Showing 12001 words to 15000 words out of 166068 words

Chapter 5 - UWAR SADIKU COMPLT BY SAKINA YAZID.txt

11 Jul 2024

25433

wata matsala, kawai dai ita din ta fi son haka ko kuma akalla ta sami complete apartment nata wato daki, bandaki, falo da kitchen; kin ga kuma idan ta zauna a nan daki kawai zata samu sauran duka hadaka ne.’

‘Um, lallai! Ai ko dai da ka hade mun ko babu komai kaji motsin mutum ma rahama ne. Da nan zata zauna ai ko mu sai mun fi samun natsuwa tunda ko dai ba kwanana ba kana cikin gida tare da iyalanka gaba daya.’

‘Wallahi, nima hakan naso amma dai ita bata son hakan sai dai ko zuwa nan gaba kafin ayi auren mu gani.’
‘Um.’

Sukayi shiru yayinda Abban Sadik ya cigaba da duba wayarsa da take hannunsa, Zahra ta gyara kwanciya ta rufe ido kamar mai bacci saboda bata son ya sake yi mata magana don ya gama bata haushi; tun kafin ma yayi auren har ya fara sauraron yarinyar da zai aura tana tsara masa yanda za ayi, yarinyar ma da yace bazawara ce ba budurwa ba.

Ita bata son ya raba musu gida; in dai har dole sai ya kara aure to ta fi so ya ajiye su gida daya da duk matar da zai aura. Gani takeyi kamar idan aka raba gida cutarta za a dinga yi, a kaiwa amarya abinda ba a kawo mata ba. Ta fi so su zauna tare ta dinga kula da motsin mijinta. Duk da ta san auren ba zai yiwu ba kamar yanda Mallam ya gaya mata, amma dole ta shirya don idan auren ya yiwu gaskiya dole ya hadesu don bazata sallamawa wata bazawara miji ba.
Haka har bacci ya kwasheta.
…….

Yau saura sati biyu daurin auren Aisha da Yusuf, tuni ake ta shirin biki ana sayayya a gidan su Aishan. Sai dai a yawancin lokuta bata bada hadin kai, don haka Zainab, Zuwaira da Hajiya sune suke ta shirinsu. Ta dai zabi gado mai matukar kyau da yake Baffa ne ya turo hotunan yace ta zaba, amma daga wannan duk abinda aka tambayeta sai dai kawai tace ayi; ta dauki ATM card dinta ta bawa Zainab ta gaya mata password saboda sayayyar.


Haka su Zainab suka gama sayayyar gidan amarya ba tare da amarya ba.

Yau ma Yaya Zainab ce da Zuwaira suka tafi kasuwa domin sayo carpets, babu yanda basuyi ba su tafi da ita amma taki. Tace sune suka siyo labule don haka su siyo carpets din da yayi matching. Don haka suka tafi suka barta a gida inda daga baya Zahida ta zo suka hadu sukayi zamansu.

A zaune suke a dakin Aisha, ita Aishan tana kashingide a kan gadonta yayinda Zahida take zaune a gefen gadon suna hira. Ta dubi Aishan wadda take ta faman danna waya tace

‘Yaya Aisha sai ana maganar aurenki sai kiyi ta basarwa, wai ko bakya son mutumin nan ne.’

Ta dire wayar a kan ruwan cikinta tana 'yar dariya tace

‘To wa ma ya sani ne? Amma fa he’s ok sosai ma, duk wani quality na miji yana da shi. Gashi ba sai na gaya miki ba ke kanki kin san yana so na. Kawai dai ina jin Mustafa ya tafi da rabin zuciyata shi ya sa nake ji kamar na bar muku garin wallahi.’

Ta harareta tace

‘Umm! To in sha Allah sai mun kai ki, komai zai tafi daidai. Allah ya ji kan Abban Abdallah amma babu yanda bawa zai yi da ikon Allah duk yanda kika ga Allah yayi da bawa daidai ne.’

‘Hakane.’

