Showing 24001 words to 27000 words out of 166068 words

Chapter 9 - UWAR SADIKU COMPLT BY SAKINA YAZID.txt

11 Jul 2024

25381

tayi shiru tana wasa da yatsunta.

Suka cigaba da hirarrakinsu kamar babu ita a wajen, don Anisa ma ko gaisheta bata yi ba. Nawal da Ummi ne kawai suke kulata da yake ta dan ja su da wasa.

Ba ta dade da zama ba Hajiya ta tashi ta shige daki, tana shigewa Mommy ta fice ta koma tsakar gida inda Hindu mai aikin Hajiya take zaune a tabarma ta zauna. Kafin wani lokaci duk sun fice sun barta ita da Rukayya.

Ita kanta Rukayyan so take tayi mata magana amma ta kasa, bata jin dadin yanda ake mata amma ba zata iya yin komai a kai ba.

Jimawa kadan Mommy ta cewa Hindu ta yiwa Hajiya magana zasu tafi. Ba jimawa ta fito ta wuce Aisha da Rukayya a falo ba tare da tace komai ba ta karaso tsakar gidan. Suka taso gaba daya sukayi sallama da Hajiya, nan take Rukayya ta fito Aisha na biye da ita itama tayiwa Hajiya sallama.

Sai da Hajiya ta bata rai sannan ta amsa, ta kauda kai. Yara suka wuce Mommy na biye da su tare da Anisa don ta yi musu rakiya. Aisha ta bisu a baya tana shafa jakarta, kudi ne dubu goma a ciki ta kawowa Hajiya amma bata ga fuskar bayarwa ba don haka kawai ta bisu suka fice.

Suna fitowa Yusra ta shige gaban mota Mommy da sauran yaran suna kokarin shigewa baya Aisha ta wucesu ta karasa bakin titi. Suka bita da kallo, Malam Sule ya yunkura zai bita Mommy tace

‘Mu tafi kawai.’

Cikin sanyin jiki ta ya koma ya shiga motar ya zauna.

Tana tsayawa kuwa ta sami mota don haka kafin ma su juyo ta shige mota direba ya ja.
Mommy ta dubi Anisa wadda take tsaye rike da hannun Nawal tace

‘Kin gani ko? Ko kallo bamu isheta ba saboda ta raina ni. Ai shike nan.’

Ta kama baki tana jijjiga kai
‘Wallahi na gani Mommy, ai kuwa sai na gayawa Hajiya.’

Sukayi sallama suka kamo hanya.
…..

Aisha tana zama a bayan tasi din da ta shiga kwalla ta fado mata. Wannan wane irin sharri ne, kallon da ake mata a gidan Hajiya ta tabbatar wani sharrin Zahra tayi mata. Ta kula da yanda bayan sun fito Yusra ta zauna a gaban mota wato ta zo su tafi, ita kuma tunda ita ta kawo kanta to ita zata mayar da kanta shi yasa ma ta wuce su.

Har taje gida zuciyarta tana tafasa saboda takaici, da yake tana shiga gidan akayi magariba sai kawai ta yi Sallah sannan ta zauna tana tunani; ita kuma wannan nata salon kishin kenan? To haka zasuyi ta zama kenan? Lallai akwai aiki.
-----

A al’adarsa kusan kullum idan ya taso daga aiki sai ya biya gidan Hajiya ya gaisheta, haka zai zauna suyi ta hira har sai dare yayi sannan ya wuce gida. Duk da yau bai taso da wuri ba haka ya wuce gidan Hajiyan don ya san gobe asabar da jibi ba lallai ya samu yaje ba tunda suna da meeting da gwamna kuma ya san sai dare.

Bayan sallar isha’i ya shiga gidan, bayan sun gaisa da Hajiya da mutan gidan, ya zauna suna hira. Wajen karfe tara da kwata ya duba agogo yace

‘Bari na tafi Hajiya, dare ya fara yi.’

‘Hakane.’

Suka dan yi Jim, har zai mike Hajya tace

‘Yusufa ita wannan amaryar taka me yasa bata da kunya ne?’

