Showing 102001 words to 105000 words out of 166068 words

Chapter 35 - UWAR SADIKU COMPLT BY SAKINA YAZID.txt

11 Jul 2024

25399

mata mota kuma ga irin wadda take so; shi kuma a halin yanzu bashi da kudin sayen irin wannan motar.
Gashi a halin yanzu baya iya yi mata musu kuma baya son ganinta a cikin damuwa, wasu lokutan idan tace yayi mata abu har ji yake kamar an kuntata zuciyarsa har sai yayi wannan abun da take so zai ji daidai. Don haka yanzun ma duk inda kudi suke nemowa zai yi kawai ya saya mata mota.
………..

Kayan electronics din da ya siyo lokacin da suka je Dubai da Aisha suna nan anata siyarwa, kokari yakeyi idan aka gama sayarwa ya hada uwar kudin da ribar ya sake komawa ya siyo wasu kayan. Yana jin dadin yanda cinikin yake tafiya domin akwai riba sosai, musamman da yake abokin kasuwancin nasa mai amana ne sosai.
…………

Ba wai dare ne yayi sosai ba amma da yake yanayi ne na sanyi yaran duk sun kwanta har an rufe gidan. Shima Abban yana dakinsa a zaune a gefen gado yana 'yan dube-dubensa a waya yayinda Uwar Saddiku take kasa tana kawar da abubuwan da suke a bude kafin ta je ta kwanta.

Sai da ta gama kintsawa tsaf sannan ta sameshi a dakin. Bayan ya amsa sallamarta ta kwanta a gefensa ta ja bargo ta rufe kafafunta.


Bata dade da kwanciya ba wayarsa tayi kara, ya amsa kiran sannan ya kara a kunnensa.

Daga inda take kwance tana dan jiyo wasu daga cikin abubuwan da ake fada a daya bangaren, bata ganewa amma so take ta gane don haka ta tattaro duk wata nutsuwarta ta kara mikar da kunnuwanta don taji me za a cewa Abban.

Tun da suka fara gaisawa ta gane abokin kasuwancinsu ne Alhaji Abubakar; duk da bata san shi ba dai amma ta saba da jin sunansa kuma ta san Abban yace shine yake masa jagoranci wajen sayar da kayansa da ya siyo daga Dubai.

Bayan sun gaisa Alhaji Abubakar din ya sanar da shi akwai wani Alhaji da yake son kayansa ya turo kudin kaya naira miliyan shida don haka Abban ya duba business account dinsa yayi confirming don mutumin zai turo a debi kayan gobe da safe. Ya kuma sanar da shi akwai wanda yake son kayan kallo da AC complete set guda biyu amma shi so yake idan ya biya yaransu suje su hada masa kayan a gidansa sai ya biya har kudin aiki. Sukayi sallama suka ajiye waya.

A take ya duba account dinsa ya tabbatar da shigar kudin, shi kansa sai da yayi murmushi da yaga kudin. Ya tabbatar ya shiga harkar nan da kafar dama kamar yanda Abubakar din yake gaya masa.

Ya kirawo Abubakar din ya sanar da shi kudin sun shigo don haka zai fito da wuri gobe don suje gidan da ya ajiye kayan a dauka. Sukayi sallama suka ajiye waya.

Ta dan muskuta a inda take tace

‘Kayan dai ashe suna tafiya.’

Cikin murmushi da sanyin jiki yace

‘Alhamdulillah gaskiya babu laifi in Sha Allahu kwanan nan zamu koma Dubai din a kawo wasu kayan.’

Kwanakin nan har fargaba yake idan taji yana da kudi domin idan ta ji haka zata dinga yi masa lissafin abubuwa yana siya har sai ta ga kudin nan sun kare.Yanzun ma wannan maganar da tayi zuciyarsa ta fara bugawa da sauri ya san zata ce wani abu don tabbas ya san sai ta ci kudin nan tunda ta ji su.

