Showing 27001 words to 30000 words out of 166068 words
kanta ba.
Ya kalleta yayi murmushi ya zare littafin da take karantawa daga hannunta. Ta dago suka hada ido, ta bishi da kallo ba tare da ta ce komai ba. Bata da niyyar magana don haka yace
‘Fushi kikeyi dani ko Aisha? To ai shikenan na ji gaskiyar zancen a bakin Malam Sule don haka komai ya wuce. Kawai dai idan irin wannan ta sake faruwa ba tafiya zakiyi ba sai ki yi min waya ki sanar da ni tukunna.’
Cikin halin ko in kula tace
‘To, in sha Allah zan kiyaye.’
Ta mika hannu ta dauki littafinta a kan cinyarsa tana kokarin budo shafin da take, ya sake zare littafin daga hannunta yana fadin
‘To kuma ai sai a daina fushin ko?’
‘Ni dama ba fushi nake ba.’
‘To ki taso muje falo inda muka saba zama, ai naga ko a can ma kina yin karatun ko.’
Ta gyara ta sauko daga kan gadon, ta dauki littafin nata a kan cinyarsa ta nufi falon. Yayi murmushi kawai ya biyota a baya; tabbas ya san Aisha tana da miskilanci amma bai yi zaton zata iya yi masa fushi haka ba. Suka dawo falon ta sami waje kujerar zaman mutum daya ta zauna ta cigaba da karatunta shi kuma yana kallon TV.
Duk yanda yaso ya jata da hira ta ki bashi hadin kai, gajerun amsoshi take bashi da basu wuce e ko a’a ba, ko kuma tace Um. Har ya gaji ya koma ya sa mata ido yana mamakin wannan dogon fushin.
Suna nan zaune har sha biyun rana tayi, ta tashi ta shige kicin ta dora abincin rana. Ta kusan gama abincin ya ce mata zai je masallaci ya dawo.
Yana ficewa ta ajiye masa abincin rana a table tayi sauri ta cinye nata, ta wuce dakinta ta kwanta. Tana jin shigowarsa tayi kamar bacci takeyi, don haka ya kyaleta ya zauna yaci abincinsa shi kadai.
………
Inda Abban Sadik ya fita ya bar Zahra nan ta zauna tana takaici; wato Yusuf har ya auro matar da zata sa yace mata makaryaciya. Dole ne ta dauki matakin don bazata zauna da wannan yarinyar ba, shima Malam Sule kuma dole ya bar mata gidan don ta san karshenta shi ya fadawa Abban Sadik yanda akayi; dama tana sane da yanda yake kokarin kin bin umarninta.
Ta ji dan danshi a kwarmin idonta, ta kai yatsanta ta taba wajen ta kalla; hawaye ne. Ta jijjiga kai cike da takaici; tabbas yanda ta fitar da wannan kwallar sai ta fitar da Aisha daga rayuwar Yusuf ko da kuwa Aishan tsafi takeyi. Tabbas yanzu ta kara gasgata maganar Malam da yace ba haka suka barshi ba.
Kamar an mintsineta ta tuna bata ma yi magana da Malam ba tunda ta nemi layar nan ta rasa, don haka ta mike ta nufi dakinta. Tana shiga ta saka mukulli ta kulle kofar saboda kar yara su dameta. Ta zauna a gefen gado ta dauki wayarta ta kirawo Malam Hatimu.
Bayan ta gama yi masa bayanin batan layar yayi ‘yar dariya yace
‘Allah sarki, masu ita sun dauke kenan Hajiya, ai kunyi sakaci. Sannan kuma yarinyar ta zo da sa’a watakila kuma da nata hatsabibancin, amma ba zata iya damu ba duk taurin kanta.'
Cikin kosawa tace
‘To yanzu ya za ayi Malam?’
‘Eh, kada ki damu akwai aiki wanda za ayi kuma aikin nan zai rabata da mijinki har abada, ke ko bayan ranki bazasu sake hada inuwa daya ba. Ammafa gaskiya aikin yana da tsada sosai, yauwa.’
