Showing 42001 words to 45000 words out of 166068 words

Chapter 15 - UWAR SADIKU COMPLT BY SAKINA YAZID.txt

11 Jul 2024

25389

na zuba maka. Amma idan kana so lallai ya sha zaka iya kiransa ka bashi, ni dai ba zan sha ba tunda na gaya maka bana bukata. Me zan zuba maka a zobon? Shekaru goma sha kana shan zobona ban taba zuba maka komai ba sai yanzu? Saboda dai ni babu abinda zanyi na burgeka. Ai shikenan!’

Ta tura kujerar ta mike ta bar masa waje ta nufi dakinta, ya bi bayanta da kallo yana mamaki.


Dama ya san haka zatayi domin hakan ne dabi’arta a duk lokacin da bata da gaskiya, ya karasa cin abincinsa ya tashi ya shige dakinsa.

Ya saba bata hakuri idan sukayi irin haka sai dai yau ya ci alwashin ba zai bata hakuri ba don shima ta bashi haushi da mamaki. Bayan sallar isha’i ya gama shirinsa ya sameta a daki yayi mata sallama ya nufi wajen Aisha.


UWAR SADDIKU


Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)


16

Tun daga lokacin da Aisha ta kama Yusra tana zuba mata sabulu a abinci sai kuma ta samu saukin fitnar Zahra, sai dai ita Aishan ta kasa sakewa da yaran gaba daya har Rukayya. Ko da Rukayyan ta zo tayata kwana sai tayi ta kula da ita tana kula da motsinta musamman a kitchen.

Tun wannan lokacin kuma sai fitnar Zahra tayiwa Aishan sauki, duk da bata fasa aniyar raba Aisha da Yusuf ba ta dai bari ne kawai tana jira ta tara kudin da zata iya bawa Malam Hatimu yayi mata aiki. Sannan kuma tunda Hajja ta bata maganin nan ta boye a bayan wardrobe ta sami natsuwa tunda duk abinda take so yayi mata yana yi, sannan kuma ko fada zai mata a kan wani abu da zarar ta bata rai sai ya fasa.
-------

Kwanci tashi har shekara ta zagayo an fara lissafin azumi, tunda aka ce azumi saura sati hudu Abban Sadik ya fara maganar kayan Sallah.


Saida ya gama magana da Zahra tayi masa total gaba daya har na Aisha, ya tabbatar mata da anyi albashi zai saka mata kudin.

Yana zaune a falon Aisha ta tada kai da cinyarsa suna hira, ya mika hannu ya dauki wayarsa yace

‘Au, bari na turawa yayarki kudin kayan sallarku don na huta, sai kuma a shiga hidimar azumi.’

Ta dauke idonta daga kallon TV din da take kallo tace

‘Wai Mommy?’

‘Eh, kin san sallar ta matso.’

Ta tashi zaune ta sashi a gaba

‘Don Allah ni dai kada ka tura da nawa, ka turo min kudin zamu saya tare da su Zahida kaga waccan babbar sallar ma haka sukayi anko babu ni.’

Yayi ‘yar dariya

‘Yanzu ku kayan sallar ma sai kunyi anko? Mata masu gari. To gaya min lambar sai na tura miki naki ita sai na tura mata nata da yara.’

Tana gaya masa kuwa nan take ya tura mata dubu dari kudin kayan sallarta, sannan ya tura wa Mommy nata da na yaranta.

Bayan ya je gidan ne take tambayarsa taga kudi amma basu cika ba; yayi mata bayani cewa Aisha ta karbi nata zasu saya da ‘yan uwanta. Babu yanda ta iya haka ta hakura da shirin tsiyar da tayiwa Aisha domin duk mitar ta yace mata shi ya riga ya gama wannan maganar.
……..

Cikin azumi ya sanar da Mommy yana shirin zai je aikin Hajji kuma da ita zai je, a take ta fara murna. Tayi masa godiya sosai sannan tace

‘Amma wallahi da ma Umrar azumi ka biya min, ka ga zuwana Hajji biyu fa zan so zuwa Umra, musamman ta azumi. Kuma ka ga ma yanzu Sumayya bata isa yayeba.’

Ya danyi tunani yace

‘Hakane, to babu damuwa. Sai muje Hajin da Yaya Bello in ya so kafin karshen shekarar sai na biya miki Umrar ko ba zan je ba sai kuje da Sadiku. Ita kuma kanwarki badi sai muje Hajin da ita.’

