Showing 120001 words to 123000 words out of 166068 words

Chapter 41 - UWAR SADIKU COMPLT BY SAKINA YAZID.txt

11 Jul 2024

25386

rungumeta. Bata da kuzarin kwacewa domin itama tayi kewarsa don haka ta rungumeshi. A hankali ya fara bin wuyanta yana sumbata yana kara kankameta, sai da tayi da gaske ta tattara nutsuwarta ta dan tureshi tana fadin
‘Muje kaci abinci fa dare yana yi.’

Ya kalleta suka hada ido ya dan kara matsawa kusa da ita ya sumbaci lebenta, taja baya. Yace

‘Aisha ba kiyi kewata ba kenan?’

Tayi murmushi ta sunkuyar da kai

‘Hmm!’

Ta wuce gaba ya bita a baya suka nufi falon.
Bayan ya zauna a dining table din ta zuba masa abinci; kuskus ne da miyar alaiyahu da hanta. Ta ajiye farantin a gabansa ta dora masa cokali a kai sanna ta ja kujera ta zauna.

Ya dubeta yace

‘Ke ba zaki ci ba?’

Ta kawar da kai sannan ta bashi amsa

‘Na ci nawa.’

‘Yau babu jira kenan aka yi min solo.’

Tayi murmushin yake

‘Ban tabbatar zaka zo ba har sai da na ganka yanzu, shi yasa dana idar da sallar isha’i baka shigo ba na ci abincin.’

Duk yanda ya kai ga jun tausayin kansa sai da yaji tausayinta fiye da yanda yake tausayin kansa, da kyar ya danne kwallar da ta taso masa saboda baya so ya kara raunana mata zuciya. Ya mika hannunsa ya kama hannunta wanda yake ajiye a kan tebur din, ya sumbaci hannun ya rike yana cigaba da shafawa. Yace

‘Ban san da bakin da zan baki hakuri ba Aisha, ban san kuma irin hakurin da zan baki ba. An cutar dake kuma an cutar damu gaba daya.’

Ya sake sumbatar hannun.

Tace

‘Ka ci abincin kada ya huce.’

Ya saka hannunsa na dama yana cin abincin yayinda hannunsa na hagu yake rike da hannunta na dama, yana cin abincin yana kallon fuskarta.

Bayan ya gama cin abincin sai da ya tayata ta kwashe kwanukan sanna ya jata suka zauna a kan doguwar kujera falo.

Duk da TV a kashe take amma ita Aisha da ta zauna gaba take kallo shi kuma da ya tashi sai ya zauna yana fuskantar Aishan. Ya kamo hannunta ya sumbata, ya juyo da fuskarta wadda ba shi take kallo ba ya sumbaci lebenta. Ta bude baki zata yi magana ya rigata

‘Aisha. Don Allah yau kada kiyi min fushi please.’

Ta yi murmushi ta share kwallar da ta taru a kwarmin idonta. Ya kara matsawa kusa da ita yana kokarin janyota jikinsa gaba daya. Ta dage sannan tace

‘Amira tana nan kada fa ta fito.’

Ya cije lebensa ya dan ja baya, ya dubeta yace

‘Tashi mu koma daki to.’

Ya mike ya jata itama ta mike tsaye.

Yana rike da ita ya zagaya ya kashe fitilun falon domin gani yakeyi idan ya saketa zata iya tafiya dakinta tace fushi take yi dashi. Sai da ya kashe fitilun tas sannan ya jata suka shige daki.

Duk yanda ta so ta dage a wannan dare Abban Sadik bai bata dama ba, haka suka kwana suna biyan bashin juna cikin walwala.

………..

Yanda Aisha da Yusuf suka kwana suna walwala haka Zahra ta kwana cikin kunci da lissafin yanda zata yi da Aisha; domin ba zata taba bar mata Abban Sadik ba.

