Showing 123001 words to 126000 words out of 166068 words
zauna, ta ja motar suka wuce.
Abban ne a kan gaba har suka hau benen da dakin da aka kwantar da Zahran yake, suna biye da shi sai da aka zo bakin kofa saboda ya san Rahma tana ciki ya ja baya yace duka su shige. Ummi ce ta bude kofar suka shige gaba daya.
Rahma da Yaya Murja suna zaune a kan tabarma daga gefe yayinda ita kuma take gefe guda yayinda ita kuma Zahran take kwance a kan gadon tana danna waya.
A hankali ta tashi ta gyara zamanta yayinda suka karasa suka tsattsaya a gefen gadon, ta dan muskuta Yusra ta dauki Sumayya ta dora mata a gefen gadon. Aisha ta karasa shiga dakin da sallama Abban yana biye da ita. Ta wuce ta zauna can daga kusa da Yaya Murja yayinda shi kuma Abban ya ja kujerar da take ajiye daga daya gefen ya zauna.
Ya gaida Yaya Murja da Rahma yayi musu ya mai jiki sannan ya mike ya karasa wajen Zahran ya tsaya a bayan yaran.
Itama Aishan suka gaisa da Rahma da Yaya Murja tayi musu yaai jiki, ta mikawa Yaya Murja kwandunan da suka zo dasu tayi musu bayani. Suka dan cigaba da hira Yaya Murja tana tamabayarta mutanen gidansu.
Bayan ya gama tambayar Zahra jikin nata ya juya yayi wa Yaya Murja sallama ya dubi Aisha yace
’15 minutes, ina jiranku a mota.’
Ya mika mata hannu kamar mai karbar wani abu, ta zura hannu a jakarta ta dauko mukullin motar ta saka masa a hannunsa ya juya ya fice bayan yayi wa su Yaya Murja sallama.
Bayan ya fita Aisha ta mike ta matsa kusa da gadon suka gaisa da Zahran sannan ta yi mata jaje tare da ya jiki. Da kyar take amsa mata tana ta faman harararta don haka itama ba tare da bata lokaci ba ta koma ta zauna.
Suna hira jefi-jefi da su Rahma tana kula da agogon wayarta, minti goma sha biyar suna cika ta yiwa Yaya Murja sallama ta dubi yaran tace
‘Rukayya ku zo muje 15 minutes din yayi kada mu bar Abba yana jira’
Ta fice.
Jimawa kadan yaran suka fice bayan Yaya Murja ta tasa keyarsu.
Su Zahra basu dade da fita ba Amina ta shigo, bayan sun gaisa Yaya Murja tayi musu sallama ta tashi yayinda Rahma ta bita don tayi mata rakiya.
Amina ta dubeta tace
‘Na ga mutuniyarki sai wani sheki takeyi tana ta yiwa miji iyayi, na ga ma itace take tuka motar saboda kauna.’
Ta ja tsaki
‘Hmm! Haka Yusra take gaya min ana ta soyayya a hanya. Ki barni kawai Amina! Yarinyar nan ta raina ni wallahi. Na tabbatar da hannunta a wannan haihuwar da nayi babu rai shine ta zo ta nuna min ta kwaci mijinta. Wallahi Amina sai nayi maganin yarinyar nan.’
‘Hmmm! Kinga dai yanzu ki kwantar da hankalinki ki sami lafiya, sai ki san yanda zakiyi ki tattaro kan kudi don kinga akwai wani malami da za a hadani da shi kwanan nan kuma an ce aikinsa babu wasa. Kin san ina ta fama da Abban Asiya ina so na dauki hutun aiki na bishi Abuja yana ta faman gocewa, zargin da nakeyi wata ya ajiye a can shi yasa ko da tsiya-tsiya sai na je.’
Suka cigaba da hirarrakinsu suna shawarar yanda za a yi a sami kudi aje wajen Malami, daga baya Rahma ta dawo don haka suka canza hirar.