Nan take ta sake cika da murna tunda taji yace zai biya mata suje ita da Sadik, tana ganin kamar ma idan ta saka shi a gaba da naci ya hada harda Yusra in ya so su tafi ita da yaranta. In ya so Hajin da yace zai je da Aisha kuma ta san yanda tayi a ka bar zancen don tana ji a jikinta kafin shekara war haka ma ta samu an yi mata aikin nan an kada mata Aishan.
……..

Saura kamar sati hudu tafiyar alhazai Aisha ta fara laulayi, amai da jiri babu sassauci. Suna zuwa asibiti aka tabbatar ciki ne da ita sati hudu, aka rubuta mata magunguna aka sallamesu.

Tun a hanya yake tsokanarta domin da ya fidda rai da yaga aurensu har ya haura shekara ko batan wata bata taba yi ba. Yana kaunar Aisha sosai don haka yake so ta haifa masa yara ko guda biyu ne, sannan ne zai tabbatar jininsa da tsokarsa ta gaurayu da ta Aisha.

Don haka suka dawo gida suka cigaba da rainon cikinsu; duk da bayan ta fara shan magungunan da aka bata laulayin yayi mata sauki tunda tana zuwa aiki kuma tana harkokinta sosai.

Sati biyu da zuwansu asibiti ya kama ranar da jirgin su Abba zai tashi.

Tsaf Abba ya gama shirinsa yayinda Malam Sule da Yaya Bello suke jiransa a mota, ya sa Rukayya a gaba ta hada kayanta, ya kaita gidan Aisha yace ta zauna a nan har sai ya dawo daga Saudiya sai ta koma wajen Mommy. Ya sanar da Mommy din kuma ta dinga duba masa Aisha don tana dauke da juna biyu. Yayi mata sallama ya fice suka kama hanya.
Yana fita ta mike ta fara zarya a falon, wato don ma raini ita yake gayawa yayiwa amaryarsa ciki ta kular masa kafin ya dawo? Tayi kwafa, in sha Allah wannan cikin sai ya bare kafin ya dawo.

A take ta dauki wayarta, har ta lalubo lambar Hajja zata kirawo sai kuma ta fasa, ta kirawo Malam Hatimu mai almajirai.


Bayan ta sanar da shi cewa wancan aikin fa tana nan tana hada kudinsa sannan ta dora da bayani

‘Malam yanzu ciki ne da ita amma gaskiya ina so ne a lalata cikin, kwata-kwata bana so ta haihu na fi so yanda ta shigo ita kadai ta fita ita kadai kawai.’

Yayi ‘yar dariya

‘Wannan karamin aiki ne, yara ma zasu iya yinsa. Akwai laya da za ayi aiki a ciki a baki ki samu ta tsuguna a kan layar nan, idan dai ta tsuguna to kafin awa daya cikin ya rabu da jikinta.’

‘To Malam yanda za ayi ta tsuguna din shine matsalar don ka ga ma ba gidan mu daya ba.’

‘Kada ki damu, ko yara ki bawa su jefa mata a masai. Na san masanku na tangaran ne layar kuma mai sulbi ce ana jefawa ko ba a kora ba zata wuce, idan dai ta tsuguna a kan wannan masan cikin nan sai ya fita daga jikinta.’

Tayi murmushin farin ciki, yayi mata bayanin kudi Naira dubu goma sha biyar. Nan take tana ajiye waya ta tura masa kudin da alkawarin washegari zai taso yaro ya kawo mata har gida ita kuma zata sallami yaron.

Cikin walwala ta karasa wunin ranar domin dama babban abinda yake firgita ta shine Aisha ta tarawa Yusuf wasu yaran. Ta ci alwashin ko sau nawa yarinyar nan zatayi ciki sai ta barar da shi muddin Malam Hatimu yana raye.
---------

Tunda Abban ya kaimata Rukayya Rukayyan take ta magiya don Allah suyi cake tunda gobe da akwai makaranta kuma yanzu ta dawo na ta huta da dafa abincin makaranta.


Haka Aisha ta tashi ta hada kayan cake, da yake ta koyawa Rukayyan ma kusan duk ita tayi aikin da yake ba Mai yawa bane. Ta gama ta zuba cake din a oven tanayi tana wanke wanke, kafin magriba ta gama.

Ana idar da sallar magriba ta sa Rukayyan ta dafa musu indomie da kwai suka juye a tray suna ci suna hira. Sun kusan cinyewa aka buga kofa, Aisha ta tsame hannunta tana fadin

‘Cinye ragowar bari naje na duba kofa.’

