Showing 138001 words to 141000 words out of 166068 words
ya kusan cika.
UWAR SADDIKU
Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)
40
Tunda sukayi maganar mota Abba ya zata zai ga Zahran ta canza masa, amma sai ya ga ta cigaba da lallabarsa don haka shima bai nuna mata wani canji ba.
Yau din ranar talata ce kuma ba a gidanta Abban yake ba. Haka ta tashi sallar asuba jikinta babu dadi, ba zata iya cewa ga inda yake mata ciwo ba amma dai ta san bata jin dadi. Kafin ta idar da sallar asuba ta fara jiyo hayaniyar yara suna shirin makaranta. Ta gama azkar dinta ta mike, ta cire hijabin ta ajiya sannan ta fito daga dakin.
A falon saman ta sami Yusra, bayan ta amsa gaisuwarta tace
‘Ina Rukayya?’
'Tana kicin din kasa tana hada musu abincin makaranta.’
'To. Ku gama shiryasu su tafi makarantar zan dan kwanta don bana jin dadi.’
'To Mommy. Ni dama bani da lecture yau ba zan fita ba.’
'Yauwa, to ga gidan nan idan Jummai ta zo sai kiyi mata bayani. Idan rana tayi a dafa shinkafa da miya.’
'To Mommy.'
Ta koma dakin ta kwanta.
Can wajen karfe tara da rabi Abban ya shigo da shirinsa na tafiya office, bayan Yusra ta gama yi masa bayanin Mommy bata jin dadi ya wuce saman don ya dubota.
Tana kwance a dakin, bayan sun gaisa yace
'Yusra tace min ba kya jin dadi, me yake damunki?’
Ta tashi zaune ta jingina da jikin gadon tace
'Ni kaina bana ce ba wallahi, ba dai na jin dadi ne amma dai kaina yana dan ciwo don haka na sha Panadol na kwanta.’
'Ok. To idan dai kin ji babu hali kiyi min waya sai na zo muje asibiti, kada ki zauna da ciwo haka.’
'In sha Allahu ma ba sai na je ba, da na sami bacci zan warware.’
'Ok. Tare da Saddiku zamu fita, zan ajiyeshi gidan Yaya Bello akwai wajen da zai kaishi don ya fara koyon gyaran computer kafin admission dinsa ya fito.’
'Uhm, to ku gaida mutanen gidan Yaya Bellon.’
Ta koma ta kwanta shi kuma ya fice daga dakin.
Ta bi kofar da ya rufe da harara ta ja tsaki a fili tana tabe baki tace
'Bello! Bello! Bello! Na kusa nayi maganin ku gaba daya.’
Ta gyara filonta ta kwanta.
……….
Har karfe daya ta wuce Mommy bata sauko ba. Lokacin Jummai ta gama abinci ta gyara gidan, itama Yusra tayi sallah har yara sun kusa dawowa daga makaranta. Ta dai san yanzu haka bacci ne ya kwashe Mommy din amma dai ta dade, don haka ta hau saman da nufin ta tashi Mommy din ko don ma tayi sallar azahar.
A hankali ta tura kofar dakin ta shiga da sallama, ta mayar da kofar ta rufe. Yanayin da taga Mommy bai yi mata dadi ba; tana kwance a kan hannunta na dama sai dai ta sauka daga kan filon ta takureshi a jikin gadon. Hular da ta kwanta da ita ta fita daga kanta ta fado gaban gadon sanna ga alamar ta dan turza kafarta a inda kafar take, abun rufar da ta rufe kafafunta da shi rabinsa yana kasa yayinda rabinsa yake jikin kafafun nata.
Da sauri Yusran ta karasa bakin gadon ta durkusa ta tabata tana fadin
'Mommy azahar tayi fa.’
Sanyin da ta ji a jikinta ya bata tsoro don haka ta mike a firgice ta rarumi wayar Mommy din ta shiga neman lambar Abba. Bata taba ganin mutuwa ba amma tabbas wannan yayi mata kama da mutuwa, bata son wannan tunanin da kwakwalwarta take biya mata nan take jikinta ya fara rawa. Da kyar ta lalubo lambar Abban nata ta buga, ta ci sa a kuwa wayar tana shiga ya dauka. Kafin ya gama yi mata sallama a gigice tace
'Abba Mommy ce ka zo bata da lafiya.’