Haka suka cigaba da hirarrakinsu Zahida tana cigaba da kwantarwa Aisha hankali game da auren tunda duk wanda ya sansu da Yusuf ya san yana sonta kuma itama tana sonshi sai dai kawai gaddama irin ta Aishan.

Sai can wajen shabiyu da rabi tayi musu sallama don zata dauko yaranta Nur da Hafsa a makaranta sannan su wuce gida.


UWAR SADDIKU


Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)


7

Saura kwana goma auren Aisha da Yusuf aka buga kati, da kansa ya kawo mata katin hade da na wuni wanda zatayi a nan gidan Umma sanna yaje ya kaiwa Baffa nasa kuma ya kaiwa Yaya Abubakar ma.

Bai san yanda Zahra zata dauki maganar ba don ya ce mata da sauran lokaci, kuma yayi sa’a Yaya Bello ya bashi hadin kai ko daya zancen bai fito ba. Tun saura sati uku bikin ya kama hayar wani karamin gida wanda gida daya ne tsakanin sa da gidansa da Zahra take, bashi ya kama gidan da kansa ba abokinsa Jafar ne ya kama shi yasa ma ko masu gidan basu san wa aka bawa ba. Da fari ma so yayi ya saya sai suka ki sayarwa sukace na marayu ne haya zasu bayar, don haka aka gama magana Jafar ya biya kudin haya na shekara biyu. Nan da nan aka shiga aikin gayara; ko da wasa bai je gidan ba, Jafar ne a kan komai don amininsa ne tun na yarinta.

Yau da wuri ya taso daga office, yana tuki yana tunanin yanda zasu kwashe da Zahra idan taga katin nan. Baya jin zata bashi matsala tunda wancan karon ma bata bashi matsala ba duk da ta san yana neman aure tunda suka hadu da yarinyar, har aka saka rana bata yi masa wata fitna ba. Abinda bai gane ba har yanzu shine dalilin da yasa ya fasa auren waccan yarinyar.

Har ya karaso gidan yana wannan tunanin da bai samo amsar ba, me gadi ya bude masa gate ya shigar da motarsa ya ajiye a gareji sannan ya shiga gidan. Ita da yaran duka suna zaune a falon kasa suna kallon TV, suka tashi gaba daya kowa yayi masa sannu da zuwa bayan ya amsa ya haye dakinsa dake sama.


Sai da ta dauko ruwa daga kicin sannan tabi bayansa, bayan tayi masa sannu da zuwa ta nemi waje ta zauna.

Ya saba zuwa gidan da envelop don haka ma bata damu ba da taga ya shigo da envelop, kafin ta shigo dakin ya boye envelope din don haka da bata gani ba sai ta cigaba da harkarta.

Saida yaci abinci ya huta, yana kashingide a falonsa na sama yana kallon tashar BBC ita kuma tana zauna a gefensa suna hira ya mike yana fadin

‘Ina zuwa.’

Kafin ta amsa ya shige daki, jimawa kadan ya fito rike da katin daurin aure kamar guda goma a hannunsa. Ya dawo inda ya tashi ya zauna ya jingina da doguwar kujera, ya ajiye katin a gefensa ya dubeta yace

‘Dama so nake na cemiki kanwar taki fa nan da kwana tara za a daura auren.’

Dauke wuta tayi saboda yanda taji kamar ya buga mata guduma a ka, ta yi kokari ta rike nutsuwarta tana yake

‘Wace kanwar tawa kenan?’

‘Ah, ba nace miki zan kara aure ba? To ita nake nufi.’

Ta danyi gyaran murya da mamaki a fuskarta

‘Ikon Allah! Kace zai kai wata shida ko ma fiye?’

Ya dan diririce saboda bai sa ran zata tambaya ba kuma da yanda yaga kamar ta dan shiga damuwa

‘Eh, daman babanta ne zai yi tafiya saboda bashi da lafiya zasu je Egypt ayi masa aiki, shine yace idan na shirya sunaso a daura auren kafin ya tafi.’

Ta kau da kai

‘Um, Allah Sarki! Allah ya bashi lafiya.’

