Showing 69001 words to 72000 words out of 166068 words
tafi wadda Abban ya bata tsada.
Tunda motar tazo hannu kuma sai ta fara yi masa tunin yayi mata alkawarin kujerar Umra, wadda ta ce masa ta azumi take so kuma shi ma goman karshe. Ya tabbatar mata kujerarta tana nan in Sha Allahu da lokacin yayi za a bata.
………
Tunda Balele ya fara aiki Sadik ya makale masa saida ya koyi mota, dama tun a wajen Malam Sule ya so koya Abbanshi ya hana.
Jarrabawarsa ta WAEC ta kusan fitowa, shi da Mommy sun hadu sun saka Abban a gaba a kan lallai sai an kai shi Dubai zai yi degree. Da fari Abban ya ki amincewa amma daga baya ya amsa don haka sakamakon WAEC din kawai ake jira.
A labarai Network News Abban ya gani cewa WAEC sun fitar da sakamakon don haka a take ya ce a kirawo Sadik ya zo a duba masa nasa a computer din Abban.
Yusra aka tura taje dakinsa wanda yanzu ya koma boys quarters ta kirawoshi, an yi sa a yana nan don haka kafin Yusran ta gama gyara zamanta ya shigo falon.
Da mamaki Abban ya kalleshi, har ya karaso kusa da shi ya zauna sannan yace
‘Kai meye haka ne zaka taho kamar zaka fada kan mutane.’
Ya sunkuyar da kai yana fadin
‘Wallahi bacci nakeyi Abba ta taso ni.’
Nan ya umarceshu ya dauko katin inda yace masa yana wajen Mommy. Ba tare da bata lokaci ba ta tashi ta dauko katin tare da computer din Abban ya karba ya duba masa sakamakon.
Yaci komai da sakamakon mai kyau sai dai bai ci English ba, wanda kuma dole sai da shi ake admission a halin yanzu.
Abban ya dubeshi yace
‘Baka ci English ba, ya akayi haka?’
Ya shafa kai
‘Wallahi Abba ina jin matsala muka samu don duk ‘yan makarantar tamu da muka yi exam tare har yanzu bamu ga wanda yaci English din ba.’
‘Babu wata matsala, kun dai fadi kawai. Ai da matsala kuka samu rike sakamakon za ayi a saka muku pending ko awaiting result. Kun dai fadi English kawai, amma zanje makarantar naji.’
Mommy tace
‘To yanzu ya za ayi da admission din nashi?’
‘Ai babu wannan zancen kuma har sai ya sake jarrabawa ya sami English wannan ai ko a nan Nigeria ba zai sami admission din ba. Kasashen waje kuma ko sun bashi admission rashin wanna English din sai yayi affecting dinsa a nan gida. Next year sai ya gyara mu gani, amma dai gobe zanje makarantar naji yanda za a yi.’
…………
Kamar yanda yayi alkawari haka yayi, yana fita ya tsaya a makarantar su Sadik. A nan principal yayi masa bayanin cewa su Sadik su biyar ne suka sami F a English, saboda sun yiwa malamin da ya zo da jarabawar rashin kunya; su dai a makarantar suna tunanin abinda ya sa ya kada su English din kenan.
Har ya tashi zai tafi principal ya tsayar da shi, yace
‘Yallabai kuma a dan duba yaron nan don ka ga da yaron babu ruwanshi amma zuwa lokacin da suka gama jarrabawa gaskiya yaran da yake bi gaskiya duk suna shaye-shaye. Gara dai a bincika kafin abun yayi nisa.’
Yayi masa sallama ya tafi yana mamaki; Bai taba zargin Sadik ba amma yanzu kam dole ya dau mataki.
Bayan ya dawo daga aiki ko abinci bai ci ba ya sa Mommy ta kirawo masa Sadik, har zata fita ta barsu yace ta dawo ta zauna.
Ya dubi Sadik din yace
‘Su waye abokanka? Kuma meye gaskiyar magana da aka ce min kuna shaye-shaye?’
