Showing 150001 words to 153000 words out of 166068 words

Chapter 51 - UWAR SADIKU COMPLT BY SAKINA YAZID.txt

11 Jul 2024

25405

ya tsawatarwa yarinyar watakila ki ga abun ya zo da sauki.’


Ta share kwalla sannan tace


'Wallahi Anti Uwani ba zai tsawatar mata ba, kuma ko ya tsawatar mata babu abinda zata fasa tunda yaran sun saba ba sa jin magabarsa. Ba zan iya rayuwa da wannan yarinyar ba wallahi don idan ta kasheni nawa marayun yaran ta cuta shi ubanta wata zai auro su cigaba da rayuwarsu. Idan kuma bata kasheni ba to in ta kureni nace zan dauki mataki a kanta wallahi kowa ba zai ji dadi ba tunda ai duk muguntarsu nima na iya Allah ne yake katangeni.’


Sukayi shiru na dan lokaci. Abun ya sha kan Anti Uwani sai dai ta san babu wanda zai fahimcesu. Ita ta san irin wadannan yaran don ta zauna da su, don daya har bayan an yi mata aure ma haka ta dinga zuwa cikin gidan tana haddasa fitna a karshe sai da ubanta ya saki Anti Uwani a kan laifin da ba nata ba. Ta muskuta tace


'Hmm! To yanzu ya za ayi Aisha?’


'Su Baffa suyi masa magana, idan ya dauke Yusra da Nana bani da matsala da sauran yaransa, ko dan shege ya bani kuma zan rike masa da amana. Amma idan dai aka ce sai na zauna da Yusra to gaskiya na hakura da aurensa.’


'A'a abun ma ba zai kai haka ba in sha Allah. Amma dai ina kokonton yiwuwar abinda kike so domin su fa maza gani suke kamar tunda suka aureki to ko me suka rakito dole ki zauna da shi. Iyayenku ma kuma goya masa baya zasuyi. Kuma daga baya idan ta kashe miki auren a cigaba da zaginki.’


'Duk ma abinda zasuyi sai dai suyi don wallahi Anti Uwani idan aka ce sai na zauna da yarinyar nan zaku nemeni ku rasa ba zaku sake gani na ba.’


Ta bata rai tana harara Aishan tace


'Bana son rashin hankali, kada na sake jin wannan zancen kin ji na gaya miki. Ki ci gaba da addu'a in sha Allah za a sami maslaha.'


Sukayi shiru na dan lokaci kowa da abinda yake tunani, jimawa kadan Anti Uwani ta tashi ta fice ta koma dakin Hajiya; inda ta tarar Farha har tayi bacci yayinda Hajiyan take zaune a kan dadduma inda ta idar da shafa'i da witri.


Nan ta zauna ta bawa Hajiya labarin abinda Aishan ta gaya mata. Cike ta mamaki da takaici Hajiya tace


'Kin ji ko Uwani, na gaya miki yarinyar nan fa bata da hankali har yanzu. Ya za ayi kina matsayin matar mutum kuma kice yaransa marayu sai kin zabi wadanda zaki rike masa?’


'To Yaya ai tayi mutunci ma tunda ita nata marayun ko daya bai zaba ba balle ya taya ta rikonsu.’


Ta harareta


'Kinga Uwani ki daina tunzura yarinyar nan fa. Ke da baki taba haihuwar nan ba ba kin zauna da ‘yayan kishiyoyin ba kala-kala, me ya kasheki? Duk sharrinsu ba haka suka hakura suka barki ba?’


Ta kawar da kai


'Na hakura na barsu dai Yaya bayan sun sa ubansu ya kore ni. Kuma zama da su din ai rayuwa ce wadda na cikin gidan yari ya fi ka ‘yanci kuma ko makiyi na bana yiwa fatan irin wannan rayuwar Yaya.'


