Showing 63001 words to 66000 words out of 166068 words
sai da safe zan turo miki Rukayyan yanzu.’
Kafin ta amsa ya wuceta ya fice daga falon ba tare da ya dubi dining table din da ta jera abincin ba harda balloon da ta rataye.
Tabi bayansa da kallo tana mamaki, ta kara bude kofofin hancinta ko zata ji warin da yace yana ji amma ita kamshi kawai take ji kuma kamshi mai dadi. Ta shansahana jikinta nan ma kamshi taji, ta dai tabbatar babu wari a gidan. To me yake faruwa? Me yasa da can bai ji warin ba saida shigo gidan?
Ta kalli abincin da ta ajiye a dining table, take kwalla ta cicciko mata ido, ta sa hannu ta goge.
Ta kashe kudi gashi ba dadi take ji ba ta daure ta hada masa abincin kawai don ta burgeshi kuma ya shigo da wannan matsalar. Take wani bakin ciki ya tokare mata kirji, ta dafe kirjin tana Lahaula.
Tana nan a zaune ta ji shigowar Rukayya, ya bude mata gate ya turo ta shi ya koma.
Nan da nan tayi sauri ta tsige balloon din ta kai kicin ta Huda ta sa a shara, tana fitowa ta sa hannu ta shafe rubutun da yake kan cake din sannan ta budewa Rukayya kofar falon ta shigo.
Ta karfin tsiya ta danne damuwarta, ta yanka kazar ta bawa Rukayya tata sannan itama ta dan ci wanda zata iya. Ta hade kayan ta saka a fridge tana mamaki da takaici da fatan gobe kada ya shigo da wannan matsalar.
UWAR SADDIKU
Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)
23
Yana leko da kansa bakin gate din gidan Aisha yaji kamar an dauke wani gungumemen dutse da aka dora masa a kirjinsa, nan da nan ya nemi ciwon kai ya rasa. Ya kalli gefe da gefe ya ya kara bude kofofin hancinsa ya shaki iska ya ji babu wani wari. Ya juya ya kalli gate din yana mamaki, ya jijjiga kai cikin damuwa sannan ya kama hanyar gidan Zahra.
To wannan warin da takurar da yaji a gidan Aishan me ya kawota? Yana zaton dai warin da yaji ne ya haifar masa da duk sauran damuwar, to amma bai taba jin wari irin wannan ba. Abinda yafi bashi tsoro shine yanda kamar warin yake fitowa daga jikin Aisha. Shi tunda ya auri Aisha ko warin gumi bai taba ji a jikinta ba tunda ita din gwanar shafa turare ce. To me ta shafa yau din? Ko wani maganin ne? Amma ai lafiyarta kalau sai laulayi wanda shima yayi sauki sosai.
Haka ya shiga gidan yana ta faman neman dalili a kwakwalwarsa amma bai samu ba, sai dai yana fatan Allah ya sa tayi wanka ta shafa turare kafin gobe domin goben ne zata karbi kwana.
………
Da yake jiya shinkafa dafa duka ta dafa da daddare bata samu tayi amfani da maganin kwarjinin da aka bata ba, sai yau ta shirya tuwo miyar kuka. Ta sami ‘yar karamar tukunya ta debar masa tashi miyar ta mayar wuta ta saka maganin, tsaf ya bace kamar ba a sa wani abu ba. Ta lashi kadan a harshenta taji babu abinda ya canza na dandanon miyar, cikin murna ta juye a flsak ta kawo ta jera a dining table.
Yana dawowa daga gidan Aisha ya zauna a table ya cinye tuwonsa tas, tana gefensa tana yi masa hira domin ita tace masa yunwa take ji shi yasa ana yin magriba ta ci nata tuwon.
……..
Duk matar da ba a wajenta ya kwana ba ya saba shiga gidanta da safe, tun asuba yake tunanin yanda zaiyi ya shiga gidan Aisha don yana tsoron ya shiga yanayin da ya shiga jiya.