Cikin farin ciki tace
‘Kada ka damu Mallam, ko nawa ne zan biya ayi wannan aikin indai zai yi yanda kace.’
‘Ai Hajiya aiki kamar yankan wuka, sai dai kudin aiki naira dubu dari uku da tamanin zai kama komai da komai.’
Ta dan dauke wuta saboda jin yawan kudin; to a ina ma za a ta sami wadannan kudin, ta danyi gyaran murya ta cigaba
‘Malam babu kuma wani ragi da za a samu?’
‘Gaskiya Hajiya a hakan ma anyi miki ragi, don kinga aiki biyu za ayi. A mallaka miki ruhin maigidan ta yanda sai yanda kikayi da shi ita kuma a nesanta ruhinta da nashi ba zasu sake sha’awar kasancewa da juna ba.’
Ta jijjiga kai, tabbas tana son wannan aikin amma bata da kudi a yanzu
‘To shikenan Malam, zan yi kokari na hada kudin nan da wani lokaci in sha Allah zan nemeka.’
Sukayi sallama tana tunanin inda zata sami wadannan kudin don gaskiya a halin yanzu bata da kudi. Jarinta na business dinma da takeyi ta dan yi musu gibi so take ta sami dama ta tambayi Abban Sadik. Bata da wata kadara sai sarka da dankunnen gwal nata da na yara kuma gaskiya ba zata iya sayarwa ba. Amma ko a jikin Abban Sadik din zata san yanda zatayi ta sami kudi.
Haka ta wuni tunani har dare yayi, tana ta lissafin yanda zata sami wadannan kudaden. Zuwa dare dabara ta fado mata, don haka nan da nan ta nemo Hajja mai kayan mata. Gaba daya ma ta manta da matar nan don kafin ma Aisha ta tare ya kamata ta nemeta ta hada mata masu zafi amma da yake ta sa ran auren ba zai dade ba sai ta manta.
Nan suka gama magana da Hajja a kan a hada mata masu zafi kamar na naira dubu hamsin don so take gaba daya ta mantar da Abban Sadik kowacce mace. Aka yi mata lissafin dubu saba’in da alkawarin in dai ta tura kudin a lokacin to gobe da azahar za a kawo mata sakonta.
Bata da kudi amma saboda akwai abinda ta shirya haka ta kwashe kudin nan a account dinta na business ta turawa Hajja, ya zama saura abinda baifi dubu ashirin ba a account din. Tana tunanin da ta fara aiki da kayan nan sai ya biya kudinsu.
………
Haka suka wuni Aisha taki kula Abban Sadik, tace masa ba fushi take ba amma kuma taki ta saurareshi idan tayi murmushi to ita da waya ne. Haka har dare yayi.
Tana yin sallar isha’i ta kwanta a dakinta tsaf da niyyar bacci, don haka shi kadai ya zauna a falo yana kallon TV.
Bayan karfe tara ya fita ya dubo wajen Zahra sannan ya dawo, ya shirya ya wuce dakinta.
Duk yanda ta so ya kyaleta a daren nan saida ta sallama masa, haka ya dinga tsara mata kalamai na lallashi a kunnenta har ya samu ta huce.
Sai da safe ya gaya mata zasu shirya asabar mai zuwa ya kaita ta sake gaida Hajiya kuma su bata hakuri.
_
Kamar yanda sukayi alkawarin da Hajja washe gari sai gata ta zo da kanta. Ta yi sa’a lokacin da ta zo yara suna islamiyya don haka babu kowa a gidan sai ita, duk da haka dai a dakin baki ta sauketa suka zauna suka turo kofa.
Nan Hajja ta baje kaya tana bayani; kayan da ta hado mata sun kai rabin ledar bagco ga kuma tsumi a galan. Ta zauna tayi mata bayani dalla-dalla tana rubutawa; bayan sun gama Hajja tace
‘Hajiya Zahra ai idan akayi maka kishiya baka zama haka, gyara zakiyi na musamman idan ba haka ba sai ki ga wankin hula ya kaiki dare. Yaran nan na yanzu masu ido a tsakar ka, wallahi kada ki saurara mata.’