Gaba daya tunaninta ya kare, duk iya satar bacci haka ya kyaleta sai bayan asuba sannan ta sami baccin.
__

Cikin walwala suka wayi gari Lahadi, sai wajen karfe goma sannan suka gama breakfast a lokacin ya fice don ya dubo Zahra da yaran. Yanda ya barta jiya haka ya sameta yau, ya riga ya san abinda yake damunta kishi ne na rashin tunani ta dorawa kanta don haka ba tare da bata lokaci ba suka gaisa ya fito ya bar mata gidan tunda yara duk suna tahfiz.

Tana so ta yarda bai fahimci wanda ya raba shi da Aisha ba amma kuma tana mamakin yanda jiya zuwa yau yake nuna mata wani hali na ko in kula. Amma dai ta san dole ta saurara yanzu zuwa lokacin da zata sami kanta.
…………..

Bayan azahar Abba ya dauki Aisha suka tafi gidan Hajiya, ya riga ya san yayi musu laifi don haka suka je ya sami Hajiya da Anti Uwani ya basu hakuri. Daga nan suka wuce gidan Yaya Abubakar shima ya sameshi yayi ta bashi hakuri. Sai bayan la’asar sannan suka dawo gidan zuwa lokacin har Amira ta dora abincin dare.

Bayan sallar isha’I tana kicin tana jiyoshi yana waya da Jibrin.

Bayan ta shigo falon yake tambayarta rasit na biyan kudin hayar gidan, ta dauko daga daki ta bashi. Kafin su kwanta bacci taji alert ya tura mata kudin hayar da ta biya harda Karin dubu dari. Ta tambayeshi to karin na menene, yace
‘Duk tsawo lokacin nan ke kike ciyar da kanki kina yin komai wanda ba haka ya kamata ba ai kinga dole na biya bashi ko. Na san abinda kika ci ma ya fi dubu dari in Sha Allahu idan aka kwana biyu zan ciko sauran don na san matata akwai cinye buhun shinkafa.’

Tayi dariya.

Babu yanda bata yi da shi a kan ba sai ya sake turowa ba amma ko sauraronta bai yi ba, suka cigaba da hirarasu.

Da sati ya zagayo kuma haka ya sake daukan Aisha suka zaga danginsa.


Yanda Hajiya ta saba karbarta cikin halin ko in kula haka ta yi mata, shi kanshi Abban sai da yaji babu dadi. Ya kara jin haushi Zahra saboda wannan matsalar da ta kirkiro a lokacin da Hajiyan ta fara haduwa da Aisha itace dalilin wannan kiyayyar; sannan kuma yanzu ga ciwo ga rikicin tsufa.

Sai da suka tsaya a gidan Yaya Bello sannan suka wuce gida.

Haka rayuwarsu ta cigaba cikin walwala da adduoi.

Ita kuwa Zahra tun tana saka rai Abba zai tutsiyeta har ta sakankance bai gane itace tayi musu asiri ba. Ta cigaba da kokarin tara kudi tunda tana son aje mata wajen boka.

Shi kuma Abban ya kyaleta ne saboda cikin da yake jikinta da kuma tunanin da yakeyi a kan makomar yaransa idan yace zai yi rigima da Zahra; yaran da daman yana ganin kamar akwai gibi a tarbiyyarsu. Yana sane da yanda idan dai tana fushi da shi toh gaba daya yaran suma sai su daina kulashi sai Rukayya da Sumayya ne kawai suke kulashi ba zai ga walwalarsu ba har sai uwarsu ta daina fushi da shi. To idan ya saketa yanzu yana jin yaki za a koma yi tsakaninshi da ‘yayanshi wanda shi din ba haka yake so ba. Don haka ya kayaleta take cigaba da rayuwarta kamar bata yi masa laifi ba, musamman da yake Malam Audurahmanu ya sanar da shi idan dai ya rike addu’ar da ya bashi to lallai babu sihirin da zai sake tasiri a kansa.
__

Lokaci ya ja don haka kowa ya koma harkarsa kamar yanda aka saba.

