Showing 117001 words to 120000 words out of 166068 words
wani a dinga karanta bakara a dakin da yake kwana. In Sha Allah bayan kwana bakwai din sai ku dawo sannan sai ya koma rabon kwana kamar da.’
Yaya Bello ya jijjiga kai yana mamakin yanda Zahra zata yi haka, tunda yake bai taba jin matar da Hajiya take yabo kamar ita ba, don ko matarsa da ita aka fara aurowa Hajiya bata sonta kamar yanda take son Zahra.
Nan suka koma ajin, bayan sun koma ya sake yi musu bayani gaba daya kuma ya gaya musu kada su zargi kowa balle a sami wata sabuwar fitna don shaidanu haka suke so.
Ya basu umarni suje su cigaba da addu’a komai zai dawo dai-dai, ya sake bawa Aisha hakuri sannan sukayi sallama suka tafi.
Sai da suka fito sannan Aisha ta tuna da Amira, take ta buga mata waya tace ta zauna ko a library ne ta jirata nan da awa daya zata karaso.
Gidan Yaya Bellon suka koma inda sai da sukayi Sallah suka ci abinci sannan Aisha tayi musu sallama ta ja motarta ta tafi.
Duk yanda yake tsananin son magana da Aisha haka ya hakura ta tafi, sai dai ya bari kawai idan ya fito daga gidan Yaya Bello sai yayi mata waya ko yaya ne yaji muryarta tunda Malam yace kada yaje gidan da take.
--------
Saida ta dauki Amira sannan suka wuce gidan, tana shiga tayi wanka ta canza kaya sannan ta zauna ta kirawo Hajiya ta gaya mata abinda ake ciki. Nan take Hajiya ta bata shawarar ta yi sadaka kuma ta cigaba da addu’a. Haka tabi ‘yan uwanta da kira duk ta sanar da su su cigaba da tayata addu’a.
Duk da Malam yace kada ya zo gidanta sai an kwana bakwai wannan bai hanata walwala ba, tunda dai an warware matsalar. Haka ta kwana tana Sallah da addu’a cikin walwala.
---------
Tunda Aishan ta fita Abban Sadik yake kokarin cewa zai tafi amma Yaya Bello ya hanashi, ya kula gidan Aishan yake son zuwa kuma Malam yace kada yaje sai an gama addu’a. Nan ya rikeshi har saida sukayi Sallar Magriba kamar yanda ya saba. Ya jaddada masa addu’oi da kuma karatun kur’ani wanda Malam yace yayi sannan yace
‘Idan bakayi karatun kur’ani a dakin ba ni zan iya dauko Malam muzo muyi maka karatun ka dai sani don haka ka tabbatar kayi abinda Malam yace.’
Sukayi sallama ya kama hanyar gidan.
Saida suka kusa shiga unguwar sannan ya sami waje yayi parking, ya zaro wayarsa da nufin ya kirawo Aisha. Ga mamakinsa babu irin binciken da baiyi a wayar ba amma babu lambar Aisha, ya budo Whatsapp ma ya duba ko zai sami chats din ya dauki lambar daga nan amma bai samu ba. Gashi dama ya san bai taba haddace lambarta ba lambar Zahra kawai ya haddace kuma da kunya ya kirawo wani yace a bashi lambar Aisha bayan tana gidansa. Haka ya gaji ya hakura zuciyarsa babu dadi ya kama hanyar gidan.
Ta gaban gate din gidan da Aishan take ya wuce, sai da yayi slow ya karewa gidan kallo yana mamakin yanda ya dade bai ga gidan a wajen ba domin kullum ta nan yake bi idan ya dawo daga aiki. Haka ya wuce gidan Zahra yana mamakin wannan abun.
-------
Yanda ta saba taryarsa cikin walwala idan ya dawo haka tayi masa; Saida ya huta yayi sallar isha’i sannan ta kawo masa abincin dare. Binta kawai yakeyi da kallo domin abubuwan da suka faru yau tabbas sun haifar masa da wasi-wasi game da wacece Zahra; canza masa akayi ko kuwa dama can haka zuciyarta take. Baya jin zai iya tunkarar ta da wannan zancen a yanzu musamman da yake Malam yace kada su tada wata tarzoma kuma da dan sauran shakkarta a zuciyarsa. Don haka ya barwa tashi zuciyar wannan batun.
