Showing 135001 words to 138000 words out of 166068 words

Chapter 46 - UWAR SADIKU COMPLT BY SAKINA YAZID.txt

11 Jul 2024

25416

tafi.


……….


Lokacin da su Zahra suka bar gidan makokin Ummulkhairi ta sanar da ita suna nan zuwa ita da yara, don haka suna shiga gidan ta sa aka fara gyara musu dakin baki na falon kasa. Sai dai suna shiga unguwar Abba ya ajiyesu a gidan Aisha yace su sauka a nan tunda kusa ne sa dinga shiga wajen Zahra da yaran.


Nan da nan Aisha ta shiga hidima da su.


Yana shiga gidan Zahra tana zaune a falon kasa yayinda Jummai take goge dakin. Bayan ya amsa sannu da zuwanta ta ce


'Ina Anti Ummun? Tace min tare zaku taho.’


'Eh tare muka taho suna gidan Aisha na san nan din ma da anjima zaki gansu.’


Bai saurari abinda zata ce ba ya haye saman; ba zai iya sauraron komai ba saboda yanda ya gaji kuma ga damuwa.


Ta kawar dakai tana mamaki; yanzu kenan ba zai ma bari ta sauki bakinsa ba! Ta tashi itama ta haye saman.


Haka aka gama jimamin rabuwa da Hajiya kowa ya koma harkokinsa, mutanen Lagos ma suka gama hutunsu suka koma gida.


—-----


Dole ta saka Zahra tana yin amfani da shawarwarin Yaya Murja tunda ko babu komai ta san sai ta kwantar da kai a wajen Abba sannan zata sami kudin zuwa wajen Malami. Tunda dama da business dinta take samun kudi kuma a halin yanzu babu zancen wani business domin duk ta cinye kudin.


Yanda take ganin walwalar Abban ta san cewa Saddiku yana lafiya tunda ya gaya mata yana zuwa duboshi kuma yana yi masa waya. Shima Abban ya sami natsuwa ne saboda yanda yake ganin cigaba a wajen Saddiku; rehabilitation center din sun bashi rahota a yanzu da Saddiku ya kai wata biyu a hannunsu an samu an raba shi da miyagun kwayoyin; yanzu aikin gyaran dabi'unsa ake yi da kuma karatun islamiyya da ake biya musu. Wannan ya sa Abban ya kara sakewa da Zahran duk da bai sanar da ita inda Saddikun yake ba.


……


Mahaifiyar Amina ta fara samun lafiya sannan kuma a halin yanzu akwai kanwar Aminan wadda take karatu a Sudan ta zo hutu, don haka tana gidan Aminan kuma tana kula da Umman nasu. Don haka suke cigaba da shirye-shiryen zuwa wajen boka; domin Amina ta samo musu sabon boka.


Yau ranar asabar ce kuma da yake ana cikin hutun makaranta kullum yara suna gida, don haka ta gaji da hayaniyarsu tana so ta dan fita. Gidan Amina take son zuwa don ta san a nan ne zata samu a saurareta kuma a bata irin shawarwarin da take so. Ba a gidanta Abban Sadik ya kwana ba don haka sai wajen karfe goma na safe ya shigo gidan. Bayan ya gama abinda zai yi da zai fita ta tambayeshi izinin fita wanda ba tare da wani bata lokaci ba ya bata dama.


Nan da nan ta shirya, ta sallami yaran sannan ta barwa Jummai abincin rana da abincin dare don batayi niyyar dawowa da wuri ba. Ta fito Malam Ali ya ajiyeta, ta sallameshi domin Aminan zata mayar da ita gida idan sun gama.


Sai da ta fara gaisawa da Umman su Aminan ta yi mata ya jiki sannan suka zauna a falo suna gaisawa da Aminan. Basu jima a falon ba suka koma dakin Aminan. Nan suka baje a kan kafet din da yake tsakar daki, Raihana kanwar Aminan ta zo ta kawowa Zahra ruwa da lemon roba suka gaisa sannan ta fice ta ja musu kofa.