Ranar Talata da yamma Zahra ta shirya ta tafi wajen scanning domin yanzu cikinta ya kai kusan wata bakwai tunda yana motsi sosai har tana ganin motsinsa. So take a kara tabbatar mata da cewa lallai namiji ne domin bata so abinda ya faru a haihuwar Sumayya ya sake faruwa. Kamar yanda ta zata haka aka tabbatar mata da cewa lallai namiji ne domin babu ma yanda za ayi ya zama mace.

Cikin walwala ta dawo gida, washegari kuma ta shirya ta tafi asibitin Nassarawa awo. Aka duba ta sosai awajen awon, likita ya tabbatar mata da lafiyarta da kuma lafiyar jaririnta. Don haka ta dawo gida cikin walwala bayan an rubuta mata appointment ta dawo bayan sati hudu domin sake yin awo.
---------

Ranar Alhamis ce wadda ta kama saura kwana biyar Zahra ta koma awo.

Yau din tunda gari ya waye take jin jikinta babu dadi, gashi cikin yayi mata nauyi sosai da kyar take jan kafa sannan ga mararta tana ciwo kadan-kadan. Nan da nan ta gama abinda takeyi ta koma ta kwanta don bata ma jin kwari.

Har bacci ya fara kwasarta fitsari ya takura mararta, don haka ta tashi ta shiga bandakin don yin fitsari. Tana sabule pant din da yake jikinta ta ga jini, nan da nan hankalinta ya tashi. Tayi fitsarin ta fito tana kokarin fita daga dakin kuma mararta ta kara tsanantawa da ciwo don haka ta koma ta durkusa a gefen gado.

Ta lalubo wayarta daga kan gadon ta kirawo Abban Sadik wanda yake office dinsa. Bayan ta sanar da shi halin da ake ciki yace ta shirya ya zo su je asibiti domin Malam Ali ya fita dauko Sumayya da Ummi daga makaranta.

Nan ya sameta a gefen gado tana faman dagewa saboda ciwo, ya kamata ta saka hijabi sannan ya rikota suka sauko. Jummai bata san halin da ake ciki ba sai da suka sauko; tayi mata sannu da fatan samun lafiya suka wuce asibiti.

Suna zuwa asibiti aka samu likita ya dubata saboda yanayi halin da take ciki. Scanning likita ya turasu wanda da kyar Abba ya riketa suka je dakin da akayi mata, aka bashi takardar ya rikota suka koma wajen likitan.
Cikin hanzari likitan ya karbi takardar ya fara dubawa, bayan ya gama dubawa ya kalli Abban yace

‘Alhaji sai dai ayi hakuri, yaro ne a cikinta namiji amma Allah yayi masa rasuwa shi yasa take bleeding. Yanzu zamu dubata mu taimaka mata ta haifeshi sai ayi masa sutura.’

Abban ya goge fuska yace

‘Inna lillahi wa Inna ilaihi rajiun, ikon Allah.’

Nan take ita kuma ta fashe da kuka yayinda mararta take kara kartawa. Nan da nan likita ya kirawo ma’aikatan jinya yace su saka ta a dakin labour room. Shi da Abban suka bi bayansu.

Aka shige da ita yayinda Abban ya tsaya, jimawa kadan ya lalubo waya ya kirawo Yaya Murja ya sanar da ita sannan ya kirawo Aisha da Yaya Bello ya sanar da suma halin da ake ciki.

Ba tare da bata lokaci ba Yaya Murja ta iso asibitin,nan suka tsaya ita da Abban suna ta jira. Sai wajen karfe uku na yamma sannan aka samu ta haifi yaron babu rai.

Likita ya dauki yaron ya mika mata yace

‘Sannu Hajiya, kin ganshi ko. Allah ya kawo wasu masu albarka.’

Ta share hawaye tace

‘To likita me ya kashe shi?’

Ya mayar da gawar ya ajiye ya dubeta yace

‘Allah ne ya kashe kayansa kinga kuwa sai muce Allah ya kawo masu albarka. Kar ki damu Hajiya wannan ba wani bakin abu bane a wajen mace mai haihuwa tunda ma ke kina da wasu yaran wannan ba zai zama matsala ba.’

Nan ya barta da ma’aikatan suna gyarata ya fito waje.


