Showing 114001 words to 117000 words out of 166068 words
na uku wato Yusuf wanda suke kira Adil, daga kallon hotunan zaka gane bikin sauka ake yiwa Adil din wanda tabbas ta tuna kamar wancan satin ta ga hoton katin gayyatar bikin saukar a status din Yaya Saratu. Daga rubutun da Anti Karima tayi a status din ne kuma ta gane saukar hadda yayi; tayi murmushi tana kallon hoton zayyanar dake hannunsa.
Idan taga yaro ya haddace alkur’ani tabbas yana bata sha’awa kuma tana alfahari da su domin Abdallah da farha ma tana fatan su haddace izu sittin.
Ana cikin bikin Sallah ta gani a status din Anti Karima an kawo kayan auren Asma’u yayar Adil din, ta manta dalilin da ya hanata koda waya ne ta yiwa Anti Karima tayi mata barka. Lallai yanzu ya kamata taje gidan nan don ba zata ma iya tuna rabonta da su ba, ko babu komai dai ya kamata taje mata murnar auren Asma’u da ake shirin yi kuma da saukar Adil din.
Nan take ta yanke shawarar ranar asabar idan ta tashi daga islamiyya zata je gidan tunda dama karfe sha daya suke tashi kuma ranar Amira tana da lecture har karfe daya; don haka daga islamiyya sai ta wuce gidan Yaya Bello daga can ta tsaya ta gaida Hajiya sai ta wuce ta dauko Amira.
Ta dan gatsina fuska a lokacin da tayi tunanin zuwa gidan Hajiya; bata son zuwa gidan Hajiya saboda yanda Hajiyan takeyi mata wanda ya sa Anisa ma da take gidan bata ganin girmanta don ko gaisheta bata yi. Ta tuno zuwanta na karshe gidan wanda bayan ta gaisa da Hajiyan haka Hajiyan ta tashi ta shige daki ta barta, itama Anisa da mai aikin Hajiya suka shige kicin suka barta ita kadai a falon Hajiya. Saida ta gaji da zama sannan ta taso ta fito kuma babu yanda bata yi ba Anisan ta kirawo mata Hajiyan tayi mata sallama taki; sai ce mata kawai tayi tayi bacci kuma idan tana bacci ba a tashinta. Haka ta hakura ta tafi tana mamakin dalilin da yasa suke mata wannan kiyayyar. Kusan zata iya cewa kaf ‘yan gidan su Abba Yaya Bello ne kawai da iyalansa suke zama da ita yanda ya kamata.
Ta kawar da tunanin ta cigaba da latsa wayar tana hakurkurtar da zuciyarta a kan haka zata hakura taje gidan Hajiyan, in ya so ta dauki dan rakiya daga gidan Yaya Bello watakila abun yayi mata sauki.
……….
Tun ranar Juma’a ta tanadin alkur’ani izu sittin da turaren mai kamshi da agogon hannu wanda ta saka a leda a kan zata kaiwa Adil. Da tayi tunanin zata dafawa Hajiya funkason alkama da farfaesun kifi to amma gaskiya bata son ta sha wahala taje su lalatar da abincin basu ci ba don haka ta yanke shawara gara ta sayawa Hajiyan tuffa da kayan shayi irin wanda ya dace da masu ciwon suga ta kai mata.
Ranar asabar suna tashi daga islamiyya ta wuce gidan Yaya Bello.
Tana tsayar da motarta a bakin gate din gidan yaran gidan suna dawowa daga tahafiz; tun daga nan yaran suka fara gaisheta, bayan ta amsa suka nufi cikin gidan a tare. Suna tafe tana yiwa Adil murnar haddar da yayi.
Cikin girmamawa Anti Karima ta karbeta, Muhammad da Asma’u wadanda basu je tahfiz ba suka gaisheta sannan Asma’u ta kawo ruwa da lemo. Suka zauna ita da Anti Karima a falo sunata hirar yaushe gamo, daga baya kuma aka janyo akwatunan kayan auren Asma’u aka bude mata ta gani tana ta sa albarka.
Anti Karima ta dubeta tana daga mata kayan tace
‘Kinga yanzu saura wata uku da kwana goma bikin.’