Saida ta zo daf da gate din tace

‘Waye.’

Cikin isa aka amsa mata

‘Mune.’

Ko bata ga mai maganar ba ta san Yusra ce don haka ta bude kofar tana Lahaula a zuciyarta saboda sharrin yaran ya fara bata tsoro.

Tana budewa suka shigo ita da Sadik, ya dubeta shekeke yace

‘Ina Rukayya, Mommy tana kiranta.’

Ta juya tana fadin

‘Ku shigo tana ciki.’

Suka biyo bayanta.

Suna shigowa falon Rukayya ta mike tsaye da kwanon abincin nasu a hannunta zata kai kicin tana tande baki saboda indomie din da yaji. Suna karasawa ciki Sadik yace

‘Kizo in ji Mommy.’

Ta kalleshi da mamaki

‘Yanzu?’

Yusra ta balla mata harara tace

‘A’a gobe?’

Aisha ta karasa tana fadin

‘Ce miki akayi fa Mommy na kiranki kike tambaya Rukayya, kai kwanon kicin ki sha ruwa ki zo kuje in ya so kya dawo.’

Ta wuce kicin din ta ajiye kwanon ta fito, ta dauki hijabinta wanda tayi sallar magriba da shi a falon ta saka tace

‘Sai na dawo Anti.’

Suka tasa ta a gaba kamar wata mai laifi suka wuce.

Ta riga ta san wannan kiran ba na Allah bane don haka ta mayar da kofarta ta rufe don ta san ba za a bar Rukayya ta dawo ba.

Haka kuwa akayi, tana shiga gidan Mommy tace an gama kwanan ba zata sake taya wannan matar kwana ba. Tayi maganar kayanta aka ce yayyenta zasu kwaso mata gobe amma ita kam ma idan aka sake ganinta a kofar gidan sai an karya kafarta. Haka ta kwana tana matse kwalla saboda takaici; ga cake dinta a gidan wanda ta san bata isa tayi maganarsa ba don ko an karbo ba za a bari ta ci ba.
……….

Haka da gari ya waye Aisha ta tashi ta gama shirin zuwa aiki, a al’ada bakwai da kwata Malam Sule yake buga mata kofa su tafi, idan ya jiyeta sai ya wuce da yaran tunda makarantar da take koyarwa ta fi kusa.
A shirye ta zauna a kan kujerar dining table tana jiransu, da taga da dan sauran lokaci ta kirawo Yaya Zainab a waya ta sanar da ita zata zo in an tashesu daga makaranta ta dauki Amira;’yar wajen Zainab din ce wadda shekarunta sun kai sha uku. Ta sanar da ita Abba ya tafi Hajji kuma Zahra ta hana ‘yar tayin kwanan tata, in ya so daga nan sai ta dinga kaita makaranta da safe suna dawowa tare tunda saura sati biyu a bayar da hutun Sallah kuma tana sa rai kafin a koma Abban ya dawo.

Suka gama waya ta ajiye ta cigaba da kallon agogo. Har karfe bakwai da rabi ta gota bata ji bugun Malam Sule ba, don haka ta kirawoshi a waya. Kafin ma tace wani abu ya fara magana cikin girmamawa

‘Afuwan Hajiya, wallahi Hajiya Babbace tace yara suna makara don haka na wuce na kaisu idan na ajiyesu na dawo na daukeki. Kin ganmu a hanya dana kaisu yanzu zan juyo in Sha Allah Hajiya ayi hakuri da ni.’

Tace

‘Babu komai Malam Sule, ba ma sai ka dawo ba yanzu zan wuce babu komai.’

Kafin yace wani abu ta ajiye wayar tana murmushin takaici; batayi mamakin hakan ba domin idan wannan munafukar matar ce mai fuska biyu abinda yafi haka ma zata iya yi tunda wanda take kunya baya nan. Haka ta mike ta fita ta hau motar haya ta kama hanyar makaranta.
Tana tashi daga makarantar kuwa ta wuce gidan Yaya Zainab, can ta wuni sai bayan la’asar suka taho tare da Amira.
……….

Tun kafin sallar azahar dan aiken
Malam Hatimu ya iso, babu kowa a gidan daga ita sai Jummai. Maigadi ne ya shiga ya sanar da su akwai yaro da yace an aiko shi wajen Hajiya.


Nan da nan ta sa aka shigo da shi bakin kofar falo, ko gaisawa basuyi ba ta karbi sakon wanda yake a nannade a bakar leda ta bashi naira dubu uku tace ya hau mota.