Bayan an gama shiryata aka fito da ita aka bata daki inda likita yace zasu riketa zuwa gobe saboda jininta ya dan hau. Aka nade gawar yaron aka bawa Abba. Bayan ya tabbatar an bata daki sun zauna ita da Yaya Murja ya sanar da ita zai je ya kaiwa Yaya Bello gawar ayi mata sutura sannan ya karbo musu abinci a gida.

Abba yana fita Yaya Murja ta matsa kusa da Zahra tace

‘Kiyi hakuri ki share wannan hawayen, in da rabo sai kiga kin haifi wani amma kina ta kuka sai kace karamar yarinya.’

Cikin shesshekar kuka tace

‘Yaya ya za ayi yaron da bai fi sati biyu ba aka duba aka tabbatar min kalau yake kuma yanzu ace ya mutu?’

Da mamaki Yaya Murja take kallonta tace

‘Hmm! Saboda ke baki taba yin bari bane shi yasa kike cewa haka. Ya za ayi ba zai mutu ba tunda rayuwarsa tana hannun Allah. Ki kwantar da hankalinki wannan ba wani abu bane, ke da kike da yara shida ai sai dai kawai ki cigaba da godiya ga Allah da fatan Allah ya sa wahala ta zama kaffara.’

Ta janyo flask din da tazo da shi ta had a mata shayi mai kauri ta sakata a gaba saida ta shanye. Jimawa kadan likita ya shigo yayi mata allura, kafin ya fita bacci ya fara fuzgarta don haka ta hakura ta kwanta ba da son ranta ba. Yaya Murja ta zauna a kan kujera tana jiran zuwan Suwaiba wadda tace zata biya ta taho da Rahma saboda jinya.

UWAR SADDIKU


Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)


37

Tun kafin Suwaiba ta fito daga gida ta kirawo Rahama, sai dai bata dauka ba. Don haka ta kirawo Innar su Rahman don ta sanar da ita zata zo sai ta dauki Rahma su wuce.

Rahama tana daki a kwance tana kallon wayarta da taga Suwaiba ce taki dauka, haka kawai jikinta ya bata gidan Zahra zasu ce taje ita kuma tayi alkawarin ba zata sake komawa wannan gidan ba.

Tana jiyo Inna ta fara magana da Suwaiba a waya tayi tsalle ta fito tsakar gidan, bayan Inna ta ajiye waya tace

‘Inna na gaya miki ba zan sake zuwa gidan nan ba, wallahi duk wani mutunci da kika ga tana yi idan mutum bai taba yaranta bane. Ni dai gaskiya bana son zuwa gidan nan.’

Inna ta jijjiga kai

‘Hakuri zakiyi, ko iya asibitin ne kije ki zauna da ita in ya so da an sallameta sai ki dawo. Tunda dai kin ga suna kallonki kina yiwa yayyenki irin wannan hidimar, hakuri zakiyi, yanzu Suwaiban zata karaso.’

Haka Inna ta sakata a gaba tana bata baki, ba tare da bata lokaci ba Suwaiba ta zo suka wuce asibitin.

Nan suka zauna a asibitin har magriba.
Ana idar da sallar Magriba Abban ya shigo, ya kawo musu abincin dare sannan kuma ya tahowa Zahra da wayarta wadda ta bari a gida lokacin da suka taho asibiti. Suna gaisawa Yaya Murja da Suwaiba sukayi musu sallama suka tafi. Jimawa kadan Abba ya yiwa Rahma sallama ya tafi ya barta da Zahra wadda take ta bacci saboda alluran da ta sha.

Sai da yayi magana da likita kafin ya bar asibitin inda likitan ya tabbatar masa zasu sallameta da zarar blood pressure dinta ya dawo dai-dai kuma ta daina ciwon kai wanda take ta korafinsa tun bayan da ta haihu.
…………

Tun a daren Abba ya sanar da Aisha, tayi maganar abincin safe ya sanar da ita Yaya Murja tace za a kai musu don haka ta bari idan yamma tayi sai ta dafa musu abincin dare suje tare su dubota; idan ba a sallameta ba zuwa lokacin.