Ta kama haba tace
‘Hmm! Ni da na gani Hajja, yarinyar daga zuwanta har ya canza min, jiyan nan dana kirawo ki nan ya kare min tijara saboda ta tsaro masa zance. Ai dole sai na tashi tsaye.’
Ta matsa kusa ta dafa gwiwarta tana magana kasa-kasa
‘To kinga akwai wani ma..’
Ta zura hannu a jakarta ta zaro wani dan kulli a farar Leda, ta cigaba
‘Kin gan shi nan ba ma bawa masu kishiya ma saboda idan kikayi amfani da shi ba zai sake jin dadin wata mace ba sai ke, gashi dubu goma ne amma ki bada biyar saboda wannan cinikin da kika yi min.’
Ta karba tana juyawa, tana fadin
‘Allah Hajja?’
‘Allah Hajiya. Ai idan baka iya kama barawo ba sai barawo ya kama ka. Idan ma kina bukatar wani taimakon akwai aikin da mukeyi sai yanda kika yi da maigidan, idan ma sakinta kike so yayi zai yi.’
‘Allah Hajja? Kin san nifa bana son aikin nan da akeyi da aljanu.’
‘Kema kin san aikina Hajiya, wannan din ma da zan kawo miki ayoyi ne da kanki ma zaki gani. Naira dubu ashirin kawai zaki bayar shikenan an gama.’
Nan take suka kulla ciniki, suka rabu a kan idan ta sami kudin zata nemo Hajja. Ita kuma Hajjan ta sake tabbatar mata da idan dai tayi aiki da wadannan kayan da ta kawo mata ko naira dubu dari ta nema sai ya bata.
……..
Ta riga ta san da fushi ya fita daga gidan gashi yau din dai a wajenta zai kwana. A sanin da ta yi masa ta san da fushinsa zai shigo don haka ta yi duk wani shiri na tarbarsa.
Duk da yanzu din itama ta so tayi masa fushin amma dole ta hakura saboda abubuwan da ta shirya; duk da daman ta riga ta saba bata son fushinsa, ko da shine yayi mata laifi da zarar yayi fushi zata fara bashi hakuri.
Tunda Hajja ta tafi tasamu ta sha tsumin nan ta koshi, ta bi sauran kayan duk tayi amfani da su, don haka kafin ma yazo ta fitni kanta.
Yana son shinkafa da salad don haka ta shirya fried rice da kaza ga lafiyayyen salad, ta jera a table.
Sai wajen tara da rabi ya shigo gidan, Yusra ce kawai a falo da Rukayya suna homework. Yana shigowa Rukayya ta shirya, suka fice ya rakata don ta taya Aisha kwana sannan ya dawo ya rufe kofa.
A falonsa ta sameta, ya shiga da sallama. Bayan ta amsa sallamarsa ta mike tana masa sannu da zuwa. Ya amsa ba yabo babu fallasa, ya wuce daki. Ta bishi da sauri, don haka kusan tare suka shiga dakin
‘Yallabai.’
Ta kirawo sunansa murya a mariraice.
Ya juyo ya dubeta sannan yace
‘Menene?’
Ta kara marairaicewa tayi kasa da murya
‘Ka san dai fushinka baya min dadi, don Allah kayi hakuri in dai nice ba zan sake ba.’
Ya juyo gaba daya ya tsaya yana kallonta, har ya bude baki zai yi magana sai kuma ya fasa. Yadan matso kusa da ita sannan yace
‘In dai baki sake ba ya wuce.’
‘In sha Allah ba zan sake ba.’
Ya mayar mata da murmushin da take ta yi masa sannan ya juya ya wuce gaban wardrobe ya debo kayan baccinsa ya fara canzawa.
Tace
‘Idan ka shirya na saka abincin dare.’
‘Ok, yanzu zan sauko.’
Ta juya ta fice daga dakin cike da takaici bashi hakurin da tayi.
