Showing 60001 words to 63000 words out of 166068 words

Chapter 21 - UWAR SADIKU COMPLT BY SAKINA YAZID.txt

11 Jul 2024

25406

yanzu wanne za ayi?’

Nan ta koro masa bayani daga karshe tace

‘Gaskiya Malam ni dai so nake a rabasu kawai, auren ya rabu muyi zamanmu ni da shi.’

Malam Hatimu ya dubi yaron Malam yace

‘Ka ji bayani.’

Ya gyada kai ya mike ya dauko wata tsummar fata a nannade. Ya dawo ya zauna a gaban Malam ya kwance fatar ya shimfida, yashi ne mai laushin gaske a kan fatar, ya gyara mata zama ya sake baza yashin. Ya rufe ido ya fuskanci sama yayi wani karatu wanda duka basa ji saidai suna ganin motsin bakinsa. Jimawa kadan ya sauke fuskarsa yayi busa a kan yashin a hankali. Ya sa yatsansa manuniya yayi digo guda uku a kan yashin ya dauke hannunsa ya zubawa yashin ido.

A take aka fara jan layi daga kan digon nan guda uku; ba shi yake jan layi ba kuma basu ga alamar akwai wani wanda yake jan layi ba.

Tun kafin layikan suyi nisa aka daina jan daya, sai guda biyun aka cigaba da ja har aka kai karshen fatar aka dire kasa har zuwa inda birbishin yashin ya kare.
Yaron Malam ya dubi Malam Hatimu yace

‘Ka gani Malam, Yusufa da Aisha tafiyarsu mai nisan gaske ce. Ko da zamu iya raba auren nan to sai an yi aiki da gaske wanda yake butara lokaci don sai dai na kaiwa Malam na gabas, kuma abun zai dauki akalla watanni takwas; amma komai fitnarsu za a rabasu.’

Malam Hatimu ya dubi Zahra yace

‘Kin ji ko Hajiya.’

Ta kara zare ido ta dubi Amina suka yi shiru na dan lokaci. Jim kadan tace

‘Malam to yanzu babu wani abun da za a iya yi a kai? Ni dai ko basu rabu ba ina so ya daina kulata, ta zauna a matarsa amma ya kasa nutsuwa da ita sai ya zo wajena.’

Malam Hatimu ya dubi yaron Malam yace

‘Kaji Yaron Malam.’

‘Wannan mai sauki me Malam, in dai da kayan aiki wannan ba zai dauki sati biyu ba ma an gama in dai sunyi abinda muka ce da kanshi zai gujeta.’

Zahra tace

‘Hakan ma yayi Malam, in ya so wancan babban aikin shima sai a fara tanadinsa don gaskiya zan fi so a rabasu.’
Yaron Malam ya matsa kusa da Malam sukayi kus-kus, Malam ya dubeta yace

‘Naira dubu dari biyu shine kudin aikinki Hajiya, da zarar kin kawo za a fara aiki.’

Ta dubi Amina wadda kudin suke jakarta, nan take ta zaro kudi suka kirga dubu dari biyu suka ajiye a gaban Malam.

Yaron Malam ya dauka ya kirga, bayan ya gama kirgawa ya mayar ya ajiye sannan ya dubi Malam yace

‘Hakane Malam, a daren yau za a fara aiki idan an gama sai ayi musu waya su zo su karba.’

Suka amsa tare da yiwa Malam sallama suka kamo hanya.




UWAR SADDIKU


Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)


22

Duk da Aisha tace ta hakura ba fushi takeyi da shi ba amma shi dai bai gamsu ba, yana ganin kamar har yanzu bata huce ba don taki sakewa da shi.

Ya santa da son ice cream don haka ranar da zai koma kwananta yana idar da sallar isha’i ya tafi neman ice cream. Saida ya fara tsayawa a Green Park ya siyo gasasshen kifi da chips irin wanda take so sannan ya siyo ice cream din ya dawo.