Jimawa kadan tace

‘To ni dai gaskiya tunda an sami kudin nan a saya min motata in ya so daga baya ko ma menene sai ayi, kada a bar ni ina ta jira. Ya kamata ace kafin satin nan ya kare motata ta zo tunda dai kudin nan gasu nan sun shigo.’

‘Wannan ai kudin business ne ba da su za a saya miki mota ba, amma in Sha Allahu za ayi kokari.’

Ta tashi daga kwance ta zauna tana harararsa

‘Business din ya fi ni mahimmanci kenan? Ka ce ba kudi kuma yanzu ga kudi in dai anyi niyyar siya min mota ina jiranta next week gaskiya.’

Ta dan shagwabe fuska ta zungureshi da hannu tace

‘Ka ji.’

‘To to in sha Allahu kafin next week din za a siyo motar.’

Ya amsa yana jijjiga kai.

Haka ta kwana tana farin ciki don ta san bai isa ya canza wannan maganar ba yayinda shi kuma ya kwana yana lissafi; anya kuwa Zahra zata barshi ya hada kudin nan ya sake yin business din, yanda take yiwa kudin gibi ya fara yawa.
…………
Tunda sukayi wannan maganar kuma sai ya zama kullum idan zai fita sai ta tuna masa da motarta.

Don haka bayan kwana biyar da yin magana an gama cinikin kayan an diba haka ya dauka a cikin kudin ya sayo mata mota irin ta Aisha sai dai ita tata ruwan gwal ce ba baka ba.

Office aka kai masa motar bayan ya gama biya, daga nan kai tsaye yace a kai mata gidan a bata mukullin; ya hada dan aiken da Malam Ali direba.

Suna fita ya kifa kansa a kan teburin da yake gabansa ya runtse idanuwansa; kwana biyun nan jin kansa yake a cikin wani mawuyacin yanayi amma ya kasa fassara yanayin. Komai ya daina yi masa dadi gashi zuciyarsa tayi kunci kullum yana cikin damuwa amma be san me yasa yake duwar ba, ga kuma yawan fushi da yakeyi na rashin dalili.
A waje daya ne yake jin dadi shine idan yana gidan Yaya Bello, don haka yanzu kusan kullum idan ya tashi daga aiki gidan Yaya Bello yake tafiya yayi zamansa suyita hira da Yaya har sai ya gaji sai ya fito ya koma gida. Yana kama hanyar gidan kuma zuciyarsa zata sake komawa cikin damuwa.
Bayan son sayen motar nan amma idan Zahra tace yayi mata abu wasu lokutan baya ma sanin yayi sai ya gama; motar ma a kan haka ya saya mata. Yana dai fatan Allah ya sa kada ta kawo wata babbar bukatar idan ta gama dokin motar, don baifi wata daya ba da ta saka shi a gaba sai ya bata dubu dari biyar ta kara jari kuma nan ma haka dole ya bayar.

Ita kuwa Zahra ana kai mata mota da ta yi masa waya ya tabbatar mata tata ce ta karbi mukullin mota ta fice, gidan Amina ta fara zuwa suka sha hira sannan daga nan ta wuce gidan Yaya Murja ta nuna mata motar sannan ta dawo gida.

Ta riga ta saba yanzu sai wajen tara na dare Abban yake dawowa gidan, tunda ta bincika ta tabbatar gidan Yaya Bello yake zuwa abun ya daina damunta.


Don haka yau din ma bayan sallar isha’i suka zauna a falon kasa ita da yaran don cin abincin dare, suna ci suna hirarrakinsu wanda duk a kan motar Mommy ne.

Yusra ta dubi Mommy din tace

‘Mommy ni dai don Allah ki sa Abban ya saya min waya, kinga mun kusa fara exam din amma shi yace dole sai mun gama exams. Kawayena duk suna da waya kullum ayi ta daukan hotuna babu ni ana min dariya. Kin ga Fathiyya Sulaiman ma iPhone ce da ita, don Allah nima ki sashi ya saya min iPhone tunda na ga kamar yanzu yana da kudi. Kin ga ma idan muka gama exam din ai an huta.’

