Showing 36001 words to 39000 words out of 166068 words
rasu tun yaronta yana karamin kuma bata sake aure ba shi yasa duk irin wadannan abubuwan ita ake kira.
Tace
‘Rahama kin san kuwa nayi scanning an ce min namiji zan haifa, amma kinga ikon Allah mace na haifa.’
Tayi ‘yar dariya tace
‘Um, ai wallahi Anti abun fa na Allah ne dama likitocin ma lalube suke a duhu abinda Allah ya boye ai mutum ba zai iya gani ba.’
‘Hhhh! Kin san da ace ba ni kadai ce a dakin haihuwar nan ba Allah cewa zanyi canza min suka yi.’
Ta kyalkyale da dariya
‘Lallai Anti, kuma kinga gata nan kamar ‘yayanki don wannan sak yanda kika san Sadiku yana jariri.’
‘Hmmm!’
Ta yarda mace ta haifa kuma tana kaunar yarinyar amma dai tabbas ta saka ran haihuwar namiji, don haka ne ma ya saka komai kayan yara maza ta siya.
Haka dai ta yi ta wasi-wasi har bacci ya kwasheta.
……..
Da wuri Aisha ta tashi tunda ta san Zahra bata nan, ta soya doya da kwai yanda zai ishesu gaba daya sannan ta dafa ruwan zafi ta zuba a babban flask, ta dafa shinkafa da miya. Bayan ta gama wajen karfe bakwai saura ta kirawoshi a waya tace ya turo yara su dauki abinci.
Ta san watakila zasu dau lokaci kafin su karaso kuma ta san idan da shi suka taho yana da mukulli don haka tayi sauri ta shiga wanka tunda itama zata je aiki.
Ta fito daga wankan daure da karamin tawul dinta ta ji shigowarsu falon yana mata sallama. Nan da nan ta dauki jilbab dinta ta zura ta fito falon tana amsa sallamar; shi da Nana ne da Rukayya.
Bayan sun gaisheta ta amsa ta nuna musu kwanukan suka fara dauka, ya dubeta yace
‘Kin ajiye min nawa ko, a nan zan yi breakfast.’
Ta bashi amsa da
‘Eh.’
Har sun kusa zuwa bakin kofa yace
‘Rukayya tunda kowa ya shirya sai ku ci abinci kawai kowa Yaya ta zuba masa na makaranta na san yanzu Malam Sule zaizo sai ku tafi. Kafin ku dawo Mommy ta dawo mana da babinmu.’
Suka amsa sannan suka fice.
Aisha ta tambayeshi kwanan masu jego ya sanar da ita basuyi waya ba sai daga baya idan gari ya kara wayewa.
Har zata shige daki sai kuma ta dawo tana fadin
‘Bari nayi serving abincin kawai da na sako kaya sai mu ci kada yara su zo suna jirana.’
Ta juyo ta kama hanyar kichin yayinda shi kuma ya juyo da kujerar dining table daya ya zauna don ya jira ta. Har ta shiga kicin din kuma sai ta dawo ta tube jilbab din jikinta ta jefa kan kujerar zaman mutum uku, ta cigaba da kaiwa da kawowa tana kwaso abinci daga kicin tana ajiyewa.
Idonsa yana kanta har ta gama, sauri takeyi don haka bata ma kula da yanda yake kallonta ba.
Bayan ta gama ajiye abincin ta bi ta gabansa ta wuce da niyyar shigewa daki. Bata kula da lokacin da ya mike tsaye ba sai ji kawai tayi ya kama hannunta ya dawo da ita ta fada jikinsa. Duk yanda ta so ta kwace kasawa tayi, don ya riketa sosai kuma dama ya gama sanin lagonta.
Wajen wata uku kenan rabonsa da ita, yau din kuma ji yake kamar zai iya biya mata bukata. Ko ma dai menene ba zai iya hana kansa ita din ba a yanzu, ya san abinda take tsoro kuma ya ji a jikinsa babu wannan matsalar don ko daga yanda ya riketa itama ta ji alamun hakan. Da kyar ta lalubo muryarta tace
‘Zamu makara fa ni da yara.’