Bai ankara ba har takwas da rabi ta wuce, ya riga ya san ta tafi aiki. Don haka kawai sai ya cigaba da shirinsa.
Sai da ya shirya tsaf ya kama hanyar office sannan ya kirawota.
Lafiya kalau suka gaisa, yanda yaji walwalarta shima ya saukar masa da walwala. Ya sanar da ita bai fito da wuri ba ya zo ya tarar ta fice don haka sai ya dawo zasu hadu.
Sukayi sallama kowa yana walwala. Itama Aishan tsoron da ta kwana da shi na abinda ya faru ya gushe, don haka cikin walwala ta cigaba da gudanar da aikinta.
……….
Kamar yanda ta saba kafin a idar da sallar Magriba ta shirya abincin dare, ta bi gidan da turare haka ma jikinta. Kamshine kawai yake tashi ko ta ina.
Bayan yayi sallama da Zahra ya nufo gidan,gaba daya ma ya manta da abinda ya faru jiya sauri kawai yake ya je ya ganta saboda bai gantaba da safe.
Yana shiga bakin gate yanayin ya fara canzawa, a fili yace
‘Subhanallahi.’
Ya karewa farfajiyar gidan kallo kamar mai neman wani abu. Ya daure ya karasa cikin gidan.
Yana shiga falon kamar a nan warin yake; ta taso daga inda take zaune da fara’arta ta nufi shi, sai dai kafin ta karaso inda yake ta kula da yanayin da fuskarsa ta shiga. Ta dan tsaya nesa da shi tana kallonsa, cikin sanyin murya tace
‘Sannu da zuwa.’
Kamar a fusace ya amsa
‘Yauwa, wai me kike shafawa ne ko kike sakawa a gidan nan mai wannan azabar wari?’
Ta sunkuyar da kai tana kokarin danne kwalla tace
‘Babu fa abinda na saka, turaren wuta na ne kawai wanda ka saba dashi kuma kaima kana yaba dadinsa.’
‘Kai! wannan ba turare bane. Gashi kaina har ya fara juyawa, bari naje daga waje na sha iska amma don Allah ki caje gidan nan ko mushen wani abun nema a ciki ba a sani ba.’
Kafin ta amsa yayi waje.
Yana fitowa ya tsaya a bakin gate yana shakar iska yana mamaki, wannan wace irin musiba ce? Ita kuwa Aisha me take sawa a gidan nan? Ya kama hanya ya nufi gidan Zahra, taku kadan sai kuma ya tsaya. Ya tuna ai daga can ya fito kuma a nan ya kamata ya kwana, to ya za ayi ya bar Aishan ita kadai?
Ya tsaya chak ya kasa gaba ya kasa baya; ba zai iya kwana a gidan Aisha ba a halin da ake ciki to amma idan ya koma gidan Zahra me zai ce mata? Har ya fara gajiya da tsayuwa bai sami wata amsa ba, don haka yaja jikinsa a hankali ya nufi gidan Zahra zuciyarsa cike da matsananciyar damuwa.
Tana zaune a falon sama tana jiransa domin yaron Malam ya tabbatar mata indai an binne wannan abun to Abban Sadik ba zai sake iya kwana a gidan ba.
Tana jiyo motsin bude gate ta kyalkyale da dariya saboda jin dadi, tana jiyo takunsa a bene ta gyara zama ta saita fuskarta.
Da sallama ya shigo, bayan ta amsa sallamar tace
‘Mantuwa kayi ne?’
Cikin yanayi na damuwa yace
‘Um um, babu abinda na manta. Akwai wata ‘yar matsala ne don haka a nan zan kwana, amma na kai Rukayya ta tayata kwana.’
‘Ikon Allah, to Allah ya warware.’
‘Amin. Ki saka min abinci idan na dan huta zan fito na ci.’
Bai saurari amsarta ba ya shige dakin.
Tayi dariya tace
‘Ka zo hannu!’
……….