A bakin gate din gidan Zahra yayi parking ya fitar da nasu ita da Yara ya kai musu, bayan ya fito ya ja motar ya wuce gidan Aishan.

Tana kwance a falo a kan doguwar kujera ya shiga, bayan ya amsa sannu da zuwa ta ya wuce ya ajiye ledodin a kan dining table, ya dawo ya zauna a kusa da ita yana duban fuskarta. Yace

‘Yaya dai? Jikin ko garin?’

Tayi murmushi

‘Babu daya, kwanciya dai nayi kawai ashe bacci ya daukeni don ban ma san sun kawo wuta ba.’

‘Kinyi abincin dare?’

‘Eh, nayi tuwo miyar kuka.’

‘Yauwa sai a rufe mana shi mayi dumame don ga kifi da chips na siyo, harda ice cream.’

Tayi murmushi tace

‘Ai kuwa ka taimaka min don wallahi kwadayi nake ji kamar naci babu.’

Yayi dariya ya mike yana fadin

‘To sai ki tashi ki fara gashi nan, ni bari na canzo kaya.’

Ya shige daki, ita kuma ta karasa gaba dining table din ta duba kayan da ya siyo.

Ta shiga kicin ta dauko babban faranti ta juye musu kifin gaba daya da chips din kamar yanda suka saba, ta dauko ta dawo da shi tsakiyar falon kan kafet din ta ajiye musu; don in ya siyo irin wannan cimar basa zama a table a kasa ake bajewa. Bayan ta ajiye ta dauko ice cream din roba daya ta zauna ta fara sha.

Ya shigo falon da sallama ya karasa ya zauna a gaban tray din yana fadin

‘Ice cream din ai zai fi dadi idan kika gama cin kifin sarkin shan sanyi.’

Tace

‘Ka fara ci gani nan zuwa.’

Saida ya gaji ya fara cin kifin sannan ta ajiye robar ice cream din ta sauko, ta zauna a gaban farantin sai kuma ta dube shi tace

‘Wallahi kamar ma ba zan ci kifin ba, karninsa hawa kaina yake babu dadi.’

Da mamaki ya dubeta

‘Haba dai, ai ko yaya ne kya ci. Don ke fa na siyo kifin nan kuma kice ba zaki ci ba.’

‘Ba zaka gane ba.’

Ta fada tana kawar da kai.

Ya yago tsokar kifin ya nade yankan dankali guda biyu a ciki ya dora yankan albasa a kai ya nufo bakinta yana fadin

‘Naga kwana biyu laziness ya miki yawa bari kawai na baki a baki ki huta.’

Tana dariya ta bude bakin ya saka mata ba don tana so ba sai don bata so yaga kamar wani abune ya sa bata son ci don ta san duk cikin neman shiri ne kuma ita abun ya wuce a wajenta.

Da kyar ta hadiye lomar kifin nan, tana hadiyewa amai ya taso mata. Nan take ta mike ta fada bandaki da yake cikin falon, ba tare da bata lokaci ba ya bi bayanta. A gaban toilet ta tsuguna tayi ta amai yana mata sannu; har saida ta amayar da duk wani abu da yake cikinta. Tana mikewa zata fito daga bandakin kuma jiri ya fara dibanta, don haka nan da nan ya riketa suka dawo falo ya zaunar da ita.

‘Sannu Aisha, baki da lafiya ne ko yau kifin karni yake da yawa haka?’

A jigace tayi murmushi tace

‘Bana jin dadi dama kwana biyun nan jiri yana dan damuna.’

Duk yanda ta so ya kyaleta ta kwanta ki yayi saida ta tashi a daren suka tafi asibiti. Asibitin da yake zuwa nan ya kaita kuma da yake na kudine suna zuwa aka samu likita ya dubata.

Nan take aka tabbatar masa da Aisha tana dauke da ciki sati hudu, sai dai likita yace lallai ta dinga cin abinci kuma tana shan ruwa don yunwa ce take galabaitar da ita.