Ba tare da ya saketa ba ya fara kokarin lalubo wayarsa a aljihunsa, ta sami damar kara dagewa don ta kwaci kanta bayan ya dauko wayar ya rada mata magana a kunnenta ta kyalkyale da dariya. Tana jinsa ya kirawo Malam Sule yace
‘Malam Sule yau Antinsu ba zata aiki ba ku wuce ka kai yara kawai sai ka wuce office ka jira ni.’
Nan da nan ya kife wayar ya jefata kan kujerar zaman mutum uku.
Ko ba a gaya mata ba ta tabbatar yau lafiyarsa ta dawo, sai wajen takwas saura sannan ya kyaleta.
Ta dubi agogon bangon dake dakin tace
‘La ilaha illallahu, yau ka makarar dani zaka sa principal tayi ta yi min mita.’
Yana dariya ya bata amsa
‘Shikenan sai kiyi zamanki a gida gobe kya je aiki.’
Haka tayi sauri ta shiga wanka, Koda ta fito ya riga ya saka kayansa yana falo yana jiranta.
Haka suka gama breakfast tana mitar ya makarar da ita.
Da taga dai karfe tara ta kusan yi haka ta hakura tayi waya makarantar ta sanar da su ba zata sami zuwa ba.
Daga baya ya shirya ya wuce asibiti ya barta a gidan yana mata dariya.
UWAR SADDIKU
Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)
14
Har Abban Sadik yaje asibiti yana mamakin yanda akayi yau lafiyarsa ta dawo a wajen Aisha, duk wani lissafi yayi shi amma ya kasa samo amsar. Abu daya ya iya yankewa duk da ya kasa tuna tabbas din abinda ya faru kuma baya son ya zargi Zahra. Yana zargin kamar duk ranar da ya sha zobo ko shayi a wajenta to idan kwanan Aisha ne baya iya komai, domin a iya lissafinsa wannan zobon ne kawai bai sha ba tunda a asibiti ta kwana, shi yasa bai sami matsala ba. Ya yanke shawarar zai sa ido ya gani kuma ba zai sake yarda ya sha zobon nan ba sai dai idan ranar kwananta ne ita Zahran.
Yana isa asibitin aka sallamosu, don haka ba tare da bata lokaci ba ya dauko su ya dawo da su gida. Nan da nan aka shiga hidima da mai jego.
A ranar ya kamata ya dawo kwananta amma ta san a bisa al’ada kamata yayi ta barwa Aisha kwanan sai tayi arba’in.
Bata da matsala da hakan don tuni ta kirawo Hajja don ta karo mata maganin da ta bata don ta cigaba da dafa masa zobo; tayiwa kanta alkawarin yanda tayi jegon nan shima haka zai yi.
Tunda yamma ta sanar da shi ta barwa Aisha kwanata har sai tayi arba’in, yaji dadi sosai kuma ta kara daraja a idonsa.
Saida ya gama duk abinda yakeyi a cikin gidan sannan ya shiga dakinta yi mata sallama. Ita kadai ce a dakin tana zaune a kan gado domin baby tana bayan Rahma kuma suna falon kasa.
Ya zauna a dai-dai kafarta yace
‘Sannu maijego. Ya kike? Ya Baby? Babu dai wata matsala ko?’
Ta jijjiga kai
‘Ko daya babu.’
‘To ni zan wuce, Sadiku zai rufe muku kofa sai ya kawo miki mukullan.’
Ta dubi flask din da yake kan durowar gefen gado tana gyara zama tace
‘Bari na zuba maka shayi gashi yanzu na gama sha nima.’
Ya jijjiga kai
‘Ai yau bazan sha shayin nan ba don a koshe nake, ki ajiye flask dinki kiyi ta tsiyaya kina sha a hankali.’
Tayi ‘yar dariya
‘Kai haba, ai kuwa shayin irin wanda kake so ne.’
‘Ki daina tempting dina, yau a koshe nake kin san daga wajen liman nake a nan muka zauna aka bankare mana kaji da gurasa muka ci. Abincin daren ma da kyar zai sami shiga yau.’