Ya zare ido
‘Wallahi Abba babu abinda muke sha, gaba dayan abokan nawa ma Mommy ta san su.’
Ya kalli Mommy.
Tace
‘Gaskiya na san abokansa dukansu babu wanda yake shaye-shaye, yaran da har nan din ma suna zuwa.’
Duk yanda ya so yayiwa Sadik fada Mommy bata bari ba, tun yana kokarin fadan har ya gaji yayi musu shiru.
Kuma da yake gaba daya yaran sun riga sun gane duk yanda Mommy ta fada haka akeyi don haka duk abinda basa so yayi magana a kai sai su tsara Mommy, don haka haka Sadik ya sa ta gaba a kan karya akeyi masa. Shikenan a haka zancen ya wuce.
Haka ya cigaba da tara abokansa suna shaye-shayensu da sakarcinsu.
Jummai tana kallon abubuwan da suke faruwa amma babu yanda zata yi don haka ta sawa abun ido.
--------
Tun ranar da suka dawo daga asibiti bai sake shiga gidan Aisha ba, wayar ma yanzu ba sosai sukeyi ba.
Ga shi idan yayiwo cefane a gidan Zahra zai ajiye ya raba sannan yace Balele ya kwashi na Aisha ya kai mata; don haka a nan Zahra zata samu ta zare duk abinda take ganin bata so a kaiwa Aishan. Ta kwashe kaji da kifi wani lokacin harda kayan shayi duk kwashewa takeyi, don haka duk wata sai Aisha tayi ciko a cefanenta. Ta riga ta san me yake faruwa don haka abun baya wani damunta.
…………
Tunda aka siyo motar nan kuwa Zahra ta sami kafar yawo, gashi yanzu baya iya yi mata fada. Wasu abubuwan suna damunsa amma sai ya rasa yanda zai yi da ita.
Ya raina hankalin Sadik don haka ma ya hana a bashi mota, amma yana ji yana gani Zahra ta barshi yana hawa motarta. Gashi bazai sami admission ba sai shekara ta zagayo idan ya gyara jarrabawarsa.
Haka dai ya zubawa gidan ido ita da yaranta suna yin yanda suka ga dama.
………..
Tunda suka bar gidan Aisha Hajiya da Anti Uwani suka kasa nutsuwa, ta san Allah ne yake bada haihuwa amma tana ganin gara a nemi taimako a kan yawan barin nan. Don haka suna komawa gida ta sa Anti Uwani ta kai abun sadaka makarantar allo ayi mata addu’a.
Bayan ta yiwa malamin bayani kuma yace ta sami ruwan zamzam ta dinga tofa fatiha kafa bakwai tana sha kullum safe da yamma, ko menene zai warware da izinin Allah.
Don haka yanzu bata rabuwa da ruwan zamzam kullum cikin tofi take tana sha. Ga sallar dare da adduointa da bata fasa ba.
Sai dai duk yanda ta so abun kar ya dameta ta kasa jurewa. Ta rame ta dan yi duhu, idan dai mutum ya santa ya san tana cikin damuwa. Da tana tsammanin ramar da takeyi ciki ne amma yanzu da babu cikin ta gane lallai tana cikin damuwa.
Duk da motsin Amira a gidan yana debe mata kewa amma dai gaskiya yanzu abun ya fara damunta sosai, tana kewar mijinta kuma zaman a haka yana damunta.
Ta sami islamiyya a kusa da unguwar tasu ta shiga duk don ta debewa kanta kewa amma dai ita kanta ta san lallabawa takeyi.
Lokuta da dama idan ta kwanta da daddare sai dai tayi ta juyi a gadon, idan kuma abun ya ciyota sai ta kwana tana kuka.
Tun tana lissafi yanzu har ta bata a lissafi, ta san dai an fi wata hudu.
__
Tunda aka fara lissafi azumi saura sati biyu tayiwa Abba tunin Umrarta, a take ya sanar da ita cewa duk wasu shirye-shirye ma ya gama su tunda tace a goman karshe take so.