Tun a hanya yake tamabayarta ko da akwai wani abu da take son ci tace tuwo take so, don haka suna dawowa gidan ya zuba mata tuwon da ta dafa ya hada mata shayi ya sata a gaba saida taci. Bayan ya kwashe kwanukan ya dawo ya zauna ya dubeta yace

‘Sannu, ina jin ma dai wannan ‘yan biyu ne shi yasa ya zo da karfinsa.’
Ta harareshi ta bude baki a jigace tace

‘Tunda ba kai zaka haihu ba ai dole kace haka.’

Haka ya kare kwana biyun nan cikin tattalin Aisha, sosai kuma taji kwarin jikinta tunda baya barinta da yunwa. Sata yake a gaba duk mitarta sai taci abinci don yana ce mata yanzu haka wancan cikin ma yana tafiya Saudiya ta fara zama da yunwa shi yasa cikin ya zube.
………

Ko da ya dawo kwanan Zahra ma haka ya cigaba da zarya wajen Aisha, tun bai gaya mata ba har dai ya gaji da yanda take masa kallon zargi ya sanar da ita Aishan ce bata da lafiya. Tun daga wannan lokacin ta saka Rukayya a gaba da tambayoyi har saida ta gane ciki ne da ita.

Tana samun wannan tabbacin ta kirawo Malam ta sanar dashi; domin bata so Aisha ta haihu ko sau daya tunda akwai yiwuwar ta haifi namiji. Ita kuma yanda ta cika gidan da yara mata ba zata taba bari haka ta kasance ma. Auren Aishan ma da take fatan nan da wani lokaci ta kawo karshensa kuma bata so a fita a bar mata wani yaro don haka ma gara kawai kada Aishan ta haihu.

A nan Malam yayi mata alkawarin cewa Aisha bazata haifi wannan cikin ba amma dai ta bari zuwa lokacin da za a gama aikinta wanda akeyi yanzu sannan sai a san yanda za ayi da cikin.

Sai a lokacin ta samu natsuwa ta cigaba da harkokinta, duk wata rawar kai da Abban yakeyi ta daina damunta don ta san da an gama mata aiki gidan Aishan zai gagareshi shiga kamar yanda Malam ya gaya mata.
……….

Ranar da suka cika sati biyu da zuwa gaya Malam ya kirawota ya sanar da ita an gama aiki don haka ta zo ko ta turo a karba. Nan da nan ta kirawo Amina domin ita take so ta je ta karbo mata. Bayan ta gama yiwa Aminan bayani tace

‘Yanzu ya za ayi kawata, bana son tura wani ayi min wasa da aiken nan kuma wallahi ba lallai na samu ya barni komawa Gaya ba kwanan nan.’

Aminan tace

‘Kinga ma ni wallahi motata ta sami matsala, naira dubu hamsin makanike yake nema a wajena ta gagareni shi yasa ma kwana biyu bana fita da motar.’

‘kai kwata.’

‘Allah, kuma kinga ba zan iya zuwa Gaya a motar haya ba, ko kece ma zaki ba zan raka ki ba wallahi in dai a motar haya ne.’

Sukayi shiru na dan lokaci kowa da abinda yake tunani. Ragowar kudin Zahra ne a hannun Aminan wajen Naira dubu dari da sittin da tace ta cigaba da ajiye mata su zata hada na daya babban aikin a wajenta. Ta riga ta kashe kudin gaba daya don haka take neman hanyar da zata bi ba sai ta biya ba. Zahran ce ta katse mata tunani

‘To kawata ki dauka mana a cikin ragowar kudin nan, ko nawane ki dauka in dai za a samu a gyara motar zuwa gobe ki sami damar zuwa.’

Da fara’arta ta amsa

‘Ai kuwa nagode, yanzu zan kirawo makanike yaje gida ya dauki motar in sha Allah zaki jini idan na dawo.’