Da murmushinta tace
‘Allah ya nuna mana, kice abun ma ya matso.’
Jimawa kadan Aishan ta dubi Anti Karima tace
‘Anti to me ake shiri? Akwai wani anko da za ayi don gara na karbi nawa kafin na tafi.’
Ta kama haba ta bude baki
‘Tab, ai Abbansu baya son anko babu ma wanda ya isa yayi wannan zance. Kina ji event center ma yace ba za aje ba wai a nan gidan zamuyi gaba dayan bikin. Har yanzu faman lallabarsa nake yana burtsewa; tunda kinga gidan ai ina muka ga filin yin biki idan banda rigimarsa.’
‘Gaskiya dai Baban su Muhammad da ya bari munje event center din. Amma fa kin san duk abun suna ne ko a nan din aka yi kalau za a gama shike nan, ai albarkar abun ake nema.’
‘Hakane.’
Suka cigaba da hirarrakinsu.
Sai wajen sha biyu da kwata sannan Aisha ta mike zata tafi. Ta nemi wanda zai rakata gidan Hajiya aka ce Asma’u ta shirya suje, don haka ta dan zauna tana jiran Asma’u ta kintsa.
--------
Kamar yanda ya saba duk ranar da babu aiki da safe yake tafiya gidan Hajiya, idan rana tayi sai ya wuce gidan Yaya Bello inda a can zai ci abincin rana. Ba zai koma gidansa ba har sai anyi sallar Magriba. Duk yanda Zahra taso ya daina zuwa gidan Yaya Bello ko kuma a kalla idan ya je ya daina dadewa abun yaci tura. Tunda yace mata a can yake cin abincin rana ta fara zargin wani abun suke barbada masa a abincin shi yasa ya kasa rabuwa da su.
Sau biyu tana turawa Yaron Malam kudi yayi mata aikin da zai raba Abban da Yaya Bello amma ko sauyi bata gani ba. Daga karshe Yaron Malam din ya sanar da ita aikin ba zai yiwu ba domin mutumin da ta bayar da bayaninsa idan sun tashi zasuyi aiki ko ganinsa basa iya yi.
Sosai abun ya bata mata rai amma babu yanda zatayi tunda tana tsoron zuwa Doguwa da cikin jikinta; musamman da yake sau biyu tana yin scanning a gurare daban-daban kuma duka biyun sun tabbatar mata namiji take dauke da shi; bata son wani abu ya sameshi.
Haka ta hakura ta daga musu kafa, amma tayi alkawarin idan ta haihu da zarar tayi arba’in zata je Doguwa duk sai tayi maganinsu ko waye malamin Yaya Bello bai isa ya mallake mata miji ba.
Yau din ma bayan ya gama cin abincin safe tana kallonsa ya shiryo ya fito, tun safe take masa korafin bata jin dadi da nufin ya fasa fitar amma bai ma kulata ba. Kawai sai ya sanar da ita idan da matsala tayi masa waya sai ya dawo. Da kyar ta bude baki tayi masa a dawo lafiya shi kuwa ya amsa ya fice ya kama hanya lokacin wajen karfe goma.
Kai tsaye gidan Hajiya ya wuce don ya san a yanzu Yaya Bello yana can, domin tunda diabetes dinta ya tashi da azumi da kanshi yake zuwa yana bata abincin safe da na dare. Sosai suke lallabata saboda bayan diabetes din kuma to tana yi musu rikici irin na tsufa domin ko abincin ma idan ta ga dama sai tace sai taci abinda likita ya hanata ci. Haka dai suke ta fama.
Lokacin da Abban ya shiga gidan Hajiya ta gama cin abincinta, suna zaune dai a falo suna hira ita da Yaya Bello. Nan ya zauna suka cigaba da hirarrakinsu gaba daya.
Can zuwa shabiyu lokacin har Hajiya ta fara gyangyadi a falon, sukayi mata sallama domin ta samu tayi baccinta. Suna fita suka nufi gidan Yaya Bello a motar Abba tunda shi Yaya Bello bai zo da mota ba.