Suka yi shiru na dan lokaci. Hajiya bata so ta tunawa Anti Uwani tata rayuwar ba don ta san tabbasa ta sha wahala a hannun yaran kishiyoyi domin ita din Allah bai taba bata haihuwa ba. Kuma haka Allah ya hada ta da mijin da ya dinga auren mata suna haifa masa yara yana sakinsu, kusan duka yaran ita ta rikesu. Duk wata fitnarsu haka zai muttsike ido yace itace bata san ciwon yara ba don bata haifa ba, haka tayi wannan rayuwar kuma daga karshe ya saketa a kan laifin da ba nata ba.
Sai daga baya kafin rasuwarsa ya dinga kokarin mayar da aurenta ita kuma a lokacin ko sauraronsa bata yi ba.


Anti Uwani tace


'Idan gari ya waye zan gayawa Abubakar ya sanar da Baffansu; ai tayi mutunci ma tunda ba duka yaran tace ba zata rike ba. Tunda na bude ido nake zuwa islamiyya har yau ban daina zuwa ba kuma ban taba ji a cikin karatu an karanta aya ko hadisin da yace dole idan kina auren mutum ki rike masa yaran da baki haifa ba, hasali ma har aka gama bayanin masu riko babu matar uba a ciki to na me za ace sai ta yi? Idan yana so ta rike masa su kuma ai matarsa ce sai yayi amfani da dabara ya lallabata ba wai ya nuna mata isa ba. Kuma idan sun sabauta Aishan ai yaranta suka cuta da mu da muka haifeta, tunda shi ubansu aure zai kara ya cigaba da rayuwarsa.’


Cikin sanyin jiki Hajiya ta dafa hannun Anti Uwani tace


'Hakane. Bari dai gari ya waye Baffa yazo, idan aka bi abun a hankali za a sami mafita in sha Allah.'


Jimawa kadan Anti Uwani tayi mata sai da safe ta tashi ta koma daki; dukansu zuciyoyinsu babu dadi. Ita Hajiya ba da son ranta ta tunawa Anti Uwani tata rayuwar auren ba wadda take cike da jarrabawa kala-kala ga rashin haihuwa, ita kuma Anti Uwani abubuwan da suka faru da ita suna dawo mata tana tunani babu yanda za ayi ta bari Aisha ta shiga irin rayuwar da ita tayi.


Haka suka kwanta bacci kowa da abinda yake ransa.


Rayuwar auren Anti Uwani ce gaba daya ta dinga dawo mata; abubuwan da tace ba zata sake tunawa da su ba balle su sa mata damuwa amma yau sun hanata bacci.
Shekaru kusan talatin tayi a gidan miji amma iya shekarar farko ne kawai zata ce tayi a nutse. Tunda ta shekara bata haihu ba dangin miji suka fara takura mata, tun baya biye musu har shima ya fara damuwa. Kuma babu wanda ya taba cewa taje asibiti sai dai ayi ta bata tsimi tana shanyewa, haka tayi ta shan rubutu da tsimi wani daga gidansu wani kuma daga wajen dangin mijin. Ga kuruciya a tare da ita don bata fi shekaru Sha biyar ba a lokacin. Shekara uku a gidansa ya kara aure; yarinyar kuwa tana tarewa ta sami ciki. Haka aka mayar da Anti Uwani kamar mai aiki a gidan; kwashe amai, wanki, girki duk itace idan kuma dare yayi maigidan yace wajen amarya zai kwana kada wani abu ya sameta. A haka cikin damuwa da hantara suka cigaba da zama da matar nan har ta haifa masa yara biyar duka mata, daga baya ya saketa ya kwace yaransa tunda dama ko da uwarsu tana nan ma duk wata hidimarsu da ta gida Anti Uwani ce take yi. Bayan ita ya auro wata wadda ita kuma tana shigowacta haifa masa yara biyu maza. Haka Anti Uwani ta cigaba da bauta mata saboda da zarar ta ki yin wani abu sai maigidan yace tana bakin ciki don Allah bai bata haihuwa ba. Daga karshe tana zaune a tsakar gidan tana hura wuta zata dora abinci yayinda amaryar gidan take janyowa maigidan ruwan wanka a rijiyar tsakar gidan karamin yaron gidan mai shekaru kamar bakwai yayiwo tsokana ya shigo gidan da gudu basuyi aune ba sai ji sukayi ya fada rijiyar nan. Nan take uwarsa tace Uwani tana kallonsa ya fada rijiyar bata rikeshi ba. Shi kuma maigidan yace idan dai yaron ya mutu to ya saki Uwani saki uku. Da kyar aka dauko gawar yaron daga rijiyar inda a nan take maigidan ya kora Uwani gida.
Bayan wanna kuma ta auri wani mutum wanda shi kuma lafiya suka zauna don shi bai hadata da iyalansa ba ma suna gari da ban da ban, shekara tara da aurensu Allah ya karbi rayuwarsa. A nan wancan ya dawo cikin zawarawa ita kuma tace gaba daya ma ta gama aure a duniya tunda ko babu komai a lokacin ta tsufa.