Bayan sun dan taba hirarsu ta duniya Zahra tace


'Aminoni ina cikin damuwa wallahi ba zaki gane ba, yanda kika ganni nan daurewa kawai nakeyi amma komai ya tsaya min.’


Ta yi dan gajeren murmushi mai ciwo, tace


'Baki kai ni damuwa ba Uwar Saddiku! Idan banda Daddy ya raina ni ya za ayi ace ina zaune nan a Kano yana Abuja yana bin matan banza; harda wadda aka ce shi ya ajiyeta kamar matarsa yake mata komai. Kuma duk abun nan ya hana ni zuwa Abujan kuma sai yayi wata biyu bai zo ba, da ya zo kuma dama kwana biyu ne zai ce yana da aiki don haka nan da nan zai koma. Ni zai yiwa tozarci!’


Ta dan zaro ido


'Ikon Allah! Kai Jama'ah wallahi maza basu da mutunci.’
'Ki bari kawai kawata. Akwai wani malami da aka hadani da shi kuma shima an ce aikinsa yana yi sosai, gashi bashi da nisa don an ce nan cikin unguwa uku yake. Kawai dai aikinsa da tsada.’


'To ai haka zamu je don kin ga ni ma na kusa hada 300k, ina ga ko bata isa an gama aikin ba zata isa a fara. In ya so idan ana bukatar ciko sai na bada dakunnen Rukayya a sayar.’


'Nima kusan na hada kudin, kin san akwai aikin da za a yiwa Ummanmu a asibitin koyarwa na A B U. To Raihana ce zata zauna da ita, so nake sai sun tafi asibitin kafin a sallameta sai muje mu gama duk abinda zamu yi. Saura sati shida, kada ki damu kawata kafin azumin bana komai ya dawo dai-dai.’


'Ina ga ma mu dan kara don ni so nake sai ya dawo min da Saddiku tukunna, ina jin shi kuma saura sati biyu ya dawo. In ya dawo na ganshi sai na fi samu nutsuwa, kai da danka saboda zalunci a hanaka ganinsa!’


Suka cigaba da tattauna yanda zasu fitowa matsalolinsu.


Sai da akayi sallar la'asar sannan Zahra ta shirya Aminan ta mayar da ita gida.


__


Kwanci tashi Saddiku yayi wata shida a rehabilitation center, kuma yau Alhamis yau ce ranar da za a daukoshi a dawo da shi gida. Cikin walwala Abba ya shirya tunda ya riga ya dauki hutu ba zai je office ba a ranar, bai gayawa kowa cewa yau zai dawo da Saddiku ba ya fice ya nufi gidan Yaya Bello.


Sai da suka kama hanya sannan Yaya Bello ya sanar da shi cewa idan sun dauko Saddikun shi ya saukeshi a kasuwa, suka kama hanya cikin walwala.


Suna isa suka sami Saddikun a shirye da kayansa tsaf a reception yana jiransu, suna shiga aka yi musu iso wajen shugaban center din wanda shine zai basu takardar sallama.


Bayan sun gama gaisawa ya mikawa Abba takardu ya sa hannu ya tura masa; yayi gyaran murya yace


'To Alhamdulillah, Sadik Yusuf ya fita daga harkar shaye-shaye da izinin Allah. Sai dai akwai bukatar a tabbatar bai koma harka da abokansa na baya ba domin ‘yan shaye-shaye suna da zumunci. Zasu iya sake janshi cikin harkar ba tare da bata lokaci ba. Ba wai hanashi harka da abokai za ayi ba, no, kawai a canza masa environment ko makaranta yanda da kanshi zai sake zabar abokai. Alhamdulillah ma yaron yana da saukin kai domin ya koyi abubuwa da yawa kuma ya haddace wajen izu sha biyar a nan din.’


Cikin jin dadi Abba yace


'Alhamdulillahi. In sha Allah za a kiyaye.’


Sukayi sallama suka dauko Sadiku suka kamo hanyar gida; sai da suka sauke Yaya Bello a kasuwa sannan suka wuce gidan.


Babu kowa a farfajiyar gidan, duka suna cikin falon kasa suna kallon TV saboda ranar children day ce don haka babu makaranta. Ita kuma Mommy tana falon sama.