Duk wayonta haka ta hakura ya fita ba tare da ya ko kalli flask din shayin nan ba, yayi mata sallama ya wuce wajen Aisha.
Yana fita ta fara nadama, ta san ba zai iya gane ta saka wani abu a shayin ba to amma me yasa ya ki sha? Gashi sai da ya bari ta barwa Aisha kwananta sannan ya wani ki shan shayin. Saida tayi kwalla saboda takaici; tayiwa kanta alkawarin zasu hadu gobe.
…………..
Da mukullinsa ya bude gidan kamar yanda ya saba ya shiga, tana falo tana karatun littafi da shayi kofi daya a gabanta tana sha. Bayan tayi masa sannu da zuwa sun gaisa ya dubeta yace
‘Ina abincinna yunwa fa nake ji.’
Ta kalleshi tana dariya
‘A’a, jegon har ya fara tabaka ne? Yau fa kwanan Mommy ne ko ka manta ne?’
‘Babu wani jego ai haka akeyi, tunda tana jego ai ke zaki karbi kwanan zuwa tayi arba’in don kema idan kika haihu haka zata yi. Don haka ki shirya ina nan har arba’in.’
Tayi dariya
‘Gaskiya dai ka koma, ni ban karbi wannan kwanan ba. Kawai saboda ta haihu sai kuma ka barsu ita kadai da Baby, ina laifi idan ka kwana a can din. Nifa idan na haihu babu wani arba’in duk da babu abinda za ayi amma ba zan yafe kwanan ba, ka kwana a nan din dai like just be there ba wai ka tafi ka barni da baby ba wai kai ka gama aikinka, tab!’
Kallonta yake da mamaki
‘To yanzu ya za kiyi dani.’
‘Abinci zan baka kaci ka koshi ka koma can in an kwana biyu ka dawo.’
Duk yanda ya so ya tsara Aisha ta karbi kwanan nan ki tayi, haka ta dafa masa taliya ya ci ya koshi ya sha shayi sannan tayi masa sallama ta rufe kofarta ya koma wajen Zahra.
…….
Ko da taji shigowarsa luf tayi kamar mai bacci domin tazata wani abun ya dawo dauka.
Sai da ya shiga dakinsa ya shirya sannan ya kirawota a waya domin da baiga Rahma ba yayi tunanin ko a dakinta zasu kwana. Ta zata ya riga ya fita don haka ta dauka tana mamaki.
‘Ina nan fa, a nan zan kwana.’
‘A’a, me ya faru kuma ka fasa?’
Yayi ‘yar dariya yace
‘Kanwar taki bata karbi kwanan ba.’
Nan yayi mata bayani kamar yanda Aishan tayi masa, suka ajiye waya tunda dama kiranta kawai yayi don ta san a gidan zai kwana.
Har bacci ya kwasheta tana tunanin wauta irin ta Aisha, ya za ayi abata miji kwana arba’in tace a barshi? Ko yanzu ma da akayi haka ta san idan dai Aishan ta haihu ko da tsiya-tsiya sai an bata kwana arba’in din nan tunda ita haka taga ana yi.
……….
Kwanansu daya da fitowa daga asibiti Aisha taje barka da kayan barkarta da ta tanada cikin leda; kayan baby ne masu kyau da tsada. Sai da ta tabbatar yana gidan ta shiga domin tuni ta sha jinin jikinta da matar nan.
Bayan la’asar ne suna zaune ita da shi a falonsa da Baby a hannunsa Rukayya ta shiga falon da sallama ta sanar da Mommy zuwan Anti Aishan. Har ta mike zata tashi ya cewa Rukayyan ta hawo da Antin nan mana. Kafin tace wani abu Rukayyan ta fice, bata dade ba suka dawo tana dauke da ledar yayinda Aisha take biye da ita.
Babu laifi suka gaisa da Zahran da yake a gabansa me, aka mika mata Baby ta dauka ta sa albarka. Suka dan taba hira gaba daya har Abban Sadik din, ta turawa Zahra ledar tace
‘Ga wannan babu yawa, Allah ya rayata ya kara lafiya.’
