Showing 30001 words to 33000 words out of 166068 words

Chapter 11 - UWAR SADIKU COMPLT BY SAKINA YAZID.txt

11 Jul 2024

25383

siyo sa kamar yanda na saba ko kuma na siyo muku raguna dai-dai ke da kanwarki yara kuma a basu biyu.’

‘Haba dai, ai sa ya fi auki. Idan ka siyo mana sa daya da rago ya ishemu gaba daya idan muka hadu muka soya sai a raba. Sai dai idan ita Aishan ta fi son rago sai a bata nata.’

‘A’a na san bata da matsala, bari dai naje kasuwar naji farashin dabbobin tukunna sai ayi wanda ya samu.’

Suka gama hirarrakinsu daga baya ta barshi a nan ta shiga kicin dora abincin dare.
……..

Sallah saura sati biyu Aisha ta tashi da wani zazzabi, da kanshi ya kaita asibiti. Aka yi mata duk wasu gwaje-gwaje da suka dace, aka tabbatar bata dauke da juna biyu, sai dai malaria don haka aka rubuta mata magunguna suka kamo hanya.
Har suka zo gida yana tsokanarta a kan shi ya fara murna har ya gama shawara idan mace ta haifa Aisha zai mayar idan kuma namiji ne Muhammad. Haka suka tsaya a chemist aka yi mata allurai sannan suka dawo gidan.

Kwana biyu ta fara warwarewa, da daddare suna zaune a falo ya mike kafafunsa ta tada kai da cinyoyinsa ta kwanta suna hira kuma suna kallon TV.

Yace

‘Wai Sallah ta kusa ke ko labarin kayan Sallah ba kya yi balle na abun layya.’

Tayi dariya tace

‘Wai da yake ba ni zanyi ba, kuma na san mai yi yana sane da lokacin.’

‘Lallai ne baki da matsala. To akwai leshina a wajen yayarki, gobe sai ki shiga ki zabi daya. Kin san tana sayar da kayan sawa shi yasa kawai nake sayen kayan sallar a wajenta.’

Ranta ya sosu, Yaya za ayi yace matarsa ce zata saya mata kayan Sallah ko an gaya masa ita babu masu sayar da kayan a danginta. Bata son ta ja maganar yaga kamar ta damu; kuma da yake tana da ragowar kaya a akwatin lefenta sai abun bai dameta ba sannan kuma akwai leshi da suka siya ita da ‘yan gidansu wanda daga Switzerland suka tura kudi aka siyo musu don nata ma yana wajen tele inda Zahida ta kai musu dinki, don haka tace

‘Ka gani ni dai ina fama da kaina gobe ban san yanda zan tashi ba, idan ka je kawai ka zabo min wanda ya burgeka.’

‘Ah bari ma kawai na kirawota ta turo min hotunansu sai ki zaba ko?’

Kafin ta amsa ya daga waya ya kirawo Zahra, wadda a take ta turo masa hotunan leshin ta Whatsapp.

Irin leshin nan ne mai hade da mayafinsa, ta san kudinsu basu wuce dubu ashirin da biyar ba. Bata raina ba, sai dai kuma leshin baya burgeta kwata kwata. Tabbas da anyi shawara da ita ba za a saya mata wannan leshin ba domin ita da a bata wannan gara a bata leshi marar mayafi ko ma atamfa. Ta duba su gaba daya ma kalolin ba wani kyau sukayi ba amma dai ta zabi wani kalar ruwan toka mai fulawoyi ruwan goro.

Ana kawo leshin ta kaiwa Hajiya tace a bawa Zahida ta kai mata dinki zasuyi waya.

Sai ana i gobe Sallah ya sanar da ita sa zai yanka da rago, kuma zuwa zatayi su soya tare a gidan Mommy in an gama soyawa sai a raba a dibarwa kowa nasa. Tsarin bai yi mata ba domin tun bayan zuwansu gidan Hajiya bata son shiga harkar Zahra, sai dai bata son tayi masa musu kada yaga kamar kullum itace take fara bashi matsala. Don haka tace babu komai hakan yayi.
Ta san Zahran ce ta shirya masa hakan kuma ta san don a cuceta ne, amma zata tsaya taga gudun ruwansu tukunna.