Da kyar bacci ya kwasheta tana tuna rayuwarta ta baya kamar mai kallon fim.


—----


Bai san tsawon lokacin da ya dauka a zaune a kan dining table din ba, gajiya kawai yayi da zaman ya tashi jikinsa babu kwari ya hau saman. Kai tsaye dakinsa ya wuce, yana shiga ya zauna a gefen gadon ya dafe kansa da hannuwansa. Motsin da ya jiyo daga daya gefen gadan shine ya janyo hankalinsa, ya sauke hannuwansa ya kalli bangaren da ya jiyo motsin. Rukayya ce a takure a kasa daga gefen gadon ta hada kai da gwiwa; sai a lokacin ya tuna shi ya ce tazo ta jirashi a daki.


'Rukayya.'
Ya kirawo sunanta.


Ba tare da ta dago kai ta dubeshi ba ta amsa a gajarce


'Um.'


'Taso ki zo nan.’


Ta taso tana goge fuskarta wadda tayi ja gaba daya saboda kuka; duk da zuwa yanzu babu hawaye a fuskarta. Ta zagayo ta dawo gabansa ta tsuguna tana kallon kasa. Ya kare mata kallo na dan lokaci cikin damuwa, ya mika hannuwansa ya kamo nata hannuwan wadanda suke ajiye a kan gwiwarta ya rike tafukan hannunta a cikin nasa ya sake kiran sunanta. Ta amsa a gajarce tare da daga Ido ta kalleshi ta mayar da idonta kasa. Yace


‘Me ya hadaki da Yayarki kuke fada haka?’


Kafin ta amsa ya cigaba


'Kin san bana son karya don haka gaskiya zaki gaya min.’


Cikin sanyin murya tana kokarin danne hawayen da yake shirin kwace mata tace


'Cewa tayi bana son Mommy.'


'Ba kya son Mommy? Yusran ce tace haka?’


Kai kawai ta daga masa alamar eh.


'To me ya sa zata ce ba kya son Mommy?’


'Saboda zamu je gidan Anti Aisha ni da Ummi?’


Ya saki hannuwan nata yana jijjiga kai yace


'Ban gane ba Rukayya, kiyi min bayani sosai. Me ya hadaku fada? Me yasa don zaki je gidan Anti Aisha za a ce ba kya son Mommynki?’


Sukayi shiru na dan lokaci, shi yana sauraronta yayinda ita kuma take tunanin yanda zata yi masa bayani ba tare da ta fadi laifin Mommy ba. Shirun ya dan tsawaita kuma ta san ita yake jira tace wani abu, ta share kwalla daga idonta sannan ta fara yi masa bayanin abinda ya faru har ya sa suka fara fadan. Bayan ya gama sauraronta yace


'To zuwa gidan Antin ne ya zama yiwa Mommy rashin biyayya ko kuwa wa yace mata zaki sake uwa ne?’


Bata son yanda yake turata kan bayanan da zasu shigo da Mommy cikin maganar amma ta san dole ta bashi amsa. Ta kosa da tsugunon sannan kuma bata son maganar, haka ta sake share kwalla ta cigaba da bayani.


Tayi masa bayanin yanda Mommy ta hanata zuwa gidan tunda ya auro Aishan sannan tace


'Kuma yanzun ma ba zama zanyi ba, zuwa zanyi na gani ko akwai kayan da zan tayata kwasowa tunda ka ce mana zata dawo shine ita kuma ta fara gaya min maganganu.’