Saura kwana biyu azumi yana zaune a falonsa yana karatun jarida ta shigo falon, ta mika masa takardar da take hannunta tace
‘Ga shopping list din azumin na rubuta yallabai.’
Ya karba ya dan duba, ya mayar ya ajiye a kusa da shi yace
‘Gobe za a kawo in Sha Allahu.’
Dama ita yake jira don itama Aisha tun jiya yayi mata waya ta turo masa kuma ta turo.
Jimawa kadan ta dubeshi tace
‘Yallabi ka shirya mana mu tafi Umra tare, ai zai fi dadi ko?’
Ya ajiye jaridar ya gyara zama sannan yace
‘A’a ai na gaya miki ni bazani Umra ba, Hajji nake son komawa kuma akwai wani business da nake son yi a Dubai don haka sai na hada kudin gaba daya da na aikin Hajji da kuma na business din in ya so ko shekara mai zuwa ko ta sama idan na gama aikin Hajji sai na wuce Dubai din.’
‘To bari naje na dage da addu’a wata kila da ni za a je Dubai din. Amma dai ka san gaskiya Umrar azumi akwai sa nutsuwa ko? Wallahi shi yasa na so mu tafi tare.’
Duk yanda ta so ya shirya su tafi Umrar nan tare yaki domin ya tabbatar mata shi Hajj zai je kuma ba zai yiwu da shi da ita su tafi su bar yara ba, don haka dai ta hakura.
Fargabarta daya kada ta tafi kafin ta dawo ya koma wajen matarsa; duk da cewa ko a daren jiya saida sukayi magana ta Whatsapp da yaron Malam ya tabbatar mata ko shekara nawa zatayi bata dawo ba ba zai iya kusantar Aisha ba, ya ma tabbatar mata ba Aisha ba ko wata mace ce ma babu abinda zai shiga tsakaninsa da ita.
Don haka ba tare da damuwa ba ta cigaba da shirinta na tafiya Umra.
………….
Ana i gobe azumi ya yiwo duk wata sayayya, kowacce list din da ta bayar shi yayi amfani da shi ya siyo mata. A nan kan barandar gidan Zahra ya sauke kayan ya kirawo Balele ya ware na Aisha yace ya kai mata yanzu shi kuma ya shige gida.
Yana shigewa Zahra ta dakatar da Balele ta caje ledodin kusan duk wani abu da yake kwalba ko roba saida ta kwashe shi irinsu mayonnaise da salad cream, butter. Ta dauke kayan shayi ma sannan ta kwashe kwai da kaji. A karshe idomie kawai ta bari rabin carton da macaroni da semovita sai sabulun wanka da Omo aka kaiwa Aishan.
Haka ta karba tana mamaki; to ya san wannan zai siyo menene zai sa yace ta rubuto list. Haka ta adana kayan ta dauki Amira suka je suka karasa nasu shopping din na kayan bukata saboda azumi.
-------
Tun saura kwana uku jurgin su Zahra ya tashi Rahma; ‘yar uwarta wadda ta zauna mata da ta haifi Sumayya ta dawo gidan, domin itace zata kula mata da yara da gidan kafin ta dawo.
Sallah saura kwana goma sha uku jirginsu ya tashi sai kasa mai tsarki.
-------
Ranar da Mommy ta tafi da yamma ana dab da shan ruwa Rukayya ta sami Abban a falo, yana kwance a kan doguwar kujera ta shiga da sallama. Bayan ya amsa sallamarta ta karasa ta zauna a gabansa, yace
‘Ya akayi ne Rukayya? Ko har an fara missing Mommy ne?’
Tace
‘A’a Abba, abinda ma sati biyu kawai zatayi.’
‘Hakane.’
Sukayi shiru na dan lokaci, jim kadan Rukayya tace
‘Abba naje gidan Anti Aisha na dinga tayata kwana kafin Mommy ta dawo?’
Da fara’a ya sa mata
‘Eh, ki je Rukayya.’
Zumbur ta daka tsalle ta mike, kafin yace wani abu tayi kasa da gudu.