Tayi dan murmushi tace

‘Ai nace za a saya miki kafin ki gama exam din kuma iPhone din za a saya, yanzu ki bari mu gani zuwa next week in sha Allah zai saya.’

Ummi tace

‘Mommy da Yaya Rukayya ma a saya mata wayar sai mu dinga yin game tare , ko Yaya Rukayya?’

Sukayi dariya gaba daya, Rukayya tace

‘Ai na san Abban ba zai taba yarda ba ni na ma hakura sai na yi candy din tunda Abba yace idan mutum yayi candy dashi za a je shop din ya zaba. Sai mu tafi tare ko Ummi?’

Suka tafa.

Mommy tace

‘Ai kuwa kin hutar da mu.’

A dai dai nan Saddiku ya shigo, ko sallama bai yi ba yace

‘Mommy na ga wata dalleliya, itace motar tamu?’

Yusra tayi caraf tace

‘Mommy kin ji ikon Allah wai motarsu; wallahi Mommy ki hanashi hawa motarki tun kafin a zo a kuma.’

Mommy ta bata rai tana hararar Yusran

‘Ki fadi alkhairi ko kiyi shiru, hatsarin irin wannan ba zamu sake ganinshi ba har duniya ta nade.’

Cikin jin dadi yace

‘Gaya mata dai Mommy, mota dai sai na hau sai dai dan bakin ciki ya mutu.’

Yusra ta zumbura baki tana harare-harare yayinda Mommy tace masa

‘Sannu sarkin fin karfi, to wannan motar ba ta hawanka bace iyakacin ka da ita kallo. Idan aka kwana biyu dai nayiwa Abban magana ya saya maka taka kaima.’

Ya zaro ido ya matso kusa da ita

‘Allah Mommy, gaskiya amma da kin gama burgeni. Amma don Allah Mommy dalleliya nake so kamar dai takin nan.’

‘Bari mu gani, ka maida hankali kaci jarrabawa kaga sai a ji dadin saya maka mota.’


Kafin ya amsa suka ji shigowar Abban gidan bayan da Malam Sajo ya bude masa gate. Babu wanda ya mike da sunan yaje ya taro Abba sai Rukayya wadda ta mike tana fadin

‘Ga Abba nan.’

Ta fice da sauri.

A take Ummi da Sumayya suka bi bayanta da gudu suna oyoyo.

Jimawa kadan Rukayya ta shigo rike da jakar laptop din Abban da mukullin motarsa ta wuce sama, bata gama hayewa benen ba yashigo yana rike da hannun Ummi yayinda yake dauke da Sumayya.


Bayan ya amsa sannu da zuwansu yace

‘Saboda motata ta tsufa shine aka saka min sabuwar mota a gareji aka koro tawa waje ko?’

Tayi dariya tana mikewa tsaye tace

‘Wallahi mantawa nayi, lokacin da nayi parking din ne da akwai rana shi yasa wai da naga mai wajen baya nan sai na dan fake ta a nan.’

Ya wuce saman yana dariya yayinda ta tashi ta bi bayansa.
……….

Yanda ta kwana tana murna haka shima Saddiku ya kwana cikin farin ciki; motar ta burgeshi sosai ya san yanzu Shima ya wuce raini a wajen abokai. Duk da ta gaya masa ba zai hau mata mota ba amma ya ci alwashin sai dai ita ta hakura ta bar masa motar; kuma kamar yanda ta fada ko da ma ta sa an siya masa mota idan dai bata kai haduwar wanna din ba to sai dai idan ita ta hau waccan shi ya hau tatan.

Kafin ya kwanta bacci sai da ya yiwa abokansa waya ya sanar dasu an saya masa mota gobe ma da ita zai fito.

