Showing 162001 words to 165000 words out of 166068 words

Chapter 55 - UWAR SADIKU COMPLT BY SAKINA YAZID.txt

11 Jul 2024

25418

zaune yake a office din yana faman duba lokaci saboda yanda ya kagu yaga Aishan. Sha biyu daidai ya ajiye aikin da yakeyi ya dan kifa kansa a kan tebur, ba tare da bata lokaci ba bacci ya kwasheshi saboda yanda ya tara bacci da gajiya kwana biyu.


A haka ta shiga ta sameshi a office din, sai motsin shigarta ne ya tasheshi daga baccin. Ya muttsike idonsa tare da mikewa tsaye yana murmushi, ya zagayo gaban tebur din ya tsaya a gabanta yana dan tokarewa da tebur din. Ya kama hannuwanta duka biyun yana murmushi, ta mayar masa da murmushin sannan tace


'Tun daga gate na jiyo minsharinka.’


Yayi dariya yace


'Shikenan kuma da mutum ya kifa kai a tebur sai a ce bacci yakeyi.’


Tayi dariya tace


'Au ashe hutawa yake yi.’


Ya karasa mikewa ya sumbaci lebenta, tayi murmushi tace


'A office fa kake.’


'Ni da wa?’


'Ko kai da waye, kayi aiki kawai aka ce.’


‘Wannan ma duk cikin aiki ne.’


Ya saki hannunta ya mika hannu ya dauko mukullin motarsa da waya yana fadin


'Fita fa zanyi, muje ki rakani.’


Tayi dariya tace


'Ko dai na wuce in ya so da yamma sai ka sameni a gida.’


'Ban yarda ba. Kizo muje idan muka dawo sai ki wuce gidan.’


Ba ta son rakiyar sai dai taga kamar ko ma ina zai je ba dadewa zai yi ba, sannan kuma ba zata iya yi masa musu ba saboda yanda tayi kewarsa kuma bata son ta bata masa rai don ta kula yana tare da damuwa. Don haka ta amsa ya sakata a gaba suka fito.


Suna fitowa daga office din yace ta bar motarta a nan idan sun dawo sai ta dauka, don haka suka shiga motarsa suka wuce.


Yana tuki suna hira, nan da nan suka iso BON hotels, Kano. Ya shiga ciki yayi parking yayinda take binsa da kallo mai cike da tambayoyi. Yayi murmushi yace


'Fito muje, wani zan gani sai mu zo mu tafi.’


'To ka je mana sai na jiraka a nan.’


'No, fitowa zakiyi mu je.’


Ya fito yayinda itama ta fito ya rufe motar suka shiga hotel din.


Daga baya-baya ta tsaya don haka bata ji abinda yake fada ba a reception, ya gama aka bashi wani kati ya juyo ya ja hannunta suka shige ciki.


Binsa kawai takeyi tana mamaki; to wanda zai gani kuma a daki zasu hadu?


Kafin ta gama tunanin sun tsaya a bakin kofar wani daki, nan da nan yayi amfani da katin da ya karba a reception ya bude kofar dakin. Ya shige ciki yayinda ita kuma ta dan noke, ya juyo ya jata ciki ya rufe kofar. Ta zazzare ido tana fadin


'Kuma sai na shigarwa mutum daki?’


Yayi dariya


'Babu kowa a ciki to.’


Sai da suka zo tsakiyar dakin ya saketa, ya karasa ya ajiye mukullan motarsa da waya a kan mudubi, ya juyo ya dawo ya tsaya a gabanta ya kama hannuwanta yana fadin


'Bari muyi sallah ko?’


Ta marairaice tace


‘Don Allah me zamu yi a nan kuma?’


Ya dan kara matsawa daf da ita yanda yana jin dumin numfashinta, ya saki hannunta daya ya dago habarta suka hada ido. Ta sunkuyar da idonta. Ya sumbaci lebenta sannan ya kai bakinsa daidai kunnenta yace


'Ki kwantar da hankalinki, ko yanzun kuma ni kike tsoro?’


