Showing 54001 words to 57000 words out of 166068 words
wannan murafun tunda ta san yara kanana ne. Ta dai fi zargin Sadikun da abokansa amma dama ta san a wajen Hajiya duk abinda Sadiku ya fada shine gaskiya.
Don haka ta zubar da murafun ta bar maganar tana fatan Allah ya sa abinda Sadikun ya fada gaskiya ne.
__
Kafin ya koma kwanan Aisha saida Zahra ta tabbatar ya sauko daga fushin da yake da ita; da taga kamar ba zai daina shareta ba ma dakanta ta same shi a daki ta bashi hakuri. Harda kukanta duk da dai a cikin ban hakurin ta gaya masa babu abinda tayi da niyya komai ta bayarda dalili. Ya riga ya santa da wannan halin ba zata taba daukar laifinta ba, shi kuma baya son kukanta don haka ya hakura da sharadin ba zata sake yi masa irin haka ba. Dare nayi ya wuce wajen Aisha.
__
Yana fita wajen Aisha a daren ta kirawo Amina don taji yanda akayi da gwal din da ta bayar a siyar. Tayi mata bayani an sayar sai dai gaba daya basu kai dubu dari biyu ba; bata ji dadin hakan ba saboda tana bukatar akalla dubu dari hudu ta tafi da su domin so take ayi mata aiki mai kyau musamman da yake zuwa yanzu duk wani ragowar hakuri da zata iya yi ya kare.
Tace
‘To ki ajiye min kudin na san zuwa karshe wata na danyi ciniki wasu sun biya bashi ba zan rasa dubu dari ba, in ya so dubu dari ko rantowa sai nayi.’
‘Ko kuma ki dan tsara Abban ya baki ba.’
‘Hmmm! Kawata barshi kawai ai yanzu baya hayyacinsa, zan nemo dai in ya so sai ya biya idan ya shiga hannuna don wannan aiyukan da kayan gyaran da na sha kafin ya dawo duk wallahi sai ya biya.’
Suka karasa hirarrakinsu suka ajiye waya.
Haka ta kwana tana tunanin inda zata sami rancen dubu dari.
Suwaiba zata fara tambaya tunda ta san tana aiki kuma ko bata da shi ta san zata ranto mata a wani wajen.
Kawai dai dole ta jira sai karshen wata ta dan hada ciniki, gashi yanzu watan ya kama. Amma bata da wani zabi haka zatayi ta zaman hakuri har karshen wata.
UWAR SADDIKU
Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)
20
Baifi sati daya da dawowa ba ta gama hada kudin motar da take son siya, don haka ranar da ya kaita ta mayar da Amira gida sai da ta sakashi ya biya da ita gidan Yaya Abubakar. Baya nan don haka ta barwa Anti Fauziya sako kan zata tura masa kudin ta account dinsa.
Duk wannan shirin da take yi bata bari Abban ya sani ba, bata son ta gaya masa don idan ta gaya masa akwai yiwuwar Zahra taji labari wanda ta san sai ta san yanda tayi ta sa ya hana sayen motar.
Sati biyu da gama maganarsu da Yaya Abubakar ya kirawota ya sanar da ita gobe zai kawo mata motar.
Abban yana wajenta amma a daren zai koma wajen Zahra.
Yana zaune a falonta bayan sallar magriba da faranti gireba a gabansa yana ci suna hira tace
‘Yallabai gobe fa Yaya Abubakar zai kawo min motata, ka san tun kwanaki nace maka zan sayi mota.’
Da mamaki ya dubeta yace
‘Ai na zata kin fasa, ni da nace ki bari zan saya muku kowa keda Zahra.’
‘Haba dai, to yanzu ba shikenan ba na hutar da kai in ya so sai ka sayawa Mommy din kawai tunda ni na riga na saya. Ka san fa tun kafin a fara maganar bikinmu kudin motar suke a hannunsa shi yasa yanzu yana yi min maganar kawai nace ya siyo.’