Haka tayi ta hidima da shi tana jansa da hira, domin tun da ta gane ba zata iya zuwa a raba shi da ‘yan uwansa yanzu ba sai ya zama duk lokacin da ya wuni wajensu idan ya dawo haka zatayi ta kokarin faranta masa rai domin ya gane ta fi su sonshi.
Bata ga alamar damuwa a tattare da shi ba sai dai ta kula da yanda tunaninsa yake yin nisa daga inda take, haka dai tayi ta fama. Ko da suka kwanta ma duk yanda ta kai ga dagewa haka ta hakura ta barshi domin gaba daya nuna mata yayi bacci yake ji ba zai iya ba. Bai fiya kin sauraron bukatarta a wannan lokacin ba don haka ta kwana cikin damuwa da fatan Allah ya sa ba wani abu Yaya Bellon yayi masa ba.
UWAR SADDIKU
Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)
36
Tun bayan da suka dawo daga gidan Malam Aisha ta fara shirin tarbar Abba, tunda tana ji aka ce bayan kwana bakwai zai fara rabon kwana.
Duka labulayen gidan ta bayar aka wanke, suka share ko ina suka gyara ita da Amira. Ita kanta sai da gidan ya bata sha’awa saboda akwai abubuwa na gyaran gidan da ta dade bata yi ba.
Musamman ta sami lokaci suka je sayayya ita da Amira saboda kayan gyaran fatar ta duk sun kare bata sayi wasu ba.
Nan da nan gida ya dau kamshi.
Ranar Alhamis taje saloon aka yi mata gyaran jiki da kitso, tsaf aka goge mata fata ta fara sheki.
Ita kanta bata san irin tarbar da zata yi masa ba domin gaskiya tana jin haushinsa sai dai tayi shirin ne don tana so ya sameta yanda take so.
-------
Ranar Juma’a da su Abba suka je wajen Malam ya sanar da su gobe su zo tare da Aishan. Anti Karima Yaya Bello ya sa ta kirawota ta sanar da ita, don haka da gari ya waye bata je islamiyya ba sai ta jira karfe goma tayi ta wuce gidan Yaya Bello.
Daga can suka hadu suka wuce wajen Malam.
Nasiha ya sake yi musu sannan ya basu addu’oin da kuma turare wanda yace Aisha ta turara shi a gidanta yau din nan kafin maigidan ya shiga. Suka yi masa sallama suka koma gidan Yaya Bello.
Sun dauki lokaci suna hirarsu ita da Anti Karima sannan tayi musu sallama ta fito, ta sami Yaya Bello tare da Abban Sadik a falon. Ta yiwa Yaya Bello sallama tare da godiya sannan ta fice.
Da hanzari Abban Sadik din ya mike ya bi bayanta, ta zauna a mota tana kokarin saka mukulli ya bude kofar gaban motar ya zauna kafafunsa suna waje.
Hannunta yana kan sitiyarin motar ta kawar da kai ta dubi daya gefen, ya dubeta yayi murmushi. A can kasan makogoronsa ya kirawo sunanta
‘Aisha.’
Yanayin muryar tasa sai da yasa taji kiran kamar a tsakar kanta. Ta juyo ta dube shi ba tare da ta amsa ba. Murmushi ya sake yi mata sannan yace
‘Kiyi min abincin dare yau a nan zan kwana.’
A hankali tace
‘Toh.’
Ya sa hannu ya dauki wayarta wadda take ajiye a kusa da giyar motar, ya lalubo lambarsa ya danna kira. Sai dai ga mamakinsa lambar ta ki shiga wanda ya sa ya gane blocking din lambarta akayi a wayarsa. Nan da nan ya dauki tasa wayar ya duba jerin blocked numbers, yana kalla kuwa ya gane lambar tata domin dama haddacewa ne bai yi ba. Nan take ya cireta daga blocking kuma ya mayar yayi saving.