Ya jijjiga kai yana murmushi; Rukayya tana son Aisha kuma Aisha tana son Rukayya sai dai yana sane da yanda Zahra ta hana wannan alakar kulluwa.
Tunda Zahra ta tafi airport yake tunani ko yace Aishan ta dawo nan gidan don watakila nata gidan ne yake warin sai dai idan ya tuna da fitnar Zahra sai ya fasa, haka yayi ta tunani ba tare da ya samo mafita ba . Daga baya bacci ya kwashe shi a kan kujerar.
Ita kuwa Rukayya tana saukowa ta gayawa Anti Rahma Abba yace taje don zata dinga taya Anti Aisha kwana. Nan take kuwa ta hada kayanta ta fice daga gidan.
Duk yanda Rahma ta so Yusra ta sa hannu wajen hidimar gidan nan ta ki, ta fahimci Zahra ce kawai take saka Yusra abu tayi don haka ta kyaleta. Ita da Jummai suke duk aiki. Don haka a dole ta nemi Jummai da ta dinga bari bayan isha’i ta dinga tafiya.
Sai wajen goman na dare a lokacin Nigeria sannan Zahra ta sami layi ta kirawo mutanen gida.
Bayan sun gaisa da Abba ta sanar da shi abinda ake ciki ta nemi ya bata yaran. Nan take ya kirawo Yusra ya mika mata wayar yana fadin
‘Ga Mommy, idan kun gama ki kawo min wayar.’
Sai da Mommy ta gaisa da kowa har Rahama, har Sumayya ma saida tayi ta surutunta a waya, da suka gama Yusra ta karbi wayar. Tana karba Mommy tace
‘Ina Rukayya ne? Ko tana wajen Abba?’
Tace
‘Hmm! Mommy ai kina tafiya yace ta hada kayanta ta koma gidan matarsa.’
Take jikinta yayi matukar sanyi. Tsoronta daya kada yaje kafin ta dawo ya koma zuwa gidan Aisha. Ta tuna da alkawarin da Yaron Malam yayi mata; to amma gashi tana tafiya har ya tura Rukayya, lallai idan bata yi da gaske ba idan ta dawo sai an sake mata aiki a kan Abba.
Shirun yayi yawa don haka Yusra tace
‘Mommy kina ji na?’
‘Ina jinki Yusra, zan dawo na samesu ita da Abban.’
Sukayi sallama Yusra ta mayarwa da Abban wayarsa.
………..
Tunda Yusra ta gaya mata Rukayya ta koma gidan Aisha ta kasa sukuni, duka wani buri da ta ciwo a kan zata zo tayi ta tuba tana ibada a nan ta watsar . Hankalinta gaba daya ya taho gida; ita da yaron Malam yace mata ko shekara nawa zatayi a Saudi Abba ba zai nemi Aisha ba gashi har ya fara shinshine-shinshine?
Lallai tana da aiki a gabanta.
Tun a wannan lokacin ta fara Allah-Allah ta gama Umrar ta koma gida, haka dai ta kasa natsuwa tayi ibada yanda ya kamata.
Ta sanarwa Yusrar ta sa mata ido da zarar ta ga wani canji a wajen Abban idan ta bugo ta sanar da ita. Kasancewar ta san ta bar Yusran a gidan ya sa ta dan sami natsuwa don ta san duk abinda ya faru a gidan sai ta gaya mata kuma tana dawowa zata dauki matakin da ya dace.
---------
Lokacin Sahur ne, kowa ya sauko ya ci abincinsa amma har an kusa ayi assalatu bata ga Sadik ya shigo daukar nasa abincin ba kamar yanda ya saba. Don haka ta zuba masa abincin ta bude kofar gidan ta fito a wannan daren ta nufi boys quarters din.
Da akwai wuta don haka bata bukatar fitila, ta zagaya ta hau barandar boys quarters din a hankali, kofar dakin a bude take kuma da alama basu ji motsin shigowarta ba sai da ta karasa har bakin kofa.
