Showing 48001 words to 51000 words out of 166068 words
bude kofar motar yana fadin
‘Shigar da motar, bari na je na ji.’
Ya fice Malam Sule ya tura motar ciki.
Yana isa gate din Aisha tana budewa, sanye da jilbab dinta. Ta dubi me ruwa tace
‘Sauke min a nan.’
Ta nuna masa wajen daga ciki.
Abba ya karasa shiga da fara’arta tace
‘Alhajin Allah, Sannu da zuwa.’
Da fara’a shima ya amsa sannan yace
‘Ya naga Dan ga ruwa?’
‘Uhm, ruwan ne Ina jin ya sami matsala shi yasa ba a kunnawa.’
Ta nunawa dan ga ruwa bokitin fentin da ta ajiye tana fadin
‘Juye a nan na dauka.’
Abba yace
‘Ke kike kaiwa ciki.’
‘Eh ai saboda nauyi, in na kai sai na dawo na kara kaiwa har na cika drum din.’
‘Gafara.’
Ya dauki jarkar ya nufi cikin gidan ta bi shi a baya yana tamabaya
‘A Ina kike juyewa?’
‘Akwai drum a kitchen.’
Yana shiga falon Rukayya da Amira suna zaune suna kallon TV. Duka suka mike suka yi masa sannu da zuwa ya amsa ya wuce kicin ya juye ruwan. Ya dawo ya sake dauko wata jarkar ya komo ciki.
Rukayya ta dubi Amira tace
‘Bari naje na gayawa Mommy Abba ya dawo.’
Ta fice da gudu suka hadu da Abban a tsakar gidan yana dauke da jarka tace
‘Abba bari naje na cewa Mommy ka dawo.’
Ta fice da gudu.
Haka ya gama juye mata ruwan ya cika mata drum biyu sannan ya fito ya sallami Dan ga ruwa ya koma ciki.
A daki ya sameta tana goge inda ruwa ya zuzzube, ya tsaya yana kallonta yana murmushi.
Ta dubeshi itama tana dariya tana fadin
‘Bari na sama maka ruwa ka dan sha.’
Ta zo wucewa ta gefensa ya sha gabanta ya janyota jikinsa ya rungumeta, suka sa dariya.
Bayan sun fito falon ta ajiye masa kunun aya mai sanyi da cake, ya ci ya koshi suna dan taba hira sannan yayi mata sallama ya wuce gidan Zahra.
UWAR SADDIKU
Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)
18
Tunda Rukayya ta kawo labarin ya dawo yana can yana diban ruwa Mommy take faman cika tana batsewa, dama Malam Sule ya shigo da karamar jakarsa.
Sai a lokacin sannan Mommy ta tuna Sadik ya yanke wayar injin janyo ruwan, ta dubeshi tace
‘Sadik baka mayar da abun nan ba ashe?’
‘Wallahi na manta Mommy, ba komai kafin dare zan mayar.’
Suka cigaba da harkarsu yayinda ita kuma ta wuce daki.
Duk nishadin da take ciki ya gushe saboda gaya mata da akayi yana can gidan Aisha yana kai mata ruwa. Ce mata yayi a nan wajenta zai sauka amma saboda munafinci yana can wajen amaryarsa yana hutawa, tabbas zai zo ya sameta.
Da sallama ya shigo gidan, tana sama ta jiyo yara suna oyoyo. A falon saman tayi zamanta tana jiransa tunda dama a nan ta saka masa abincinsa.
A zaune ya sameta a kan kujera tana ta cika tana batsewa, bai ma kula da yanayin fuskarta ba.
Yana rike da hannun Ummi ya shiga falon da sallama, bayan ta amsa sallamarsa ta bude baki kamar wadda aka yi wa dole tace
‘Sannu da zuwa.’
Ya karaso ya zauna a kusa da ita bayan ya amsa yace
‘Ya akayi babu ruwa a gidan Aisha ne, me ya sa ba a kunnawa ruwa yaje can na ga kuma nan da ruwa don fanfon waje ma a kunne yake?’
Ta dan gatsina fuska
‘Lalacewa yayi ina ga don kullum kuwa ana kunnawa, kuma bata fada baya zuwa ba ai da an duba.’
