Showing 105001 words to 108000 words out of 166068 words

Chapter 36 - UWAR SADIKU COMPLT BY SAKINA YAZID.txt

11 Jul 2024

25426

ko man motarta bata taba saye ba, da zarar tace babu mai zai turo direbansa ya dau motar a ciko mata tanki; haka yake mata har wancan lokacin ma da ya kasa shiga gidan bai taba fasawa ba.
Amma yanzu komai ita takeyi, hatta katin wutar NEPA duk ita take siya ga subscription na TV da sauran cefanen gidan. Yanzu kuma gashi an ce mata kudin hayar ya kare; tabbas dole ta nemi kudi.

Ta fara jiyo kiran sallar la’asar don haka ta mike; gara tayi sallah sai ta wuce gidan Zahida suyi shawara tunda yanzu sai karfe biyar zata je ta dauko Amira daga makaranta.


UWAR SADDIKU


Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)


33

Zahida tana kallonta ta tabbatar da matsala; bayan sun gaisa ta dubeta tana dariya tace

‘Me kika kunso ne bakinki yake motsi haka?’

Tayi dan murmushi tana mamakin yanda Zahida take iya fassara duk wani motsi nata tun kafin ma tace wani abu, ta gyara zama tace

‘Hida akwai matsala fa.’

Nan ta gayawa Zahidan abinda yake faruwa ta kara da

‘Yanzu ban san yanda za ayi ba, kinga dai albashi na yanzu duk a kan cefane da kula da gida suke tafiya. Wallahi sai caji kaina yake.’

Ta dafa cinyarta

‘To ke Yaya Aisha ki koma gida mana, ya za ayi ma ki biya masa kudin haya? Ki tashi ki basu gidansu ki koma gidan Hajiya tunda idan ya dawo hayyacinsa ya san inda zai sameki.’
Ta jijjiga kai, tace
‘Ba zaki gane ba Hida. Ai na gaya miki ko zan bar gidan nan to sai ya dawo hayyacinsa; kin san matarsa cewa tayi wai tana bani shawara na koma gidanmu, idan na tafi ai bukatarta ta biya kuma in Sha Allahu bata isa ba. Ina nan sai karyarta ta kare.’

‘Hmmn! To ko Yaya Abubakar zaki gayawa?’

Ta kama haba tana zaro ido

‘Wa! Wannan ai kadan yake jira ya murdewa auren nawa wuya saboda takaici, ba zan gaya masa ba wallahi.’

Sukayi shiru na dan lokaci, jimawa kadan Aishan tace

‘Ni kin san me nake tunani? Account din da nake tara kudin hayar gidan zoo road ina da kudi sosai a ciki, duk da kudin kinga ni da su Abdallah ne. Da na yi niyyar ba zan taba account din ba sai nan da shekaru kamar goma lokacin Abdallah ya gama secondary watakila ma ya gama jami’an, amma dai inaga a ciki zan biya.’

‘Kinga kuwa Abdallah yanzu ma zai shiga secondary din. To amma ai zaki iya yin hakan mu gani, Allah yasa dai kada abun ya dauki lokaci. Kuma ma kafin Abdallah ya gama secondary din inaga zaki samu ki mayar da kudin sai kiyi abunda kika tsara da su.'

‘Uhm, hakane.’

Haka suka karasa hirarrakinsu bayan sallar la’asar Aisha tayi mata sallama ta wuce ta dauko Amira daga makaranta sannan suka koma gidan.
……….

Bata son Jibrin ya san itace ta biya kudin hayar don haka sai da ta bari washegari taje banki ta turawa mai POS kudin, daga baya ta turawa mai POS din account number din Jibrin din shi kuma ya tura masa kudin.

Bayan ya biya kudin ya tattara rasit din da sauran takardun biyan kudin ya bayar aka kai mata, ta karbi takardun ta adana.

Haka rayuwar Aisha ta cigaba, tun tana lissafin rabonta da Abba har ta daina rayuwarta kawai takeyi.
__

Kwanci tashi har lokaci yayi; duk yanda Sadiku ya so Abba ya canza masa makarantar da zai sake zana jarrabawar WAEC da NECO ya ki don haka dole ya hakura ya shiga cikin ‘yan ajin su Yusra.

