Showing 156001 words to 159000 words out of 166068 words

Chapter 53 - UWAR SADIKU COMPLT BY SAKINA YAZID.txt

11 Jul 2024

25421

ajiyeta a kan durowar gefen gado ya matsa gaban wardrobe ya goge fuskarsa da tawul ya fice daga dakin. A falon kasa ya samesu inda ya zauna suka gaisa, Yusra da Saddiku wadanda basu je makaranta ba suna zaune suma. Bayan sun gaisa ya dubi Saddiku yace


'Ka bude mana dakin Mommynka Saddiku, za a duba kayan ne a kwashe masu amfani a sayar a raba gado kamar yanda Allah ya ce.’


Ba tare da ya amsa ba ya mike ya haye sama tunda mukullin dakin nata yana dakin Abban inda Saddikun ya ajiye. Abban ya mike tsaye yana yiwa su Yaya Murja iso zuwa saman. Suna mikewa wayarsa da take aljihunsa ta fara kara, ya ja baya yayi musu iso su wuce saman inda suka wuce Yusra tana biye da su. Ya lalubo wayar ya amsa da saurin tana daf da tsinkewa ganin cewa Yaya Bello ne.


Suna gama gaisawa Yaya Bello yace


'Ina ka tsaya ne? Kace zamu je wajen iyayen Aisha sha daya da rabi gashi sha daya da rabin har ta yi baka zo ba balle mu tafi.’


Ya dora daya hannun nasa a ka yana fadin


'Subhanallahi! Wallahi Yaya na manta shaf. Kai Jama'ah! Kuma ka ga ma baki ne da mu a gidan ‘yan uwan Zahra ne zasu duba kayanta a fitar don a rabawa magada. Kai! Ni kaina wallahi yanzun ba a nutse nake ba Yaya, ina ga bari kawai na kirawo Abubakar din su yi mana uzuri ma je da magriba don wallahi yanzu bani ma da nutsuwa.’


Yaya Bellon yace


'Akwai wata matsala ne a gidan? Na ji ka kam lallai ba ka da nutsuwa.’


'Wallahi Yaya, idan na zo dai zaka ji. Bari na kirawo Abubakar din.’


Yana ajiye wayar ya kirawo Abubakar ya sanar dashi suyi masa uzuri zasu zo da Magriba, nan ya sanar dashi dama an yi rasuwa Baffa yana son yaje jana'iza don haka suka bari sa hadu da magriba.


Yana ajiye wayar ya mayar da ita aljihunsa ya haye saman, yana isa falon saman kuma ya tsaya ya jona wayar tasa a chaji sanna ya shige dakin Zahran.


Yana shiga ya tarar da su sun fito da kayanta na sawa suna ta lodawa a akwati, ga wasu kuma a gefe wadanda sababbi ne sai kuma manyan leshinanta wadanda Yaya Murja take ganin a bawa yara su dinka. Nan da nan Yusra da Saddiku suka taya su suka lode kayan a akwatuna, wadanda akwatunan basu dauka ba aka waresu gefe zuwa lokacin da za a sami mazubi a san yanda za ayi da su.


Dan akwatin sarkokinta an dauko shi inda Yaya Murja ta ware na good ta mikawa Abban tace


'Wannan gwal ne sai a ajiyewa yaran.’


Ba tare da ya duba ba ya karbi dan akwatin ya bawa Saddiku ya kai masa daki.


Wani akwatin ya hango a saman wardrobe na agogo, ya mika hannu ya dauko. Yana daukowa yaji wani abu ya fada bayan wardrobe din. Ya zauna a gefen gadon ya bude akwatin; agogunata ne a ciki da sarkokinta na fashion. Ya mayar ya rufe ya mikawa Suwaiba yana fadin


‘Wannan ma ai sai ku zabawa yaran na ga masu kyau ne.’
Ta karba ta ajiye a gefe suka cigaba da zazzage durowoyin mudubin ta, wadanda duk tarkacen kayan mata ne a ciki. Su ma su Suwaiban karewa sukeyi suna fatan Abban ya fita ya basu guri amma ya ki.