Mamaki ya kamashi yace

‘Hajiya! Wani abu tayi ne?’

‘To na zata Sule direbanka ne kuma kai kace ya kawosu tare da Zahra?’

‘Eh, hakane. Basu zo bane?’

Ta tabe baki

‘Sun zo mana. Amma yarinyar nan don rashin mutunci wai ba zata biyo Zahra su taho a mota daya ba sai dai Sule ya koma ya daukota ya kawota da ban.’

Mamakinsa ya karu

‘Ah! To garin Yaya? Kuma fa tare nace su taho gaba daya.’

‘To haka dai sukayi, sai da Sulen ya kawosu ni kuma nace kada ya koma shine ta biyo motar haya ta zo ita kadai kuma ta shigo tana yiwa mutane gani-gani. Da zasu tafi ma kuma haka, Anisa ma tana kallo yarinyar nan ta wuce Zahra da yaran a mota ta hau motar haya.’

‘Ikon Allah!’

‘Ki zo ki tarar da mace da mijinta kice ba kya son mu’amala da ita? Dama shi yasa tace ka raba musu gidan?’

‘Ba haka bane Hajiya, watakila dai akwai wata matsala…'

‘To gaskiya dai ya kamata ka taka mata burki, idan tana sonka to ta soka da iyalanka.’

‘Bari naje gidan, in Sha Allah zan dau mataki a Kai.’

Suka dan kara hira Hajiya tana jaddada masa lallai ya dau mataki, daga baya yayi mata sallama ya tafi.
……

Ranshi yayi matukar baci, wannan wane irin wulakanci ne Aishan tayi kuma ta rasa ma a inda zatayi sai gaban Hajiya. Idan ta san ba zata hada tafiya da Zahra ba me yasa ba zata gaya masa ba; to don me ma zata ce ba zata hada tafiya da iyalansa ba? Ya kasa gane meye dabarar hakan da ta aikata, don kuwa ya san Hajiya ba zata yi mata karya ba.

Kafin ya isa gida dare ya yi don haka sai ya fara tsayawa gidan Zahra tunda ba nan zai kwana ba idan yayi musu sallama sai ya koma gidan Aishan inda zai kwana.

Ruwa kawai ya sha da yake yaran ma duk sun yi barci, ya zauna a falon kasa itama ta zauna. Bayan ta sake yi masa sannu da zuwa ya dubeta yace

‘Wai me ya faru ne da kuka je gidan Hajiya?’

Kamar bata gane me yake nufi ba tace

‘Na me fa?’

‘A’ah, Hajiya tace min ba tare kuka je ba. Me ya faru ne?’

Ta gatsina baki

‘Uhm, to mun dai fita mun tsaya a mota Malam Sule ya buga mata kofa ta fito ina zaune a bayan mota taki shiga tace wai ya kaimu sai ya dawo ya kaita, bata fadi wani dalili ba don ni ko gaisheni ma batayi ba. Haka dai muka gaji da tsayuwar nace mu tafi tunda yamma tana yi, da muka je kuma Hajiya tace Malam Sule ba zai dawo ya dauketa ba, can kuma sai muka ganta ta zo a motar haya. Da muka fito dawowa ma kuma haka, bata ko kallemu ba ta wuce ta hau tasi don haka muma muka taho.’

Ya kalleta yana mamaki da takaici

‘To wannan wanne irin wulakanci ne haka?’
‘To ai ta gaya maka bata son zama damu, sai ka daukar mata nata direban ka bata.’

Yayi shiru yana takaici, ta riga ta san zugarta tayi aiki don haka ta gyara zama tayi shiru. Jimawa kadan yayi mata sallama ya tashi ya nufi gidan Aisha.

……..

A zaune ya sameta a falo tana kallon TV, yana shiga falon ta mike da fara’arta tana yi masa sannu da zuwa. Babu walwala a fuskarsa ya amsa, ya wuceta ya ajiye ledar burodi a kan dining table ya shige daki.

Ta kula da yanda yake a fusace don haka bata bishi ba, ta tsaya ta gyara abincin da ta ajiye masa a kan dining table sannan ta bishi dakin.