Yanda Aisha ta kwana cikin damuwa da rashin bacci shima haka ya kwana. Duk yanda Zahra ta so ta kwana a dakinsa sai hakura tayi, domin kiri-kiri ya gaya mata ba kwananta bane don haka ta bari sai kwananta.
Wannan bai dameta ba saboda ko babu komai ta san yana nan a cikin gidan, kuma kwanan ma ta san nan da wani dan lokaci zai fara bata.
……….
Duk yanda Aisha ta so yin bacci a daren nan gagararta yayi, har wajen karfe biyu na dare idonta biyu. A hankali ta tashi ta fice daga dakin, ta koma dakinta ta yi alwala ta tayar da sallar nafila; shine kawai abinda ta tabbatar zata iya yi ta sami natsuwa.
Gari yana wayewa suka shirya ita da Rukayya suka fice.
Wunin ranar gaba daya bata gansa ba sai dai kawai yayi mata waya da safe sun gaisa, da dare yayi kuwa ko shigowa bai yi ba ya turo mata Rukayya.
__
Yau sati biyu kenan rabon da Abban Sadik ya shiga gidan Aisha, tun tana kasa bacci har ta hakura yanzu baccinta takeyi.
Wasu lokutan tana jinsa zai bude gate ya shigo sai ya kusa shigowa falon sai ya koma da sauri.
Tun abun yana bata mamaki har ya fara bata tsoro, addu’a kawai takeyi tana sadaka.
Duk karshen wata da kansa yake kawo mata cefanenta har cikin gida, amma wannan watan da akayiwo cefanen Malam Sule aka bawa ya miko mata. Ya ajiye mata a kan baranda ta kwashe ta shigar ciki, washegari kuma ya turo mata kudin cefane ta account dinta.
Kiri-kiri yanzu sun koma tsakaninta da shi sai waya. Idan suna magana a waya sai ta zata babu wata fitna da zata hanashi zuwa wajenta, amma haka za a sakeyi ba zai iya zuwa inda take ba.
------
Ta gaji da zaman gidan saboda komai baya mata dadi, idan ta taso daga aiki sai dai kawai ta zauna tayi ta zare ido tana tunani. Don haka ta yanke shawarar tunda yau Juma’a idan ta tashi daga makaranta zata wuce gidan Zahida; tunda ta riga ta sanar da shi ta waya.
Sai da suka tashi daga makaranta sannan ta kirawo Zahida ta sanar da ita, inda Zahidan ta sanar da ita suna gidan Hajiya ita da yaranta a nan zasu wuni. Don haka itama sai ta wuce gidan Hajiya kawai.
A nan ta tarar da Zahida da yaranta, ta gaya mata Yaya Zainab ma tace bayan masallaci zata zo.
Bayan ta gaida Umma ta karasa kusa da Anti Uwani, bayan sun gaisa Anti Uwani tace
‘Shatu cikin nan dai yana baki wahala, naga duk kin wani kara figewa gashi ko wata uku bai karasa ba. Don Allah ki dinga dan cin abinci, idan kuma wani abu kike so a dafa miki kiyi min waya ni sai na dafa na rufo kaina na kawo miki har gidan.’
Suka zauna nan ana ta hirarraki.
Kowa ya kula da ramar da Aisha tayi amma gaba daya su sun dauka cikin da take da shine ya saka ta ramar don haka babu ma wanda ya tambayi wani bahasi.
Har bayan la’asar anata kaiwa da kawowa, su Farha sai murna sukeyi Mama ta zo ga kuma ‘yan wasa.
Aisha da Zahida tare sukayi Sallar la'asar a dakin Anti Uwani, bayan sun idar da sallar ne Zahida ta mike tana nade daddumar tana fadin
‘To bari mu zo mu kama hanya mu da bamu da mota don yau babansu baya gari balle yazo daukanmu.’
Aisha tace
‘Don Allah ki bari sai munyi sallar Magriba sai mu fita gaba daya in ya so sai na kaiki gida na wuce tunda ma maigidanki baya nan.’
