya manta, sai da yamma bayan ya tashi daga aiki sannan ya tuna. Yana tunanin yanda za ayi da yammannan ya sami likita sai kuma ya tuna kwanan Zahra ne yau ita kuma dama ba cikakkiyar lafiyace da ita ba, don haka ko bai kulata ba ma babu damuwa.
Haka ya koma gidan.
Kamar kullum bayan ya gama hidimarsa ya kwanta, tana lalubensa yana gocewa saboda baya son abinda ya faru jiya da Aisha ya sake faruwa. Amma kuma a hankali sai yaji kamar zai iya, nan da nan kuwa suka shiga hidima yana jin dadi. Don haka sai yayi tunanin matsalar ta jiya ce kawai abun ya wuce.
Haka yayi kwana biyun nan a wajen Zahra lafiya kalau don haka cikin walwala ya koma wajen Aisha.
Ga mamakinsa duk yanda ya kai ga dagewa tsakaninshi da Aisha sai kallo, haka yayi kwana biyun nan yana mamaki. Ita kuma sai dai ta dinga kwantar masa da hankali tana nuna masa ba komai bane, musamman da yake ya gaya mata zai je yaga likita.
A hankali ya zama kullum idan dai ya shigo yiwa Zahra sallama zai tafi wajen Aisha zai tarar ta ajiye zobo, shayi ko kuma kunun zaki, shi kuma da ta yi masa tayi sai ya sha sannan zai tafi.
………..
Haka rayuwarsu ta cigaba, yaki yaje asibiti musamman da yake yana samun biyan bukata a wajen Zahra. Sai dai yana mamakin yanda akayi ranar da yake wajen Zahra lafiya amma da yazo wajen Aisha sai ya kasa komai.
A cikin tattaunawarsu da Aisha ya sanar da ita idan yaje wajen Zahra baya samun wannan matsalar. A tunaninta asiri ne Zahran tayi amma ta kasa gaya masa, sai dai ta dage da neman maganin karya sihiri.
Musamman ta sami ruwan zamzam take yi addu’ar karya sihiri tana sha tana wanka, shi kuma duk wani ruwa da zai sha a gidan nan sai ta yi masa addua’ar a ciki amma babu wani cigaba. Yanzu ma an kai matsayin da ta daina bari ya jagwalgwala ta, shima kuma ya daina rawar kai a kanta. Sai dai kullum cikin bata hakuri yake yana yi mata alkawarin zai je asibiti a duba shi amma dai ya kasa zuwa, ita kuma bata bashi kwarin gwiwar yaje asibitin ba saboda ta riga ta yarda sihiri ne, don haka dai ta dage da addu’a.
__
Ranar Alhamis Zahra ta tashi da ciwon nakuda sai dai da yake ciwon bai zo mata gaba daya ba ta cigaba da aiyukanta tana yi tana hutawa. Ba kwananta bane amma dai ta riga ta sanar da shi tana nakuda don haka ranar gaba daya a cikin sauraron kiranta yake.
Tun wajen karfe biyar na yamma ya dawo daga aiki, wajen Zahran ya fara shiga bayan ya dubota sai ya koma wajen Aishan tunda yana nan da ta ji wani ciwo sai tayi masa waya.
Sai bayan sallar magriba sannan ta kirawosa, a gurguje ya shirya yayi sallama da Aisha bayan ya sanar da ita idan akwai abinda yaran suke bukata zai ce su karba a wajenta.
Tun wajen karfe bakwai suka shiga asibitin aka shigar da ita labour room, sai wajen karfe taran dare sannan ta haihu.
Dakin da ta haihu ita kadai ce a ciki sai ma’aikatan lafiya da likita, likitan yana tsaye a daidai kanta yayinda matron da kuma nurses uku suke daidai kafafunta suna dubawa suna taimaka mata. Tara da minti biyar tayi yunkuri ta haifi yarinyarta santaleliya, a take matron ta yanke cibiya ta dauki yarinyar ta mikowa likita. Ya karba ya dubi Zahra da take kwance yace
‘Sannu Hajiya.’
Ta amsa tana murmushi.
Ya juyo al’aurar yarinyar ya nuna mata yace
‘Kinga abinda kika haifa, me kika samu?’
Sosai mamaki ya bayyana a fuskarta tace
‘Mace?’
Likita yace
‘Yauwa, gata nan kuma lafiyayyiya Alhamdulillah.’
Nan da nan ma’aikatan lafiya suka shiga kokarin wanke mai jego da abinda ta haifa, daga baya aka fito aka sanarwa Abban.
Bayan likitan ya fito yayi masa duk wani bayani kuma ya sanar da shi zasu riketa ta kwana in ya so zuwa gobe da yamma za a sallameta.
A hanyarsa ta komawa gidan ya dauko kanwarta wadda zata tayata kwana a asibitin suka wuce gidan. Nan da nan ta zabo mata kaya ta hado mata dan abinda zata ci. Babu yanda bai yi da su Yusra su tafi gidan Aisha su kwana ba suka ki, kananunma sun riga sun fara bacci don haka tace zasu iya kwana. Haka ya hakura ya sa Sadik ya rufe musu gidan suka koma asibiti.
Ko da suka koma asibitin saida ya siyo musu duk abubuwan bukata ya kawo kudi ya bata sannan ya kamo hanyar gidan.
Wajen Aisha ya fara shiga inda dama a nan ya kamata ya kwana, yana shiga yayi mata sallama ya sanar da ita zai kawo mata Rukayya sai ya kwana da sauran yara.
Tace
‘Dare yayi wallahi, don Allah ka barta tayi baccinta sai da safe kawai. Idan kuna bukata wani abu kawai ka sanar da ni.’
Sukayi sallama ya fita ta rufe kofa.
……..
Tunda aka canza mata daki aka gyara Baby aka kwantar da ita a kusa da ita take mamaki, tayi scanning an gaya mata namiji zata haifa yanzu kuma ta haifi mace.
Ta dubi Rahma; wadda kanwace a wajenta wato ‘yar kanwar babarsu, mijinta ne ya