Yayi shiru na dan lokaci yana so ya hada zantukan gaba daya ya basu ma'ana, sai dai kansa gaba daya ya cushe sai sara masa yake. Da kyar ya daga kwayar idonsa ya kalli Rukayyan saboda yanda duk wani motsi na kwayar idon nasa yake kara masa ciwon kai. Yace


'To kiyi hakuri, idan kin je gidan Aisha ba yana nufin zaki sake uwa bane don babu wanda yake iya sake uwa, sai dai Aishan itama uwarku ce gaba daya tunda kinga yanzu nan zata dawo ta dinga kula da ku. Amma bana son ki sake yiwa wani irin dukan da kika yiwa yayarki, rashin hankali ne zaki iya jiwa mutum ciwo.’


'To Abba.'


'Tashi kije, kada ki sake kulata kuyi wani fadan idan ta yi miki wani abu ki zo ki gaya min ko ki gayawa yayanku.’


'To.'


Har ta kama hannun kofar zata bude ya sake kiran sunanta, don haka ta dawo ta tsuguna daga gefe. Yace


‘Akwai wani abu da Anti Aishan takeyi ne wanda yasa Mommy din bata son kuje wajenta?’


'Wallahi Abba babu wani abu, haka kawai ne sai Mommy din taga kamar Antin zata cutar damu kuma wallahi ba haka bane. Ita kuma Yaya Yusra sai ta dinga zugata ba zata bata hakuri ba.’


Ya jijjiga kai ya sallami Rukayya wadda ta fito daga dakin ta rufe masa kofa.


Gaba daya kansa ya kulle; tabbas ya san Zahra bata son Aisha kuma ya san akwai lokutan da take hana Rukayya zuwa gidan amma bai san abun ya kai haka ba. To ko shi yasa Aishan tace ba zata zauna da Yusra ba? Watakila wani abune na kiyayya da Yusran take bayyanawa Aishan yasa take jin ba zata iya zama da ita ba. To amma ai babu inda zai kai Yusra don haka dole Aishan tayi hakuri ta zauna da yaran gaba daya. Zai yi magana da Yusran zuwa da safe kuma zai sakata a gaba suje ta bawa Aishan hakuri in yaso ma sai ta tayata kwaso kayanta kafin su Rukayyan su dawo makaranta ta dawo gidan.


Sarawar da kansa yakeyi tayi yawa don haka ya mike ya matsa gaban karamin fridge din da yake dakin ya bude ya dauki ruwa sannan ya koma gaban mudubi ya dauki Panadol ya hadiya. Ya shiga bandaki ya yiwo alwala da nufin yayi sallar Magriba wadda bai yi ba ya tsaya rabon fada gashi har ana kiran isha'i; sai dai yanda yaji da ya fito ya tabbatar ba zai iya yin sallar a lokacin ba.
Don haka ya kwanta a gefen gadon ya dafe kai tare da rufe idanuwansa.


…….
Washegari da wuri ya tashi duk da kasancewar ranar asabar ce. Karfe bakwai na safe ya sauko daga saman, yaran gaba daya suna kan dining table suna cin abinci domin akwai tahafiz wadda karfe takwas saura kwata ake shiga. Yusra ce kawai wadda bata tashi daga bacci ba bata wajen amma har Saddiku ma yana zaune. Bayan ya amsa gaisuwar su ya tambayesu Yusra inda suka tabbatar masa bata tashi daga bacci ba. Surutunsu ya sa Jummai ta fito daga kicin inda take aiki, ta tsuguna ta gaisheshi. Bayan ya amsa ya koma ya haye saman inda Rukayya ta bi bayansa da abincin safen sa ta ajiye masa a table din saman ta sauko.


Ya shige dakinsa ya kashingide a kan gado ya fada tunani; tabbas yana bukatar mace a gidan don da ace da mace a gidan wadda ba ‘yar aikin gidan ba da ya san yanzu yana bacci amma dole ta sa kullum sai ya tashi ya tabbatar yaran sun shirya sannan idan sun tafi makaranta shima ya shirya ya fita nasa aikin. Ya san Aisha karfe takwas take tafiya islamiyya don haka bari zai yi sai bayan azahar lokacin ta dawo yaje suyita ta kare. Domin shi yau din nan yake son ta dawo gidan.