Kafin yace wani abu ta jefa wayar kan gadon ta fice daga dakin da sauri jikinta yana rawa. A guje ta sauka daga been tana yi tana tsallake wasu, ba tare da ta tantance inda zata tafi ba ta nufi fita daga falon kasa.
Har ta fita sai kuma ta tuna Jummai tana kicin don haka ta dawo da gudu ta shiga kicin din tana haki tana fadin
'Jummai zo ki gani, zo ki ga Mommy.'
Kafin Jummai ta amsa ta ja hannunta don haka ba tare da bata lokaci ba ta bi bayanta da gudu suka nufi sama. Suna shiga dakin Yusran tace
'Kin gani fa Jummai, Kinga Mommy kamar fa bata motsi kinga yanda na fita dazu har yanzu bata motsa ba ko suma tayi?’
Jummai ta tsuguna a gaban gadon ta dubi fuskar Mommy din; tabbas mutuwa Zahra tayi. So take ta fasa ihu amma bata so tayi hakan gidan daga ita sai Yusra, don haka ta mike tana fadin
'Bari naje gidan commissioner da gudu na kirawo Mama, Allah ya sa bata tafi asibiti ba. Idan tazo na san zata san abun yi ko kuma su tafi asibiti tunda Abban baya nan.’
Nan ta fito ta bar Yusran tana tsaye ta rasa abinda zata yi kuma ta kasa sake taba Mommy. Jummai bata dade da fita ba itama Yusran ta fito daga dakin ta zauna a falon sama tana share hawaye tana fatan Allah ya sa Mommy suma tayi.
Jummai tana fita ta tsallaka da gudu ta shiga gidan commissioner, tayi sa'a Mama bata fita ba tana tsaye a tsakar gida tana bayarda kayanta da za a wanke mata. Cikin gaggawa ba tare da ko sun gaisa ba Jummai tace
'Mama don Allah ki zo ki duba mana Mommy ce ba lafiya, kamar ma ta suma.'
Cikin damuwa tace
'Subhanallahi!’
Ta juya ta shiga falonta, ba tare da bata lokaci ba ta fito sanye da hijabi tace
'Muje na gani Jummai.'
Jummai da Mama suna shiga farfajiyar gidan Abban shima ya tura gate din ya shiga, yana shiga suka juyo yayinda Abban yace
‘Dr. an tasoki ko?’
Kafin ta amsa ya dubi Jummai yana fadin
'Wai me yake faruwa ne Jummai, me ya sami Mommy din.’
Mama ce ta bashi amsa tace
'Shine zamu je mu gani.’
Suka shige gidan gaba daya kai tsaye suka haye saman Abban yana biye da su. Suna shiga Jummai ta ja hannun Mama suka wuce yayinda Abban ya tsaya a kan Yusra yana tambayarta
'Yusra me ya sami Mommy din? Kukan me kikeyi?’
Bata bashi amsa ba sai hawayenta da yake karuwa. Zuwa yanzu shima hankalinsa ya Kai koluwar tashi duk da bai fahimci abinda yake faruwa ba to amma me zai sami Zahran?
Ya mikawa Yusran hannu yana fadin
'Tashi muje mu gani ga Dakta nan ta zo, yanzu zamu t….’
Muryar Jummai ce ta katse shi yayinda cikin daga murya take fadin
'Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun!’
Cikin hanzari ya rabu da Yusran ya nufi dakin, yayinda itama Yusran ta dafa masa baya kamar zata ture shi. Kusan tare suka shiga dakin suka tsaya a gefen gadon inda Mama take kokarin gyarawa Zahran kwanciya. Jummai ya fara kalla wadda take durkushe a gaban gadon da hannuwanta a kanta hawaye yana gudu a kan fuskarta da bakinta a bude. A firgice yace
'Dakta me yake faruwa ne?’
Ta jijjiga kai
'Ai sai dai muyi hakuri, Mommy Allah yayi mata rasuwa few hours ago don gashi har ta fara sandarewa.’
Zubewar Yusra suka ji wadda tana jin ance Mommy ta rasu ta sume.
Take gaba dayansu sukayi kanta, Mama ta dan tabata sannan ta tallafo kanta ta dubi Abban tace
‘Dauketa mu fita da ita daga nan.’