Suka dauki lokaci a zaune a haka; shi yana faman kare mata kallo ita kuma ta ki kallonsa kuma taki magana.
Jimawa kadan ya kirawo sunanta yana murmushi, ta juyo ta kalleshi ba tare da ta amsa ba. Suka hada ido, ta dauke kanta yayinda shi kuma yayi mata murmushi. Yace
‘Bari na barki ki tafi, sai na shigo.’
Tace
‘A dawo lafiya.’
Sai da yayi kokawa da zuciyarsa sannan ya fita daga motar, kafin ya gama shigewa cikin gidan ta ja mota ta kama hanya.
Yana shiga cikin gidan bayan ya zauna ya lalubo lambar account dinta ya tura mata Naira dubu hamsin. Bayan kudin ya tafi ya tura mata sakon text message
“Ban san me ake bukata ba a gidan amma na turo 50k kiyi cefane kafin nazo.”
Ya ajiye wayar suka cigaba da hirarrakinsu.
…………
Babu yanda Yaya Bello bai yi da shi ya tafi da wuri ba saboda ya kula da yanda yake dokin ganin Aisha, amma Abban Sadik yaki tafiya har sai da sukayi Sallar la’asar sannan yayi masa sallama ya tafi.
Kai tsaye gidan Zahra ya wuce.
Yaran duk suna islamiyya don haka ita kadai ce a falo tana zaune tana ta cin goriba. Bayan ta amsa sallamarsa tayi masa sannu da zuwa. Ya dubeta yace
‘Yau kuma goruba kika samu?’
Tace
‘Wallahi. Yarane suka siyo zasu tafi islamiyya shine na dauki guda biyu.’
Yayi dariya ya haye saman.
Sai da ta gama cin gorubar sannan ta bi shi saman; yana kashingide a kan gado yana hutawa. Bayan ya amsa sallamarta ta zauna a gefen gadon kusa da kafarsa tace
‘Sannu da hutawa yallabai.’
Da walwalarsa ya amsa
‘Yauwa sannunku da kokari.’
‘Kaci abinci ne ko na kawo maka?’
‘Naci abinci sosai ma a gidan Yaya Bello.’
Suka cigaba da hirarsu.
Ta kula kamar hutawa yake son yi don haka ta mike tana fadin
‘Bari naje na fara shirin dora abincin dare.’
Har ta juya zata fice yace
‘Yauwa, kada kiyi abincin dare da ni a wajen Aisha zan kwana yau.’
Take ta daskare ta bishi da kallo da bakinta a bude.
Fuskarta yake kallo domin daman yana so yaga yanda zata yi idan yace mata zai koma wajen Aisha.
Ta kula da yanda yake kallon nata don haka ta rufe bakinta ta dan yi gyaran murya tace
‘Uhm, to!’
Ta fice daga dakin cikin sauri kafin yace wani abu.
Ya tashi ya gyara zama yabi kofar da kallo yana mamakin Zahra, tabbas yanzu ko ba a gaya masa ba ya san tana da hannu a cikin abubuwan da suke faruwa.
To ya zai yi da Zahra? Gashi ta cika masa gida da ‘yaya, sannan kuma yana ganin idan ma ya rabu da ita yanzu gaskiya bai yi mata adalci ba. Soyayya sukayi sosai ya aurota, gashi yanzu gani yake kamar bata da kowa sai shi domin iyayenta duk sun rasu kuma gidansu ma an raba gadon an siyar. Sai gidan Muhammad yayanta da shine kamar waliyinsu da kuma gidan kakanni kawai. Kuma idan ya kori Zahra ma to ya zai yi da ‘yayanta;shi har yanzu uwarsa tana nan yana jin dadin zama da ita baya yiwa yaransa fatan su rayuwa babu uwa.
‘Inna lillahi wa Inna ilaihi rajiun!’
Ya fada a fili.
Ya gyara zama , ya dubi agogon bangon da yake dakin yaga karfe shida saura. Ya koma ya sake kwanciya a gefen gadon yana tunanin yanda zai yi da Zahra.