Amma dole a sake wannan tsarin don ba zata dauka ba.
------

Kudin kayan sallar da ya turo mata a ciki ta samu ta fidda dubu ashirin kudin aikin da Hajja tace zata yi mata; domin ko leshin da ta bawa Aisha ma dubu ashirin da biyar take sayar da shi amma a kan dubu hamsin ta bawa Abban.


Nan da nan ta kirawo Hajjan ta sanar da ita kudi sun samu, tayi mata alkawarin zata kawo mata aikin ana saura kwana uku Sallah.

Ranar asabar kuwa sai ga Hajja, bayan sun gaisa ta zaro farar kwalba irin ta fiya-fiya. Tarkace ne kawai a cikin kwalbar sai wani guntun tsoka da aka sokawa allura ga kuma takarda wadda ke dauke da rubutun larabci a jiki wadda aka nannade aka sakata a tsaye. Ta mikawa Zahra kwalabar tare da wata mitsitsiyar kwalbar baka tace

‘Kin gansu nan; wannan babbar ki sami singiletinsa wadda ya saka yayi gumi a jikinta ki gutsiri dan mitsitsi ki saka a ciki. Idan kika saka sai ki juye man da yake cikin wannan kwalbar ki mayar ki rufe. Ki samu waje mai duhu ki boye kwalbarki; idan kikayi haka to zaki sha mamaki don ya daina musa maganarki kuma duk abinda zai bata ranki ba zai yi shi ba.'

‘Allah Hajja.’

‘Ai sai dai idan bakiyi yanda nace ba, amma tabbas idan kinyi yanda nace to baki da matsala.’

Sukayi sallama tana ta jin dadi.

Ranar a wajenta ya kwana don haka singiletin da ya cire ita ta samu ta yanka ta hada kamar yanda aka umarceta. Ta samu waje a dakinta bayan wardrobe ta boye kwalbar. Ta kwana tana walwala da farin ciki.
Ranar Sallah ba a wajen Aisha yake ba, amma dai ya sanar da ita da safe zasu tafi da tuwon Sallah don su kaiwa Hajiya idan an sauko idi don haka itama ta zuba nata.

Tun dare Rukayya ta tayata ta gama miyar taushenta sannan ta hada zobonta mai dadi. Asuba nayi ta dora tuwo, da yake ba yawa ne da shi ba nan da nan ta gama. Suka gyara gidan tare da Rukayya suka yi wanka. Atamfa ta saka sabuwa kar dinkin doguwar rigar mai matukar kyau, tayi kwalliyarta sannan suka budade gidan da turaren wuta.


Zuwa karfe bakwai da rabi sun gama komai don haka Rukayya tayi mata sallama a kan zata je gida don kayanta suna can.

Bata dade da fita ba ya shigo tare da Sadik; tunda aka kawota yaune rana ta farko da Sadik ya shigo gidan kuma yaune rana ta biyu data taba ganinsa, don ko a unguwar bata hangoshi. Bata son yanda yake mata wani kallo mai cike da raini, amma dai haka ya gaisheta ta amsa.


Abbansa ya wuce daki tabi bayansa.

Basu dade da shiga ba suka fito, ta basu abincin gidan Hajiya a flask da kuma zobo a kula suka kama hanya.
………

Ya riga ya sanar da ita tsarin yanda suyar naman Sallah zata kasance, ya gaya mata ranar Sallah ake farawa a karasa washegari don haka idan an yanka za a zo ayi mata magana.

Sai wajen sha daya aka turo Rukayya ta kirawota, nan take ta canza kaya suka tafi tare da Rukayyan.