Sai da yayi da gaske ya iya daukar Yusran saboda yanda jikinsa yake karkarwa, gashi idanuwansa basa gani sosai saboda yanda hawaye suke fita babu kakkautawa. Kansa yana juyawa kafafuwansa suna neman su kasa daukansa haka ya karasa falo da kyar ya kwantar da Yusra a kan kafet din tsakar falon. Yana ajiyeta ya juyo ya nufi komawa dakin yayi da Mama ta tsuguna a gefenta tana kwalawa Jummai kira
'Jummai bani ruwa.’
Cikin sanyin jiki ta fito daga dakin tana share hawaye; fitowar tata tayi dai-dai da shigowar sauran yaran gidan daga makaranta, Rukayya ce kawai bata tashi ba saboda ta tsaya lesson. Turus suka tsaya ganin Yusra a kwance ga Mama a kanta. Ummi ce ta fara magana tana fadin
'Jummai Yaya Yusra bata da lafiya ne na ganta a haka.’
Mama tayi sauri tace
'Eh, bata da lafiya amma yanzu zata tashi.’
Sumayya tace
‘Bari na cewa Mommy mun dawo.’
Kafin a bata amsa ta nufi dakin. Mama tayi sauri tace
'Zo Sumy, zo nan ki gani. Ku zauna a nan tukunna Abba ma yana ciki yanzu zai fito.’
Cikin sanyin jiki suna karewa kowa kallo suka wuce suka zauna a kan kujerar zaman mutum uku suka jeru kamar masu jiran wani abu.
A hankali Mama ta dinga shafawa Yusra ruwan har aka samu ta farfado, tana bude ido tayi yunkurin tashi Mama ta dafe ta tana fadin
'Yi hakuri Yusra kin ji, kada ki jiwa kanki ciwo kiyi hakuri kiyi tayi mata addu'a kawai.’
Ta fashe da kuka tana fadin
'Mutuwa tayi Mama! Wayyo Mommy Inna lillahi wa Inna ilaihi raji'un!’
Ta fada jiki Mama wadda ta rungumeta tana fitar da hawaye.
Daidai nan Abba ya fito daga dakin yana share hawaye. Da gudu Ummi ta tashi ta fada jikinsa tana fadin
'Abba ina Mommy ai bata mutu ba ko?’
Sauran yaran da suke biye da ita suka tashi da gudu suka shige dakin yayinda Jummai ta bisu da gudu. Itama Ummin sai ta saki Abban ta bi bayansu. Kukansa ya kara tsananta yayinda yake ta maimaita
'Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun!’
Ya nufi dakinsa ya shige ya turo kofar. Yana shiga ya kirawo Yaya Bello ya sanar da shi sannan ya kirawo Malam Liman ya sanar da shi. Bashi da kuzarin da zai sake kiran wani don haka ya jefa wayar kan gado ya sa tafukan hannunsa ya rufe fuskarsa ya saki hawayen da yake ta faman makalewa.
Yanzu shikenan Zahra ta rasu? Wannan din wacce irin mutuwa ce haka ba tare da wani notice ba. Ya dafe kirjinsa wanda yake kara kuntata yace
'Astagfirullah.'
Ya mike ya shige bandakinsa ba tare da ya san abinda zai yi a bandakin ba.
Daga nan falon inda su Jummai suke zaune da yaran suka jiyo sallamar namiji daga falon kasa. Jummai ta mike ta ajiye Sumayya tana share hawaye ta fice daga falon. Jimawa kadan ta dawo saman, ta karewa yaran kallo; yanda suke a gigice gaba daya bata ga alamar akwai wanda zai iya kirawo mata Abban ba don haka ta wuce ta kwankwasa kofar dakin nasa.
Ya bude yana share ruwan alwalar da yake fuskarsa, yana budewa tace
'Malam Liman ne a falon kasa da mutane suna magana.’
Ya daga mata kai ya koma ciki.
Yana shiga ya dauki wayarsa ya kirawo Aisha ya sanar da ita halin da ake ciki, Bai saurari tambayoyin da take yi masa ba ya ajiye wayar ya fito ya nufi falon kasa. A nan falon Abban ya zauna shi da su Malam Liman suna jajantawa suna jiran isowar Yaya Muhammadu da Yaya Bello.