Tana shiga shi kuma ya gama shiryawa, ya wuce ta gefenta ba tare da ya kalleta ba.

Ta tsaya a nan ta sunkuyar da kai; tabbas ta san an gaya masa karya da gaskiya shi yasa zai shigo yana cin magani. Ta share kwalla ta bi bayansa.

A dining table ta sameshi yana cin abinci, sai ta wuce ta zauna a gaban TV ta cigaba da kallonta. Bai dade ba ya gama cin abincin don bata jin ma ya koshi ya taso ya dawo inda take, ko kallonsa bata yi ba har ya zauna.

‘Aisha.’

Ya kirawo sunanta a fusace. Bata amsa ba ta juyo ta dubeshi.

‘Me ya sa baki bi su Zahra kun tafi gidan Hajiya ba kika tafi a motar haya?’

Ta kara bata rai

‘Sun shiga bayan mota ita da Yara, nace su matsa na zauna tace wajen ba zai ishemu ba, nace to Nana ta koma gaba sai na zauna ni a bayan. Tace yaranta baza su shiga gaban mota ba sai dai ni na shiga, ni kuma naga da aurena, ina matarka kuma na shiga gaban mota da direbanka ai ba daraja. Shine tace ya kaisu ya dawo ya kaini, ni kuma kafin ma ya dawo na hau tasi na tafi.’

‘Ni ba haka aka gaya min ba, kuma bana jin Zahra zatayi haka tunda yaran ko makaranta Sule zai kaisu suna shiga gaba. Kuma a dawowa me yasa baki biyosu ba tunda a lokacin Anisa tace Yusra gaba ta zauna.’

Ta riga ta fuskanci inda zancen ya dosa don haka cikin halin ko in kula tace

‘Saboda ban san irin shirin da suke dashi ba a dawowar shi yasa kawai na dawo ta hanyar da na tafi.’

Suka yi shiru na dan lokaci, sannan daga baya yace

‘Aisha! Bana son fitna irin wannan, saboda na raba muku gida ba zai yiwu kice ba zaki hada mu’amala da Zahra da yarana ba. Shekaru wajen sha bakwai nake zaune da ita ban taba samun matsala da ita ba, gaskiya ba zan dauki irin wannan ba.’

Ta hadiye malolon da ya tokare mata makoro tace

‘Ai baka taba yi mata kishiya ba sai yanzu ku…'

Ya katseta

‘Ni dai na gaya miki gaskiya ba zan dau wannan ba, yanzu Hajiya sai fada takeyi saboda abun da kuka yi.’

‘To ai na gaya maka ba laifina bane, ka bincika kafin ka yanke hukunci.’

‘Mtsewww! Ni dai na gaya miki don kin sa na raba miki gida da iyalina ba wai yana nufin ba zakiyi mu’amala da su ba, kuma kece karama dole kiyi hakuri ki bita idan wata sabga ta hadaku. Wannan din ma kuma zan bincika kuma zan dauki matakin a kan mai laifi.’

Ya mike ya shige daki ya barta a nan.

Ta bishi da kallo tana murmushin takaici, har ya shige ya turo kofa.
Wannan shine a doke ka a hanaka kuka; ita aka yiwa wulakanci amma ita ake zargi tayi laifi. Ai kuwa ko me zai yi sai da yayi amma bazata taba daukan laifin da ba nata ba.

Ta riga ta gama shirin kwanciya bacci domin kayan bacci ne ma a jikinta, don haka itama ta mike ta kashe wutar falon ta wuce dakinta ta kwanta.


Ba zata iya binsa dakinsa ba don bata son zama da mutum idan yana jin haushinta; ko waye shi, kuma bata ga laifin da ta yi masa ba balle ta bashi hakuri. Ta kashe fitila ta kwanta bayan tayi adduointa.

Sai da ta kwanta sannan hawaye ya kwace mata; fadan da yazo yana yi mata ya fi bata mata rai a kan abinda Zahra tayi mata don ita za a iya cewa kishi ne. Amma shi ya zo yana gaya mata dole ta kula iyalansa; kenan ma har yanzu ita bata zama iyalinsa ba kenan? A haka har bacci ya kwasheta.