Ta dan ji kunya don bata zata tsoron da take ji ya bayyana a fuskarta ba, yayi murmushi yace


'Aisha na gaji ne da yawa kuma da zan iya samun hutu ni kadai da ba zaki ganni haka ba har ki dinga tambayata ko bani da lafiya. 2 hours kawai zaki bani zaki ga na warke. Ai zaki iya ko?’
Ba zata iya ce masa a'a ba saboda yanda yake mata maganar da salo na magiya da lallashi, sannan kuma ita kanta tayi kewarsa kuma ga hakkinsa na aure a kanta wanda ta san dole ta saukeshi. Don haka tayi murmushi ta daga masa kai alamar eh.


Cike da farin ciki yace


'Good! Bari muyi Sallah tunda lokacinta yayi.’


Ya shige bandaki ya barta tana karewa dakin kallo.


Ta gama kallon dakin sannan ta zauna a gefen gadon, ta zaro waya ta kirawo Anti Uwani ta sanar da ita kada suga ta dade bata dawo ba sun fita da Abban Sadik. Kafin ta ajiye wayar aka buga dakin aka ce room service ne. Ta mike ta bude kofar a hankali, ma’aikatan hotel din su biyu suka turo dan teburin nan mai taya da abinci kala-kala a kai suka ajiye mata suka fice. Abban yana fitowa itama ta shiga tayo alwala. Sai da suka idar da sallah sanna suka zauna suka ci abincin suna ci suna hira cike da walwala. Yanda yake cin abincin yasa ta dube shi da tausayi tace


'Wai ba kayi breakfast bane?’


Ya dubeta yace


'Hmm! Nayi breakfast. Kawai dai na dade rabon da na ci abinci a nutse kuma naci na koshi shi yasa yunwa tayi min yawa. Yanzu kuwa inaa ci kina min hira ai dole na ci na koshi.’


Tayi dariya.


Bayan sun gama cin abincin ta tashi ta wuce bandaki ta wanko hannu, tana tashi shima ya bita. Suka wanko hannu a tare suka fito.


Suna fitowa ta nufi gefen gadon zata zauna, ya karaso kafin ta zauna ya sha gabanta. Ya kama gefen laffayar da take jikinta wadda ta ki cirewa tunda suka shigo yana fadin


'Ai sai ki cire wannan nadin ki huta tunda ba yanzu zamu tafi ba ko, nifa bacci ma zan yi kuma dai ai kya tayani ko?’


Tana ji tana gani ya warware laffayar, yana ajiyeta a gefen gadon ya kare mata kallo daga ita sai straight skirt na atamfa da kuma bakar riga irin fitted dinnan mai kamar roba ta bi jikinta duk ta kwanta. Kamar a can kasan makoshinsa yace


'Nace ki daina fita da wannan fitnanniyar rigar fa, ai gara ma da hijab kika sa.’


Kafin ta bashi amsa ya fara sumbatar wuyanta.


Haka ta biye masa yayi yanda yake so, sai da ya dauki lokaci ya gamsu sannan ya gyara kwanciya ya jata jikinsa ya rungumeta. Kafin tayi wani yunkuri bacci ya kwasheshi, ta duba agogon wayarta sannan ta dan gyara kwanciya ta lumshe ido itama bacci yayi gaba da ita.


Itace ta fara farkawa wajen karfe uku da da rabi, ta yunkura zata zare jikinta ya riketa yana dariya


'Ina zaki je?’


Ta koma ta langabe tana fadin


'La'asar fa ta kusa, ai gara muyi wanka mu tafi.’


'Um.'


Ya rufe bakinta da nashi bakin yayinda ta fara kokarin ture shi, sai dai kafin ta samu ta kwace ya ci karfinta haka ta sake biye masa.


Sai da hudu ta gota sannan suka tashi suka kintsa sukayi Sallah suka kamo hanya. Suka koma office din sa don ta dauki motarta. Ya karbi mukullin motar ya bawa Malam Sule yace ya kai mata gidansu suma zasu hadu a can, ita kuma yace ta zauna shi zai kaita ya gaida Hajiya.


…………


Yana ajiye Aisha a gida magriba ta kusa don haka kai tsaye ya wuce gidan Yaya Bello. A can ya tarar da su Yusra gaba dayansu don tun tuni Malam Ali ya kawosu.


Bayan sun gaisa Yaya Bello ya dubeshi yace


'A'ah! Ashe ba alhinin mutuwa ne ya sa ka fita hayyacinka ba tsoron kada ka rasa Aisha ne, daga jiya mun je an ce zata dawo shine har kayi kiba kana sheki haka?’