___
Kwana daya Zahra ta kara a asibiti aka sallameta, suna dawowa gida Rahma tayi musu sallama ta koma gidansu.
Duk wani ban baki da ban hakuri likitocin sun yiwa Zahra shi domin likita ya tabbatar mata idan ta cigaba da zama da damuwa zata haifarwa kanta da hawan jini na din-din-din, sai dai ita bata ga yanda za ayi ta kwantar da hankalinta ba. Duk wata kulawa Abba yana bata sai dai har yanzu tana ji a jikinta cewa ya san abubuwan da ta shirya kallonta kawai yakeyi.
A hankali tana kara samun lafiya tana cigaba da tunanin hanyar da zata bi ta sami kudi. Bata son ta siyar da babbar saitin gwal dinta amma dai ta fara tunanin sayar da na yaran. Bata son ta tambayi Abba kudi domin bata ga fuska ba duk da komai yana yi mata kamar yanda ya saba sai dai kawai ita din ta kasa sakewa.
Haka dai rayuwarsu ta cigaba.
---------
Kwanci tashi har an kai wajen wata uku da haihuwar da Zahra tayi babu rai, basu samu sun je wajen boka ba saboda har yanzu mahaifiyar Amina a kwance take; domin kusan za a iya cewa ta zama sai dai a kwantar a tayar. Don haka babu halin Amina tayi nisa musamman da yake tana matukar kaunar mahaifiyar tata. Haka ta hakura tana kallo mijin nata yana can Abuja ga shi Asiya tana kawo mata rahotannin cewa yana tare da matan banza a can din amma babu yanda zata yi don ya ma hanata zuwa Abujan gaba daya.
Hankalin Abba ya dawo jikinsa don haka ya nemi kudi ya sake fara business din sa; sai dai wannan karon duk wani abu da zai yi na harkar business din sai idan yana gidan Aisha ne yake yi domin ko wayar abokan kasuwancin nasa baya amsawa idan yana gidan Zahra.
Haka kowa ya cigaba da rayuwarsa.
__
Tun tuni aka samarwa Saddiku da Yusra admission a jami’ar Maryam Abacha American University wato MAAUN; Yusra tana karantar Business Administration yayinda Saddiku yake karantar Accounting. Da yake kwanci tashi babu wahala gashi a halin yanzu har suna zana jarrabawar zango na farko wato zasu gama level 1 su shiga level 2.
Tunda suka fara jarrabawa Saddiku yake gayawa Mommy ta karbar masa kudi a wajen Abba naira dubu hamsin zasu hada suyi end of session party. Sai kaucewa zancen takeyi saboda ta san yanzu bata da dama a wajen Abban yayin da shi kuma Saddikun yake sake dagewa da yi mata naci. Haka dole ya sakata tayi masa alkawarin ko da Abban bai bashi ba ita zata bashi ko da bai kai dubu hamsin din ba.
Kudaden da take hadawa domin suje wajen boka su kadai ne a account dinta domin ta hada kusan dubu dari biyu; garwar motarta da akayi accident wadda take ajiye a tsakar gida ita take jira ta sami mai siya ta hada kudin sai suje.
Wanna magiyar da Saddiku yake mata a kan kudin party ma ya kara mata kaimi wajen ganin ta dawo da hankalin Abban kansu, bata son ganin yaranta a cikin damuwa musamman Saddikun.
---------
A dakinta ya sameta tana zaune a kan dadduma ta idar da sallar isha’i, bayan ta amsa sallamarsa ya wuce ya zauna a gabanta kamar mai daukar karatu. Ta dan kare masa kallo; zuciyarta tana so ta yarda lallai Saddiku yana shaye shaye; to amma bata ga lebensa da hannayensa suna yin baki ba irin na 'yan wiwi. Abinda bata gane ba shine shi din ba hayaki yake sha ba kwayoyi yake sha masu tsada da kuma dauke hankali nan take. Ya kwantar da kai yace
‘Mommy baki turo min 50k din ba, gobe fa zamuyi final paper kuma ranar Saturday zamuyi party din.’