__
Lokacin da Yaya Bello da Abban Saddiku suke shiga gidan Yaya Bellon yayi daidai da lokacin da Aisha suke fitowa tare da Asma’u yayinda Anti Zalihan take biye dasu tana yiwa Aisha sallama da godiya.
Kana shiga gate din gidan dan karamin farfajiya ne inda daga nan zaka shiga wata kofar mai irin siririn soron nan sannan ka fada tsakar gidan. Kasancewar kofar falon baki wanda take a farfajiyar farko a rufe take sai Yaya Bello ya wuce gaba suka nufi cikin gidan ta wannan soron.
Suna daf da kaiwa karshen soron Aisha ta sako kai Asma’u na biye da ita. Ganin Yaya Bello ta tsaya ta fara kokarin kaucewa ta bashi hanya ya shige, tana shirin rage tsawo ta gaisheshi ta hango Abban Sadik a bayansa.
Take ta manta da gaisuwar da take niyyar yi ta bi shi da kallo baki a bude. Ta kusan shekara biyu rabon da ta ganshi kamar haka, ya dan yi kiba amma kuma ya kara tsufa. Yanda take binsa da kallo shima haka yake binta da kallon.
Yaya Bello ne ya katse musu kallon yace
‘A’a! Aisha. Sannu da zuwa.’
Ta kauda kanta ta rage tsawo ta gaishe da Yaya Bello. Bayan ya amsa ya juya bayansa ya dubi Abba yace
‘To kai kaga amarya ta biyoka fa.’
Kamar bai ji abinda yace ba ya bude baki a hankali har yanzu idonsa a kan Aishan cike da tsananin mamaki yace
‘Aisha! Daman nan kika dawo?’
Ta kawar da kai ta dan share kwallar da ta fito daga idonta, a dai-dai lokacin Asma’u ta koma cikin tsakar gidan ta zauna a kan kujera domin jiransu.
Cike da mamaki Yaya Bello ya fara binsu da kallo daya bayan daya yana kokarin ya fahimci abinda yake faruwa. Ya gyara tsayuwa yace
‘A’a! Me yake faruwa ne? Me yake faruwa ne? Ya zaka ce nan ta dawo bayan da na fita ma bata zo ba.’
Kafin ya bashi amsa ya kama hannunsa ya dubi Aishan yana nuna mata cikin gidan yana fadin
‘Mu koma naji abinda yake faruwa, kunata kallon juna kamar wasu baki.’
Ta bude baki zata yi magana yayinda Yaya Bello ya janyo Abban suka nufi cikin, bata da wani zabi don haka ta wuce gaba suka bita a baya domin idan ta tsaya wajen ma ba zai isa su wuce ba.
A falon suka ci karo da Anti Zalihan ta mike tsaye tana fadin
‘A’a, kin tsintosu Aisha.’
Babu wanda ya amsa mata don haka ta matsa Abban Sadik da Yaya Bello suka zauna a kujerar zaman mutum uku yayinda ita da Aishan suka zauna a kujerun zaman mutum daya. Yaya Bello ya dubi Aishan yace
‘Aisha me yake faruwa ne, kamar mamakin ganin juna kukeyi ke har kina share kwalla. Me yake faruwa ne?’
Bata sami bakin bayar da amsa ba saboda hawayen da take ta faman tokarewa ne ya kwace ya wanke mata fuska gaba daya, ta sa hannu ta fara share hawayen.
Cikin tsananin damuwa da mamaki Yaya Bello ya gyara zama yana dubansu daga wannan ya dubi wannan. Yace
‘Yusufa wai me yake faruwa ne? Kayi min bayani.’
Ya sa hannu ya goge fuskarsa yana muttsike ido kamar wanda ya tashi daga bacci, a hankali ya bude baki yace
‘Yaya babu komai fa, na dai dade ban ga Aishan bane kawai.’
Ya dubi Aishan wadda ta sunkuyar da kai tana share hawaye yace
‘Ikon Allah! To yaji tayi ko rabuwa kuka yi amma baku sanar ba.’