………..
Tana fita daga dakin ta wuce dakinta, nema take tayi karo da bango saboda yanda idonta yake rufewa. Ya za ayi ace aiki ya karye, kenan yanzu ya tuna da Aisha? Ita yake gayawa gidan Aisha zai je?
Ido rufe ta fada kan gadon tana huci saboda takaici. To yanzu ya zata yi? Ta shafa cikinta saboda yanda yake ta mutsu-mutsu. Ta ja numfashi, gaba daya kwakwalwarta nema take ta daina aiki.
Ta lalubo wayarta sai kuma ta tuna wayar tana falon kasa, ta tashi tana bin bango saboda yanda jiri yake kwasarta. Ta lallaba ta sauka ta dauko wayar ta dawo dakin. Har ta zauna a gefen gado sai kuma ta tuna zai iya biyota kuma idan ya tsaya a bayan kofar akwai yiwuwar ya jiyo abinda take fada, don haka ta tashi ta shige bandaki ta turo kofa. Ta rufe toilet ta zauna a kai sanna ta lalubo lambar Amina ta danna mata kira.
Da sallama ta amsa wayar, amma ko amsa sallamar bata yi ba tace
‘Aminoni kin san aikin mutumin nan na Doguwa ya karye kuwa?’
‘Ban gane me kike fada ba? Me yake faruwa ne?’
‘Mtsewwe! Amina Ina cikin damuwa yanzun nan Abban Sadik ya dubi tsabar idona yake gaya min wai a gidan Aisha zai kwana.’
‘Eyee! Aisha kuma? To me ya faru? Don kuwa mutumin nan bai taba yin aikin ya karye ba wallahi?’
‘To wallahi wannan dai ya karye don yanzun nan yake gaya min wai kada nayi masa abincin dare a can zai kwana. Amina yarinyar nan so take ta kasheni da raina ba zata bar min Yusuf ba.’
‘Gaskiya da matsala, to yanzu ya za a yi?’
‘Wallahi ban sani ba Amina, bana son zuwa Doguwa da cikin nan kuma gashi kince shi ba a masa waya.’
‘Shifa baya bada lambar waya ma don ka’idarsa ce ba waya gaskiya sai dai idan aje. Kuma kinga ni yanzu ba zan iya zuwa ba saboda kinga Ummanmu ma jikinta yayi tsananin shekaran jiya aka kawo ta nan don mu dinga zuwa asibiti, kinga ba zan fita na barta ba.’
‘Allah ya Allah ya bata lafiya. Yanzu ya zanyi Amina? Ni ba ma tafiyar tashi ce ta dameni ba idan suka gane cewa nice nayi musu asiri fa? Don ko yanzu na ga Abban Sadik din yana yi min wani kallo.’
‘To ki daga musu kafa a kwana biyu in ya so ma ki gane inda ya sa gaba. Kinga yanzu idan dai ina lissafi daidai cikin ki yayi wata biyar kinga nan da wata hudu zaki sauka, da kinyi arba’in sai muje. Idan kuma ma nan da kwana biyu jikin Ummanmu yayi sauki sai naje miki Doguwan. Ke dai kawai ki tanadi kudi.’
‘Uhm, kin ji wata matsalar kuma don wallahi bani da kudi ma amma dole na nemo. Bari mu gani kafin lokacin ko wani abun sai na daga na siyar kawai aje.’
Suka ajiye wayar ta fito daga bandakin tana ta faman hada gumi, ta zauna a kan gadon ta kafa tagumi.
Tunani daya ne a ranta kada taje Abba ya gane itace tayi wannan asirin. A hankali hawaye ya fara bin fuskarta.
Lallai ta yarda Aisha ta fita hatsabibanci, amma tabbas idan dai da bokaye da malamai a garin nan sai tayi maganin Aisha; sa’arta daya yanzu tana da ciki, ga laulayi gashi kuma tunda aka tabbatar mata da namiji ne take kaffa kaffa da shi. Bata son taje wani daji ta kwaso masa matsala.