Ko da gari ya waye da wuri Abban ya fita bayan Malam Ali ya fita da ‘yan makaranta, shi kuwa Saddiku yana ta kaiwa da kawowarsa a falon kasa tare da Sumayya don ya cewa Mommy sai karfe goma zai tafi computer school dinsa.

Sai da ya bari ta shiga wanka sannan ya shiga dakinta ya dauki mukullin motar ya fice daga gidan.

Tana wanka ta ji an bude gate tayi zaton Malam Ali ne ya dawo don haka bata damu ba.


A lissafinta idan ta fito daga wankan ma fita zatayi ta je gidan Suwaiba sannan ta biya sahad tayi sayayya duk don ta kara dana motar; domin yanzu idan zata je unguwa ta daina gayawa Abba sai dai idan babu direba a gidan ta kan gaya masa don ya turo mata direba.

Sai da ta fito daga wankan ta gama shiryawa sannan ta fito daga dakin, tana fitowa ta sauko falon ta sami Sumayya a kicin wajen Jummai, bayan sun gaisa da Jummai tacewa Sumayya

‘Ina Yaya naki?’

‘Ya tafi unguwa.’

Jummai tace

‘Ai ya fice Hajiya.’

‘To nima fitar zanyi, bari na karasa shiryawa.’

Har ta kama kafar benen hawa sama ta dawo ta leka tsakar gida, babu komi a garejin Abba inda ta ajiye motarta. Take ranta ya baci; wato Saddiku sai da ya fitar mata da mota kenan?
A fusace ta dawo cikin gidan ta haye sama, tana shiga dakin ta dauki wayarta ta fara kiran lambar Saddiku. Ta kirawo shi ya fi sau goma amma bai dauka ba, don haka dole ta hakura ta zauna tana ta faman cika tana batsewa. Gashi Malam Ali ma baya nan balle tace masa ya kai ta.

Wuni guda Saddiku bai dawo gidan ba sai bayan magriba ya dawo; hakan ma don Abba ya hanashi kaiwa dare a waje ne ya dawo. Ko da ta taso masa zata yi fada tsayawa yayi yana mata muzurai yace mata jarabawa yayi a makaranta shi yasa bai dawo da wuri ba. Haka tana ji tana gani ta hakura.
__

Sati biyu da sayen motar nan ta Zahra kuma ta saka shi a gaba da maganar ya sayawa Yusra waya. Ko da Saddiku yaji ana maganar wayar Yusra shima sai ya sayar da tashi wayar yace ta fadi. Don haka Mommy ta sa Abba a gaba saida ya sayi waya iPhone guda biyu kowacce kusan dubu dari da saba’in.
__

Kwanci tashi Aisha tana lissafi yau wata shida rabon da Abba ya leka gidanta, duk wata hanya da zata bi don taga tayi magana da shi abun ya ci tura. Duk wanda yake da alaka da ita ko ta waya baya iya samun Abban a waya.

Idan Abba ya tashi biyan kudin hayar gidan Aisha na shekaru biyu yake biya, ita bata ma sanin lokacin da yake biya domin kafin lokacin ya gama wucewa zai turawa Jibrin kudin kawai ya biya.

Shekararsu ta hudu kenan da aure yanzu shekara ta hudun zata kare don haka lokaci yayi na biyan kudin hayar.
Tun ana saura wata biyu shekarar ta kare Jibrin yake neman Abban, idan sun hadu sai yayi ta zullewa yaki saurara maganar. Daga baya kuma sai ma ya kasa samunsa waya, idan kuma yaje nemansa duk abinda zai faru ba zasu hadu ba. Masu gidan kuma duk da sun san Abban amma sun saba ba shi yake biya ba Jibrin ne don haka suke ta faman yiwa Jibrin din tuni.

Sosai ya shiga damuwa domin ya tabbatar karkari su kara wata biyu zasu sa Aisha ta fitar musu daga gida su sa wani, tunda neman kudi suke da gidansu. Shi kuma gashi bashi da kudi balle ya biya kuma ma saboda me zai biya?