Masu aiki ne su biyu Uwar biyu da kuma Hansatu, sai Jummai, sannan kuma ga Asiya wadda itace ‘yar autar su Zahran wadda ta koma hannu Yayansu Muhammad tun bayan rasuwar mahaifiyarsu. Ana ta aikace-aikace, su Hansatu suna kokarin hura wuta, ta karasa suka gaisa da Mommy babu yabo babu fallasa. Su Jummai ma duk suka gaggaisheta, amma tana kallon Yusra bata gaisheta ba kuma babu wanda yace wani abu. Ta zauna ta kamawa Jummai nama suka cigaba da yankawa.

Murahu biyar aka dora don haka aikin nasu ya fara da sauri. Gaba daya naman san gida aka shigo musu da shi, sai raguna guda uku. Ya raba rago daya da rabi aka bayar sadaka a waje, aka sake shigo musu da rago daya da cinyoyin na biyun.

A take Mommy ta ware naman da za ayiwo musu dambun nama ta bayar aka tafi kaiwa.


Ragowar kuma ana soyawa ana kulle wani ana kai mata freezer.
Duk kaskon da aka sauke za a watso naman a faranti ace kowa ya taba, haka har magriba suna aiki. Babu laifi an soya da yawa don haka ana yin Sallah Mommy tace a barshi haka gobe a karasa.


A gajiye Aisha ta dauki ‘yar jakarta da ta shigo da ita tayi musu sallama ta koma gida.

Ta gaji, bata taba yin aikin sa ba don ita kullum raguna ake yanka musu. Ta so ace an bata nata naman tayi yanda take so da shi amma da yake wannan ne karon fari ta hakura; amma tabbas bazata sake wannan aikin hadakar ba. Danyen naman da taga ana sakawa a freezer tayi zaton za ace ga nata amma bataji an ce ba, tana jira taga goben tukunna.

Ranar ma ba a wajenta zai kwana ba don haka ita da Rukayya suka kwana. Tun bakwai na safe yayiwo mata waya yace su taho an fara aiki; da kyar ta tashi suka shirya suka fice. Tana sane taki cin abinci suka fice. Suna zuwa suka dan taba aikin ta fuskanci tayi kamar awa daya tana aiki ta cewa Mommy zatazo gidan tayi breakfast yanzu zata dawo. Ta fice ta barsu a ranta ta san ba zata koma ba don ta gaji.


Tana shiga gida taci abincinta ta koma bacci.
Sai can wajen azahar Zahra ta sami Abban Sadik din ta ce masa ya je ya turo musu Aisha saboda aiki yayi yawa. Take ya tashi ya nufi gidan.

Tsit gidan kamar babu kowa, don haka ya wuce daki. Tayi dai-dai a kan gado tana baccinta don ko motsinsa bata ji ba, saida yayi gyaran murya ya zauna a gefen gadon sannan ta farka.


Ta mutssike idonta tace

‘A’a sannu da zuwa.’

Bayan ya amsa yace

‘Lafiya dai ko, anata aiki ashe kina nan kina bacci.’

Ta yatsina fuska tana daga kwance

‘Jiri naji yana kwasata ga kaina yana ciwo shi yasa na zo na kwanta, ka san zazzabin nan ba wai ya gama sakina bane.’
‘Eh hakane.’

Ya kai hannu ya taba wuyanta

‘To kin sha Panadol?’

‘Eh, na sha kafin na kwanta da yake ban dade da kwantawa ba ka shigo.’

‘Ok, to sannu. Kwanta, bari naje sai nayi musu bayani.’

Yayi mata sallama ya fice.

Yana shiga ya wuce falo, don haka mommy ta bishi. Yana kokarin kunna TV tace

‘Abban Sadik lafiya dai Aishan bata dawo ba?’

‘Uh, bata jin dadi ne. Jiri take da ciwon kai kin san bata gama warwarewa ba tayi zazzabi kwanan na.’

Ta hadiye malolon da ya taso mata ta yage baki tace

‘Mhmm! Ko dai kanwata ciki ne da ita ne ake mana laulayi a fakaice.’

Yayi dariya yana shafa kai

‘A’a Babu wannan zancen tukunna, zazzabi ne dai kawai.’