Tunda ya zauna dama ta san abinda zai tambaya kenan, ta jijjiga kai tana murmushi
‘Ku yanzu ba za ma ku iya tsayawa ku ga result ba kafin kuyi party din idan fa ba ku ci jarrabawar ba.’
‘Haba Mommy, ai duk mun ci. Kin san a ajin wasu foreigners ne don haka ana gama exam kowa zai tafi gida shi yasa zamuyi party din. Kusan kowa ma ya biya mu uku ake jira. Don Allah Mommy ki karba min kudin nan kinga ina cikin organizers fa.’
Suka yi shiru na dan lokaci, jimawa kadan tace
‘Abbanku yace bashi da kudi kuma ka san idan nace masa party zakuyi ma ba zai bari kaje ba, amma idan kana son 30k ni zan turo maka zuwa gobe idan kuma tayi kadan to sai dai kai kaje ka tambayi Abban.’
Da sauri yace
‘A’a Mommy please ki turo 30k din kawai.’
Suka dan taba hira yayi mata sallama ya fice.
Yana fatan idan ta bashi dubu talatin din daga baya sai ya san yanda zai yi ya takureta ta kara masa ashirin din.
Party suka shirya su uku shi da abokansa, ‘yan ajinsu na Jami’a ma basu san da wannan party din ba. Ya riga yayi alkawarin dubu dari biyu zai bayar gudummuwar party din. Ya riga ya yagi mafi yawan kudin a wajen Abban ta hanyar karyar abubuwan da aka ce su saya a makarantar, a halin yanzu dubu hamsin din kawai yake bukata ya gama hada kudin su je suyi party dinsu.
………..
Babu yanda ta iya haka ta turawa Saddiku dubu talatin daga kudin da take ta faman tarawa, sai dai duk nacinsa ta ki ta kara masa wasu kudin; ta dai gaya masa ya samo makanike ya sayi gawar motarta da yayi accident idan an biyata sai ta kara masa.
Haka ya samo har mutum biyu, sai dai babu wanda ya taya motar a kan dubu dari ma. Domin duk cewa sukeyi ba zata moru ba don har injinta ma ya tashi daga aiki. Haka ta hakura ta sayarwa da na karshen a kan naira dubu sittin da biyar. Wanda a hakan ma yace sai dai su bashi sati biyu zai kawo kudin sai ya dauki motar.
Sai bayan ya tafi Saddiku ya bishi ba da sanin Mommy ba ya karbe naira dubu goma sha biyar a kan ya kai cikon ya dauko motar.
…………..
Tun bayan la’asar ya shirya yayiwa Mommy sallama. Ya dauki motarta ya tafi party; motar da tana kallo yanzu ta zama ta Saddiku tunda da tana kokarin ta sa Abba ya saya masa tashi motar amma yanzu ta san bata da wannan damar.
Kamar yanda Abba ya saba bayan magriba ya dawo gidan. A gidan Aisha zai kwana don haka gidan Zahra ya sauka; bayan ya huta suka dan taba hira ita da shi da yaran. Sai da ya dawo daga sallar isha’i sannan yayi mata sallama ya tafi. Kafin ya fita kuma ya sanar da ita idan goman dare tayi Saddiku bai dawo ba tayi masa waya.
Ta san yace mata sun tafi party don haka bata sa rai zai dawo kafin karfe goma na dare ba, don haka wajen tara da rabi ta kulle gidan ta turawa Saddiku message cewa idan ya dawo yayi mata waya tunda ba ciki zai shigo ba a boys quarters dakinsa yake.
Tunda ta kintsa ta kwanta bata farka ba sai karfe biyu na dare; agogonta ta fara dubawa a wayarta taga lokaci.
Nan take ta dannawa Saddiku kira, har wayar ta tsinke bai dauka ba sai kawai tayi zaton ya dawo bacci ne ya kwasheshi tunda ya kwaso gajiya don haka itama sai ta gyara kwanciyarta ta cigaba da bacci.