‘To Allah ya sa albarka, Allah ya tsare hanya. Ko nima na sami ta zaga gari ko kuma idan na fara neman aure na sami ta tsara bazawarata.'
Ta harareshi, ya kauda kai yana kallon gafe. Ta sa kafa ta dungureshi tana zumbura baki tace
‘Bazawara ko?’
Yana dariya yace
‘Au, ashe fa na cike gidan.’
Gaba daya suka sa dariya.
Shima yaji dadin sayen motar amma dai ya so ace ta bari shi ya saya, sai dai hakan ma yayi masa dadi tunda a halin yanzu dama baya son sayawa Zahra mota domin ya kula gaba daya ta canza hali.
Haka suka karasa hirarrakinsu yayi mata sallama ya tafi ya barsu ita da Rukayya.
_
Ranar babu aiki saboda gwamnati ta bayar da hutu. Yana zaune a falon sama ya gama cin abinci tana zaune suna dan taba hira. Wayarsa ce da take ajiye a gefensa ta dauki waka, saida ta dan yi dogon wuya ta leko screen din kafin ya dauke wayar. Sunan A’eesh ne ya fito a kan screen din wanda ta san Aisha ce, don haka ta kara nutsuwa ta tada kunnuwanta ko zata tsinci wani abun.
Yana dauka bayan sun gaisa tace
‘Yaya Abubakar ne yazo shine yake tambayarka.’
‘An kawo motar kenan?’
‘Eh, an kawo.'
‘To ma sha Allahu. Bari na dauko tukwici na taho.’
Suka ajiye waya ya mike yana dariya.
Ta dubeshi tace
‘Tukwicin me kuma zaka bayar?’
Da fara’arsa yace
‘Aisha ce ta sayi mota shine aka kawo mata, ai kinga dole na bayarda tukwici.’
Kafin tace wani abu ya shige dakinsa ya barta a zaune.
Tana nan zaune ya fito daga dakin a shirye yayi mata sallama ya fice.
Tabi bayansa da harara har tana kwafa; wato mota ma ya sayawa Aisha kenan? Bayan ta bashi hakuri kuma tana kallo yana zuwa yana kaita aiki yana daukota shine zai saya mata mota ita kuma ta barta da Malam Sule? Tabbas yau za ayi bala’i don bazata yarda ba. Ai tun kafin ya auri Aisha take lallabarsa ya saya mata mota amma kullum yana shirya mata zance don haka wallahi dole ma ya zo yaji bayaninta.
………..
A tsakar gidan ya samesu a tsaye da Yaya Abubakar din da kuma Yaya Zainab suna ta duba motar; baka ce kirar Honda Accord ta zamani sai sheki takeyi. Kudin da Aishan ta tura masa naira miliyan dayane da dubu dari ta san bazasu sayi wannan motar ba don haka tana tsaye ta rike hannun Yaya Abubakar din sai faman tsalle take ta kasa tsayuwa guri daya saboda tsabar murna. Ko shi ma Abban da yaga motar yayi mamaki don bai yi zaton Aisha tana da kudin da zata iya sayen wannan motar ba.
Ya karasa suka gaisa sannan ya ja hannun Abubakar suka koma falo, ta kawo musu lemo da cake sannan ta ja Zainab suka dawo wajen motar. Zainab ta dubeta tace
‘Allah ya sa dai baki manta tuki ba, don fa tun rasuwar Abban su Abdallah rabonki da tuki.’
‘Ban manta ba, kuma shima yace zamu dan fita tare na kwana biyu ya tuna min kafin na fara fita ni kadai.’
Suka dan taba hira sannan sukayi sallama, Abban Sadik ya kawo naira dubu ashirin sababbi kar ya bawa Zainab yace tayi tukwici.
Nan suka bar Aisha ita da Abba tana ta murna ta kasa barin wajen motar.
Saida aka fara kiran Magriba sannan ya fita masallaci daga can ya koma gidan Zahra tunda dama kwananta ne.