Sukayi shiru na dan lokaci kowa da abinda yake tunani, ya dauko katunan gayyatar da ya ajiye ya mika mata

‘Ga wannan saboda mutanen gidanku, Yaya Muhammad ma dazu na kai masa office.’

Ta karba jiki a sanyaye, ta kalli sunan da kwanan watan ta yi lissafi nan da nan ta gano saura ma kwana taran kamar yanda ya fada. Ta bude baki da kyar ta ce

‘Allah ya sanya alkhairi.’

Ya washe baki yana wani murmushi da yake kara bata haushi

‘Amin ya Allah Uwargida sarautar mata.’

Ta hadiye malolon da ya tokare mata makogoro saboda takaici; wato har ya mayar da sunanta Uwargida ma kenan?

‘To kuma tarewa zatayi ko har sai Baban nata ya dawo zata tare?’

‘A’a, ranar da aka daura zata tare, ai wannan gidan na jikin gidan Bashir na kama hayarsa ina jin ma har an gama gyarawa idan dai ba Jafar yayi min shiririta ba kin san shi na dora a kan neman gidan.’

Wani abu ya tokare mata zuciya a dai dai lokacin da duk wata dama da take da ita ta kwace mata.
A da har ta fara tunanin suna da lokaci Malam ya gama aikinsa ta yanda ko an daura bazata tare ba amma yanzu da yace mata a ranar zata tare tana jin kamar za a sami matsala saboda jiya Malam yace mata akwai aikin da za ayi amma wanda zai yi aikin ya tafi umra sai sati mai zuwa zai dawo sannan ayi aikin.

Da sauri zuciyarta take harbawa; ya za ayi ta iya zama da kishiya bayan itace matar Yusuf ta rufin asiri, sai yanzu da yayi kudi yake jin zai auro wata. Gaskiya sai inda karfinta ya kare, gobe zata kirawo Malam idan babu hali ma zata nemi wani malamin. Ba za a zo gidanta a mayar da ita kalar kwatance ba.

‘Baki ce komai ba?’

Muryar Abban Sadik ta katse mata tunani yana ta wannan murmushin nasa da take ganin kamar da gayya yake yi.

Ta yi yake

‘To me zan ce? Wannan shirin aure da ba a saka da ni ba ai dole na koma cikin ‘yan kallo.’

Ya kalleta na dan lokaci

‘Ya zaki ce haka, ai na miki bayani ni kaina ba wai haka na shirya ba.’

‘Um, to ai nima ban ce komai ba. Allah ya bamu zaman lafiya.’

Ya kara fadada murmushinsa

‘Ko ke fa, ai ba wani abu bane.’

Sukayi shiru na dan lokaci, jimawa kadan yace

‘Ban sami lokaci na siyo miki kayan fadar kanwa ba amma da safe zan tura miki kudi naira dubu dari biyu sai ki sayi duk kayan da kike so da kuma sauran shirye-shiryenki.’

So take tace bata so amma ba zata iya ba domin ta san idan ta barsa to zai je ya karawa amaryar, don haka tace

‘Nagode, Allah ya kara budi.’

Sukayi shiru suka cigaba da kallon TV din da take gabansu, kowa da tunanin da yake ransa.


Jimawa kadan ta mike tana fadin

‘Bari naje na kwanta, bacci nake ji.’

‘To sai na shigo.’

Ta wuce ta nufi dakinta wanda yake kusa da nashi dakin, yayinda shi kuma ya bi bayanta da kallo yana mamakin abinda ya bata mata rai bayan wancan karon da zai yi aure bata nuna haka ba. Ya dubi katin gayyatar da ya bata yanda ta barsu a nan,ya kawar da kai. Allah yasa dai kada ta tayar masa da wata fitna kuma.

Ita kuwa Zahra tana shiga dakin ta turo kofa ta tsaya a bayan kofar, ta saki hawayen da take makalewa ya gangaro kan kumatunta.

Wato dai ta tabbata Yusuf aure zai yi, lallai namiji kanin ajali! Menene bata yi masa?