Da fara’arta tace
‘Na bari, kudina sun huta matar Yusufa.’
Sukayi shiru na dan lokaci.
Zahida ta gama ninke daddumar ta matsa lokon mudubi inda ake ajiye dadduman ta ajiye, ta juyo ta zauna a gaban Aisha wadda har yanzu take kan daddumar ta dubeta tace
‘Wai ni ina Yayarki ne? Bata saki sabon film bane ko har idea ta kare.’
Ta kawar da kai tace
‘To ina ga dai wannan film din nata ta hannun ‘yan tsubbu ta biyo don yanzu abinda ke faruwa idan na gaya miki ji zakiyi kamar almara.’
Ta zaro ido
‘Ke haba?’
A nan ta bata labarin halin da suke ciki, ta kara da
‘Yau kusan sati biyu kenan baya shigowa gidan, ina jinsa zai shigo har kofar falon amma nan da nan zai koma kamar wanda aka razana. Kuma wallahi babu wani wari; kin san ni dai da turare ko? To bayan yayi maganar ma sai da nayi order din wasu daga Xee Yazeed Incense and Perfumes amma duk da haka mutumin nan wai wari gidan yakeyi har yana sa masa ciwon kai. Yanzu tsakani na da shi sai waya amma sati biyun nan ni ban sa shi a ido na na.’
Da mamaki Zahida take kallonta, tace
‘Wannan ma ai daga ji kin san aikin asiri ne, ke kuma kina zaune baki fada ba balle a nemi magani. To jira kike ta kasheki ko me?’
‘To me zan ce Hida, kin san yanzu da na gayawa Hajiya zata ce a gayawa Yaya Abubakar, kuma shi ba lallai ya yarda cewa asiri bane. Cewa zai yi sai an yiwa Yusuf din magana, kuma wannan ba zai magance komai ba tunda kana magana ne da mutumin da yake a hayyacinsa shi kuwa kina ganin yanda yake birkicewa ma kin san ba lafiya ba.’
‘Eh, da wannan don wannan! To ke din me kike yi a kai?’
Ta karyar da kai tace
‘To ina dai addu’a kuma ina sadaka, na san babu abinda ya gagari Allah. Don ni tsoron ma fada nake kada nima naje na kauce hanya gara idan wuta take son shiga taje ta shiga ita kadai abinta.’
‘Hakane, amma gaskiya cikin biyu ayi daya; ko a gayawa Hajiya duk da na san yanzu ana gaya mata zata tada hankali har sai jininta ya sake hawa ko kuma dole mu gayawa Yaya Zuwaira sai a nemi mafita. Ai akwai malaman da zasu baka adduoi kana yi suna tayaka har a sami lafiyar abun.’
‘Gara dai Yaya Zuwaira, duk da dai kin san duk abinda aka gaya mata sai ta gayawa Hajiya amma dai duk da haka gara a gaya matan.’
Nan suka yanke shawarar zasu tafi kafin magriba in ya so sai su fara biyawa gidan Zuwaira kafin su wuce gida.
Sai wajen biyar da rabi sannan suka kama hanya, Yaya Zainab ma da ita suka tafi don ita kadai ta zo ba tare da yara ba. A hanya Zahida ta sanar da ita abinda yake faruwa suka hadu suka yita sallallami.
A kitchen suka sami Yaya Zuwaira tana kwashe tuwo don haka nan suka zauna a kichin din suka mayar mata da abinda ya kawo su.
Saida ta gama kwashe tuwon suka dawo falo sannan ta dubi Aishan tace
‘Sannu! Yanzu da da kika yi shiru haka zakiyi ta zama tsakaninki da miji sai waya? Wannan ma ai ba sai an fada ba kowa ya san tsafi ne. Akwai malamai sosai da muke karatu da su wasu ma su ke karantar da mu a islamiyya, in Sha Allah gobe asabar idan naje zan nemi malamai na tambaya.’