Gaba daya su suka yi shiru kowa yana ta faman zare ido, itama Anti Zulaiha sai kallonsu take tana mamaki don bata ma fahimci kan zancen ba. Yaya Bello ya katse shirun ya dubi Aishan yace
‘Aisha me yake faruwa ne? Ya sake ki ne ko me ya faru?’
Ta share hawaye tace
‘A’a bai sake ni ba, ya dai kusa shekara biyu bai zo gidan da nake ba shi yasa muka dade bamu hadu ba.’
Yaya Bello ya sake shiga rudani, ya kalli Aishan ya kalli Yusuf din. Aisha ta sake share hawaye, ta bashi labarin yanda abubuwan suka faru. Binta kawai yake da kallo yana mamaki. Ya dubi Abban Sadik din yace
‘Yusufa kai kuma kana auren mace kawai sai baka ganta ba kuma ba zaka nemeta ba?’
Ya share gumi yace
‘Wallahi Yaya ni kaina har yanzu ina mamaki, don ni sai yanzu ma fa da na ganta na tuna da ita. Na kasa gane me yake faruwa ma gaba daya wallahi.’
‘Ikon Allah! To ni kaina ma ban fahimceku ba. Amma Yusufa ya za ayi ace kai da matarka kuma ga gidan da take kusa da daya gidan amma kace wai ka kusa shekara baku hadu ba. Wannan din wacce irin rayuwa ce?’
‘Wallahi Yaya nima sai yanzun nake mamaki, kamar ma gaba daya mantawa nayi da wani bangaren na rayuwata. Gaba daya ma na kasa ganewa.’
Sukayi shiru kowa da abinda yake ransa. Jimawa kadan Anti Karima tayi gyaran murya tace
‘Gaskiya Abban Muhammad ni ina ga ka kirawo Malam Sama’ila tunda yau asabar watakila yana gida, domin wannan abun yayi kama da aljannu ko shaidanu. Gara ka gane kan komai a dauki mataki kafin su bar nan su sake komawa ruwa.’
Yace
‘Hakane gaskiya, bari nayi masa waya na san yanzu zai shigo in sha Allah.’
Ya dauko waya ya kirawoshi, yace masa yana bakin titi zai fita amma yanzu zai dawo.
Sukayi shiru suna jiransa.
Jimawa kadan Yaya Bello ya kasa hakuri ya kirawo Muhammad yace masa ya fita waje da zarar Malam Sama’ila ya zo su shigo tare. Yana fitowa suka hadu suka shigo ya nuna masa falon.
Bayan sun gaisa Abban Muhammad yayi masa bayanin abinda yake faruwa, ya rufe da
‘To Malam Sama’ila abun ne naga kamar na mutanen boye, to shine nace gara ka zo muji ko da akwai abinda za a taimaka da shi.’
Yayi shiru yana jijjiga kai, jimawa kadan yace
‘To gaskiya Alhaji wannan bayanin da kayi min ya fi kama da sihiri, Allah ne ma ya takaita abun. Watakila kai din kana da wata kariya ko kuma gidan naka na da makari shi yasa da suka shigo suka ga juna. Tunda idan ban manta ba lokacin da na yiwa Asma’u rukiyya na baka taimako kala-kala naka da na yaran.’
‘Hakane. To yanzu ya za ayi Malam? Na iya barinsu su koma gidan don ni gaskiya ina tsoron su koma su sake mantawa.’
Suka sake yin shiru na dan lokaci.
Jimawa kadan Malam Sama’ila yace
‘Akwai Malam Audurahmanu, kai ka san shi ai wanda yake zuwa mana limancin sallar dare da azumi. Sai dai shi a unguwar koki yake, shine ya kware a aikin sihiri ni dai ka barni da rukiyya idan aljani ya bayyana a jikin mutum.’
‘To ai sai mu tashi muje in dai zamu sameshi yanzun.’
‘Zamu sameshi tunda ko baya gida makarantarsu kusa da gidan ne’
Yaya Bello ya dubi Abban Sadik yace
‘To kaji ai sai ka tashi muje ko?’
Cikin sanyin murya ya amsa
‘To Yaya, yanda kace.’