Haka yayi ta kokarin ganin Abba amma basu hadu ba gashi yanzu ko ya kirawo Abban wayar bata shiga. Baya son yaje gidan Aishan kuma tunda bai saba zuwa ba a zata wani abu. Sai a hankali ya tuna ya taba kai matarsa wajen Aishan lokacin tana amarya, don haka yana komawa gida ya sameta ya karbi lambar Aishan da niyyar gobe idan ya shiga office sai ya kirawota domin gara ya sanar da ita koda tashi ne ta tashi ba sai an zo an yi mata wani tozarci ba; don ya kula masu gidan sun fara jin haushi.
__

A halin yanzu jarrabawa dalibansu sukeyi don haka malaman da basu da aiki su kan zauna a gida suki zuwa makaranta. Haka itama Aishan tayi, domin tana kai Amira makaranta sai ta dawo gida.

Zaman da take a gida ga damuwar Abba ya manta da ita ta kusan wata bakwai ya fara damunta; don haka ta biya kudi aka koya mata yanda ake yin mayafai na zamani kuma nan take ta sayi injin stoning da sauran kayan aiki ta fara yi.


Yau din ma da taki zuwa aiki zama tayi a gida ta yi wasu mayafai da aka bata aikinsu guda shida.

Tana cikin aikinta wayarta tayi kara. Kafin su gama gaisawa ta gane muryar duk da bata tabbatar ba. Yana yi mata bayanin kansa ta fara tambayarsa matarsa da sauran iyalai. Bayan sun gama gaisawa yace

‘Amarya ya mutumina, yana kusa kuwa?’

‘A’a baya nan ina jin yana office.’

Ya danyi jim yace

‘Aisha wato akwai ‘yar matsala ne.’

Nan yayi mata bayanin halin da ake ciki game da kudin hayar gidan da take ciki.

Bata taba wannan lissafin ba don haka bayanin nashi ya shammaceta. Ta dan yi jim sannan tace

‘Um. Don Allah kace su dan yi hakuri zuwa gobe zan kirawo ka in Sha Allah kafin nan munyi magana da shi.’

Sukayi sallama suka ajiye wayar.

Ta dawo jagwaf ta zauna a kan kujera dining table.


Ita ta manta ma cewa a gidan haya take; gashi yanzu babu yanda zatayi taga Abba sai ta hannun Zahra wadda ta san idan banda tozarci babu abinda zata yi mata.
To kuma ta san idan ta bari tabbas masu gidan zasu zo ne su tasheta; ita kuma tayi alkawarin ba zata bar gidan nan ba har sai wannan tsafin da Zahra tayi ya karye domin ta tabbatar yanda take addu’a da sadaka lokaci kawai ake jira.
Ta tuna bata ma san nawane kudin hayar ba don haka ta dauki waya ta kirawo Jibrin din ta tambaye shi. Ya sanar da ita wancan karon dai dubu dari biyu da hamsin aka biya amma yanzu sun ce dubu dari uku za a biya.

Suka ajiye waya ta cigaba da tunanin mafita.

Yaya Abubakar ya kamata ta gayawa domin zai iya biya mata, sai dai ta san shi yanzu zai ce ta tashi daga gidan don tun da yaji labarin yake so ta koma gidan Hajiya. Sai da Baffa yayi masa magana yace ya bari abi komai a hankali domin shima ya sa ana addu’a, kuma tunda Aishan ta nuna ita zata zauna bai kamata a raba ta da gidan ba har sai komai ya warware. Don haka ta san yanzu idan taje masa da wannan maganar kamar tana tuna masa ne.

Ta muskuta kadan a inda take zaune.

To yanzu ya zata yi; ai duk inda ma kudi suke dole ta nemosu tazo ta biya kudin hayar nan don ba zata bar gidan ba har sai Abba ya dawo hayyacinsa.


Gashi yanzu cefane da kula da gida ya koma kanta duk ita takeyi; lokacin da Abban yana zuwa kuwa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login