Basu dade da zama ba Rukayya ta shigo, wadda Malam Ali ne ya koma makaranta ya daukota da ya fahimci abinda yake faruwa. Bai gaya mata abinda ya faru ba don haka da ta hango Abba a falo sai ta dafe kirji tayi dan gajeran murmushi, ta kasa magana domin ta kula zaman nasu ba na lafiya bane don haka da gudu ta haye sama.
Yanda ta ga Yusra a kashingide kanta babu dankwalu da Mama zaune a kusa da ita ya sa ta karasa falon da gudu. Ta zube a gaban Yusra ta dafa ta tana haki tace
'Yaya Yusra me ya sameki? Ina Mommy?’
Yusran ta kara rushewa da kuka ta matso ta rungume Rukayyan tana fadin
'Mommy ta mutu Rukayya, ta mutu ta barmu.’
Da karfi Rukayyan ta banbare Yusra daga jikinta ta tureta, ta fara bin fuskokin ‘yan uwanta da kallo. Ta kama hannun Mama wanda yake dafe da cinyar Yusra yayinda ta sa hannunta na hagu ta dafe kirjinta tana fitar da hawaye tana fadin
'Mama ai Mommy tana nan ko?’
Kafin a bata amsa numfashinta ya fara yin sama don haka Mama ta saki Yusra ta dafe Rukayya tana umartar Jummai ta debo ruwa.
A daidai nan Saddiku ya shigo falon; wanda tare da Yaya Bello suka zo gidan. Ya kare musu kallo na dan lokaci da jajayen idanunsa. Kai tsaye ya shige dakin Mommy. Kallo daya yayi mata ya tabbatar ta mutu, nan ya tsuguna a gaban gadon yana kallon gawar yana fitar da hawaye.
Daidai lokacin da aka fara samo kan Rukayya a lokacin Aisha ta shigo falon saman. Kusa da Jummai ta karasa tana fadin
'Jummai me yake faruwa ne ban gane bayanin Abban ba.’
Cikin hawaye Jummai tace
'Wallahi Anti ni yau ko haduwa bamuyi da Mommy ba, Yusra tace min bata jin dadi ta kwanta. Muna kasa ni da Yusra muna hidimar mu Yusran ta shigo ta koma tana ihu Mommy babu.’
'Inna lillahi wa Inna ilaihi rajiun.’
Ta tashi ta karasa kusa da Rukayya wadda Mama take kokarin samo kanta, tana tsugunawa a wajen Rukayyan ta fado jikinta ta rushe da kuka tana fadin
'Anti Mommy! Mammy ta tafi ta barmu!’
Rungumeta tayi itama ta fashe da kuka tana bin yaran da kallo na tausayi yayinda rasuwar mahaifinta ta dawo mata sabuwa, don a lokacin bata fi shekarun Rukayyan ba.
Jimawa kadan ‘yan uwan Zahran suka shigo, su Yaya Murja suka zauna nan wajen yaran yayinda su Yaya Muhammad suka shigo suka duba gawar.
Nan da nan aka sauka da ita falon kasa inda a nan ne su Yaya Murja zasu yi mata wanka da sutura da taimakon malamai mata guda biyu da Malam Liman ya kirawo domin wankan.
………
Kafin wani lokaci gida ya dinke da mutane. Nan da nan aka yi mata sutura maza suka dauka aka nufi masallaci domin yin Sallah saboda can ya dan fi sarari domin babu laifi ta sami mutane.
Ana idar da sallah aka kwasa aka tafi makabarta.
Abba da Saddiku suna kan gaba an kama gawa za a saka a rami Saddiku ya saki ya dafe kai, wani daga gefe yace
'Subhanallah! Ku rikeshi zai fadi.’
Nan da nan aka dafeshi, aka karasa sakata. Shima Abban da kyar ya jure tsayuwar saboda yanda kansa yake sarawa. Aka sakata aka rufe mutane suka tattaro suka dawo gida.
Haka aka cigaba da karbar gaisuwa. Itama Aisha hutun aiki ta dauka don a gidan makokin take wuni sai dare take komawa gidanta.
A hankali har aka kwana uku. Ranar kwana uku bayan sallar isha'i ana zaune a falon kasa Suwaiba kanwar Zahran ta dubi Yaya Murja tace
'Yaya ba zaki tafi da Sumayya ba kuwa? Ni nayi nayi da ita tace ba zata bini ba kuma wallahi tunda akayi rasuwarnan fa bana jin ta ci abincin kirki.’