Tun kafin a gama jarrabawar Sadikun suka hada baki da Yusra suka saka Mommy a gaba da magiyar so suke idan jarrabawa ta fito Abba ya kaisu Dubai ko Malaysia. Don haka ta saka Abban a gaba, kuma da yake sai yanda tayi da shi ba tare da wata matsala ba ya amince.

Musamman ya nemi agent wadanda sukewa mutane hanya zuwa kasashen; duk wani lissafi an yi masa kuma an bashi zabin jami’oi biyu a Dubai daya a Malaysia. Kudaden da aka lissafa masa suna da matukar yawa; ba wai ba zai iya biya bane to amma abu ne da za a dinga biya duk shekara. Gashi yau saura abinda bai fi shekaru biyar zuwa shida ba yayi retire. Duk wasu kudi da ya tanada don yayi business Zahra ta cinye; domin idan tace yayi mata abu baya iya musa mata, ita kuma gani take kamar daman kudi ya tara don haka da ta fadi abu daya yayi sai ta fado wani. Tun tuni yayiwa kudin business din illa don shine ma dalilin da ya sa ya kasa komawa Dubai din, tun Alhaji Abubakar yana masa tuni har ya gaji ya kyale shi. Yanzun ma kuma da take maganar a kai yara Dubai karatu ragowar kudin business din zai kwashe ya kaisu tunda registration din farko yana da tsada sosai.
……………

Kamar yanda ya saba kwanakin nan idan damuwa tayi masa yawa gidan Yaya Bello yake tafiya ya samu ya huta su yi hira domin a can baya samun wata damuwa, yau din ma bayan ya tashi daga aiki can ya nufa.
Tun safe yake lissafi a office din domin kansa har ciwo yake; a yau ne ya kamata ya biyawa Yusra da Sadiku kudin wata jarrabawa da suke bukatar su rubuta kafin tafiya kasar Dubai karatu. Sai dai har yanzu ya kasa tsayar da tunaninsa guri guda duk da dai ya amsawa Zahra.

Wajen karfe biyar saura kwata ya shiga gidan, nan take Karima ta bude masa falon baki ya zauna. Bayan sun gaisa ya tambayeta yaran tace suna islamiyya. Yace

‘Yayan bai dawo daga kasuwa bane?’

‘Ya dawo, kayansa kawai ya ajiye ya tafi masallaci ina jin hira ya tsaya a can.’

Ta fice daga falon domin kawo masa ruwa yayinda shi kuma ya kashingide domin ya jira dan uwan nasa.
Bai dade da zama ba Yaya Bello ya shigo gidan da sallama, nan take ya shige falon wajen dannuwan nasa.


Ya fahimci dan uwan nasa yana da damuwa amma sai dai duk wata dabara da zai masa don yaji cikinsa ya gagara. Duk da yana gani kamar wata fitnar ce mata suke masa a gidan tunda dama masu mace sama da daya basa rasa irin wannan abubuwan, don haka sai ya kyaleshi kawai yana yi masa addu’a. Domin ya kula idan ya cigaba da takura masa to lallai zai iya daina zuwa gidan ma.

Bayan sun gaisa da Abban ya kwalawa Karima kira yace

‘Kawo min furata mu sha ni da dan uwana.’

Ba tare da bata lokaci ba ta kawo damammiyar furar tare da kofuna.
Suna shan furar suna hirarrakinsu na duniya.

Jimawa kadan Yaya Bello yace

‘Ina Saddiku kuwa? Yana dai yin jarrabawar ko?’

‘Yana yi.’

‘To ma Sha Allah, Allah ya bada sa’a. Ai jiran ya isa haka idan ba ayi wani abu ba sai kaga yaro ya kama shiririta. Ga Hauwa’u nan itace ‘yar ajinsu yanzu har ta shiga level 2 a Bayero.’

‘Hakane Yaya. Shi din ma ai shi yayiwa kansa shirirta kuma uwarsa ta goya masa baya.’