Ta sanar da mutanen gidansu wanda kafin wani lokaci Hajiyanta ta yiwa Hajiyan Abban waya ta jajanta mata sannan kuma suka sa cewa gobe zasu je asibitin su dubota.

Suma su Yusra tunda Abban ya dawo gida suke ta tambayar labarin Mommy, don haka yayi musu alkawarin gobe ko bai je da su duka ba zai je da wasunsu idan dai ba a sallameta ba.
----------

Sai wajen karfe biyu Abba ya kirawo Aisha ya sanar da ita ta dafa wa Zahra abinci zai zo da anyi sallar la’asar su wuce asibiti. Nan da nan ta fada kicin ta dafa farfesun kaza sannan ta dafa shinkafa ta dafa macaroni tayi miyar dage-dage wadda ta sha nama sannan ta hada coleslaw. Ta sami flask ta cika musu da ruwan zafi saboda shan shayi.

Bayan ya fito daga office ne ya kirawo Yusra ya sanar da ita cewa su shirya ita da kannenta in ya dawo zasu je asibiti, tunda ranar Juma’a ce babu islamiyya. Nan da nan Jummai ta tayasu suka shirya ta tambayesu ko za a dafa wani abun Yusran tace Abba yace Anti Murja ce take kaiwa.
---------

Sai da ya tsaya a wajen Aisha ya ci abinci sannan Aisha ta shirya cikin abayarta mai kyau ta rufe kanta da mayafi mai kalar olive green ta dauki 'yar jakarta sannan suka fito. Suna fitowa ta zare mukullan motar daga aljihunsa tana dariya tana fadin

‘Ka gaji da yawa, bari na tukamu.’

Yayi dariya yace

‘Za dai ayi min wayo a more min mota.’

Itama tayi da dariya.

Suka karaso gaban motar ya bude booth yana fadin

‘Zuba abincin a nan da yara zamu je sai su zauna bayan motar.’

Suka zuba abincin ya zauna a gaban motar ta ja suka fito daga gidan.

Tayi parking a kofar gidan Zahra, Abban ya fita ya shiga don ya fito da yaran.

Gaba daya su sun riga sun shirya don haka yana shiga suka fito yana dauke da Sumayya yayinda yake rike da hannun Ummi ragowar suna biye da shi. Sai da Yusra tayi turus da ta hango Aisha a motar Abba tana tukawa, ya karaso da su duk suka shiga bayan motar.

Rukayya ce ta fara gaida Aisha wadda ta juya tana amsawa, suka suka gaisheta har Yusra saboda Abban ya riga ya shiga motar. Ta ja motar suka kama hanya.
Sai da suka kamo hanya sosai yacewa Aishan idan sun zo kan tin gidan gwamna ta tsaya zasu sayi fruit. Don haka suna zuwa ‘yar kasuwar nan da take kusa da Yahuza suya ta tsaya; da hannu ya yafito mai fruit din wanda ya taho da guda. Yayi masa lissafin lemon, ayaba da kuma apple na kusan dubu bakwai yace a saka a leda kuma ya taho da POS machine ya karbi kudin.

Nan da nan mutumin ya juya da hanzari ya dauki leda ya fara cikawa yayinda shi kuma Abban ya gyara zama ya fara laluben aljihunsa don dauko wallet dinsa wadda ATM card dinsa suke ciki. Sai dai ga mamakinsa babu komai a cikin aljihun; ya dan yi tunani yana rike da aljihun ya kalli Aisha wadda take kallonsa yace

‘Kin san na baro wallet din a falo!’

Tayi murmushi tana dubansa, cikin rada tace

‘Kanata santin shinkafata.’

Yayi dariya yayinda ta mika hannu inda kafarsa take ta dauko jakarta, ta zaro ATM card dinta ta mikawa Abban a daidai lokacin da mai fruits din ya karaso dauke da manyan ledodi guda biyu.

Abban ya fita ya karbi kayan ya saka a booth yayi amfani da katin Aisha ya biya kudin sannan ya dawo ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login