Kafin ayi magana Sumayya ta noke a bayan Rukayya tace
'Ni ba zani ba.’
Aisha ta mika mata hannu ta janyota tana fadin
'Wajena zaki kwana ko?’
Ta daga kai alamar eh. Aishan ta dubi Yaya Murja tace, bari a jima kadan idan muka je can sai taci abincin.
Wajen karfe tara Aisha ta mike ta ja hannun Sumayya da Ummi ta yiwa su Yaya Murja sallama ta fice.
Cikin hanzari Yusra tabi bayansu. Motsin da Aishan taji ya sa ta juya, ganin Yusra ya sa ta tsaya don ta zata wani abun zata fada ko ta bawa ‘yan uwanta.
Ta matso dab da Aishan ta sha gabanta a lokacin da Ummi da Sumayya har sun kusa isa gate don haka suka tsaya daga nan.
Murya kasa-kasa cikin gadara Yusran ta kalli Aisha tar tace
'Ina ruwanki da su da zaki tafi dasu?’
Da mamaki Aishan ta bude baki zatayi magana Yusran ta daga mata hannu ta cigaba
'Ki bar ganin Mommy ta rasu ki zata zaki maye gurbinta, baki isa ba kuma ba zaki taba isa ba. Nan ba gidanki bane kada ma ki taba tunanin zan barki ki shiga dakin uwata wallahi kin yi kadan, kuma idan wani abu ya sami su Ummi wallahi sai kin gwammace zama da Mommy da zama da ni. Eye service kawai.’
Kafin Aishan tace wani abu Yusran ta wuce ta koma ciki ta barta da baki a bude tana mamaki. Sai da Ummi ta gaji ta dawo ta taba Aishan sannan ta tuna ya kamata su tafi ne.
Ta ja yaran suka fice tunani kala-kala yana yawo a kwakwalwarta.
UWAR SADDIKU
Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)
41
Ranar da Zahra ta kwana hudu da rasuwa bayan azahar Abba ya sallami mutane, ya sanar da su Yaya Muhammad an tashi daga makoki. A cikin gida ma an sanar da mata don haka nan take aka fara watsewa, itama Amina wadda da ita aka yi zaman kwanaki ukun tayi musu sallama ta tafi. Zuwa la'asar ya zama gidan babu kowa sai Yaya Jummai da Rahma wadanda suka ce sai washegari zasu tafi inda zasu bar yaran da Goggo Binta wadda goggon su Zahran ce; idan an yi kwana bakwai ita kuma zata tafi.
—----
Ranar kwana biyar gidan ya dan sami natsuwa domin mutane sun yi saukin zama, sai dai da an zo babu dadewa ayi musu gaisuwa a tafi. Yaran gaba dayansu suna cikin tsananin damuwa, musamman masu wayon daga kan Saddiku zuwa Nana. Ummi da Sumayya dai suna dan sakewa sai dai tun ranar da aka kwana hudu Yusra ta hansu bin Aisha idan ta shigo don haka suka rage samun wanda zai saka su a gaba su ci abinci.
Abba yana kokarin kulawa da su don bai koma aiki ba, sai dai shima a cikin damuwar yake wuni. Ya kasa gane abinda yafi yi masa zafi a ransa; mutuwar Zahra ko kuma halin maraicin da yaransa suka shiga. Yana iya kokarinsa wajen basu hakuri sannan kuma ga Goggo Binta ma tana kokari amma duk da haka da damuwa yake ganinsu.
Bayan an idar da sallar isha'i sai da ya siyowa Ummi yoghurt sannan ya shiga gidan. Rukayya ya samu a falo tana kwance kamar mai bacci, sai dai yana shiga falon ta tashi zaune. Bayan ta amsa sallamarsa tayi masa sannu da zuwa. Ya mika mata ledar yoghurt din yace ta kaiwa Goggo nata sannan ta raba sauran ita da ‘yanuwanta.
Ta karba ta nufi daki domin kaiwa Goggo nata.
Tana karba ya wuce sama, kai tsaye dakinsa ya shige ya turo kofa ya zauna a gefen gado yana tunani. Bai dade da zama ba ya dauki mukullinsa ya fito ya rufe dakin; sai da ya leka dakin Sadik ya