Sukayi sallama kowacce cikin walwala.
…………

Washegari sai can bayan la’asar sannan Amina ta kirawo Zahra ta sanar da ita ta dawo kuma yanzu zata zarto ta kai mata.
A bakar leda irin ta VIVA ta shiga gidan da sakon, nan da nan Mommy ta mikawa Jummai Sumayya suka shige dakin baki na nan kasa suk kullo kofa.

Suna zama Aminan tace

‘Kawata kin taro match, akwai aiki fa.’

Ta zaro ido

‘Allah kawata bana jin komai idan bukata zata biya, kinga kuwa yanda matar nan take kokarin mayar da ni kalar kwatance? Ai komai ma zan iya yi.’

Ta zura hannu a ledar ta zaro wata karamar farar roba irin ta man shafawa ta mika mata, ta bude tana kallo ita kuma tana yi mata bayani.

‘Yaron Malam yace wannan abun sunanshi kwarjini, kuma sai da kara masa dubu talatin ya bayar. Yace idan kika kusa sauke abincinsa zaki saka a ciki, narkewa yake kamar kitse kuma bashi da wari. An yi sa ne musamman da sunanki a jiki, in dai yaci wannan ba zai sake yi miki musu ba duk abinda kike so shi zai yi.’

Ta jijjiga kai cike da farin ciki ta mayar ta rufe tana fadin

‘Ina kuma babban?’

Amina ta sake zura hannu cikin ledar ta fito da wata buta irin ta alwala, amma da bakin karfe aka yi ta. Ta mika mata tana fadin
‘Kada ki bude don Malam yace azabar wari gareshi. Shi kuma binnewa zakiyi a tsakar gidanta, yace in dai kika binne wannan a gidan da take to ko yaje ba zai iya zama ba balle ayi wata mu’amalar aure. Yana shiga zai fito.’

Ta janyo ledra ta mayar da butar, ta dubi Amina ta dafa hannunta tace
‘Na gode kawata, Allah ya bar zumunci. Kin nuna min kauna kawata wallahi baki san yanda naji dadi ba.’

‘Babu komai ai yiwa kaine.’

Cikin damuwa Zahran tace

‘Yanzu inda matsalar take yanda za ayi na sami wanda zai shiga gidan ya binne min wannan abun, don kin san nifa ban taba shiga ba don ba zan iya kayan takaici ba.’

Sukayi shiru na dan lokaci kowa yana tunanin yanda za ayi. Jimawa kadan Aminan tace

‘Kinga tunda shi yana da mukullin ki faki ido ki dauki hotonsa yau da daddarem nan in ya so sai ki turo min hoton ni kuma zan sa a samo me kama da shi a kawo miki zuwa gobe da safe. Jibi da safe sai ki faki idonsa ki zare na wajensa ki musanya masa don kar ya gane, tunda tana zuwa aiki yaron da zai kawo miki zai jiri in ya so da zarar Abban ya fita sai kawai ki bashi yaje ya bude gate ya shiga ya nemi waje can gefe daya ya binne. Yana dawowa tunda wajenki yake fara zuwa sai ki yi sauri ki mayar masa da mukullin.’

Ta mika mata hannu suka tafa

‘kawata kin san kan tsiya wallahi, gaskiya ban ma san irin godiyar da zan yi miki ba. In Sha Allahu yana dawowa zan turo miki hoton.’

Nan da nan suka gama sukayi sallama Aminan ta kama hanya saboda magriba ta kusa, tana tafe tana jin dadin ribar dubu talatin din da ta ci. Yanzu kudin Zahra saura dubu saba’in kenan a hannunta kuma su din ma cinyesu zata yi.

--------

Yanda Abban yake kula da ita ya sa laulayin yana yi mata sauki, wani abun har da gangan ma yi take yana biye mata sai kace wanda ba a taba yiwa haihuwa ba. Ya na yawan gaya mata yana sonta shi yasa yake so ta haifa masa yara masu kama da ita kuma masu irin dabi’arta.