A nan Yaya Murja ta sanar da shi ta sami mai sayen gadon amma nan zai zo ya gani ayi ciniki idan ya biya sai ya dauka. Ya dubi Saddiku wanda yake kwashe tarkacen kayan shafawa da kwalliyarta a kwali yace


'Bar wannan in suka duba sa kwashe zo ka kama min wardrobe din nan mu matsar a dauko abinda ya fada tunda an kwashe kayan ciki gaba daya. Idan muka dauko sai mu kwance gadon don mai sayen ko bana nan idan suka zo sai kawai ya duba suyi magana da Antinka.


Suka kama wardrobe din da kyar suka dan matsar da shi gaba, Abban yace Saddiku ya shiga bayan ya dauko duk abubuwan da suka fada. Nan ya shige ya dinga kwaso tarkacen; wasu warin dankunnaye, agogo guda daya wanda shine ya fada lokacin da Abban ya dauko akwatin da irin lallen nan rani wanda ya ma riga ya bushe. Ya zo fitowa daga bayan ya taka kwalbar fiya-fiya, ya tsuguna ya dauka yana gogewa. Abban ya mika hannu ya karba yana cewa


'Meye wannan kuma?’


Saddikun ya amsa


'Ban sani ba, kamar wani magani ne ko me a ciki oh.’


Ya karasa goge kwalbar yana dubawa; wani dan abu ne a ciki kamar busasshiyar fata da allurai guda biyu a jiki sai kuma wani guntun farin tsumma ko takarda bai gane ba. Abun yayi masa kama da tsafi sannan kuma ya tuna masa abun da aka cire a gidan Aisha lokacin da ana shuka bishiya, don shima allurai ne a jikin abun. Ya tuna wancan warin don haka yaji tsoron bude kwalbar fiya-fiyan ya jefe a aljihunsa da niyyar sai ya kaiwa liman ko Malam Sama'ila sai a bude.


Yaya Murja tana kallonshi ta dauke kai, duk da bata fahimci menene abun ba amma dai ta ga kamar abun ya karawa Abban damuwa. Suka cigaba da tattara kayan suna duddubawa.


Abba da Saddiku suka kama katifar suka jingine bayan Yusra ta cire zanin gadon. Nan da nan suka kama kwance gadon. Katako ne mai nauyin gaske don haka da kyar suke kamawa suna jinginewa. Kan gadon yafi komai nauyi don haka sai da Suwaiba ta sa hannu ta bangaren Saddiku sannan suka cicciba suka jingine. Ta juyo ta dauki wata bakar robar da ta gani a bayan gadon, kafin ace wani abu ta bude tana mamaki don babu ko rubutuba jiki balle tace mai ne.


Tana budewa wani farin hayaki ya fito daga cikin robar ya kanannade yayi sama; Saddiku, Abba da Murja da Yusra duk suna tsaye suna kallo. Suka zaro ido kowa ya ja baya yayinda Suwaiban itama ta saki robara kasa ta ja baya tana fadin


'Wayyo Allah!’


Haka hayakin da ya fita daga robar ya nannade yayi sama suna kallo ya bace, suka yi cirko-cirko. Abban ya karasa ya daga robar a kasan ba tare da ya dauka ba. Wani abu ne a ciki kamar kwan agwagwa sai dai shi akwai rubutu a jiki. Suka dan matso suka zubawa abun ido. Abban ya fara karanto ayatul kursiyyu a fili ya tofawa wannan robar sannan ya ci gaba da jan ‘la haula wa la kuwwata illa billah’; yasa hannu ya zaro kwan a hankali. Babu nauyi kwata kwata, yana dubawa ya ga kwan ya tsage kuma babu komai a ciki; kamar bawon kwan ne kawai. Ya juya yana karanta rubutun da yake jikin bawon kwan; sunansa ne da sunan mahaifinsa da na mahaifiyarsu aka rubuta da jan rubutu. Sai kuma aka rubuta sunan Aisha da na iyayenta da bakin rubutu kuma aka sokeshi da jan rubutu.


Cikin sanyin murya Saddiku yayi tambayar da kowa yake son yi ya kasa


'Abba menene wannan din kamar abun aljannu?’


Ba tare da ya dauke idonsa daga kallon abun ba yace


'Ban sani ba Saddiku, amma dauko min wayata a falo tana chaji na kirawo Malam Liman Muji. Tunda ma abun ya fita a gidan kada muje ya cutar da wani.’


Nan da nan Saddiku ya fice.