Ya gyara zama ya zaro waya, ya lalubo lambar wayar plumber ya danna masa kira, tana ji yana cewa lallai ya zo kafin la’asar don yau yake so a gyara ruwan nan.
Ranta ya kara matukar baci; tun da ya dawo unguwarnan yake hidimar Aisha kuma har yanzu ma ya shigo wajenta kallon kirki bata isheshi ba balle ma ya san yanayin da take ciki.
Ta daure ta tashi ta nufi dining table don ta kula sai ma tayi da gaske sannan zai dubeta. Ta dauko jug din zobon da kofi ta dora a kan tray ta kawo inda yake zaune shi da Ummi ta ajiye. Ta fara zubawa yace
‘Kai ba zan sha zobon nan ba ruwa dai zaki bani.’
Ta bishi da kallon mamaki, to me yake nufi?
Ta dauke zobon ta mayar kan table ta dauko masa ruwan roba ta kawo masa ta koma ta zauna.
Ya bude ya sha kamar rabin roba sannan ya dubeta yace
‘Ya na sameku? Ya gidan da yaran?’
Ta dan yi murmushi tace
‘Lafiya muke gaba daya, ya ibada? Ya gajiyar hanya?’
‘Lafiya kalau, mun gode Allah. Bari na watsa ruwa na fito na ci abinci kin san ban yi breakfast ba.’
‘Sai ka fito.’
Ya shige dakin tabi bayansa da kallo.
Sai da ya dauki lokaci ya shirya sannan ya fito, ya ce ta saka masa abincinsa a kan kafet ba zai ci a tebur ba don haka nan ya baje a kan kafet ya ci funkaso sosai ya shanye romonsa.
Naman sallan da ta sa masa a plate kuma ya ajiye a gefensa yana ci suna hira da yara. Sai a lokacin ne take jajanta masa barin da Aisha tayi, duk ba bata je ko kofar gidan ba haka kiri-kiri tace masa ta je.
Can zuwa azahar yana zaune a falo yana hutawa maigadi ya shigo ya sanar da shi isowar plumber, don haka ya tashi ya fice.
Kamar yanda al’adarsa take idan dai za ayi wani gyara a gidan nan to sai dai ayi a gabansa, don haka yau din ma tare suka zagaya bayan gidan.
Mai gyara yayi 'yan dube-dubensa ya juyo ya dubi Abban yace
‘Yallabai yara sun yi wasa a wajen nan dai ko?’
‘Ka san bana gari, ba zan iya sani ba. Me ka gani?’
Ya janyo wata waya ya dan matsa yadda Abban zai hango yana fadin
‘Ka ga wayar da aka yanke nan Alhaji, don gaskiya ba tsinkewa tayi ba sai dai ko idan reza aka saka aka yanketa gaskiya. Tunda kuma ka ga ita kadai aka yanke balle ace bera ne ko wani abu, kuma idan bata jiki ruwa ba zai shiga wancan tankin ba.’
Jijjiga kai kawai yake yana mamaki, to waye zai yi haka?
‘To yanzu ya za ayi da wayar kenan.’
‘Kada ka damu yallabai, ai yanzu za a fiketa a hada ai wannan karamin aiki ne.’
Nan da nan kuwa aka gyara wayar, ya sallami mai gyran ya saka kujera a tsakar gidan ya zauna yana tunani.
Ya gaji da zama ya tashi ya shiga ciki ya sanar da Mommy zai je gidan Aisha.
A tsakar gida ya sami Rukayya da Amira suna ‘yar gala-gala, bayan ya amsa sannu da zuwan da suke masa ya shige ciki.
Tana zaune a kan kujerar dining table tana cin dabino wanda shine yazo da shi yayinda take karatun littafi.
Tayi masa sannu da zuwa bayan ta amsa sallamarsa. Ya karasa ya ja kujera kusa da ita ya zauna yana fadin
‘Matar Alhaji, dabino kika saka a gaba haka kina ci kamar wani nama.’
Tayi dariya tace
‘To me yafi raina.’
‘Ina naman Sallah na ko baki ajiye min ba.’