Tare suka amsa da Zahran da Abban Sadik.
Tayi musu sallama ta sauko ta koma gida, zuciyarta fari fes saboda yanda tayi barkarta a gabansa tunda ta san Zahran bata yi mata komai a gabansa.
……..
Saida aka kwana biyar sannan ya sanar da su sunan yarinya, ya saka mata Sumayya. Da kyar Aisha ta daure ta sanar da ‘yan uwanta sunan inda ta nemi Yaya Zuwaira da Yaya Zainab su zo amma kada su taho da yara don bata son fitna.
An ci burin wannan sunan kuma an shirya taro inda aka gayyato mutane da yawa, dangin Abban Sadik din ma haka suka zo da yawansu saboda Yaya Saratu aka bawa goronsu na gayyatar ta tabbatar ta hado kansu sannan suka taho.
Aisha ta riga ta tambaya ko akwai aikin da zata tayasu amma Zahra tace mata babu domin komai bayarwa za ayi a yiwo daga waje, don haka ranar sunan ba tayi shirin tafiya gidan da wuri ba. A tunaninta ma ‘yanuwan Abban zasuyi ta shigowa gidan nata amma har shadaya babu wanda ya shigo. Batayi mamaki ba domin dama ta san babu wanda yake kaunarta a danginsa, tun lokacin da suka je da Zahra gaba daya suka ki sakewa da ita. Duk da sun je ita da Abban sun bawa Hajiyan hakuri amma har kawo yanzu basu saki jiki da ita ba.
Sai wajen sha biyu saura sannan Zuwaira da Zainab suka iso, ba tare da bata lokaci ba suka shirya tare da Aishan suka wuce gidan sunan.
Tun daga bakin gate Rukayya ta hangosu, da gudu ta karasa ta kama hannun Aishan tana yi mata sannu da zuwa, ta gaida su Yaya Zuwaira sannan ta wuce gaba suka bita a baya.
Tun daga falon duk ‘yan uwan da Rukayya ta san basu taba haduwa da Aishan ba sai tace musu
‘Ga amaryar Abbanmu.’
Haka har suka wuce falon sama inda Mommy take, su Yaya Saratu ma duk suna wajen anata hira.
Suka karasa kusa da Mommy Aisha ta zauna kusa da ita su Yaya Zainab din ma suka zauna.
Gaisheta sukeyi suna mata barka amma da kyar take amsawa tana wani dauke kai.
Suka juya wajen Yaya Saratu wadda itama da kyar take amsa gaisuwar.
Yaya Murja ce kawai ta sauraresu da girmamawa, ragowar mutanen da suke wajen suka cigaba da hirarrakinsu babu wanda yake bi ta kansu. Don haka suma suka gyara zama suka fara kus-kus dinsu su kadai.
Basu dade da zama ba wata dattijuwar mata ta shigo, tun daga kafar bene take zabga kirari tana guda
‘Uwar gida Uwar Saddiku, kinyi taki kinyi ta raggo. Uwargidan Yusuf maki gani ido ya makance. Yanda duk kika dama haka za a sha Uwargida ta Uban Sadiku ko mahassada sun ki. Haihuwa kyautar Allah, ba rawar kai bace ba iyawa bace, ke Allah ya zaba uwar SADIKU matar Yusufa….’
Yaya Saratu ce ta fara mikewa ta lika mata naira dubu tana fadin
‘Kin min daidai, babu karya a cikin zancenki uwar Sadiki taci dubu sai ceto.’
Abun nata ya fara yawa kuma duk wanda ya san Aisha kishiyarta ce ya san da ita akeyi. Yaya Murja ce ta mike ta dauki kudi a jakarta ta ja matar sukayi kasa ta sallameta.
Bata dade da fita ba su Aisha suka mike Yaya Zuwaira ta karasa kusa da Zahra ta ajiye mata kudi naira dubu goma tace a siyawa Baby sabulu. Sukayi musu sallama suka fito.