Da sallama Saddiku ya shiga falon yana dauke da karamar jakarsa wadda kayansa suke ciki, gaba daya daskarewa suka yi na dan lokaci suka kasa magana. Rukayya ce ta fara mikewa ta sa ihu


'Yaya Sadik!’


Kafin ayi wani abu ta mike ta daka tsalle ta fada jikinsa ta rungumeshi tana dariya. Gaba daya su suka taso suka fada jikinsa da gudu banda Yusra wadda ta fito daga dakinsu ta tsaya tana kallonsu tana dariya.


A nan Abban ya shigo dauke da sauran kayan Saddikun yana dariya yace


'An tareka a nan kenan?’


Suka karasa ciki gaba daya bayan Abba ya amsa sannu da zuwan da suke masa. Yusra wadda ta zauna a hannun kujera tace


'Yaya Sadik bamu san fa zaka dawo ba don ko dakinka ba a gyara ba, gashi yau Jummai bata nan.’


Kafin ta sami amsa ta kalli Rukayya tace


'Ke Rukayya sai kije ki share masa dakin in ya so idan Jummai tazo gobe sai ta kara gyarawa.’


Rukayya ta dan bata fuska saboda haka suka saba duk lokacin da ake bukatar wanda zai yi wani aiki to nan da nan Yusra zata ce Rukayyan tayi don ita kusan bata moruwa.


Nan da nan kuma ta dan yi murmushi ta mike tana fadin


‘Bari ka gani Yaya Sadik in ba haka ba Ya Yusra bata ki ka kwana a kan kurar ba.’


Da sauri ta shiga kicin ta kwaso tsintsiyoyi ta fito ta nufi kofar waje da niyyar ta gyara masa dakinsa na boys quarters. Abba ya mike yana fadin


'Rukayya dakinsa na cikin gida zaki gyara masa nan zai dawo, boys quarters din ma a rufe yake.’


Ta amsa yayinda Sadik din ya mike yana fadin
'Bari na gaida Mommy sai na zo na tayaki sharar.’


Ya bi bayan Abban wanda ya riga ya haye saman.


Tun da taji ana ihun dawowar Saddiku ta leko ta kafar bene ta hangosu ta koma ta zauna a falon saman tana jiran shigowarsu. Bata hango Saddiku sosai ba amma dai ta ganshi a tsaye don haka ta tabbatar Saddiku ta ya dawo lafiya, yanzu jiran shigowarsa kawai takeyi.


Abba ne ya fara shigowa falon; cike da walwala ta mike ta tareshi. Shi kansa ya dade bai sami irin wannan tarbar daga daga gareta ba, bayan ya amsa sannu da zuwanta ya dubeta yace


'Ga danki nan na dawo miki dashi babu abinda ya gutsurar miki shi ko?’


Tayi dariya tace


'Ni dama ban ce za a gutsureshi ba ai. Bari na samo maka ruwa.’


Ya shige daki yana dariya yayinda ita kuma ta nufi kicin, kafin ta karasa kofar kicin din saman Saddiku ya shigo da sallama don haka ta juyo tana kallonsa tana amsa sallamar cike da farin ciki. Matsowa take tana kare masa kallo yayinda shi kuma yake ta murmushi; ya canza gaba daya. Ya kara girma da kwarjini gashi yayi haske da kiba, harda wani dan gemu wanda da ta tabbatar babu shi. Murmushi kawai take tana kallonsa yayinda ta karasa ta zauna a kujera, ya kula ta rasa abinda zata ce masa don haka yace


'Mommy na dawo.’


Ta dafa gwiwarsa tace


'Sannu Saddiku. Ya makarnatar? Lafiya kake ko?’


'Lafiya Lau Mommy.'


Suka dan taba hira sannan Saddikun ya tashi ya sauko inda ya shiga dakinsa ya taya Rukayya suka gyara.


……..