Tunda ya shiga gidan ya kula da yanayinta ya san a kan taji ya ambaci mota ne, don haka shima ya shirya mata. Ta riga ta fara bayyana masa halayenta don haka yanzu kwata-kwata ba zai sake saurara mata ba.
Ta so ta danne ta bari sai yaje sunyi sallama da Aisha idan ya dawo sai ta tada maganar amma ta kasa hakuri.
A zaune suke a falon sama suna cin abincin dare, tuwon ne miyar kubewa danya tayi. Gaba daya hankalinsa yana kan abincin yayinda ita kuma take yafutar abincin tana satar kallonsa. Ta dai kasa daurewa tace
‘Wai ni dazu mota ka siya ne naji kana zaka bada tukwici, ban fahimci zancen ba.’
Ya hadiye lomar da take bakinsa ya mayar da cokalin cikin kwanon sannan ya dubeta yace
‘Bakiji me nace miki ba dazun, Aisha ce ta sayi mota shine Yayyanta suka kawo mata. To kinga ai dole na bada tukwici tunda an kawo mana abun arziki.’
Ta ajiye cokalin da take tsikarar tuwon da shi tace
‘Ban gane Aisha ta sayi mota ba, ko dai ka saya mata mota?’
‘Ni ban saya mata mota ba, idan da na saya mata ai tare zan saya muku. Ita da kudinta ta sayi mota sai dai ko idan Yayan nata yayi mata ciko don shima yana da dukiya sosai.’
Ta kalleshi yana ta faman zura lomar tuwonsa ba tare da wata damuwa, ta kare masa harara sannan tace
‘Kana nufin kace min albashin malamin makarantar ne ya sayi mota? Koko dai kana nufin kace min kun hada baki ka saya mata mota don kayi min wulakanci.’
Sai da ya kalleta suka hada ido sannan ya kai lomar tuwonsa, ya ture kwanon ya sha ruwa sannan ya sake dubanta yace
‘Ni ban saya mata mota ba domin idan na saya mata mota zan gaya miki don baki isa nayi miki karya ba, Aisha ta siya mota. Idan baki manta ba lokacin da kike ikirarin ta aureni saboda kudina na gaya miki ba haka bane don itama nan da kike gani mai kudin kantace, abun duniya ne bai dameta ba shiyasa kika ga tana rayuwarta haka.’
‘To naji mai kudi ta sayi mota, ni yanzu ya zakayi dani?’
‘Yanda na saba yi dake mana! Naga ga Malam Sule nan wanda dama kin hanashi yayi aikinta, kinga yanzu hankalinki kwance iya ke kadai da ‘yayanki Malam Sule zai dinga yiwa hidima. Ita idan na bata kudin mai sai ta kai kanta inda zata je.’
Ta share kwalla
‘Amma Abban Sadik tun yaushe nake maka magiyar ka saya min mota shine yanzu zaka zaga ka sayawa amaryarka kuma kazo kana ninkeni bai-bai ko!’
Yayi tsaki ya mike tsaye sannan ya bata amsa
‘Zahra! Bani na sayawa Aisha mota ba, ita ta saya. Ke kuma ba zan saya miki mota ba saboda na gaya miki bani da ra’ayin matata ta ja mota na fi so na sa driver ya kaiku duk inda zakuje. Itama din da kin bari Malam Sule yana kaita inda zata da ba zan bari ta sayi mota ba to amma kin hanashi yayi mata aiki. Ba zan iya daukar mata wani driver din ba kuma ba zan iya barinta tana yawo a motar haya ba kamar yanda bana barinki don haka kinga dole na barta ta sayi mota da kanta ko zan samu na huta da kaita unguwa da daukota. Wannan din tsarinki ne ai tunda da alama haka kika fi so, amma ni babu wata mota da zan siya.’
Kafin tace wani abu ya wuce ya barta a zaune.
Ta dauki lokaci tana zaune a wajen tana mamakin maganganusa, ita tunda take da shi ma bata taba tunani ya iya maganganu na tura haushi kamar haka ba.
Tayi kwafa ta mike ta wuce dakinta.