__
Tana idar da sallar asuba ta sauko ta bude kofa ta leko tsakar gidan, so takeyi ta tabbatar Saddiku ya dawo gidan jiya. Ga mamakinta babu motarta a tsakar gidan wanda hakan yake nufin Saddiku bai kwana a gidan ba. Ta fito ta tsaya a kan baranda ta kwalawa Malam Sado kira, da gudu ya taho yana rike da carbinsa da yake wiridi. Bayan ya gaisheta ta amsa tace masa
‘Malam Sado Saddiku bai dawo gidan nan ba jiya da daddare?’
Ya shafa kai yace
‘Bai dawo ba Hajiya sai dai ko nan gaba.’
Ta koma cikin gidan jikinta a sanyaye.
A kan dining table din kasan ta zauna ta lalubo lambarsa a waya ta sake kira, ringing kawai wayar take yi Amma ba a dauka ba. Hankalinta ya kai kololuwar tashi da ta tuno haka yayi mata wancan lokacin da yayi accident. Nan da nan idanuwanta suka cicciko da kwalla; da sauri ta fara laluben lambar wayar Abbansa. Sai da ta zo kan lambar tasa sai kuma ta tsaya ta kasa kiransa; to yanzu idan ta kirawo shi me zata ce masa? Ce mata yayi idan goma tayi Saddiku bai dawo ba ta kirawoshi amma bata yi hakan ba sai yanzu da safe ta kirawoshi tace masa me? To idan fa accident Saddikun ya sake yi
‘Inna lillahi wa Inna ilaihi rajiun.’
Ta fada a fili yayinda idonta ya cicciko da kwalla. Gashi bata san abokansa ba don haka ma bata da lambar ko daya daga cikinsu. Ta tashi jikinta babu kwari ta koma saman, ta zo daidai kofar dakin su Yusra taji motsinsu. Nan dabara ta fado mata; ta karasa ta tura kofar ta kirawo Yusra. A dakin Yusran ta sameta, bayan ta amsa gaisuwar ta tace
‘Yusra yayanki bai dawo gidan nan ba jiya gashi kuma ina ta kiran wayarsa bai dauka ba, ko kina da lambar abokansa da suke party din tare na kirawosu muji?’
Da mamaki Yusran tace
‘Mommy party sukeyi?’
Itama mommy din mamakinta ya karu
‘Au baki sani ba? Yace min end of year party zasu yi shi da ‘yan ajinsu jiya da daddare.’
‘To gaskiya Mommy ni ban sani ba, kuma a abokansa mutum daya nake da lambarsa. Bari na kirawo shi muji.’
Nan ta koma daki ta dauko wayarta ta dawo wajen Mommy din. Ta lalubo lambar Babs wanda dan ajin su Saddiku ne, shima ta sami lambarsa ne saboda yana sonta duk da ita din bata sauraronsa.
Sai da ta zauna a kusa da Mommy sannan ta danna masa kira ta sa wayar a loudspeaker. Yana dauka yace
‘Today is going to be a good day tunda ke kika fara kirana Babe, to ya kike?’
Tace
‘Uhm! Lafiya. Ka san wani abu? Ya Sadik nake nema ka san tun jiya da daddare bai dawo gida ba yace wai ‘yan class dinku suna end of year party shine nake son naji me ya hanashi dawowa gashi Mommy tana nemansa.’
Da mamaki a muryarsa yace
‘Party? Gaskiya ba dai ‘yan class din mu ba sai dai ko wasu friends din nasa, don gaskiya duk mun koma gida ko nima kin ganni a KD.’
Sukayi shiru na dan lokaci, jima kadan yace
‘Amma bari na tambayar miki su Bigi duk da dai na san ba da su bane amma dai idan har guys din mu ne suka shirya party din to lallai Bigi zai sani.’
Sukayi sallama bayan ya sanar da ita idan ya ji wani abu zai kirawota.
Ta dubi Mommy tace
‘Kin ji Mommy!’