‘Ai ka san sha’anin mata sai a hankali, sai kasa ido sosai.’

Sukayi shiru na dan lokaci.

Jimawa kadan Abban yace

‘Yanzu ma wai so suke a kaisu Dubai suyi Jami’an a can.’

Yaya Bello ya tashi zaune daga kashingidar da yayi ya dubi Abban yace

‘Dubai kuma? To kai kuma sai kace me?’

‘To Yaya ne me zance, sun hada kai da uwarsu sai faman magiya sukeyi.’

‘Wannan ma zance ne wanda bai kamata ka saurareshi ba, tarbiyyar nan mai wahala sannan ka dauki yaro dan shekara goma sha ka mikawa duniya. A’a ni ban yarda da wannan shirin ba. Da su da uwarsu tunaninsu duk ai iri daya ne idan ka barsu zasu kai ka su baro ka ne. Ga jami’oi nan muna da su a nan cikin garin Kano harda ma na kudi, ka zabi wadda zaka iya ka saka su. In ya so shi Saddiku idan ya fito da sakamako mai kyau sai a tattare kudi a biya masa ya tafi Dubai din yayi degree na biyu, ita kuwa Yusra ai kaga mace ce sai abinda hali yayi, tunda ko kafin ta gama Allah ya fito mata da miji aure za ayi mata.’

Ya jijjiga kai

‘Hakane Yaya.’

Jimawa kadan yace

‘To ai uwarsu ta matsa ne Yaya.’

‘To ai ba saurara mata zakayi ba, idan Kuma tsoronta kake ji ni sai na zo gidan na sameta. Amma yara babu inda zasu je gaskiya, kuma musamman shi Saddikun wanda nake ta gaya maka sai ka kara sa masa ido.’

‘Hakane Yaya, in Sha Allah an bar wannan maganar tunda kace haka, ko babu komai kuma zancenka gaskiya ne.’

Haka suka gama hirarsu Saida sukayi Sallar Magriba sannan Abba yayi masa sallama ya kama hanya.
……….

Tunda suka rabu da Yaya Bello yake neman hanyar da zai sanarda Zahra ya fasa kai su Saddiku Dubai karatu amma ya rasa, ya dai sanarwa agent din da yake masa aiki cewa ya fasa. Har sati ya zagayo bai sanarwa Zahra ba sai dai kawai shi a zuciyarsa ya yanke ba zai kaisu din ba.

Ranar Lahadi ce lokacin yara sun tafi tahfiz sai Yusra da Saddiku wadanda kowannensu yana dakinsa.

Yana zaune a falon sama yana kallon TV yayinda take kasa tana yiwa Jummai bayanin aiyukan da zata yi mata a gidan. Bayan ta gama bayar da bayanin ta haye falon saman ta shiga da sallama, bayan ya amsa sallamarta ta karasa ta zauna a kusa da shi tana fadin
‘Barka da hutawa.’

‘Yauwa.’

Dukansu suka mayar da hankali kan kallon talabijin din da take gabansu, jimawa kadan tace

‘Uhm, jarrabawar su Yusra ta tafiya Dubai din an saka ranar ko har yanzu shiru?’

Ya dan muskuta ya dubeta yace

‘Oh, ashe fa ban gaya muku ba Yaya Bello yace ma a barsu a nan in ya so duk wanda ya gama degree dinsa na farko da sakamakon mai kyau sai a kaishi Dubai din yayi degree na biyu. Ai na ma sallami agent din ina ga su fara a nan BUK.’

Ta kalleshi cikin bacin rai

‘Yaya Bello kuma? To yanzu don Allah yaushe ya fara zaba maka abinda zaka yiwa yaranka? Shi da ba shi zai biya musu kudin makaranta ba. Kuma sai da aka gama magana ni da yara duka mun gayawa dangi zasu tafi Dubai karatu kuma sai kazo ka fasa.’

Cikin halin ko in kula yace

‘To sai ki gaya musu sai sun gama first degree zasu je Dubai din, tunda kin ga dai ai ba zan saba maganar Yaya Bello ba ko?’