Haka ta kwana ita kadai a dakinta tana tunanin yanda zata bullowa lamarin nan; don tana son mota kuma ba zata taba bari ace kishiyarta tana da mota ita kuma bata da ita ba.
------
Tunda aka ce Aisha ta sayi motar nan Zahra ta kasa samun natsuwa, gashi bata son taja doguwar rigima da Abba tunda bata so ya bata mata shiri. Gaba daya ma yanzu zargi takeyi Abban yana kaiwa Aishan abubuwan da baya kawo mata, don haka a hankali ta samu take tura Yusra da Nana gidan don su gano mata abinda akeyi a gidan.
Aisha bata son suna shiga, musamman Yusra to amma babu yanda zatayi da su saboda gidan ubansu ne. Sai dai kawai idan suka shiga gidan sai ta sa mukulli ta kulle kicin dinta, dama basa shigar mata dakuna don haka suna falo itama sai ta zauna a dining table tana kula da motsin kowa. Basu cika dadewa ba saboda suma suna kula da yanda Aishan take kaffa kaffa da su.
………..
Ranar Juma’a ce don haka kamar yanda ta saba tana tashi daga aiki ta wuce ta dauki su Abdallah a makaranta suka je gidan Umma ta hado musu kayansu don gidanta zasuyi weekend.
Duk lokacin da sukayi irin wannan zuwan ta saba sai tayi musu cake ko wani snack, suci su koshi sannan su tafi da shi gidan Umma.
Tunda suka shiga mota yau Farha take mita
‘Mama yau ki soya mana kaza da yawa, Umma bata soyawa kullum a miya take sawa ba dadi.’
Abdallah da yake gaban mota yace
‘Mama wallahi karyane, idan an dafa ma da dadi. Kullum fa idan Anti Uwani ta soya na sawa a miya sai ta bamu dai dai.’
Tace
‘To idan kun yarda na soya muku kaza amma fa ba zan yi muku cake ba, kun yarda?’
Take suka hada baki sukace sun yarda.
Tana da kaza a gida amma wannan Abban Sadik ne ya siyo kuma miya takeyi da su tana yi musu peppersoup, don haka a hanya suka tsaya ta siyo kaji gidan gona manya guda hudu sannan suka wuce gidan.
Saida ta gama abinda takeyi wajen bayan la’asar sannan ta shiga kicin din, nan da nan ta gyare kajin nan ta sulalasu sannan ta zauna ta fara suya.
Kafin ta kwashe suyar farko Yusra da Nana suka shigo tare da Rukayya. Bayan sun gaisheta duka suka zauna a falo suna kallon TV.
Wajen Rukayya Abdallah da Farha suka samu suka zauna sunata yi mata surutu domin sun saba da ita, ita kuwa Yusar saboda yanda take kyararsu basa ko zuwa kusa da ita. Tana yawan kiransu Agola, ko kuma tace da su sun zo cin arziki kullum sai dai Aishan tayi ta yi musu bayani tana basu hakuri.
Tana kwashe suyar farko ta zubo a tray ta kawo falon kowa a cikin yaran ya dauki guda suka kama ci, Yusra ce kawai tace ta koshi don haka ta koma da yanka dayan nata.
Nan da nan ta gama, tana cikin juyewa a tray don ya sha iska Abban Sadik ya shigo, bayan yaran sun gaisheshi ya wuce kicin inda ya jiyo motsinta.
‘Hmm! Dabge ake mana ne nake jiyo kamshi tun daga kan kwana.’
Tayi dariya tace
‘Kaji ne nake soyawa yara, yau Farha tace basa son cake kaza suke so.’
Ya karasa ya sa hannu ya dauka, ta bude fridge ta zuba masa zobo a kofi ta mika masa tana fadin
‘Ga wannan a kora.’
Ya karbi kofin a hannu daya daya hannun kuma yana dauke da naman da ya fara ci ya fice daga kicin din ya shige dakinsa.