Sukayi shiru na dan lokaci, jimawa kadan Zuwairan ta cigaba
‘Wasu abubuwan kana jinsu kamar almara ashe suna faruwa, Allah ka shirya zukatanmu.’
‘Amin.’
Suka amsa gaba daya.
Ana kiran Magriba sukayi mata sallama suka wuce.
__
Cikin walwala Zahra take gudanara da lamuranta musamman tunda ta gane Abban Sadik ya daina musa duk wani abu da ta fada ko dai-dai ne ko ba dai-dai bane. Gaba daya ma ya rage magana da walwala, sai dai wannan bai dameta ba tunda yanzu duk yanda ta tsara haka akeyi.
Sadik ya gama jarrabawarsa ta WAEC da NECO don har ma sunyi candy, sai dai bai fasa tara abokai a boys quarters din gidan ba. Duk yanda Jummai ta so ta karkatar da hankalin Zahra ta duba abinda Sadik yake aikatawa ta ki ta duba, sai dai kullum ta tambayeshi inda kai tsaye zai ce mata ba haka bane.
……….
Ya riga ya amsa zai saya mata mota sai dai ya gaya mata ta saurara zuwa nan da sati daya akwai kudin da yake sa ran zai samu in ya so sai ya saya mata motar.
Ya gama cin abincin darensa yana zaune a falon sama yana kallon tasahar Aljazeera inda take zaune a kusa da shi tana chatting a waya. Ta ajiye wayar ta dan matso kusa da shi tace
‘Yallabi maganar mota ta tana nan dai ko?’
Yayi murmushin yake wanda yanzu ya zamar masa dabi’a, duk murmushin da zai yi baya kaiwa zuciyarsa. Yace
‘Tana nan mana, na ma biya kudin sai dai akwai dan ciko da zanyi musu next week sai a kawo motar.’
Ta sake gyara zama cike da tsananin farinciki sannan tace
‘To gaskiya a sallami Malam Sule don bana son ya koya min mota tunda kai kace baka da lokaci, sai a kawo wani direban.’
‘Wannan babu matsala, Malam Sule dama direban gwamnati ne ai. Ranar litinin mai zuwa sai ya koma office, akwai Alin Kano sai ya karbi aikin.’
‘Gaskiya ni dai dama ka bari na samo direban, tunda kaga akwai matasa sosai a ‘yan uwan Abban mu don wasun suma direbobin motar haya ne. Idan na samo a dangi ai ya fi ko, sai ya koya min kuma ya cigaba da rike aikin Malam Sule.’
Ya dan gatsina baki yace
‘To babu laifi, ki duba din in ya so idan an samu sai ya karbi aikin Malam Sule din.’
A cikin daren ta kirawo Amina tace ta samo mata direba, ita dai ba komai ta damu da shi ba kawai tana son wanda zai yi duk abinda tace ba tare da ya kawo mata tangarda ba. Idan ya gama koya mata tuki sai kuma ya dinga kai yara makaranta da motar Malam Sule da za a bashi.
Haka ta kwana cikin walwala saboda burinta ya kusan cika, itama zata mallaki mota ta dinga fita a gari kowa yana kallonta.
………
Ya riga ya sanar da Malam Sule cewa sati mai zuwa zai koma office da aiki saboda za a kawowa Zahra mota da sabon direba. Ko daya Malam Sule bai nuna damuwa ba saboda wannan abune da yake ta jiran faruwarsa saboda abubuwan da suke faruwa ‘yan kwanakin nan.
Yana office aka kirawoshi aka sanar da shi ga motar da ya saya ya fadi inda za a kai masa, nan take yace a kai masa gida amma idan an kai a jirashi a bakin gate.
Kusan lokaci guda suka Isa gidan da yaron da ya kai motar, maigadi ya bude musu gate suka shiga gaba daya. Bai gaya mata yau za a kawo motar ba don haka bata sa rai ba, ko da taji shigowar