Tace
‘Nama kai, ya za ayi naci na manta da mai gida.’
Ta tashi ta shiga kicin, jimawa kadan ta fito da nama a faranti tangaran ta ajiye masa. Ta koma ta dauko kunun aya a fridge ta ajiye tana fadin
‘Ga wannan saboda naman ya fi saurin wucewa.’
‘Yauwa matar Alhaji.’
Ta zauna tana dariya. Ya dan ci naman ya kora da kunun aya, bayan ya ajiye kofin yace
‘Wannan ma ai naman rago ne, ina naman san yake. Naman ragon ma da ba wani yawa ne da shi ba amma shi kika soya har ya kawo yanzu?’
Tayi dariya
‘Kai dai kaci nama, bari in sa maka filo a bayan kujerar kada ka fadi saboda santi don naman nan ya ji onga.’
Shima dariyar yayi, ya rike hannunta wanda take kokarin karo bayansa da shi ya kalleta suka hada ido na dan lokaci, ta sunkuyar da kanta. Ya kirawo sunanta
‘Aisha.’
Ta dago suka sake hada ido, yace
‘An kawo miki naman Sallah ko ba a kawo ba.’
Tayi murmushin yake ta kawar da kai, ta so ace ya bari idan aka kwana biyu ya huta sai ayi wannan maganar amma daga dawowa ya rutsa ta. Tace
‘Ba a kawo ba.’
Ya saki hannunta ta gyara zamanta, yace
‘To a ina kika sami wannan naman?’
Ta kalleshi tace
‘Nayi layya fa kuma ka sani, a gidan Umma aka yanka aka soya danyen kuma yana freezer na sawa a miya.’
‘Kice bana baki barwa Umma naman ba gaba daya ragon kika kwaso.’
‘A’a wallahi, Umma kam nama ai sai dai ta bayar don ya ma yi mata yawa.’
Ya cigaba da cin naman yana dan janta da hira; sai dai ko ita kanta tana iya gane ransa a bace yake. Suna hirar yana tunani; shekara ta kusan biyu kenan da aurensa da Aisha amma zai iya cewa bai taba bata naman layya ba kawai saboda mugunta irin ta Zahra. Yana mamakin ma yanda ita Aishan wadannan abubuwan basu dameta ba, don bata ma so ayi zancen. Ya tabbatar da Zahra aka yiwa haka tabbas da duk garin nan sai kowa ya ji.
Ya ajiye kofin yayi mata sallama.
Rukayya da Amira suna nan a inda ya wuce su da zai shiga, ya kirawo Rukayya ta taho wajensa da sauri ta sameshi a kan barandar falon.
‘Gani Abba.’
Ya kama hannunta ya dubeta suka hada ido yace
‘Rukayya bayan kwana biyu da tafiyata Hajji Anti tace ki kunna mata ruwa me yasa baki kunna ba?’
Ta kalleshi da sauri tana zaro ido
‘Allah Abba na kunna, ina shiga gidan ma na wuce baya na kunna.’
‘To ya akayi gidan Antin naki babu ruwa?’
‘Wallahi ban sani Abba, nifa ban ma san gidan nan babu ruwa ba sai yau da na dawo.’
‘Kika dawo daga ina?’
Ta zaro ido tare da rufe bakinta saboda ta tuna wannan abu ne da Mommy tace mata kada ta sake Abban ya sani amma bata san yanda akayi tayi wannan maganar ba. Ta kalleshi idonta ya ciko da kwalla tace
‘Ba daga ko ina.’
Ya ja hannunta ya zauna a kan dakalin da fulawowi suke ciki, ya tsugunar da ita a gabansa ya kalleta suka hada ido. Tayi sauri ta sunkuyar da kanta tana fitar da kwalla.
‘Kin san bana son kuka ko Rukayya?’
Ta daga kai alamar e, yace
‘To maza ki share hawayenki, babu abinda zan yi miki kuma na tabbatar bakiyi min laifi ba.’
Ta share hawayen tana murmushin yake.
‘Kada kiyi min karya, tunda dama karya ba dabi’arki bace gaskiya kawai zaki gaya min.’
Ta daga kai alamar to, ya cigaba
‘Ina kika tafi da kika dawo yau din?’