Yayi dariya yace


'Haba dai wallahi ba haka bane Yaya.'


'Ai kuwa ko ka ki ko ka so hakane. Inaga dai nima auren nan zan kara ko na danyi kyan gani.’


Umman Muhammad da take jiyosu daga kitchen ta yiwo gyaran murya. Suka tuntsire da dariya. Abba yace


'Ai ki barshi Umma babu wadda zata aureshi sai ke, daga ke sai shi har Aljanna.’


Daga can tace


‘Ina dai jinku.’


Suka cigaba da hirarrakinsu.


Ana yin kiran Magriba Abban yayi musu sallama suka wuce masallaci da Yayan inda daga can yayi masa sallama ya koma gida.


_


Ranar Talata da safe ma'aikata suka zo, nan aka fito da kayan cikin gidan gaba daya har kujerun Abba yace a fito da su a hada da gadon dakin Zahra a sayar a rabawa magada kudin. Duk wasu gyare-gyare da zasu yi masa ya nuna musu, har kofa yasa ayi masa daga dakinsa wadda kai tsaye zata kaishi dakin Aishan.
A gyara bandakuna da kitchen din gidan duka biyun sannan a sakewa gidan gaba daya fenti. Nan da nan aka fara kwaso kayan ana fitowa da su tsakar gidan.


………


A zaune yake a office yana aikinsa, sai ya tuna ya kamata ya kirawo Amina don ya tambayeta ko akwai wadanda suke bin Zahra bashi kuma yayi mata maganar kudin da yaga Zahran ta tura mata.


Nan take ya ajiye biron da yake hannunsa ya janyo waya, ya lalubo lambar Aminan wadda ya kwafa a wayar Zahra. Bugu daya ta dauki wayar tare da yin sallama; bayan sun gaisa yayi mata bayanin kansa. Ta sake yi masa gaisuwa sannan ta tambayi yaran. Ya tambayeta ko akwai wadanda suke bin Zahra bashi a kawayensu, ta tabbatar masa babu wanda yake binta bashi. Sannan ya tambayeta bayanin kudin da Zahran ta tura mata har naira dubu dari biyu da saba'in. Ta dan diririce sannan a hankali ta janyo nutsuwarta tace


'A'a daman wasu kayane fa da ta siya, kuma ta riga ta karbi kayan tun kafin ta rasu don tana turo min kudin ma na turawa mai kayan.’


Ya amsa suka yi sallama ya ajiye wayar yana mamakin ta.


Daga jin bayanin da tayi ya san karya takeyi sai dai kawai ya kyaleta saboda baya sha'awar ya daga zancen balle wani yaji kudin na menene aka tura.


—-----


Duk yanda ya so a gama aikin gidan nan a sati biyu abun bai yiwu ba, domin ko fitar da kayan ma sai da aka dauki kusan sati ana yi.


Don haka lokacin da sati biyu ya cika da kansa yaje har gidan Baffa ya sanar da shi ba'a gama aiki ba sannan ya je ya sanarwa Hajiya ma.


_


Sai da aka dauki sati hudu ana aikin gidan nan sannan aka kammala. Don haka a farkon sati na hudun ranar asabar da safe Abba yaje gidansu Aisha don ya dauketa su je su yi sayayyar furniture.


Tun kafin ya karasa kofar gidan yayi mata waya don haka kafin ma ya gama tsayar da motar ta fito. Ta bude kofa ta zauna a gaban motar, tana rufe kofar motar kuma ta fara gatsina fuska yayinda yake kokarin jan motar. Da hannu ta fara yi masa alamar ya tsaya ta bude kofar motar ta zuro kanta sai amai. Ya dafe bayanta yana yi mata sannu, ya dauki ruwan roba a gefensa ya mika mata. Bayan ta dauraye bakin ta dubeshi tace


'Bana jin dadi kamar ma nace mu bari sai gobe.’


'Me yake damunki?’


'Malaria ne. Na ma fara shan maganinsa tun jiya da daddare, to kasan maganin ma ba dadi gareshi ba.’


Ya mika hannu ya rufo kofar tata ya karya kan mota yana fadin


'Bari dai muje asibiti a duba ki.’


'A duba me kuma? Ai da ka bari idan na shanye maganin ban warke ba sai naje.’