Tana nan zaune bata san me take tunani ba taji shigowar ‘yan islamiyya. Yusra ce ta fara shigowa ta sameta a dakin, nan ta gaya mata bata jin dadi su zauna a falon kasa. Haka ta kwanta ta rufe idonta saboda kada su dameta, domin ko abincin dare sai Jummai ta gayawa ta dafa musu.
Tana jin lokacin da Abban ya fito domin tafiya masallaci sallar Magriba, ta san idan yayi tunanin tana kasa can zai wuce idan bai sameta ba kawai yaran zai gayawa suce mata ya tafi masallaci. Hakan kuwa akayi, sai da ta lumshe Ido da ta ji saukarsa kasa bai shigo dakin nata ba domin bata son ganinsa a halin yanzu.
…………
Ana idar da sallar Magriba Abban Sadik yayo sauri ya ja liman suka koma gefe, yayi masa bayanin halin da ake ciki sai dai bai gaya masa daga gida bane. Nuna masa yayi a office ne ake neman jifansa da sihiri. Ya bashi addu’oin da zai dinga yi sannan kuma yayi masa alkawarin akwai abinda zai karbo masa zuwa wani satin, suna nan tsaye suna hirarrakinsu har akayi kiran sallar isha’i don haka suka koma masallaci suka tada Sallah.
………….
Tun bayan da aka idar da sallar Magriba take sauraron dawowarsa amma har akayi isha’i bai shigo ba.
Da kyar ta tashi ta hade sallar Magriba da isha’i tana yin sallar tana tunani wato ma wucewa yayi gidan Aishan ba tare da yayi mata ssallama ba.
Nan ta zauna a kan daddumar tana ta tunani kala-kala na yanda zata bullowa wannan al’amari, domin ba zata yarda ba.
Bata ji lokacin da ya shigo gidan ba saboda tunaninta baya wajen, jinsa kawai tayi ya turo kofar dakinta ya shigo.
Bayan ya amsa sallamarta yace
‘Yanzu kika idar da sallar ne?’
‘Eh, saura shafa’i da witri.’
‘To ni zan wuce, don Allah a rufe gidan da wuri kuma idan Saddiku ya kai goman dare bai dawo ba kiyi min waya.’
‘To in sha Allah.’
Ya juya ya fice bayan ya amsa a dawo lafiya da tayi masa.
Tayi kwafa ta share kwallar da ta taru a kwarmin idonta.
---------
Ba karamar jarumta yayi ba da ya daure bai je wajen Aisha ba har akayi sallar isha’i.
Tun daga bakin gate kamshin turaren wutarta yayi masa maraba, shi kanshi ya san yayi kewar wannan turaren. Ya karasa ya sa mukullinsa ya shiga kofar falon. Babu kowa a falon, ya dan tsaya ya karewa falon kallo; sai yanzu ya tabbatar ya dade rabon da ya shigo gidan nan. Ya ji motsi a dakin baki wanda ya san Amira ce, bai hango fitila a dakinsa ba sai a dakinta don haka ya tura kofar dakin a hankali ya shiga da sallama.
Tana zaune a kan gado ta mike kafa tana ta faman danne danne a waya, bai sani ba ko ta amsa sallamarsa ko bata amsa ba don shi dai bai ji muryarta ba.
Ya karasa ya zauna a gefen gadon yayinda ta dan janye kafarta, yana ta faman binta da kallo kamar yau ya fara ganinta. Ta bude baki kamar bata so tace
‘Sannu da zuwa.’
Sai da yayi ajiyar zuciya sannan ya amsa
‘Yauwa Aisha.’
Ya cigaba da binta da kallo ba tare da yace komai ba.
Jimawa kadan ta gaji da kallon da yake mata, ta zuro kafafunta kasa daga kan gadon ta mike tsaye tana fadin
‘Ga abincinka can a kan dining table muje na zuba maka kaci dare yana yi.’
Nan da nan shima ya mike ya sha gabanta, kafin tayi wani yunkuri ya janyota jikinsa gaba daya ya