Suka dan taba hira sannan ta tashi ta wuce dakinta, tana shiga ta zauna a gefen gado cike da damuwa; tabbas cikine da Aisha don jiyan ma tana kula da yanda take abubuwa jikinta babu kwari. Tab, ya za ayi ta bari a haihu da mijinta, gashi ta cika gida da yara mata yanzu idan Aishan ta haifi maza uku ko mutuwa yayi sai ta fita gadon arzikin da aka tara da ita. Gaskiya ba zata yarda ba.

Ta shafa hannunta inda aka saka mata inplant na family planning; tabbas da an koma aiki zata je a cire mata wannan abun don ya zama ko da bata sami hanyar lalata cikin Aisha ba to sai dai suyi haihuwar tare. Ba zata sha wahalar talaucin Yusuf ba kuma ya tara dukiya a fi ta gado. Haka ta zauna tayi ta tunani har saida Nana ta shigo kiranta ta sanar da ita an sauke wani ta zo ta nuna wanda za dora sannan ta taso ta fito.

Zuwa la’asar sun gama soya duk naman da za a soya, sai su Jummai da suke ta faman gyara wajen. Danyen naman kuma duk an lode a babbar freezer.

A falon kasa ta zauna ta dibarwa Hajiya nata naman cikin wata babbar roba mai murfi! Duk da Hajiyan ma ya yanka mata rago a gidanta amma haka suka saba sai an kai mata. Ta sami ‘yan bakaken ledodi ta zubawa su Jummai nasu tunda dukansu ta basu danye da yawa sun kai gida sannan kuma biyansu zata yi kudin aikinsu.

Ta dauko kwanon samira mai kamar girman langa tuwo da miya ta zuba naman har ta cika sannan ta rufe sannan ta dauko roba irin ta take away din nan ta zuba kayan ciki ta rufe.


Ta dubi Rukayya wadda take zaune tana ta cin naman tace

‘Rukayya dauki ki kaiwa matar ubanku.’

Tace

‘Anti Aisha?’

A fusace mommyn tace

‘Ba ita ba ni, kuma idan kin je ki zauna tunda uwarkice.’

Ta gane sakon don haka nan da nan ta dauka ta fice.

A falo ta sami Aishan tana zaune tana kallon TV tana shan zobo da cake. Bayan ta sake gaisheta ta mika mata kwanukan tace

‘Wai gashi inji Mommy.’

Bata zata nama bane a tunaninta ko abinci ne don haka tace da Rukayyan ta ajiye a kan dining table. Bayan ta ajiye ta kuma ce mata

‘Ki debo zobo a fridge ki sha, ga cake nan a kan dining table ki dauka.’

Ta shiga ta debo zobon ta fito ta dauki cake din ta wuce ta zauna a kujerar zaman mutum daya. Ta kurbi zobon sannan tace

‘Anti kikayi cake din bana nan, ina so fa na koya Anti.’

‘Kada ki damu in dai cake ne next time in zaki tayani kwana sai mu bi dare mu yi miki na zuwa a school ko? Sai dai fa ina tsoronki a kicin kin yi kankanta fa. Shekarunki sha daya fa, bar ganin kinyi tsawo.’

‘Kai Anti, Allah zan iya. Ai dai kema kin ce ina da natsuwa don haka kin san ba zan yi barna ba ko?’

‘Tabbas kina da natsuwa Rukayya, in sha Allah za muyi cake mai dadin gaske kuwa.’

Saida ta shanye zobon nan suna hira sannan ta tuna da gargadin da akayi mata ta tashi ta fice ta koma gidan.

Bata dade da fita ba Aisha ta tashi ta bude kwanukan, ta bude baki tana mamaki; kada dai ace duk naman nan da aka soya wannan ne rabonta, ko kuwa dai daga makota aka aiko da wannan din.

‘Ikon Allah.’

Ta fada a fili tana mamaki da dariya. A yanka sa guda kato da rago amma a sammata wannan, ai ko su Jummai ta san sun cancanci kason da yafi wannan. Amma dai zata jira tunda yau maigidan a nan zai kwana taji bayani.
Ta mayar da kwanukan ta rufe ta barsu a wajen.
……..