Tun shekarar da ta wuce taso tayi masa bikin zagayowar ranar haihuwa; duk da ba kowa zata gayyato ba iya su biyu kawai; sai kuma ya zama waccan shekarar bata sami dama ba a daidai lokacin. Don haka ta shiryawa wannan shekarar duk da laulayin nan yayi mata bazata.

Tun saura kwana biyu ranar ta tanadi duk wasu abubuwa da take bukata wadanda zata shirya masa abinci.


Ranar ta kama ranar Talata sannan kuma ba kwananta ba don haka haka dai ta shirya ta fice wajen aiki da niyyar idan ta dawo sai ta zo ta fara shiri. Batayi niyyar rikeshi ba don haka ta shirya idan ma abun zai zama damuwa tunda ba kwananta bane to idan ya shigo ya kwasa yaje can gidan Zahra din yaci. Ita dai kawai tana so ta burgeshi a ranar.

Bata gane an shiga gidan ba data dawo daga aiki domin yaron da Amina ta turowa Zahran irin yaran nan ne na unguwa da suka saba haura gidajen mutane suna yin sata. Yanda suka tsara masa haka yayi kuma kafin ya fito saida ya tabbatar ya kawar da duk wata alama da zata sa a zargi wani abu. Inda ya binne abun kuwa ma tsaf ya baje wajen kuma da yake baya ne daga nesa kadan da tagar dakin maigidan babu ma wanda zai gane.

Don haka tana dawowa daga aiki ta fada kicin; ta gasa cake dinta dan karamin don haka kwalliya kawai tayi masa ta mayar da shi fridge, ta gasa kaza gashin larabawa sannan ta hada masa lafiyayyaen salad da kunun aya. Ta siyo masa agogo mai matukar kyau da turare mai i dankaren tsada ta hada ta ninke a takarda mai kyalli ta ajiye masa a kan mudubi tare da wata karamar farar takarda da aka rubuta

“Happy Birthday My Love”

Idan ba kwananta bane sai an idar da sallar Isha’i yake shigowa, in ya gama hirarsa shine in ya koma can sai ya dawo mata da Rukayya. Don haka tana idar da sallar Magriba ta fada wanka, doguwar riga kawai tasa irin ta zaman gida sai turaruka da ta feshe jikinta da su. Duk da kamshin da gidan yake sai da ta kawo turarukan wuta masu dadin kamshi ta kara kunnawa domin so take ya ji dadi kuma ya tafi kwana biyun nan da kewarta.
Nan da nan gidan ya dau kamshi ga sanyi, Kuma da yake da akwai wuta sai abun ya kara armashi.

Kamar yanda ta zata kuwa ana idar da sallar isha’i ya shigo gidan.
Da sallama ya shigo kafin ya karaso ciki ta mike ta tareshi kamar yanda ta saba, ta fada jikinsa tana fadin

‘Sannu da zuwa.’

Dif walwalar fuskarsa ta dauke, sabanin da da in ta rungumeshi yake riketa, sai ya dan cireta daga jikinsa yana karewa gidan kallo. Ta dan matsa gefe tana kallonsa cikin damuwa, tace

‘Akwai wata matsala ne Yallabai?’

Cikin yatsina fuska yana waige-waige yace

‘Wani wari nake ji wallahi kuma a cikin gidan nan ne, ko kinyi amfani da wani abun ne me wari?’

Mamakinta ya karu, ya wuceta ya zauna a kujerar zaman mutum daya yayinda tabi bayansa tana fadin

‘Wari ko dai kamshi?’

‘A’a, wari ne mai karfi wallahi don har kaina ya fara ciwo.’

Ta karaso ta zauna a kusa da shi, tana zama ya mike kamar wanda aka tsikara. Ya dubeta yace

‘Kuma babu abinda kika shafa a jikinki ko na magani.’

‘Babu.’

Ya fara karewa gidan kallo yana dafe goshi, tana tsaye tana kallonsa tana mamakin da ya fara komawa tsoro. Ya dan kara matsawa daga kusa da ita yace

‘Bari na tafi kaina har ya fara ciwo, dama zuwa nayi nayi miki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login