Su Murja da Zahra duk sun kasa magana sai kallon-kallo kawai sukeyi suna zare idanu. Ba jimawa Saddiku ya dawo ya mikawa Abban wayar yana cewa


'Baba ma ya kirawoka ga missed calls nan har biyar.’


Yana karbar wayar ya kawar da missed calls din Yaya Bello ya lalubo lambar Malam Liman ya kirawo. Aka yi sa'a yana kusa don haka ba tare da bata lokaci ba ya ce gashi nan zuwa.
Daga su Murja har su Zahra duk jikinsu yayi sanyi don haka gaba daya suka hakura da aikin suka fara diban kayan da zasu fito da su suna fitowa dasu falon.


Kafin su gama Malam Liman ya bugo wayar Abba ya sanar dashi yana kasa, ya umarci Saddiku da ya shigo da shi. Ya sauko daga saman da sauri.


Yana zuwa bakin kofar falon kasan ya ci karo da Yaya Bello yana sallama a bakin kofar. Bayan ya amsa gaisuwarta yace


'Saddiku Ina Abban naka ne? Lafiya dai kuke gaba daya? Ina kannenka? Ina ta kiran wayar Abban baya dagawa.’


‘Yana nan, aiki mukeyi a dakin Mommy. Malam Liman ne yake jiransa a waje yace na shigo da shi, bari na kirawoshi sai nazo na kirawo Abban.'


Yaya Bello ya karasa shigewa falon yayinda Saddikun ya fice da sauri.


Jummai ta fito daga kicin da taji motsin Yaya Bellon, bayan ta gaisheshi tace


'Suna sama ma shi da su Hajiya Murja ne, bari na kawo maka ruwa.’


Kafin ya amsa ta koma kicin din.


Tana shigewa Saddiku suka shigo tare Malam Liman, bayan sun gaisa da Yaya Bellon Saddiku yace


'Cewa yayi ka hawo saman.’


'To bismillah.'


Ya bi bayansa.


Sadik din ya juya yacewa Yaya Bello


'Baba kazo muje saman Abban yana can.’


Ya mike gabobinsa babu kwari don ya zata wata lalura ce ta sami Abban wadda tasa ba zai iya saukowa ba zai ce a zo da mutum.


Suka bi bayan Saddiku suka haye saman.


Cirko-cirko suka tarar da su Abban a daki babu mai magana, yana ganin yayansa yace


'A'a! Yaya a ina ya samoka?’


'To na kasa nutsuwa ni din ma, sai waya nake maka baka dauka ba sai na zata wata matsalar ce a gidan.’


'Ta ba za a ce babu matsalar ba, ku karaso.’


Suka karasa ciki suka gaggaisa a tsattsaye. Abban ya nunawa Malam Liman robar wadda take ajiye a kasa da kuma kwan a kan murfin yayi masa bayani sannan kuma ya mika masa kwalbar fiya-fiya da ya jefe a aljihu. Suka tsuguna gaba daya Abban yana sake yi musu bayanin hayakin da ya fita daga cikin robar Liman yana dubawa.


Jimawa kadan yace


'Inna lillahi wa Inna ilaihi rajiun!’


Ya bi mutane dake dakin da kallo gaba daya sannan ya cewa Abban


'To ka san idan mutum ya mutu duk wata tashin-tashina barinta ake yi. Yanzu a nan waye bare wanda ba dan uwan ita marigayiya ba? Don ka ga idan da wanda ba zai rike mata sirri ba sai ya fita.’


Ya nuna su Yusra yace


'Wadannan dai yaranta ne ka san su, wannan yayana ne shi kadai gareni dan uwa, wadannan kuma yayarta ce da kanwarta uwa daya uba daya.’


Yaya Bello yace


'Bari na jiraku daga falo nan.’


Liman yace


'Ai ba ma sai ka fita ba ina ga duk nan amintattune, sai dai kawai zan bamu shawara duk abinda muka ji muka gani mu barshi a nan mu cigaba da yi mata addu'a.’


Duka suka amsa sannan yace


'Gaskiya wadannan abubuwan guda biyu da ka bani tsafi ne ko sihiri, hayakin da kuka ga ya fita ba zan yi mamaki ba idan aka ce aljani ne to amma ba zan sani ba tunda ban gani ba. Ko ma menene ya fitan bana jin zai tsaya nan kusa tunda kamar ya sami ‘yanci ne.’