Ta dauki dan faranti ta zuba masa naman ta fito don ta kai masa. Farha ta taso da gudu ta sha gabanta tana fadin
‘Mama ki kara min, ki bani gizzard.’
‘To shiga gashi nan a tray ki dauki gizzard din.’
Ta wuce daki yayinda Farha ta shige kicin din da gudu.
Tana shiga dakin ta wuce kan mudubi ta ajiye masa naman tana fadin
‘Ga kari.’
Ya mika hannu ya kara daukan yanka daya yana dariya yana fadin
‘So kike ki cika min ciki idan ban ci abincin Yayarki ba ta hanani sukuni ko?’
‘Kada ka damu duka zaka cinye cikin ai danyar fata ce bata fashewa.’
Sukayi dariya.
A daidai nan ta jiyo Farha ta tsandara ihu, da hanzari ta fito yayinda Abban ya rufo mata baya domin ihun bai yi kama da na lafiya ba.
Tana isowa falon Yusra da Nana suna ficewa suka mako kofar.
Ta karasa da sauri tsakiyar falon inda Farha ke tsaye tana shesshekar kuka Abdallah yana tsaye rungume da ita shima yana kwalla. Rukayya tana shafa kansu tana basu hakuri.
Da gudu Farha ta karasa jikin Aisha tana kara kuka rike da kumatunta, ta dauketa suka karasa kan kujera ta zauna ta dorata a cinya yayinda Abba ya tsaya a bayan kujerar.
Aisha tace
‘Me ya faru Farha? Abdallah me aka yi mata?’
Yana share kwalla yace
‘Yusra ce ta mareta.’
‘Mari?’
Sai a lokacin ta dagata ta duba kumatunta. Yayi jazur musamman da yake Farhan fara ce sosai, ga alamar yatsu nan a fuskar har kan kunnenta.
Ta sake rungumeta saboda yanda take kuka har jikinta yana rawa.
Ta dubi Rukayya tace
‘Rukayya me ya faru ne? Har Yusra ta mareta?’
Ta sunkuyar da kai cikin sanyi murya tace
‘Ban kula ba ina jin dai bayan ta dauko naman ta zo wucewa ta takata shine ta mareta.’
Abdallah yace
‘Nima ta tureni saida na fadi na buge kaina, kuma tace mana shegu agololo ‘yan cin arziki.’
Ya karasa jikin Aishan yana fadin
‘Mama kawai ki mayar da mu gidan Umma, ai muma muna da gida ko?’
Abban Sadik ya zagayo ya zauna ya ja Abdallah yana shafa kansa tana fadin
‘Nan ma ai gidankune Abdallah kaji, bari naje naji yanzu zan gamu da Yusran.’
Ya fice ya bi bayan Yusran.
Yana shiga ya samesu a falon kasa suna zaune da Mommy suna mayarda maganar.
Bayan ya amsa sannu da zuwansu yace
‘Yusra me yasa kika mari Farha?’
‘Abba takani tayi, nayi mata magana tace min me siffar karuwai shi kuma Abdallah ya kawo min duka wai zai tare mata.’
Mommy tace
‘Kai daga jin wannan maganar ka san fada akeyi a gabanta tana ji tunda karamar yarinya kamar wannan ai bata kai ta san menene karuwa ba. Kuma idan banda cin fuska da wulakanci tana auren uban Yusra amma ta dinga ce mata me siffar karuwai, kawai saboda tana takamar ka daure mata ginda. Idan ita yaranta cikin gari suke rayuwa wadannan ai a nan muke da su cikin GRA a ina zasu koyi zagi irin wannan?’
Ta mike ta haye sama ta barshi a nan.
Ya dubi Yusra yace
‘Bana son karya Yusra, ita Farhan ce ta gaya miki haka?’
‘Wallahi Abba haka tace.’
Nana tace
‘Nima ina ji.’
Ya zauna yana jinjina zancen; tabbas yaransa basu iya zagi ba kuma basu saba yi masa karya ba, amma gidan su Aisha a cikin gari yake unguwar kofar Nassarawa; duk