Tana jinsa ya fita masallaci da asuba, itama ta tashi tayi sallah ta sake komawa, sai wajen karfe bakwai sannan ta fito ta shiga kicin. Nan da nan ta soya doya da kwai ta zuba ta dora a dining table ta koma daki ta yiwo wanka ta shirya, har ta fito bai fito ba.
Don haka ta zuba nata abincin ta zauna ta kunna TV tana ci tana kallo.

Ta kusan cinyewa ta ji motsinsa, yana shigowa falon ta gaisheshi ya amsa ba yabo babu fallasa. Kan table kawai ya wuce ya zauna zai fara cin abinci, ta tashi ta hada masa shayi ta zuba masa abincin kamar yanda ta saba sannan ta koma ta zauna ta cigaba da kallonta.

Yana gama cin abincin ya tashi ya fice ba tare da yace mata wani abu ba, duk da dai ta san gidansa ya tafi.

Yana zuwa bakin gate din gidan Malam Sule yana sauka daga acaba, ya karasa da sauri ya kwashi gaisuwa.


Abban ya matsa gefe ya ce

‘Yauwa Malam Sale, dama Ina nemanka. Ni jiya wai ya akayi kuka tafi gidan Hajiya ba tare da Aisha ba?’

Ya shafa kai

‘Ranka ya dade ai mata sai hakuri, rashin fahimta ce aka samu ni kuma na rasa yanda zanyi da su ranka ya dade. A dai bata hakuri.’

‘So nake ka gaya min tsakanin da Allah Malam Sule don Allah kada ka boye min, me ya faru? Ya akayi baku tafi da Aisha ba?’

A hanakli malam Sule ya koro bayani, yayi masa bayanin abinda ya faru har zuwa lokacin da suka dawo. Ya dora da

‘To kaga yallabai babu yanda zanyi, kuma ai bai kyautu Ina tuki ace ta zauna a gaban mota ba, ai ko Yusra ta girma kamar haka ai ta shiga baya na tuka ta balle matarka ta aure ranka ya dade. Amma a dai yi maslaha yallabai lamari ne na kishi.’

Ya jijjiga kai kawai yace

‘Nagode Sule, nagode.’

Ya juya ya bude gate din suka shiga.


Kansa ya kulle gaba daya; yanzu ya za ayi Zahra tayi haka, kuma sannan jiya ta zauna ta tsara masa zance yaje yanata yiwa Aisha fada. Ya tuno yanda take kallonsa lokacin da ya hakikance yana fada.

A zatonsa ya san Zahra shi yasa ya kama zancenta don bai zata zata yi masa karya ba, ashe ma bai santa ba. Ranshi yayi matukar baci; babban damuwarsa yanda ta dora Hajiya a kan karya har take jin haushin Aishan, ya san kawo yanzu kaf danginsa sun ji zancen nan.
Ya karasa cikin gidan ya shiga da sallama.


UWAR SADDIKU


Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)


11

Ranar asabar ce don haka yana shiga ya samesu a falo ita da Yusra, Nana da Ummi domin ragowar basu tashi ba. Da gudu Ummin ta rungumeshi tana masa oyoyo, gaba daya suka gaisheshi. Itama Mommy tayi masa sannu da zuwa ya amsa ba yabo babu fallasa, ta san dai akwai matsala daga yanayin yanda ya amsa ba tare da bata lokaci ba ya haye sama. Nan take ta tashi ta haye tabi bayansa.

A zaune ta sameshi a dakinsa a kan kujera, ta wuce ta zauna a gefen gado tace

‘Ya kwanan amarya?’

‘Alhamdulillah.’

Sukayi shiru na dan lokaci, jimawa kadan yace

‘Zahra, me yasa kika yi min karya?’

Taji wani banbarakwai, mamaki ya kamata

‘Uhm, karya kuma?’

‘Eh, kika ce min Zahra kin binku tayi ku tafi gidan Hajiya bayan cewa kikayi ta shiga gaban mota?’