Ta tuno rayuwarsu lokacin yana malamin makarantar firamare; albashinsa baya isarsu, haka take hakura da abubuwa da yawa sannan kuma ‘yan uwanta suna yawan taimaka mata. Ko da ya sami sauyin aiki ya fara samun cigaba bata taba tsammanin zai yi mata kishiya ba, ta samu ta barar da wancan yanzu kuma ya dauko wannan; kuma harda munafurci don ta tabbatar zancen da ya gaya mata na dalilin da yasa aka matso da ranar auren kusa karya ne.

Tayi kwafa, ta bar bayan kofar ta wuce bandakin ta turo kofar, ta karasa gaban mudubin sink ta tsaya ta dafa sink din tana kallon fuskarta a mudubi.


Babu abinda take gani sai hawayen da ta kasa daina fitar dasu; idan ta tuna yiwuwar Yusuf dinta zai kwana da wata matar har wani daci take ji a bakinta.

Haka ta dauki lokaci tana hawaye tana kallon mudubin ba tare da ta san me take tunani ba, saida ta fara gajiya da tsaiwa sannan ta kunna fanfon sink din ta wanke fuskarta. Tana fitowa daga bandakin ta sami waje a gefen gado ta zauna ta cigaba da tunanin mafita.

Sai wajen sha daya da rabi na dare Abban Sadik ya gama abinda yake, har zai kwanta sai kuma ya fasa. Ya fito daga dakinsa ya nufo dakin Zahra; don bata saba barinsa ya kwana shi kadai ba ko da kuwa tana jego ko rashin lafiya. Duk da ya san yau din ya dan motsa kishinta amma dai gara ya lallabota su shirya.


A hankali ya tura kofar dakin ya shiga; tana kwance a gefen gadon a takure da kayan da ta wuni da su gashi ko fitila bata kashe ba. Ya kalleta yayi murmushi don ya san tabbas bacci ne ya kwasheta.

Ya karasa ya zauna a gefen gadon ya tabata a hankali, ta mutssike ido ta bishi da kallo sannan ta tashi zaune a hankali.
Bayan ta zauna yace

‘Bacci ya kwasheki baki ko canza kaya ba? Ko a nan zamu kwana ne?’

‘Um, ban ma san nayi bacci ba wallahi. Bari dai yanzu zan shirya na taho gara dai mu kwana a can din.’

Ya mike yana fadin

‘To ina jiranki.’

Ya fice ya barta a dakin inda ta shirya ta bishi daga baya.
……

Kwanciya kawai Zahra tayi amma duk yanda ta so tai bacci kasa daukanta yayi, sai bayan asuba sannan ta samu baccin ya kwasheta. Inda Allah ya taimaka mata ranar asabar ce yara babu makaranta don haka shima Abban Sadik da yaga tana bacci sai kawai ya fito daga dakin ya rufe mata kofa, ya zauna a falonsa yana karance-karancensa.

Sai wajen karfe goma sannan ta farka, nan da nan ta wanke fuska ta sako kaya ta fito falo. Ta kalleshi tayi yake sannan tace

‘Sorry Yallabai, na barka da shan shayi ba bread. Wallahi bacci ne ya kwasheni kuma ka ki tashi na.’

Yayi dariya

‘Na ji kinata minshari ne, nace bari na barki ki kai ragon.’

Ta harareshi sanna ta bashi amsa

‘Bari nayi sauri na hada mana breakfast, 'yan gidan ma na san sun tashi don ga muryarsu can a kasa.’

Ta wuce da hanzari ta nufo falon kasa.

Kafin ta karasa saukowa Ummi ta sheko da gudu ta rungumeta tana mita

‘Mommy, tun dazu nake nemanki Yaya Yusra ta hanani zuwa dakin Abba na kirawoki, muna tashi ta sauko da mu kasa ta hanamu komawa kuma ta hada mana shayi ba dadi. Ai zaki bani wani shayin ko?’

Ta riko hannunta suka karasa saukowa ta zauna a kan kujerar zaman mutum uku kusa da Rukayya da Khadija wadanda suke zaune suna kallon cartoon, ta dorata a cinyarta tana murmushi tana bata amsa

‘Uwata ta kaina, Yaya Yusra bata kyauta ba bari mu ci abinci sai nayi mata fada.’