Ta gyara zama ta ja tsaki

‘Wannan ai sai ya koma bakin ciki, don mutum ba zai iya kai yaransa ba sai ya hana a kai na wani? Gaskiya sai ka sake shawara don wannan ai mayar da aiki baya ne.’

Ya gyara zama ya fuskanceta

‘Ban tara kudin da na isa Yaya Bello yayi min bakin ciki ba kuma bana taba jin zan taba yi, kuma yana da damar ya yanke hukunci a kan dukiyata ko ‘yayana. Sai dai idan hukuncin bai yi miki ba ki sameshi kiyi masa magana.’

Ya tashi ya shige daki ya turo kofa.

Ta bi bayansa da kallo cike da takaici; tabbas wannan bakin ciki ne muraran ina ruwan wani Yaya Bello da kai yara karatu shi da ba da kudinsa za a kai yara makaranta ba. Kuma ya za ayi yace ta yiwa Bello magana. Kaf danginsa babu mutumin da yake mata kwarjini kamar Bello, ita gara ma ace ta yiwa Hajiya magana a kan ace ta yiwa Bello.

Ta ja tsaki ta mike a fusace ta shige dakinta.

Yaya Bello bai saba yi musu shisshigi a al’amuransu ba, kwata kwata ma sau daya ya taba bata haushi lokacin da ya sa sunan Rukayya ba tare da yayi shawara da ita ba. Amma yanzu tana zargin yawan zuwan da Abban yakeyi gidansa a nan yake zuwa ya zazzage masa cikinsa shi kuma ya sami damar yi musu shisshigi. Yanzu ta riga ta gama gayawa danginta da kawaye cewa yaranta Dubai zasu tafi karatu yanzu kuma ya zo ya sa a fasa. Su kansu yaran bata san yadda zasu dauki abun ba musamman Saddiku. Ba zata iya yiwa Bello magana ba amma tabbas zata san yadda zatayi don ita kanta ta fi gamsuwa da karatunsu a Dubai din.

Tana jinsa ya fita, sai dai duk da bai gaya mata inda zai je ba ta san gidan Hajiya zai je kuma daga nan yaje gidan Yaya Bello.

Sai da ta tabbatar ya fita sannan ta fito daga dakin ta wuce falo ta dauko wayarta ta koma dakinta ta zauna a kan gado. Ta lalubo lambar Yaron Malam ta danna masa kira; domin tana ganin gara kawai a toshe mata bakin Yaya Bello ya fita daga idonta.

Tana daf da tsinkewa ya dauka, bayan ya amsa sallamarta yace

‘Hajiya yi hakuri ina kan wani aiki ne, idan kina son magana dani da gaggawa ki turo sako ta Whatsapp idan ba haka ba kuma da na gama aikin zan kirawo ki.’

Kafin ta amsa ya katse wayar.

Ba zata iya jira ba don haka ta budo Whatsapp ta fara tura masa sakon voice note

“Yaron Malam wani aiki nake son ayi min. Akwai wani wan mijina wanda ya fara yi min shisshigi ni da yarana saboda ya ga danuwanshi ya fara samun kudi. Ina so a kawar min da idonsa daga kanmu ko kuma ma a hana dan uwan zuwa inda yake.”

Bayan ta tura wannan kuma ta rubuta wani sakon ta tura

‘In ka gama aikin mayi magana.’

Ta tura sannan ta fice daga dakin.

Sai can bayan la’asar sannan Yaron Malam ya kirawota; tayi masa bayanin abinda take so wato Yaya Bello ya fita daga harkarta. Yayi mata alkawarin zai yi mata aiki inda suka amince zata tura masa naira dubu talatin kudin aiki. Suna ajiye waya ta tura masa kudin, bayan kudin sun shiga ya sake kiranta ya sanar da ita yaga kudin, sannan yace
‘Bayan kwana biyar ki sake tayar da maganar, in Sha Allah ba zai sake yi miki shisshigi ba.’