Ya mikawa Abban karamin kyallen da ya zaro daga cikin kwalbar ya cigaba


'Ka ga wannan gutsure na na rigar wanda aka yiwa sihirin gashi nan. Sai a tattara wadannan tarkacen a kona sannan a binnesu tare da zancen, wadanda suka rigamu gidan gaskiya Allah ya yafe musu.’


Sukayi dif kamar ruwa ya cinyesu kowa da abinda yake tunani. Sai da Malam Liman ya gaji da shirun yace


'Kai Saddiku sai ka kwashi wannan ka kona ka binne shike nan a cigaba da addu'a.’


Abba yace


'Malam babu wata matsala idan an one din.’


'Babu wata matsala. Ai na riga na tofesu da ayoyin Allah kuma tunda me shi ta rasu ba zai yi tasiri ba. In ya so dai yara su karanta suratul bakara a gidan don a sami natsuwa gaba daya.’


Yayi musu sallama Abba da Yaya Bello suka bi bayansa don yi masa rakiya.


Suna fita Murja ta kalli Suwaiba tace


'Uhm! Ina ga sai mu tafi, ragowar kayan ma dawo. Ko kuma bari Abban ya dawo sai na tsaya mu kona wannan tarkace.’


Suwaiba tace


‘Allah ya kyauta.’
Suka fara hada kayansu don tafiya; gaba dayansu kowa zuciyarsa a jagule har Yusra wadda ta kasa magana. Nan falon saman suka zauna suna jiran Abban. Tunani kala-kala ne yake yawo a ran Yaya Murja; to yaushe Zahra ta fara tsafi? Ga shi ta mutu? Kuma ga dukkan alamu Abban take yiwa wanda gashi yanzu ya gani.


Haka suka zauna har Abban ya dawo saman suka yi masa sallama cike da jin nauyin abinda ‘yar uwarsu ta aikata suka fice cike da tsananin damuwa da mamaki. Godiya daya suke yiwa Allah da Liman yace kada a fita da zancen don haka ma suka fice ba tare da sun cewa Abban komai ba a kan zance.


Suna tafiya Abban ya koma dakin ya rufo kofa yayin da Yusra da Saddiku suka shige dakinsu.


UWAR SADDIKU


Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)


45


Su Yaya Murja suna fita daga gidan suka wuce gidanta don dama a nan zasu ajiye kayan da suka kwaso kafin su san abinda zasuyi da su. A dakinta suka zube a gajiye cike da damuwa. Kowa ya kasa magana saboda damuwa.


Jimawa kadan Suwaiba ta dubi Murja ta kirawo sunanta, sai dai kafin ta fadi abinda take son fada hawayen da take tarewa ya kwace. Itama Murjan ta kama share kwalla, sai da sukayi mai isarsu sannan Suwaiban ta goge fuska tace


'Yaya kin ga yanzu dole mu bar maganar Abban Saddiku ya auri Rahma, tunda na san mu kanmu kallonmu kawai yake yi. Wannan abun da Yaya Zahra tayi ai dole ya zata duka haka danginmu suke. Aishan kuma da muke kokarin mu kare yara daga fitnarta kinga ashe ba itace mai fitnar ba.’


Cikin tsananin damuwa tace


'Hmm! Suwaiba ai dole a bar wannan maganar tunda jiyan nan dama na yiwa Rahman maganar itama ta sakawa idonta toka tace ba zata aureshi ba kada ma mu soma maganar. Watakila ko ita ta san da wadannan abubuwan da Zahran take yi shi yasa taki shiga gidan.’


'Babu mamaki, amma dai ina mamakin yanda akayi Zahra ta zama haka. Kullum fa nusar da ita nakeyi yanzu dubi abubuwan da muka gani, da wanne ido zaka fuskanci ubangiji ka yi wannan aika-aikar?’


Nan suka dauki lokaci suna jimami da jajantawa, sai da aka fara kiran azahar sannan Suwaiba tayiwa Murja sallama ta tafi.


……..


Tunda Abba ya shiga dakin ya rufo kofa ya zauna a gefen gado ya zuba fuskarsa a tafukan hannunsa cikin damuwa. Tunani sun yiwa kwakwalwarsa yawa don haka bai ma san me yake tunani ba.


'Zahra.'