Har bayan azahar yana gidan yana sauraro ko zai ji shigowar Aisha amma bai ji motsinta ba. Don haka wajen karfe uku bayan yara sun tafi islamiyya ya shirya ya nufi gidan Aishan da shirin zai je yaji abinda ya hanata dawowa, da shirinsa na wucewa gidan Yaya Bello bayan ya gama da Aishan.


Har ya isa gidan yana mamakin wannan taurin kan na Aisha.


Da mukullinsa ya bude gate din ya shiga, yana zuwa kofar shiga falon yaganta a garkame da kwado. Mamaki ya rufe shi; tunda yake da Aisha bata taba fita ba tare da ta tambayeshi ba. To daga islamiyya ne bata dawo ba ko Kuma wani wajen ta wuce bata gaya masa ba?


Har ya saka mukulli zai bude kofar sai yaga idan ya shiga ma babu abinda zai yi don haka ya juya ya fice daga gidan ya nufi gidan Yaya Bello yana san ra duk ma inda taje kafin ya dawo ta dawo in ya so sai yaji.


A farfajiyar gidan ya sami Yaya Bellon yana zaune yana shan fura da ‘yar autarsa Minal wadda zazzabi ya hanata zuwa islamiyya. Bayan Minal ta gaisheshi ta shiga gidan ta karbo masa kofi don ya sha furar, tana ajiyewa ta koma cikin gidan.


Bayan Abban sun gaisa da Yaya Bello suka cigaba da hirarrakinsu. Yaya Bello ya dubeshi yace


'Ya yaran? Aishan ta koma wajen nasu?’


Cikin yanayi na damuwa yace


'Wallahi Yaya bata koma ba, sai wasu dokoki da ta kafa na shirme. Ni gaba daya ma na kasa fahimtar ta. Wai ita bazata rike yaran duka ba sai dai dole na cire Yusra da Nana su bazata iya zama da su ba.’


'Ah, kamar Yaya? Wannan ai zancen banza ne ma. To su Yusran da Nana gidan marayu zaka kai su kenan ko ya take so kayi dasu?’


'Wallahi Yaya nima dai na kasa fahimta.’


'To kuma bata baka wani dalili ba?’


'To basa dai jituwa da Yusra, ita kuma Nana zaka iya cewa ko uwarsu bata kai Yusran iko da ita ba. Kuma da Zahran ma ai basu sami wata jituwa ba tunda ka ga abinda ya faru har na shekara ban shiga gidan Aishan ba ko ba a fada mata ba Zahran take zargi kamar yanda kowa ma ita yake zargi. Da wasu abubuwa dai na cutarwar da rashin kunya da tace ana aika Yusran tana yi mata. Don haka tace ma wai Yusran ta tareta bayan rasuwar Zahran ta gaya mata ba zata barta ta maye gurbin uwarta ba.’


Ya daga hannuwa ya yarfe kamar mai Shirin fada yace


'Ai ka ji! Duk shirme ne nasu na mata. Nawa Yusran take da Aishan zata ce ta rasa yanda zata yi da ita? Wanna ma ai ba wani abu bane, idan ka koma sai ka hadasu ka jawa yaran kunne a gabanta. Kuma in ta dawo nan din ma ai ba kyalewa zaka yi ba, duk wanda yayi ba dai-dai ba sai ka dau mataki kuma gidan ma sai ka sa ido tunda yanzu babu irin muguntar fa da mata basa yiwa dan kishiya.’


'Hakane. Sai na koma gidan yanzu zan saka ta a gaba mu koma can din.’


'Gara haka, Kai ma ka huta da biyan kudin hayar. Amma idan kace zaka biye ta tata sai ta tarwatsa maka iyalin don haka ma kada ka saurara mata. Idan ba zata zauna maka da wadannan marayun yaran ba yanzu kam bata da wani amfani a wajenka.’
Suka cigaba da hirarrakinsu Yayan yana kara karfafa masa gwiwa lallai kada ya kyale Aishan dole ta koma ta kula masa da yaran.


Sai wajen karfe biyar na yamma sannan Abba yayi masa sallama ya kama hanyar gidan. Yana shiga unguwar ana kiran sallar Magriba don haka kai tsaye masallaci ya wuce. Sai da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login