Dawowar Saddiku ta yiwa Zahra dadi sosai, domin ita kanta ta kula da canjin da aka samu a tare da Saddikun wanda haka yake kara burgeta; ta tabbatar yanzu Saddikunta ya zama mutum sannan kuma yanzu Saddikun ya zama na hannun daman Abban. Domin kusan kullum idan dai Abban yana gida to suna tare, koda kuwa yana gidan Aisha, kuma suna yawan fita tare duk da basa gaya mata inda suke zuwa. Abu daya ne bai yi mata dadi ba yanda Abban ya sanar da ita Saddiku zai sake JAMB kuma BUK zai koma a daidai lokacin da zai zama Yusra kanwarsa tana shirin shiga level 2 ko ma gama level 2 din. Duk da yanda ta kula shi Saddiku wannan bai dameshi ba. Ita a tsarinta ta fi so a mayar da shi Maryam Abacha American University ko kuma a kalla a samar masa wata jami'ar ta kudi amma ba BUK ba; ta san wannan shawarar Bello ce kuma a halin yanzu ba zata iya ja da maganar ba don bata so ta bata wannan walwalar da suke ciki ita da Abban. Don haka zata bari tunda tana sa rai nan da sati biyu zasu je wajen malaminsu ita da Amina ta san da an musu aiki zata samu ta canza komai. A yanzu ma maganar da akeyi ta riga tayi magana da Yaron Malam yayi mata aiki na kwarjini irin wanda yayi mata wancan karon don tana so Abban ya dan fara sauraronta kafin wancan aikin ya fara.


Kwanan Saddiku biyu da dawowa Yaron Malam ya bayar da aikinta aka kawo mata. Ta Whatsapp ya turo mata da sakon yanda zata yi amfani da abun wanda ba tare da bata lokaci ba ta aikata kuma ta bawa Abban ya cinye.


………


Tunda lokacin da Saddiku yana asibiti ta tambayi abba motarta yace ta tambayi Saddiku bata sake tayar da maganar ba. Sai yanzu da taga Saddikun ya dawo sannan ta sameshi ta tambayeshi inda ya bar mota. Ya sanar da ita da motar yaje hotel din da sukayi party din amma daga nan bai san yanda akayi da motar ba. Ta so ya tambayi Abban amma ya sanar da ita shi ba zai iya tambaya ba sai dai ita ta tambaya. Tana son motar musamman yanzu da take ganin Saddikun yayi hankalin da zai bar mata motarta, don haka ta shirya zata tambayi Abban inda motar take ko kuma a kalla ya bata wata. Tabbatarwa da tayi cewa tayi amfani da kwarjinin da Yaron malam ya bata sannan kuma ga kayan mata da ta siya a wajen Hajja shi ya kara mata kwarin gwiwar tambayarsa.


………
Daga sallar asuba ya dawo, ya riga ya saba baya son komawa bacci bayan sallar asuba. Don haka kawai sai ya zauna a falo ya kunna TV tunda bashi da wani aiki da zai yi. Nan ta fito falon har yanzu tana sanye da rigar baccinta wadda ta dora babbar rigar a kai. Bayan ta gaisheshi ta shige kicin ta hado masa shayi, bayan ta ajiye masa shayin ta zauna a kusa dashi suka cigaba da kallon tashar BBC din da ya kunna.


Jimawa kadan tace
'Yallabai.'


'Na'am.'


Ya juyo yana fuskantar ta, tayi murmushi sannan ta cigaba


'Ni kuwa wai ina motata? Ka san tun Saddiku yana asibiti baka gaya min inda motar take ba.’


Ya kurbi shayinsa, ya rike kofin a hannunsa ya dubeta ya kau da kai sannan yace


'Daga baya an sameta a hannun wasu yara, sai dai an sakata a kasuwa an sayar tun tuni.’


Ta dan yi gyaran murya


'To yanzu ya za ayi da ni? Ai ko wata sai a dan bani ko na sami ta fita unguwa.’


Ya sake kurban shayin sannan ya ajiye kofin a kan teburin da yake gabansa, ya kalleta suka hada ido na dan lokaci yayi murmushi sannan ya dauke kai yace


'Zahra! Kin san daman ba wai ina sha'awar baki mota bane, kin dade da sanin cewa wannan ba ra'ayina bane. Sau biyu ina baki mota ba da son raina ba, kuma duka lokutan biyun saida nayi nadamar baki. Waccan motar ma da Saddiku yayi accident ina cikin gidan nan kika san yanda kikayi da ita ba tare da kin yi shawara da ni ba. Ita kuma ta biyun kinga yanda aka kare. So ni dai ba zan sake saya miki mota ba.’