Ya kirawo sunanta a karo na babu iyaka cike da matsanancin mamaki.


To shi kuwa me yayi wa Zahra zata cutar da shi da Aisha? Me yayi zafi har ta barar da imaninta? To tun yaushe take wadannan abubuwan?


'Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un!’


Ya fada a fili yana goge fuska. So yake ma ya fitar da hawaye ko zai ji sanyi a ransa amma ko digon hawaye idonsa ya kasa fitarwa.


Lallai wadannan sune abubuwan da Aisha ta san ana yi mata har take jin ba zata zauna da Yusra ba. Yanzu haka Yusran ake turawa tana binne mata irin wadannan abubuwan shi ya sa tace ba zata zauna da ita ba; kuma bai ga laifinta ba a yanzu. Domin ko shine ya san halin Zahra to da tuni ya dade da rabuwa da ita.


Ya daga hannu sama kamar mai addu'a yace


'Allah ka hana yarana bin wannan hanyar da uwarsu ta bi, Allah ka shiryesu ka hana su shirka.’


Kwalla ta gangaro kan fuskarsa, ya sa hannunsa ya share.


Sai a lokacin ya samu ya hadiye malolon da ya tokare masa makogoro.


Yanzu wannan dabi'ar Zahra ta dora Yusra a kai? Lallai yana da aiki.
Zahra bata yi masa adalci ba, ta cutar da shi.


A take nadama ta rufe shi, bai taba nadamar auren Zahra ba kamar yanda yakeyi yanzu.


Yanzu ya zai yi da wannan matsalar?


Haka ya wuni a dakin yana ta tufka da warwara shi kadai, don ko masallaci bai fito ya je ba balle ya nemi abinci.


Yanda ya wuni cikin damuwa haka shima Saddikun ya wuni.


Itama Yusra haka ta wuni, sai dai ita damuwarta ba me yawa bace. A iya tsawon rayuwarta ta san kullum Mommy tana tsaye a kan nema musu kariya, wannan abubuwan da aka samu a dakin Mommy din ta san suna cikin wannan kariyar wanda Mommy din ta sanar da ita duk addu'oi ne don haka ita bata ma ga wani abun tashin hankali a ciki ba. Fatan ta daya Allah ya sa kada wata cutarwar ta samesu saboda wadannan abubuwan da aka kona.


—-----
Yana dakin har bayan karfe uku, sai wajen la'asar yunwa ta dameshi. Yana fitowa ya hango abincinsa a kan dining table don haka ya zauna ya ci. Yanda yaji gidan shiru ya san yaran sun tafi makaranta don haka yana gamawa ya sauko ya sami Jummai a tsakar gida ya tambayeta in Saddiku, ta sanar da shi Saddikun yace mata ya fita amma kafin magriba zai dawo. Yayi mata sallama ya fice ya nufi gidan Yaya Bello.


Ya san sai dare ya kamata suje gidan su Aisha, to amma zaman dakin ya isheshi. Gara ya bi Yayan gidan su tattauna ko ya samu zuciyarsa tayi sanyi.


Tun a farkon layin ya hangi Yaya Bello yana tsaye da ‘yan unguwa, yana wucewa shima Yayan yayi musu sallama yabi bayansa.
Yana yin parking Yayan ya karaso suka hadu, bayan sun gaisa suka wuce cikin gidan. Yaran da Ummansu duka basa nan sun tafi biki sai Muhammad kadai, bayan ya kawowa Abban ruwa ya koma dakinsa.


Sukayi shiru na dan lokaci, jimawa kadan Abban ya ajiye kofin ruwan da yake hannunsa yace


'Na kasa nutsuwa Yaya, ace ina zaune da mace shekaru masu yawa kowa yana kyautata mata zato ashe matsafiya ce ban sani ba?’


Yayi gyaran murya


'Gaskiya dai nima har yanzu ina mamaki; don ka ga da ace a lokacin tana raye an ce ka zabi daya ko ita ko Aisha to tabbas na san da mu da duk wani danginka zamu ce ka rabu da Aisha ka dauki Zahra, ashe itace bara-gurbin.’


Ya jijjiga kai


'Yanzu Yaya ya zan yi da Aisha? Wallahi ina sonta kuma bana jin a yanzu a shekaru na zan iya wani kara aure. Kuma a halin yanzu Aishan ita kadai ce na yarda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login