Bayan sun gama cin abinci suka zauna a falonsa suka dan taba hira, da ta kula ya fara jin bacci ta tashi ta shige dakinta ta sake shiryowa ta sa rigar bacci ta fito ta shige dakinsa.
A dabi’arsa baya neman matarsa sai yayi bacci kai daya, lokacin dare ya raba sosai kuma dukansu sun rage baccin. Ga mamakinsa yau yana kwanciya ta fara lalubensa, bai kawo wani abu don wannan ba bakon abu bane tunda matarsa ce; kawai dai ya san ta saba jira sai sun rage baccin musamman da yake mafi yawa cin lokuta kafin ya kwanta ita din bacci ya dauketa.
Haka sukayita fama; yana yi yana mamakin yanda yau gaba daya take kamar a gigice tunda ya riga ya saba shi yake sarrafata kuma a hankali yanda yake so. Bai yi mamaki sosai ba don ya san akwai abubuwan da mata suke Sha musamman don wannan harkar, don haka yake tunanin itama wani abun ta sha.
Suna gamawa kamar yanda ya saba ya zare jikinsa yaje yayi wanka, bayan ya fito ya tabata yace mata taje tayi wanka ko kuma tayi alwala idan ba yanzu zata yi wankan ba. Haka ta tashi taje ta wanko jikinta tayi alwala ta fito ta sake kwanciya.
Can cikin dare baccinsa yayi nauyi ta sake lalubarsa, kamar a mafarki ya farka. Ya gyara kwanciya yace
‘Yau bakya jin bacci kenan?’
Tayi ‘yar dariya ta amsa
‘Um.’
Suka cigaba. Baya son ya rasa sallar asuba a masallaci don haka suna gamawa ya tashi yayi wanka, itama ta tashi tayi nata wankan lokacin wajen karfe uku da rabi na dare. Suka koma suka sake kwanciya.
Ko da yaje masallaci ya dawo yaci burin biyan bashin baccin da ya ci, saida yayiwa sakatarensa message yace masa zai dan makara don ya samu yayi bacci sannan ya koma ya kwanta.
Tana idar da sallah itama ta dawo ta kwanta, yayi zaton bacci zasuyi kamar yanda suka saba don wani lokacin sai wajen karfe shida take tashi ta shiga kicin don shirya ‘yan makaranta.
Tana kwanciya ta laluboshi, duk yadda ya so ya kyaleta kasawa yayi; ba wai saboda yana bukatarta a wannan lokacin ba sai don yana ganin matarsa ce ba zai iya kyaleta ba musamman da wannan bukatar. Suna gamawa lokacin har shida ta gota don haka a gurguje ta mayar da kayanta ta wuce kasa don shirya ‘yan makaranta. Ta fuskanci gajiyawarsa wanda dama haka takeso; so take ta sauke masa duk wata sha’awa da yake da ita saboda idan yaje kwanan Aisha sai ya kwanta yayi ta baccin a can ba tare da ya kusanceta ba.
Tana fita daga dakin ya tashi ya shiga wanka, bayan ya fito daga wankan ya zauna a kujerar gaban mudubi ya kafa tagumi; me ya sami matar nan ne? Ko ma me ta sha gaskiya yau ta jigata shi. Bacci yake so ya koma amma ya hakura saboda yana tunanin idan ta sameshi a kwance bayan yara sun tafi makaranta to lallai zata sake nemansa shi kuwa ya san ba zai iya ba. Don haka nan da nan ya shirya ya sauko dai-dai lokacin yara sun fice.
Ta saka mishi abincinsa wanda yana gama ci yayi mata sallama ya fice, gidan Aisha ya shiga don ya dubata inda ta sanar da shi sati mai zuwa zata koma aiki. Yayi mata sallama ya fice bayan ya sanar da ita zasu dinga fita da yara idan Malam Sule ya ajiyeta sai ya wuce da su.
UWAR SADDIKU
Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)
12
Kwanakin nan biyu haka Abban Sadik yayisu babu baccin kirki saboda yanda suke kwana hidima, har Allah-Allah ya dinga yi kwanan Zahra ya kare ya koma wajen Aisha.