Sai bayan sallar isha’i ya shigo gidan, kamar yanda ya tsira ‘yan kwanakin nan haka ya mike a kan kujerar zaman mutum uku ya fara gyangyadi. Har ta gama jera masa abincin dare ta zo ta tsaya a kusa dashi bai ji motsinta ba; ta rasa gane wannan yawan gyangyadi da baccin da yake mata ‘yan kwanakin nan, sai kace wanda yake kokawa da zaki a office din. Tabbas da ace shine matar da zata ce ciki ne da shi. Tayi gyaran murya ta zauna a hannun kujerar tace

‘Habibi abincin daren fa, ko har kaci a mafarki?’

Ya tashi zaune ya dungure mata kai yana fadin

‘Sai dai idan mafarkinki nakeyi kika bani abincin a mafarki, ba dama mutum ya kashingida sai kice yana gyangyadi.’

Tayi dariya

‘Uhm, to a dai taso aci abinci kafin na cinye abuna.’

Saida suka gama cin abinci suna hira sannan yace mata

‘Dan debo min naman nan mana, Zahra tace ta raba an kawo miki naki ko?’

Ta kalleshi da mamaki tace

‘Au wai wannan shine rabon nawa?’

Kafin ya amsa ta mike ta dauko kwanukan nama ta ajiye ta zauna tace

‘Kaga fa abinda Rukayya ta kawo, wallahi na zata ma daga makota ne.’

Mamaki ya bayyana a fuskarsa yana buda kwanon da robar, yace

‘Wannan din shine rabon naki?’

‘To ni dai shi aka bani. Shiyasa nima na zata daga makota aka kawo. Wannan nama ai ko su Jummai kason su ai ya kamata yafi wannan balle ni, duk da ban san yanda tsarin yake ba.’

Yayi shiru yana mamakin wannan rabo na Zahra, domin ko yanzu da zai fito ya ga nama zai kai fanteka biyar a falon sama kuma ya san akwai wani ma a kicin.

‘Bari idan naje yi musu sallama maji yanda aka yi.’

Nan ya sa naman a gaba, kafin wani lokaci ya ci rabi.
……..

Sai wajen goman dare sannan ya tafi wajen Zahra don yayi musu sai da safe. Babu kowa a falon sai Sadik yana kallon TV yana cin nama da burodi. Bayan yayiwa Abban sannu da zuwa ya amsa ya wuce sama.

A dakinta ya sameta tana kwance a kan gado sai dai ba bacci takeyi ba, bayan ya amsa sannu da zuwanta ya karasa ya zauna a gefen gadon yayinda ta nade kafarta don ya sami wajen zama.


Yace

‘Gajiya ce ta sa kika kwanta da wuri yau?’

‘Wallahi kuwa, duk jikina ciwo yakeyi.’

‘Sannunku da kokari, Allah ya maimaita mana.’

Suka yi shiru na dan lokaci, jim kadan yace

‘Kika ce min an raba nama an bawa Aisha nata?’

Da mamaki ta amsa

‘Eh, Rukayya ta kai mata, sai dai idan shirme tayi.’

‘Bana jin, na dai ga naman ne a ‘yar Samira don ko kafin na fito ma na cinye rabinsa. Duk wannan naman ya za ayi kuma ace wannan ne rabonta, ko ba ke kika zuba bane.’

Ta bata rai

‘Ikon Allah, na kula kai dai idan dai a kan Aisha ne ba zan taba burgeka ba. Gani nayi ita kadai ce a gidan nata, idan ta cinye wannan ba sai ta turo a kara mata ba? Kai kuma ai ga naka can na ajiye maka a dakinka kamar yanda muka saba. Nan fa mu shida ne ni da yara ga masu aiki, baki da danginka duk nan suke shigowa kuma a nan zasu ci ga makota ma duk a nan zan dibar musu. Naman Sallah kuma dama ina yaga wani auki da mutum zai zata zai samu da yawa?’

Binta kawai yake da kallo yana mamaki, so yake

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login