A gidan Aishan suka karasa wuninsu suna jajanta mata zama da wannan matar don ko su kansu sun kula da yanda ita da ‘yan uwan Yusuf din basa ko kaunar Aisha.
Tun tuni Aisha ta san dangin Yusuf basa sonta amma sai yau ta kara tabbatarwa, don zata iya cewa a ‘yan uwansa matar Yaya Bello ce kawai ta saurareta sai kuma Innani wadda ita din ‘yar uwar Hajiya ce.
Haka aka gama taro aka watse, abincin sunan nan kuwa Aisha ko kalarsa bata gani ba domin lokacin da suka fito daga gidan ba a fara rabo ba kuma da aka fara babu wanda ma ya tuna da ita duk da an kaiwa makota abincin gida-gida.
…...
Wajen sati biyu da gama taron suna sai Yusra ta tsiri shiga gidan Aisha, haka kawai da rana ko da daddare musamman idan Abbansu yana gidan sai Yusra ta shigo. Wata rana ita kadai take shiga wata rana kuma ita da kannenta. Hatta Rukayya saida tayi mamaki saboda Yusra bata taba shiga gidanba amma sai gashi yanzu kusan duk ranar da Abbansu yake gidan sai ta shiga.
Amma da zarar Abban ya zauna an kawo abinci aka ce ta zo ta ci sai taki, tace ita ta koshi. Sai dai kawai su zauna a falo suna kallon TV.
Yau shinkafa da miya Aisha ta dafa ta hada salad ga kuma zobo. Tare suka zauna da Abban suka fara cin abincin, sai dai da kyar ta hadiye lomar farko saboda dandanon miyar bai yi ba. Ta ajiye cokalin tana jira taji mai zai ce.
Shi din ma da kyar ya hadiye wanda ya saka a bakinsa ya dubeta yace
‘Yau me ya sami miyar ne?’
Tace
‘Wallahi nima na ji, na zata ma bakina ne.’
Kamshin miyar ya canza gaba daya, gashi yana wani santsi da dandanon mara dadi. Dole ta dauke wannan miyar ta kawo musu mai da yaji suka ci abincin nan domin bata ma da wasu kayan miyan gashi abincin dare ne.
Haka suka kwana tana mamakin abinda ya bata mata miya, har gari ya waye bata gane ba don haka ta cigaba da harkokinta.
Bayan an kwana biyu kuma ranar asabar tayi tuwon shinkafa da miyar gyada da rana shima ga mamakinsa yanda waccan miyar tayi wannan ma haka tayi.
Dandanon babu dadi ga shi kuma har wani bashi miyar takeyi, dole ta tashi tayi sauri ta kada musu miyar kuka suka ci tuwon.
Sanda ta ajiye abincin dare tana kula da Abban Sadik sai da ya dandana kadan sannan ya saki jiki yaci.
Daga baya kuma suna zaune a falo suna hira da daddare yake tambayarta
‘Wai kuwa kin gane abinda yake bata miki miya, ko kayan kamshi da kike sakawa ne?’
Cikin damuwa tace
‘Wallahi ban gane ba, bana jin kuma kayan kamshin ne amma dai zan cigaba da dubawa.’
‘Ya kamata dai ki kula sosai, idan ma wani abune yake shiga abincin sai ki mayar da hankali ki gyara.’
‘In Sha Allah.’
Ta kula da yanda yake kokarin ya zargi ko tana saka masa wani abun a abinci wanda hakan ya sosa mata rai, sai dai itama ta rasa abinda yake faruwa da miyar tata.
Haka ta cigaba da kula ko zata gane.
A ‘yan kwanakin nan saida abincinta yayi irin haka wajen sau biyar, domin har dafa duka tayi wadda ta dinga yi musu kanshi da kumfa kamar sabulu.
Gaba daya ta shiga damuwa, amma ta kasa gane inda matsalar take. Gashi Abban Sadik ya fara hakura da abincinta sai yaje waken Zahra yaci. Don haka ta mayar da hankali take ta rokon Allah ya yaye