'Kiyi hakuri muje.’


Ta kwantar da kanta a jikin kujerar motar tayi masa shiru suka nufi asibiti.


Suna zuwa bayan likita yayi mata tambayoyi ya rubuta mata gwaje-gwaje yace taje tayi ta kawo sakamakon yanzu. Suka wuce suka nufi dakin gwajin da yake cikin asibitin.


Ba tare da bata lokaci ba aka dauki jinita aka yi gwajin aka miko musu takardun, ana mikowa ta karbe. Ta bude; guda daya gwajin malaria ne kuma binciken ya nuna akwai malaria din dayar kuma gwajin cikin kuma shima ya nuna akwai ciki. Dama tayi tunanin hakan sai dai ta riga ta cire rai da haihuwa musamman yanda taga shekarun Abban sun ja kuma itama yanzu tana jin kamar ta wuce haihuwa, shi yasa ma tafi karkata ga malaria din.


Yanayin yanda ta ninke takardun yasa Abban ya zare takardun daga hannunta ya bude ya karanta. Ya leka fuskarta yana dariya yace


'Haba, ni na san wannan aman ya fi karfin malaria. Alhamdulillah! Allah ya sa ‘yan biyu ne mata.’


Ta kalleshi yanda yake murna kamar wani yaro tace


'In sha Allahu daya ne.’


'In sha Allahu biyu ne tunda sau biyu kika karba.’


Ta jijjiga kai kawai suka shige office din likitan yana mata dariya.


Likitan ya kara yi musu bayani sannan ya canza mata magani ya sallamesu suka kama hanya.


Suna zama a mota ta dubeshi fuskarta da damuwa tace


'Yanzu don Allah yaushe za a gama aikin gidan nan na koma, ka ga ba sai Hajiya da Anti Uwani sun gane nayi ciki tun ban koma ba.’


Yanayin yanda take magana ya bashi dariya, ya kuwa kyalkyale da dariya yayinda ita kuma ta bishi da harara. Yace


'To menene? Ai ni na san ni nayi.’


'Ni dai gara na koma din.’
Ya gintse dariyarsa saboda ya kula da yanda take kara shan kunu


'Nan da sati biyu, ai Anti Uwani ma ta tayaki laulayin.’


Ta harareshi ta zumbura baki tace


‘Kuma ya ka kama hanyar gida bayan ka ce sayayya zamu je?’


'Mu bari sai zuwa gobe kafin nan kin kara samun sauki sai mu je.’


Ta sake hade fuska tace


'Yanzu zamu je don ko ka je gidan ma ba zan fita daga motar nan ba, muje kawai muyi sayayyara.’


Ya sake gintse dariya ya kalli gefen tagarsa, ya karya kan mota suka nufi kasuwa.


Ya fahimci so take suje suyi sayayyar don ta koma da wuri kafin a gane tana da ciki, shi kuwa yanda yaji dadin cikin nan bai ki aje gidan radio ma a fada ba. Haka suka karasa shagon kayan dakin inda ta nuna duk wadanda take so ya biya kudin sannan suka tafi bayan ya bada adireshin gidan da lambar Saddikun don idan sun gama loda kayan su kai.


Yana tsayar da motar a kofar gidan ta kalleshi tace


'Yaushe zasu gama kafa kayan?’


Har ya fara dariya ya gintse saboda yanda ta bata rai tana shirin fashewa da kuka, ta kama hannun motar zata fita yayi sauri ya riketa. Yace


'Tsaya kiji mana.’


Ta gyara zama ta kalli gaba tana kaucewa idonsa


'Kinga gobe ma ya isa su gama daurawa in ya so jibi sai nazo mu tafi ko?’


Kai kawai ta daga masa. Sukayi sallama a kan ta shirya kayanta zai zo jibin ya juya ya nufi gidan.


………


Kamar yanda yayi mata alkawari haka aka yi. Ya zo da kansa ya dauketa suka koma gidan. Cikin walwala tayi sallama da su Hajiya da su Abdallah; wadanda suma nan da sati biyu zasu koma gidan kanin babansu wato Baba Abba. Ta shiga mota suka kama hanya.