Da kyar ta bude baki tayi magana saboda ta san zata sha fada a wajen Mommy
‘Dama ranar da ka tafi da daddare shine Mommy ta turo Yaya Sadik da Yaya Yusra suka tafi dani tace ba sai na dinga taya Anti kwana ba, shine sai yau da safe tace na dawo.’
Mamaki ya kara cikashi, yana so ya boye tsananin fushin da yake ciki a gaban Rukayya don haka ya dan yi gyaran murya yace
‘Sai me kuma ya faru?’
‘Shikenan Abba.’
‘To je ki cigaba da wasanki.’
Ta tashi cikin sanyin jiki ta shige falon domin tun tuni Amiran ta shige ta barta.
Shi kuwa Abba kasa tashi yayi daga inda yake zaune, zuciyarshi sai kuna take saboda takaici. Kenan ma bai isa yace ga yanda yake so ayi a gidansa ba idan Zahra bata yarda ba; lallai dole ya nunawa Zahra bata isa ba.
Sai da ya fara gajiya da zaman sannan ya tashi ya fice daga gidan.
Yana bude gate din yaci karo da Malam Sule yana shirin kwankwasa gate din
‘Ya dai Malam Sule?’
Ya dan rage tsawo cikin girmamawa
‘Barka da fitowa Ranka ya dade.’
‘Yauwa Malam Sule. Nemana ake yi ne na ganka a gaggauce haka?’
Ya dan Shafa kai yana sunkuyar da kai
‘A’a Yallabai, zuwa dai nayi nayi maka bayani kuma na ce ka kara bawa Hajiyan hakuri, duk da dai tace min ba fushi tayi ba amma dai a bata hakurin.’
Mamaki yake yana kallon Malam Sule
‘Me ya faru da za a bata hakuri?’
Ya kalli Abban ya dan zaro Ido, don ya zata Aishan ta gaya masa shi yasa yake sauri yazo ya wanke kansa kada Abban yayi fushi da shi. Ya dan yi gyaran murya yace
‘Uhm, Ranka ya dade dama da baka nan ne bama samun tafiya da ita mu kaita makaranta saboda Hajiya Babba tace yara suna makara, to kuma ko nace mata zan dawo na kaita sai tace na bari ta tafi a motar haya.’
‘Malam Suleman! Kana nufin tunda na tafi a motar haya Aisha take zuwa aiki?’
Ya sunkuyar da kai yana shafa keya
‘Wallahi Alhaji ba laifina bane, babu bayanin da banyiwa Hajiya ba. To tace yara suna makara, to ba yanda zanyi.’
Sukayi shiru na dan lokaci, Abban yace
‘Shikenan Malam Sule.’
Ya sake rankwafawa
‘To Alhaji tuba dai nake, a kara bata hakuri. Um idan ba wani aiki ina so naje gida ne.’
‘Shikenan Malam Sule, babu wani aiki.’
Ya zaro mukullin daga aljihunsa ya mikawa Abban yana fadin
‘Sai a sanarwa Hajiyan gobe in sha Allah zamu jirata.’
Yayi masa sallama ya wuce.
Ya rasa tunanin me zai yi, kenan tunda ya tafi Aisha take zaman hakuri gashi har bari tayi amma bata nuna wata damuwa ba. To kenan ma ba Malam Sule ne ya kaisu asibitin ba da ta ce masa suna asibiti. Tabbas yau dole Zahra ta gane kurenta.
Yana bude gate din gidan zai shiga aka fara kiran sallar la’asar don haka kawai sai ya tsaya a fanfon tsakar gida yayi alwala suka jera da maigadinsa suka nufi masallacin da yake nan kan layin.
Bayan an idar da Sallah saida ya tsaya suka gaggaisa da mutane don haka sai wajen karfe biyar saura ya shiga gidan. Yana shiga ya kirawo maigadi yana tambayarsa wanda ya taba injin ruwa, yace
‘Wallahi ban sani ba Alhaji, ai kaga ba ni nake kunnawa ba Sadiku ne kawai yake taba wajen nan sai ko kannensa da wani lokacin suke kunnawa.’