Tayi tsuru-tsuru, ta sunkuyar da kai zuciyarta cike da takaicin kiranta makaryaciyar da yayi

‘To motar ta cika, gaban motar ne kawai da waje aka ce ta zauna kuma taki.’

‘Amma kin san gaban mota ba wajen zamanta bane tana matar aure, don me Yusra ko Nana bazasu shiga gaban motar ba?’

Ta sha kunu ta kauda kai, sukayi shiru na dan lokaci yana kallonta yana sauraron amsarta. Tace

‘To yanzu kafi kishin matar da ka auro kwanannan a kan yaranka, naga dai suma sun balaga ko?’

Mamakinsa ya karu

‘Oh! Da baki san sun balaga ba kike barinsu suna shiga gaban motar idan zaku fita ko kuma idan za a kaisu makaranta? Ko kuwa sai jiyan suka balaga?’

Ta murgude baki ta kawar da kai

‘Gaskiya bana so, kada ki sake yi min irin wannan. Ba zan dauka ba, yara su shiga gaban mota ku ku shiga baya idan ba haka ba wallahi zan dau mataki a kai kuma matakin ba zai yi miki dadi ba.’

‘Uhm, yanzu dai zugo ka tayi dani da Hajiya kazo kace mu makaryata ne kenan.’

Yayi yake cike da takaici

‘Karyar dai da kika biyawa Hajiya, ai Hajiya bata san me ya faru ba sai abinda kika gaya mata. Kada ki sake yi min irin wannan na gaya miki.’

Kafin tace wani abu ya fice daga dakin yana saukowa ya fice daga gidan ya nufi gidan Aisha.

……..

Yana shiga ya sameta a kicin tana wanke-wanke, yanda bai yi mata sallama ba bata sa rai zai ce mata ya dawo ba. Ga mamakinta sai ya karaso kichin din yace

‘Na dawo.’

Ta juyo tana rike da kwanon da take wankewa tace

‘Sannu da zuwa.’

Ya amsa yayinda ta juya ta cigaba da wanke-wankenta shi kuma ya shige ciki.

Har yayi wanka ya fito tana kicin din, tana hada kayan abincin rana saboda idan ranar tayi sai kawai ta dora. Ya leko kicin din tana tsaye tana yanka kabeji, yace

‘Har yanzu ba a gama ba?

Ta juyo tace

‘Um, aikin ne da yawa.’

‘To sannu da aiki.’

Ya koma falo ya zauna ya kunna TV, yana kallo amma hankalinsa baya wajen, yana ta tunanin yanda zai yi da Aisha don ya kula fushi takeyi da shi. Yana sane da cewa jiya bata kwana a dakinsa ba amma shima a jiyan fushi yayi saboda abinda aka ce masa tayi, saida ya ji daga bakin Malam Sule da kuma yanda Zahran tayi masa da yayi mata magana sannan ya san bai kyautawa Aisha ba.

Yana nan zaune ta zo ta wuce daki, yayi zaton zataje ta dauko wani abun ne yaji shiru bata fito ba har wajen minti talatin. Don haka ya tashi ya bi bayanta; dakinsa ya fara dubawa bata ciki sai dai kawai ta gyara dakin don haka ya wuce dakinta.

Tana zaune a kan gadonta ta mike kafa da novel a hannunta tana karantawa, bayan ta amsa sallamarsa ya karasa ya zauna a gefen gadon. Ta gyara zama ta dan matsa don ya sami wajen zama sosai.


Yayi gyaran murya yana ta wani murmushi da yake bata mamaki tunda a saninta fushi yake da ita don ko da zai fita bai ko kalleta ba.

Yace

‘Um, ya kika zauna a nan? Yau ba kallon Zee World don ne?’

Ba tare da ta kalleshi ba tace

‘Um, karatu nakeyi.’

Suka yi shiru na dan lokaci yana kallonta, yaga dai bazata kulashi ba, ya kirawo sunanta

‘Aisha’

‘Na’am.’

Ta bashi amsa ba tare da ta dago

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login