Sukayi sallama tana cike da jin dadi.
---------

Saida ta bawa maganar sati biyu sannan ta sake tayar da ita. Sai dai abinda ta sakankance zai faru ba shine ya faru ba, domin Abba yana nan a kan bakansa. Ya jaddada mata cewa yara babu inda zasu je karatu suna nan a Nigeria sai dai idan Yaya Bello ya yarda. Ya sanar da ita cewa jiya ma sun yi magana da Yaya Bello kuma yace da zarar result dinsu ya fito a bashi akwai wanda zai bawa a samar musu admission a BUK ko Northwest.

Sosai hankalinta ya tashi don ta zata an bar wannan maganar. Duk yanda ta so ya saurareta ya ki, sai dai ya bata dama taje ta sami Yaya Bello idan har yace a kai yara Dubai to za a kaisu amma muddin bai ce ba to suna nan a BUK.

Ranar da sukayi magana ranar Juma’a ce da daddare don haka ranar asabar wajen karfe takwas na safe ta dauki mota ta wuce gidan Yaya Bello; ta gaji da wannan fin karfin gara taje taji da kanta musamman da yake yaron Malam yace mata yayi aiki a kansa.

Lokacin da ta shiga gidan daga Yaya Bello sai Umman su Muhammad wadda, suna zaune a falo suna karin kumallo domin yaran gidan duk sun tafi tahfiz sai Muhammad kawai da Shukuriyya wadanda sune manya kuma su ‘yan Jami’a ne.

Bayan sun gaisa Umman Muhammad ta kwalawa Shukuriyya kira daga kicin tace

‘Shukuriyya kawowa Antinku wainar geron idan kin kwashe.’

Ta dubi Zahra tace

‘Bari a kawo miki wainar geron.’

Ta mike tana fadin

‘Shigo mu koma ciki.’

Zahra tayi murmushi tace

‘Ki barmu a nan ma daman wajen Yaya nazo, sai dai ko muje ya gama cin abincin tukunna.’

Ya kurbe ragowar kununsa ya ajiye kofin yace

‘Na ma gama, kuyi zamanku. Ya yaran nawa? Duk lafiya kuke ko?’

‘Lafiya Alhamdulillah, duk suma sun tafi tahfiz.’

Sukayi shiru na dan lokaci alamar yana sauraronta. Ta gama nukunukunta tace

‘Yaya dama a kan maganar yara ne, Saddiku da Yusra da suke WAEC yanzu. Mun gama magana da babansu za a sama musu admission a Dubai kuma an fara shirye-shirye yanzu ya zo yace wai BUK zasu yi. To kuma Yaya yaran duka suna da kokari su don saura ma kadan a sami admission din yace a bari.’

Yayi gyara murya don ya so ya fuskanci inda zancen ya dosa

‘Eh, munyi magana da shi don nine ma nace masa ya barsu su fara a nan din idan sun fito da sakamakon mai kyau sai su tafi kasar waje karatun degree na biyu. Ina ganin kamar hakan zai fi tsari da tarbiyya musamman a wajen ita Yusra din. Kuma karatun ma na nan ai ba gagararsu zai yi ba kamar yaune zaki ga sun gama musamman da yake dukkansu suna da kokari sosai.’

‘Uhmm!’

Ta hadiye malolon da ya tokare mata makogoro.

Har yanzu ta kasa gane dalilin da yasa mutumin nan yake mata kwarjini, duk inda ka tsaya a gabansa sai ya sha gabanta ya cika maka ido. Yau din nan zuwa tayi ta kora masa jawabi amma gashi ta kasa, tayi zaton ma zata ga ya rage kwarjini saboda aikin da akayi a kansa amma sai taga kamar ma kara masa kwarjini aka yi.

Umman Muhammad tace

‘Hmmm! Ka san dai karatun a can yafi a nan nutsuwa da sauri Alhaji, sai dai kawai da yake kayi maganar taribiyya amma fa da banbanci.’

Yayi gajeriyar dariya yace

‘To ai komai lokacine, yaran da wataran ma da kansu zasu kai kansu duk inda suke so a duniya musamman shi Saddikun da yake namiji.’

Tayi gyaran murya tana murmushin yake

‘Bari na tafi don nayi sauri na koma.’

Suka mike kusan lokaci guda ita

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login