Cike da damuwa tace
‘Hmm! Na ji Yusra. Ni haka yace min da 'yan class dinsu don sai da na bashi 20k sannan kuma ya zagaya ya karbe kudin da aka sayar da garwar tsohuwar motata ba tare da ya gaya min ba kuma cewa yayi duk a kan party din ne. To ina ya tafi?’
Jimawa kadan ta sallami Yusran don taje ta shirya mata yara su tafi tahfiz.
Haka tayi ta faman jan kafa cikin matsananciyar damuwa har wajen karfe goma saura.
Wajen karfe goma Abban ya shigo don ya dubasu ita da Yaran. Bayan ya amsa gaisuwar Yusra a falon kasa ya haye saman. A dakinta ya sameta tana kashingide a gefen gado, bayan sun gaisa ya zauna a gefen gadon kusa da kafafunta yace
‘Ya dai? Jikin ko garin na ganki a kwance.’
Ta tashi ta gyara zama sannan ta bashi amsa
‘Uhm, babu ko daya. Hutawa dai nake yi kafin ‘yan gidan su dawo.’
‘Saddiku har ya fice ko? Ai sun gama exam tunda ke bakya hawa motar yau in ya dawo ya bani mukullin motar ya huta yawon ya isa haka, da anyi magana yace zasu je lecture ko kuma zasu hadu suyi karatu.’
Ta dan muskuta
‘Um nima haka na gani, bari ya dawo sai na karbi mukullin motar na boye saboda in zan fita.’
Suka dan taba hira daga baya yayi mata sallama ya fita; yana mamakin Zahra! Tun tuni yake so ya karbe mukullin mota daga hannun Saddiku amma ta hanashi sai tace ita zata kwace kuma bata iyawa. Lokuta da dama yana mamakita, yanda har yanzu ta kasa gane cewa bata tarbiyyar Saddiku takeyi. Shi yasa har yanzu bai gayamata cewa ba zai biyawa Saddiku kudin registration ba sai ya je makarantar da kansa ya ga result dinsu.
Ta kasa gayawa Abba cewa bata ga Saddiku ba kuma ta rasa wanda zata gayawa gashi har sha biyu saura, ta dai yanke shawarar idan aka yi kiran azahar bata sameshi ba zata gayawa Abbansa.
Karfe Sha biyu da kwata wayarta tayi kara, ta dauki wayar kamar wadda aka yiwa dole sai kuma ta ga sunan Saddiku, sai da zuciyarta ta nemi tsayawa lokacin da ta kara wayar a kunnenta. Kafin tayi magana aka ce
‘Hello.’
Ba Saddiku bane yake magana, haka dai ta daure ta amsa. Bayan mai maganar ya gaisheta yace
‘Don Allah ina magana da mahaifiyar Sadik Yusuf ne?’
Cikin hanzari tace
‘Eh, ina Sadik din?’
‘Um gamu nan da su a asibitin Malam Aminu Kano emergency shi da abokansa, suma sukayi tun jiya a wajen party da suka sha kwaya, har yanzu basu farfado ba.’
‘To gamu nan zuwa.’
Ta saki wayar a kan cinyarta daidai lokacin da hawaye ya wanke mata fuska.
Saddiku ya sha kwaya tun jiya ya suma? Yanzu me zata cewa Abbansu, bayan ta gama gaya masa da safen nan Saddiku ya fita.
‘Inna lillahi wa Inna ilaihi rajiun!’
Ta mike tsaye, wayar da take ajiye a cinyarta ta subuce ta fadi kasa ta dauke wayar ta ajiye a kan gadon. Ta karasa gaban wardrobe tana share hawaye ta dauko hijabi ta saka sanna ta dauko jakarta a kan mudubi ta dawo ta dauki wayar ta jefa a ciki ta nufi ficewa daga dakin.
Har ta kama hannun kofar sai kuma ta tsaya ta kasa murdawa; to ina zata? Babu mota a gidan kuma Malam Ali baya nan, shi kuma Abban da yake ba a nan ya kwana ba bata ma