Ya sallameshi ya karasa cikin gidan, babu kowa a falon domin yaran sun tafi islamiyya. Sadik ne kawai a dakinsa domin tunda ya shiga SS 3 ya daina zuwa islamiyya; sai yace wai karatu yake, ita kuma Mommy sai tace a barshi tunda Shirin jarrabawa yake.
Yana shiga tsakiyar falon ya kwalawa Sadik kira, tana zaune a falon sama da Sumayya a hannunta tana jiyo kiran da yakewa Sadiku ta san wani laifin yayi, ta ja tsaki ta fada a fili
‘Daga dawowa mutum ya ishi mutane da fada akan mace sai kace wata ‘yar gwal.’
A birkice Sadiku ya fito daga dakinsa saboda yanayin kiran.
‘Gani Abba.’
‘Wanene ya yanke min waya a injin zuko ruwa?’
Bai yi zaton tambayar ba don haka ya dan diririce, idanuwan Abban suna kansa don haka ya sunkuyar da kai yana wani cin magani cikin in ina yace
‘Ba ni bane.’
‘To wane shegen ne idan ba kai bane? Waye yake kunna injin kuma waye ya iya kwance kayan wuta a gidan.’
Ya shafa kai yana wasu
‘yan fisge-fisge na rashin gaskiya yace
‘Abba ni dai ba ni bane, sai dai idan ko bera ne don gaskiya ba ni bane.’
Bai yi aune ba sai saukar mari yaji a fuskarsa, ya dafe kumatun yana fitar da kwalla. Abban ya nuna shi yace
‘Kaine ka sa reza ka yanke wayar saboda kada ruwa ya dinga shiga tankin gidan Aisha, to Ina tabbatar maka ba zan dauka ba. Gidana ne don haka yanda nake so dole haka za ayi, da kai da duk wanda yake saka ku sani ba zan dauka ba.’
Har ya gotta Sadik din zai wuce ya dawo ya tsaya a gabansa yace
‘Na sa plumber ya gyara wayar sai ka sake zagayawa ka yanketa tunda kaine ka ajiye ni.’
Ya haye saman ya barshi a nan tsaye yana fitar da kwalla saboda takaici; ya manta rabon da Abba ya daukeshi. Tun yana JS 1 da sukayi fada a makaranta Abban ya zaneshi, sai yanzu zai mareshi saboda wannan banzar matar tasa. Dama Mommy saida ta fada zuwa zatayi ta rabasu da Abba; ai dole ma ya koyawa matar nan hankali. Yayi kwafa ya shige daki ya mako kofa.
………
Duk abinda ya faru tsakaninsa da Sadiku tana jiyowa, don haka yana shiga falon tace
‘Sadik wani abun yayi ko?’
Ko kallonta bai yi ba sai da ya kusa shiga dakinsa ba tare da ya juyo ya kalleta ba yace
‘Kizo yanzu, ina jiranki.’
Kafin ta amsa ya shige dakin ya mako kofar, don haka ta tashi ta wuce dakinta ta kwantar da Sumayya wadda ta riga tayi bacci.
Ta fuskanci da fada ya shigo don haka itama ranta a bace ta shiga dakin, yana tsaye a gaban mudubi ya rungume hannayensa ita kuma ta wuce gefen gado ta zauna.
Sukayi shiru na dan lokaci, Jim kadan tace
‘Gani.’
Ya zuba mata ido har saida ta gaji da kallon da yake mata ta kawar da kai.
Yace
‘Zahra.’
Ta kalleshi, suna hada ido ta sunkuyar da kanta.
Ya cigaba
‘Ranar da na tafi Sadik yaje ya yanke waya wadda take kai ruwa tankin gidan Aisha, na barku a kan Malam Sule ya cigaba da kaita aiki tare da ‘yan makaranta amma tunda na tafi kika hana kika ce yara suna makara kuma basa makara. Na bar Rukayya ta tayata kwana amma ina tafiya kika turo aka kirawota kika barta ita kadai. Na ce a kai mata danyen naman sallah kika hana a bata, kuma waccan sallar ma haka kika sam mata naman shine wannan kika hanata gaba daya. Me yasa? Wanne irin wulakanci ne wannan Zahra?