Ranar da zai koma wajen Aisha kuwa da wuri ya dawo daga wajen aiki, ana cikin kiran sallar isha’i .
Wajen Zahra ya wuce kai tsaye, bayan sun masa sannu da zuwa ita da yaran ya amsa ya dubeta yace
‘Bari na wuce don yau a gajiye nake wallahi, don Allah da zarar karfe tara tayi ki rufe gidan nan kar a sake budewa sai da safe.’
‘To in Sha Allah zan rufe.’
Yayi musu sallama ita da yaran ya fice.
Ta bi bayansa da kallo tana murmushin jin dadi, domin aikin da tayi ta san yau din nan idan banda bacci babu abinda zai iya.
Hakan kuwa aka yi; ita Aisha bata kawo komai domin bata da matsala da hakan, suka kwana suna baccinsu har asuba. Ko da gari ya waye haka suka gama hirarrakinsu ya shirya yayi tafiyarsa aiki.
Har saida aka sake kwana bayan ya dawo daga masallaci sannanne wani abu ya shiga tsakanin sa da Aisha, a nutse yanda ya saba kuma yanda yake so suka farantawa juna. Da dare yayi kuma ya koma kwanan Zahra.
Yana fargaba da addu’ar Allah ya sa yau bata sha abinda ta sha wancan karon ba don gaskiya ya fi so yaji dadi yana cikin hayyacinsa.
Yanda akayi wancan karon din kuwa haka aka sakeyi, babu yanda ya iya haka ya dinga hakura da baccinsa. Saida ya koma wajen Aisha sannan ya maimaita mata yanda yayi.
Haka suka cigaba da yi duk da ita Aisha bata dauki abun a matsala ba, sau dayan nan ya isheta musamman da yake yana daukan lokaci ya tabbatar bukatarta ta biya. Haka rayuwa ta cigaba.
Zahra bata taba shiga gidan Aisha ba kuma bata turo yaranta, tunda tana amarya dai data tura Yusra da waya ta dauko mata hoton falon bata sake tura su ba. Rukayya ce kawai take zuwa tayata kwana, itama don babu yanda Zahran zata yi ne. Sai kuma Allah ya sa Aishan da Rukayya jininsu ya hadu sosai, don haka Rukayyan take jin dadi zuwa kwana; duk da dai idan gari ya waye ta fito daga gidan Mommy hanata komawa takeyi har sai wani daren.
_
Yanda ya saba duk karamar sallah kaya kala uku yake yiwa kowa, tsakanin Zahra da yaranta. Idan kuma babbar sallah ta zo to kaya kala daya yake musu, sannan kuma ya kawo sa da rago wanda za a yanka na layya.
Ranar asabar ce don haka yana gida da yamma, suna zaune shida Zahra a falonsa suna hira; da yake yaran duk sun tafi islamiyya. Ya dubeta yace
‘Sallah fa ta matso, ya za ayi ne da kayan sallarku?’
Tayi ‘yar dariya
‘Yanda aka saba mana, ka san dai a wajena ake siya ko business din nawa ya dan samu cigaba.’
‘Hakane, to zan tura miki dubu dari da hamsin, yara kowa dubu ashirin ke kuma hamsin. In ya so sai ki kawo muku abinda kike so, ita kuma kanwarki itama sai na tura mata hamsin din.’
Ta langabe kai
‘Haba yallabai, to ita ba zata yi min cinikin ba? Ka turo har natan mana na dai san ba zai wuce leshi ba. Za a kawo su kala-kala in ya so sai tazo ta zaba.’
‘E kuma kinga hakan ma zaifi, ta huta da shiga kasuwa.’
‘Kwarai kuwa. Amma gaskiya da zaka karawa yara ko da dubu biyar-biyar ce ka san fa kayan yanzu sun dan kara kudi.’
‘A’a hakan ma zai isa. Kin san fa Babbar Sallah ce dole sai na tanadi abun layya. Ni ban ma sani ba na