Tayi zaton zata tarar da su Rukayya a gidan sai dai ga mamakinta babu kowa daga ita sai shi. Haka suka zagaya ya nuna mata dakinta da nashi sannan ya nuna mata sauran sassan gidan. Bayan sun koma saman ne ta tambayeshi ina yaran, ya bata amsa


'Saddiku yana nan fita yayi, amma kafin magriba zaki ga ya dawo. Su Rukayya kuma sai next week Yaya zai dawo dasu kafin nan kin shirya gidan yanda kike so.’


'Allah ya kai mu.’


'Kayanki na can gidan ma sai muje gobe ki kwaso wadanda kike bukata sauran kuma ki fadi yanda za ayi miki dasu ko?’


'Allah ya kai mu.’


Ya fice yayinda ta cigaba da kintsa kayanta a dakin.


Ta ji dadin yanda yayi mata kofar shiga dakinsa ta cikin dakinta, yanda zata iya shiga dakinsa ba tare da yaransa sun san ina take ba; musamman matan da dakinsu yake saman a kusa da nata.


……….


Bayan sati daya da tarewarsu Yaya Bello ya kawo su Rukayya. Ya sake yiwa Aishan nasiha da kuma bata hakuri sannan yayi musu sallama ya tafi.


Nan da nan suka hau hidima anata baje kaya.


Rukayya ta fito da keken dinkinta ta cewa Abban ya kamata ayi masa table, nan take kuwa ya amsa da alkawari zuwa wani satin za a yi mata table tunda ta kusa candy kafin admission ya fito sai ta samu ta koyi dinkin.


Haka suka cigaba da rayuwarsu cikin walwala.


_


Tunda suka je gidan Yaya Bello yake faman yiwa Yusra nasiha a kan ta samu ta bawa Aisha hakuri amma sam ta ki. Idan akayi magana sai tace wai ai ta kirawota itace taki saurararta.


Kafin ya mayar da su Rukayya ma sai da ya sa Umman Muhammad tayi mata magana amma da aka tambayeta sai tace ta yiwa Aishan waya wai Aishan ce ba zata fadi gaskiya ba saboda bata son Yusran. Haka suka kyaleta saboda Umman su Muhammad din ta gane karya takeyi kuma tana jinta a lokuta daban-daban tana gayawa yaran cewa idan dai sai ta bawa Aisha hakuri zata zauna a gidan to sai dai ta hakura da zaman gidan ta san Abbanta ya zabi matarsa a kanta. Don haka Yaya Bello yace a barta a nan din kawai don ya kula idan ma ta koma can din ba zata yiwa Aishan biyayya ba.


___


Satinsu uku da tarewa a gidan aka fara azumin Ramadan. Cikin walwala suka gabatar da azuminsu, inda kullum Jummai da yaran suke taya Aisha hada abincin shan ruwa.


Ranar Juma'a ya kama ranar Sallah, don haka washegarin Sallah ranar asabar Yaya Bello da kansa ya kawo su Yusra da Nana tare da nasa yaran, yayi musu sallama a kan zai dawo ya daukesu da magriba.
Cikin walwala Aishan ta karbesu don dama bata da niyyar yanke musu zumuncinsu, sai dai ko gaisuwa Yusra tayi mata ne albarkar idon Yaya Bello. Yana fita ta ja su Sumayya suka shige dakinsu na kasa.


Ita kuwa Aisha sai ta hau saman ta sa mukulli ta kulle duk dakunan da suke saman ta sauko da mukullin. Ya zama dakin su Rukayya na sama ne kawai yake a bude. Ta dawo ta zauna a falon kasa cikin yaran suna ta raha ana ciye-ciye. Suna nan zaune Yusra ta fito daga dakinsu rike da hannun Sumayya suka haye saman, a hankali ta dinga hawa benen ko Aishan zata ce wani abu sai dai har ta haye bata ko kalli wajen ba.


Bayan ta gama ganin dakin kannenta ta fito a gadarance ta nufi dakin Aisha, sai dai tana kama hannun kofar dakin taji a rufe. Haka ta bi duk dakunan har kicin ta jisu a rufe don haka tayi kwafa suka sauko, ta koma dakinsu na kasan ba tare da ta cewa kowa komai ba yayinda ita kuma Sumayya ta kwace ta koma cikin ‘yan uwanta suka cigaba da wasansu da Hanan ‘yar wajen Yaya Bello.


Sai bayan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login