Daya bayan daya yaran suka gaida Mommy, bayan ta amsa ta dubi Yusra tace

‘Ina Yayanki?’

‘Bai fito ba Mommy, kin san shi da baccin tsiya.’

‘Bari nayi sauri na dafa mana indomie, yau bacci ya daukeni duk an ji yunwa har an bawa Uwata shayi mara dadi.’

Yusra tayi dariya tace

‘Mommy kin san fa tsohuwar yarinyar nan ba a iya mata.’

Ta harareta

‘Nagode kin ji Yaya.’

Suka saka dariya gaba daya, ta mike ta nufi kicin Ummi tana biye da ita.


Nan da nan ta dafa musu indomie da kwai, ta jera a dining table sannan ta hau saman ta kirawo Abban Sadiku wanda suka sauko tare. Kafin ta sauko duk yaran sun zauna a table sai Sadiku wanda bai fito ba har wannan lokacin, ta wuce dakinsa ta tura kofar. Ta sameshi yana kwance rub da ciki a kan gadonsa daga shi sai gajeran wando, motsinta ya tasheshi ya juyo yana dubanta yana mutssike ido.

Ta harare shi tace

‘To sarkin lalaci, a tashi gari ya waye.’

‘Mommy na tashi fa.’

‘Da kaji shigowata ba, to ka fito ga abinci can indomie na dafa, idan ka bari tayi sanyi ba zaka dafa wata ba haka zaka ci.’

Ta juya ta fice ta wuce ta zubawa kowa abincinsa sannan itama ta zuba nata ta zauna suka fara ci; yara suna ta hira da Abbansu ita kuma tayu shiru kawai tana cin abincin. Hankalinta yana kan maganar aurensa, ta kasa nutsuwa.

Kafin su gama cinye abincin ita ta cinye nata tunda dama kadan ta zuba, ta mike ta dauki kwanonta ta shigar kicin ta ajiye. Tana fitowa ta wuce sama ta koma dakinta ta turo kofa ta cigaba da tunanin mafita.

Saida suka kusa gama cin abincin Sadik ya fito daga dakinsa, bayan ya gaida Abban ya zauna ya ja kwanonsa wanda Mommy ta riga ta zuba masa abinci. Haka ya hakura ya ci indomie wadda ta riga tayi sanyi saboda Abba yana zaune, da ya san Abban bai koma sama ba jira zaiyi sai ya tashi sannan ya fito ya dafa mai dumi; don ya san Mommy ba zata iya hanashi ba fada kawai takeyi.

Bayan sun gama karyawa nan suka zauna a falon kasa suna kallonsu, jimawa kadan wajen Sha biyu saura Jummai mai aikin Mommy tazo. Bayan sun gaisa da yaran ta kama aikinta, Yusra ta haye sama don ta sanar da Mommy zuwanta.

A hankali ta tura kofar ta shiga da sallama, tana daga kwance a gefen gado ta amsa sallamarta. Ta turo kofar ta karasa ta zauna a gefen gado kusa da kafar Mommy yayinda ita kuma ta fara kokarin mikewa zaune.
‘Mommy Jummai ta zo, ta ma fara aikinta.’

‘To.’

Ta amsa a gajiye kamar wadda batayi bacci ba
Yusra ta sake binta da kallo; har yanzu kayan bacci ne a jikinta wanda tabbas ba dabi’arta bane. Da kalau take da yanzu tayi wanka ta canza kaya tana tashin kamshi, tabbas ko dai bata lafiya ko kuma ciki ne da ita. Mommy ce ta katse shirun tana kallon Yusra

‘Lafiya dai kike kare min kallo kamar yau kika fara ganina Yaya?’

Ta kawar da kai tana murmushi

‘Mommy baki da lafiya ne?’

‘Lafiyata kalau Yusra, me kika gani?’

‘Kawai dai na ga kamar ba kya jin dadi.’

‘Babu komai.’

Sukayi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login