Sadik din yana tsaye a gaban irin teburin robar nan, kwalbar magani ce a hannunsa wadda yake juyewa a cikin robar lemon coke babbar, kusa da robar kuma kwayoyin magani ne kanana guda hudu a kan takarda. Kafin ta karasa sallamar da ta fara yayi sauri ya dure maganin ya ajiye kwalbar ya gyara tsayuwarsa ya kare abinda yakeyi.
Abokinsa wanda yake kuryar dakin wanda bai hango me yake faruwa ba yace
‘Kana da matsala, kayi sauri ka hada mana kayan nan don wallahi ni ko an yi assalatu sai na sha don ba zan iya kai azumin ba idan ban chake ba wallahi.’
Saida ta karasa shigowa dakin sannan abokin nasa ya gane dalilin daga masa hannun da Sadik din yake faman yi. Ta ajiye flask din a gefen Sadik din tana fadin
‘Abincin Sahur ne ba kazo ka karba ba Sadiku shi yasa na kawo maka ka na ga an kusa assalatu.’
Ya shafa kai yana wani kifta ido yana fadin
‘Dama yanzu zan zo ai, makara muka dan yi ne.’
Har tayi kamar zata tafi tayi wuf ta shammaceshi ta dauke robar coke din, da kwalabar maganin da kwayoyin da bai riga ya dura a robar ba; ta fice daga dakin tana fadin
‘Wallahi shaye-shaye kakeyi Saddiku sai na nunawa Abbanka, har Mommy ma sai na nuna mata.’
Kafin yayi wani yunkuri ta fice da hanzari.
Tana fita shi da abokin nasa sukayi tsuru-tsuru; nan da nan dabara ta fadowa Sadikun. Ya sallami abokin nasa ya sa maigadi ya bude masa gate ya fice. Ya koma dakin ya dauki abincin ya juya kamar yaci sannan ya koma ya kwanta. Ya dauki waya ya kirawo Mommy, tana dauka yace
‘Mommy kinga Anti Rahma ko, haka kawai ban san me ya kawota dakina ba yanzun nan tana shigowa ta ga robobi a kan tebur tace wai Ina shaye-shaye. Kuma wallahi Mommy ba nawa bane Balele ne ya manta su da yake a nan ya Sha ruwa don ni ban ma san menene ba tunda a robar coke ne. Na gaya mata ba nawa bane amma ta tafi da su wai sai ta gayawa Abba ina shaye-shaye.’
‘Subhanallah! Bana son karya Saddiku, idan kana shan wani abu ka gaya min idan ma baka sha ka gaya min.’
‘Wallahi Mommy kema kin san babu abinda nake sha haka kawai dai take son yin min sharri. Kuma ina jin Jummai ce ta saka ta don itace me cewa ta ga murfin magani a bq din.’
‘Tabbasa biri yayi kama da mutum! Bari na kirawo Abban naka, su kuma duk zasu ji daga gareni. Na rasa me yasa suke nemana da sharri musamman ma Jummai.’
Motsin Abban ya jiyo ya taho dakin a fusace yayi sauri ya katse wayar ya kifeta, ya juya kamar yana bacci.
Da karfi ya bangaji kofar yana shiga dakin ya sa hannu ya kunna fitila.
‘Sadik.’
Ya kirawo sunanshi a fusace.
A tsaye Sadik din yake a kan katifarsa ya jingina da bango da alamar razana a fuskarsa.
‘Na’am.’
Ya amsa a firgice.
Ya karewa dakin kallo sannan yace
‘Ina abokin naka da kuke shaye-shayen tare?’
Ya zaro ido
‘Shaye-shaye Abba? Ai babu kowa ni kadai nake kwana, jiya ne ma da aka sha ruwa abokaina suka zo su uku kuma da muka tafi asham daga can suka wuce ni kadai nake kwana.’
Ya juyo ya kalli Rahma wadda take tsaye a bayansa, tace
‘Ai kuwa sai dai in yanzu yaron nan ya fita don yana nan har maganar da yake fada naji.’
‘Wallahi Abba ni ban san wa ta gani ba kuma ni kadai na