Showing 165001 words to 166068 words out of 166068 words

Chapter 56 - UWAR SADIKU COMPLT BY SAKINA YAZID.txt

11 Jul 2024

25425

da suka idar da sallar la'asar sannan Nana ta samu taja Rukayya suka fito tsakar gidan, ta dubeta idonta ya ciko da kwalla tace


'Yaya Rukayya ni na fi so na zauna a gidan nan don Allah ki cewa Abba ko Anti nima a dawo dani.'


Rukayyan tace


'Wani abun ake miki a gidan Baban?’


'Kema kin san dai babu abinda za a yi min amma dai ai nan ne gidan mu ko? Kawai na fi son nan.’


'To kije ki cewa Anti Aisha kina so ki zauna, da kanta zata gayawa Abban sai kawai a barki a kawo miki kayan.’


Ta sunkuyar da kai tayi shiru na dan lokaci, ta dago ta share kwalla tace


'Yaya Yusra tace kada mu bata hakuri zata raina mu kuma cutar damu zatayi, amma ni dai ina son zama a nan.’


Rukayya tayi dariya tace


'To ki biyewa Yaya Yusra kiyi ta shan wahala a banza, baki gaji da wahala bane.’


Nan Yaya; Yar wajen Yaya Bello yayar Hanan ta fito ta samesu don itama duk da sa'ar Yusra ce amma ta fi kusanci da Rukayya saboda ta fi saukin mu'amala. Rukayya ta dafa Nana tace


‘Kije ina nan.’


Ta shigo falon jikinta a sanyaye. Babu kowa a falon sai Saddiku da yake zaune a kan dining table yana karatu a computer dinsa don yanzu ya sami gurbin karatu a BUK inda yake karantar Computer Engineering. Ya kalli Nanan tana tafiya kamar wadda kwai ya fashe mata a ciki, yace


'Ke, zo nan.’


Ta karasa ta tsaya a kusa dashi.


'Menene haka kike sanda kamar wata mara gaskiya.’


'Yaya so nake na zauna a nan shine Yaya Rukayya tace naje na gayawa Anti.'


Ya harareta


'Kina so ki zauna saboda Yusra ta dinga aikoki kina mata rashin kunya ko?’


'Wallahi Yaya ba haka bane, ita Yaya Yusra ma bata san zan zauna ba don tace kada na kuskura na bata hakuri na bari ita zata sa a koreta a dawo damu.’


Ya yi mata fada sosai tare da gargadin kada ta kuskura ta sake sauraren Yusra in ba haka ba da kanshi zai mayar da ita gidan Baban, sannan yace


'Antin tana kicin, kije ki gaya mata.’


Ta juya ta wuce kicin din inda Aisha da Jummai suke kokarin dora tuwon dare.


Har ta shiga kicin din Aishan bata ce mata komai ba don ta zata wajen Jummai ta shigo, sai da ta tsaya a gefenta ta kirawota cikin sanyin murya


'Anti.'


Ta juyo tace


'Na'am Nana. Ya akayi?’


'Anti don Allah ki cewa Abba a barni a nan gidan ni gaskiya na fi so na yi zamana a nan.’


Ta bita da kallo na dan lokaci sannan tayi murmushi tace


'To Nana zan gaya masa.’


Da mamaki ta dago idonta kalleta don bata zata zata amsa da sauri haka ba, tace


'To in Baba ya zo ba zan bi su Yaya Yusra ba.’


Tayi dariya tace


'To. Ki dauko min wayata a falo na kirawoshi na gaya masa.’


Nana take ta dauko mata wayar ta kirawo Abban a gabanta ta sanar da shi idan Yaya Bello ya zo ya sanar dashi ya bar mata Nana.


Dadin da yaji ba zai misaltu ba, ya so yayi mata maganar Yusra sai dai baya son ya taso fitna don shi a yanzu bai ma san da Aishan da Yusran wacece tafi taurin kai ba. Don haka yayi mata sallama ya kirawo Yaya Bellon ya sanar da shi.


Da gudu Nana ta fito daga kicin din ta karasa ta dafa kafadar Saddiku tace


'Yaya har ta gayawa Abba yace idan Baba ya zo ya barni a nan zai je ya taho min da kayana.’


Ya dungure mata kai yace
'Saura naji rashin kunya.’


Ta fice wajen su Rukayya ta barshi a nan.


Sai bayan magriba sun gama cin abincin dare sannan Yaya Bello yazo daukansu.


Tabbas Yusra ta shaki haushi amma tana kan bakanta na Aisha bata isa ta bata hakuri ba. Shi ma Abban nata haushinsa take ji saboda tana tunanin ya zabi Aisha a kanta. Da ba don Yaya Bello ne yazo daukansu ba da wallahi babu wanda ya isa ya fitar da ita daga gidan; to amma Yaya Bello yana mata kwarjini ba kadan ba, kuma ta san shi baya daukan taurin kai kamar Abbansu. Yanzun nan zai bata kashi ko ya gaya mata maganganu masu ciwo. Don haka ta wuce suka shiga bayan motar ita da Yaya yayin da Hanan ta dane gaban motar.


__


Haka rayuwar gidan Abba ta cigaba. Gaba daya yaran Aisha ta hada tana kula da su, su kuwa su Farha sai dai idan su zo wuni. Ita kuma Yusra ta ki ta bawa Aishan hakuri shi kuma Yaya Bello yace kada wanda ma ya sake yi mata maganar gidan nasu, gara a bar masa ita a nan don yana ganin kamar idan ta koma can ma lalacewa zata yi. Shi kuwa Abbanta gaisuwa ce kawai take hadata da shi don ta sawa ranta ya daina sonta don ya fi son Aisha. Sai dai kawai idan ta tuna da Mommy tayi ta kuka tana fadin Mommy itace uwarta itace ubanta don a yanzu ita bata da Uba. Wajen su Yaya Murja kawai take zuwa taji sanyi a ranta, tunda suma suna jin haushi yanda a zatonsu Aisha ta sa Abba ya rabu da ita. Ga kuma labarai na karya da gaskiya da take yawan kai musu, tunda in ta ga dama ko daga makaranta sai ta hau motar haya ta wuce gidan Suwaiba ko Murjan.


Shima Abban rashin dawowar Yusra gidan yana ci masa tuwo a kwarya sai dai babu yanda zai yi. Bai ga alamar Aisha zata saurareshi a kan maganar Yusra ba kuma baya son rabuwa da ita musamman ma da yake yana jin dadin kulawar da take bawa yaran, sannan kuma gashi Yaya Bello ya ma ce ba zai bashi Yusran ba shi zai yi mata aure. Don haka ya tattara ya hakura.


Baya son ya tuna Zahra saboda yanda tunaninta yake bata masa rai, gashi in ya tunata ma sai ya kasa nema mata gafarar Allah sai dai kawai cutarwarta a gareshi da yake tunawa.


Idan ya kalli Aisha da cikin da yake jikinta sai ya kara jin haushi Zahran; domin yanzu ya tabbatar itace ta san kulle-kullen da tayi ta hana Aishan haihuwa.


Idan ya kalli Yusra kuma sai ya kara jin haushin Zahran saboda yanda yake ganin ita ce ta turawa Yusran wasu akidu masu muni wadanda suka sa ya rasa yanda zai yi da Yusran.


………


Babbar Sallah ta wuce da wata hudu Aisha ta haifi yaronta lafiyayye, aka saka masa suna Muhammad Bello. Yayyensa suka yi masa lakani da Baba karami.


KARSHE.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login