Ta sunkuyar da kai yayinda shi kuma ya mayar da hankalinsa kan TV din da take gabansa.


Jimawa kadan tayi gyaran murya


'Hakane. Sai dai ina ga ai yanzu na koyi hankali, kuma in sha Allah abinda ya faru a baya ba zai sake faruwa ba.’


'Haka nake fata.’


Suka sake yin shiru na dan lokaci, shi yana shan shayinsa ita kuma tana tunanin ta inda zata fara; domin ba zata hakura da mota ba musamman da yake Aisha tana jan mota. Abu daya ne take jin zai sa ta hakura da mota shine idan ya hana Aisha ma hawa mota. Ta dan yi gyaran murya tace


'Hm! Ina ganin tunda ita Aisha tana da tata motar ai nima zai fi zama dai-dai ka bani wata motar tunda yanzu nace duk abinda ya faru na kiyaye; in ya so sai a sallami Malam Ali. Yaran ma ni sai na dinga kaisu makaranta ina daukosu kamar yanda itama Aisha take kai kanta duk inda zata.’


Ya kurbe dan ragowar shayinsa ya ajiye kofin, ya fuskanceta gaba daya yace


'Zahra. Kece kika yiwa Aisha dalilin da ta sa kudinta ta sayi mota saboda kin hana direban da na ajiye muku yayi mata hidima, yanzu kuma bata yi min wani laifi da motarta ba balle nace ta daina hawa mota. Ke da kanki ki janyo dalilin da ya rabaki da mota; tare da cewa sau biyu ina saya miki mota ba tare da na sayawa Aisha ko taya ba. Ba zan sake saya miki mota ba, duk inda zaki je direba ya kaiki ko kuma ni na kai ki. Alfarma daya zan iya yi miki shine idan kin sami kudi kema zaki iya sayawa kanki mota sai dai ko kin saya idan motar ta fara barazana ga tarbiyya da lafiyar yarana to za a fitar min da ita daga gida. Mun gama maganar mota ni dake.'


Ya mike ya dauki wayarsa ya shige daki ba tare da ya saurari jawabinta ba.


Ta bi kofar da kallo tana murmushin yake; wato duk wannan ban hakurin da tayi ba za a yafe mata ba kenan? Saboda tsabar wulakanci wai ita yake gayawa ta tara kudi ta sayi mota saboda yana takama ya auro ma'aikaciya mai kudi.


'Hmmm!’


Tayi gajeriyar dariya ta mike domin ta san yanda ya saya mata waccan motar ba tare da yayi niyya ba yanzun ma hakan za a sake yi, domin sun gama magana da Amina saura kwana goma sha biyu Ummansu ta tafi Zariya wanda washegarin ranar da ta tafi su kuma zasu je wajen malamansu.


Tana shiga daki ta tuna ya kamata ta turawa Amina kudin da ta hada a account dinta tunda zuwa yanzu ta tabbatar ba zata sake samun wasu kudi kafin nan da lokacin ba. Don haka ta dauki wayarta ta tura naira dubu dari biyu da saba'in zuwa account din Amina. Tana ganin sun shiga ta kirawo lambar Aminan, bayan sun gaisa tace


'Kawata na turo miki 270k gara ki rike a wajenki don wallahi bana jin zan sami cikawa su kai 300k kafin upper week din nan. Wadannan din ma da kyar suka hadu da fizga-fizga sai dai ko bayan an yi aikin lokacin an bude min bakin aljihu.’


'To babu komai, nima nan da kyar na hada 200k amma na san zuwa next week zai turo min kudin cefane na next month don haka da su zan yi amfani ya sake bayarwa idan aiki yayi.’


Suka yi dariyar mugunta sannan sukayi sallama suka ajiye waya kowacce cike da yakinin burinta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login