Gaba daya suka mike suka fito, har sun kusan fita Yaya Bello ya koma yacewa Anti Karima
‘Ina ga ki dauko mayafi muje saboda ita Aisha din kya zauna da ita.’
Don haka ta saka hijabinta suka shiga motar Abban Sadik Yaya Bello ya tuka suka kama hanya.
A makaranta suka sami Malam Audurahmanu, babu dalibai don an tashi ‘yan islamiyya don haka ya nuna musu aji suka zauna.
Bayan Malam Sama’ila yayi masa bayani ya tambayi Aisha itama tayi nata bayanin, shi kuwa Abban Sadik da aka tambayeshi ma kasa bayanin yayi; abinda yake tunawa kawai shine ya dade bai ga Aishan ba kuma ya san bai saketa ba.
Malam Audurahmanu ya dubi Yaya Bello yace
‘Ina zuwa.’
Ya fita daga ajin.
Jimawa kadan ya dawo dauke da robar ruwa karama guda biyu da kuma wani mai a 'yar roba kamar ta Robb. Ya mikawa Aisha robar ruwan guda daya yace ta shanye, ta kalli Anti Karima ta daga mata kai don haka tayi Bismillah ta shanye. Ya mikawa Abban Sadik din dayan yace shima ya shanye, ba tare da wani musu ba ya shanye.
Ya dubi Yaya Bello yace
‘Ayoyin karya sihiri ne, sune matakin farko za a sha na kwana bakwai.’
Aisha tace
‘Ni dama tunda abun ya faru kullum sai na tofa ayoyin na sha sai dai a ruwan fanfo ne ba na zamzam ba.’
Malam yace
‘Ma Sha Allahu to shi ya sa ma abun baiyi wani tasiri sosai a kanki ba, karanta min ayoyin naji.’
Nan take ta karanta masa ayoyin ba tare da wani kuskure ba.
Yana murmushi yace
‘Ma sha Allah, in dai kika rike wannan babu wani sihiri da zai yi tasiri a kanki, ko yayi ma na dan lokaci ne tunda Allah yana jarraba bawa da abinda ya so.’
Ya mikawa Abban Sadik ‘yar robar hannunsa yace ka lakaci wannan ka shafa a kanka. Ya karbi robar ya rike amma ya kasa ko budewa, jujjuyata kawai yakeyi yana kallonta. Kafin yace wani abu Yaya Bello ya karba ya bude, ya lakaci man da yake ciki ya muttsike a hannunsa ya cire hular Abban Sadik din ya kama kan nasa ya shafe masa man tas. Nan da nan idonsa yayi ja ya fara neman birkicewa, Malam Sama’ila da yake gefensa ya dafe shi ya fara karatu.
Ba a fi minti biyar ba yayi atishawa ya dawo dai-dai. Ya goge gumin da yake fuskarsa, Yaya Bello ya mika masa hularsa ya saka yana ta faman satar kallon Aisha wadda suke zaune a gefe daya ita da Anti Karima.
Malam Audurahmanu ya mike yana fadin
‘Bismillah Malam Bello.’
Ya bi bayansa suka fice.
Sai da suka shiga ofishinsa suka zauna sannan Malam yayi gyaran murya ya dubeshi yace
‘Wato Malam Bello sihiri ne aka yiwa dan uwanka don a rabashi da mai dakinsa, aljanine aka saka masa wanda gaba daya yake hanashi tunawa da ita. Saboda yanda aljanine yake tare da shi kuma duk ma wanda ya so ya tuna masa ita to ba zai yarda su hadu ba. Amma Allah ya kawo makarin abun tunda ka ga wannanan man da ka shafa masa a kansa kamshin mutuwa yayiwa aljanin don haka ba zai sake dawowa ba. Sai dai da yake yana da wata matar kuma ga maganganun da ta gayawa wannan din za a iya cewa itace tayi wannan aika-aikar; duk da dai bai halatta a zargeta ba domin shaidanu makaryata ne. Amma yanzu idan kun tafi to a barshi ya cigaba da kwana gidan ita waccan din, zan bayar da ruwan tofi da zai dinga sha tsawon kwana bakwai kuma da addu’oi. Sannan a samu ko shi ko