Yayi godiya ya tafi.

Tun lokacin take tunanin yanda za ayi ta aika Yusra ta jefa wannan abun a toilet. Tun lokacin da ta fasa mata murfin tukunya Yusran ta daina shiga gidan, gashi jiya batayi tunani ba ta aika suka taho da Rukayya. Da ta sani ma da ta bari in ya so yau din sai su yi amfani da wannan damar a jefa maganin kuma a taho da Rukayya. Rukayyan ta riga ta bawa Mommy tabbacin a dakin baki suke kwana don haka a nan ne take so a jefe layar tunda ta san shiga dakin Aishan zai yi wahala. Amma in dai tana kwana a dakin bakin to tabbas ko cikin dare sai ta shiga bandakin.

Suna zaune a falo suna kallon TV bayan magriba Rukayya ta dubi Mommy cikin sanyin murya tace

‘Mommy, kayana fa suna gidan Anti kuma harda books dina ina son naje na dauko don gobe da su zanje school.’

Bude baki tayi zata yi mata tsawa sai kuma ta tuna dama tana neman damar da zata yi aike gidan, ta dubeta tace

‘To, bari Yayarki ta rakaki ku dauko.’

Ta mike tana fadin

‘Ina zuwa.’

Sai da ta hau sama sannan ta kwalawa Yusra kira, tana zuwa ta jata daki.

Layar ta bata a hannunta tayi mata bayani yanda zata yi mata da ita, bayan ta gama bayanin tace

‘Ki kula fa kada wanda ya gani, idan ta wuce ko bakiyi flushing ba babu matsala amma idan kinga bata wuce ba to ki kora.’

Ta amsa

‘To.’

Har ta juyo zata fito ta juya tace

‘Mommy layar ta mecece?’

Ta harareta tace

‘Ina ruwanki? Kiyi abinda aka saka ki kawai.’

Ta juya ta fice ba tare da tace komai ba.

Falon kasa ta dawo ta zauna bayan ta nade layar a siket dinta, ta cigaba da harkarta kamar yanda Mommy din ta tsara mata. Jimawa kadan Mommy din ta sauko, tana zama ta dubesu tace

‘Kuje ku debo kayan Rukayyan, maza kada ku bata lokaci.’

Ta harari Rukayyan tace

‘Saura ki zauna wani shisshigin.’

Suka tashi suka fice.
………
Suna zaune ita da Amira a falo suka ji bugu, ta tashi ta bude kofar. Kamar yanda Yusra ta saba ko gaisheta bata yi ba ta sa kai cikin gidan, Rukayya ce ta gaisheta sannan a kunyace tace

‘Kayana Mommy tace mu debo.’

Ta dafa kafadarta tace

‘To muje ku diba, suna nan a inda kika barsu.’
Suna shiga falon Aishan ta zauna a kan kujera tace

‘Kuje ku debo.’

Suka nufi dakin baki inda nan ne kayan Rukayyan suke.

Suna shigewa Aisha ta dubi Amira tace

‘Bisu Amira, ki sa min ido musamman a kan Babbar.’

Nan take ta tashi ta wuce, Rukayya na tsaye a gaban wardrobe tana fito da kayanta wadanda dama ba yawa ne da su ba yayinda Amira take jingine a jikin mudubi wanda yake kusa da kofar bandaki. Amira tana shiga ta wuce ta zauna a gefen gado, ta kula da yanda Yusra take mata kallon raini don haka itama ta tsare gida.

Bayan ta gama fito da kayan daga wardrobe din ta dauki jakarta ta makaranta ta bude kamar tana neman wani abu. Ta dubi Yusra tace

‘Yaya Yusra dan zuba min kayan a ledar gata nan kusa dake, bari na tambayi Anti books din da nayi homework naga bata sa min a nan ba.’
Kafin Yusran ta amsa ta fice tana dauke da jakar.
Tana fita Yusran taja tsaki

‘Ki kwashi kaya kawai sai kin bata mana lokaci.’

Ta dubi Amira tana kokarin bude bandaki tace

‘Bari nayi fitsari.’

Tayi wuf da shige bandakin ta turo kofar, tana shiga ta jefa layar a toilet tayi maza ta kora. Ta tsaya a gaban sink ta wanke hannunta ta danyi jinkiri sannan ta fito.
A dai-dai lokacin Rukayyan ta shigo tana rufe jakarta wadda cake dinta ne taje ta juyo tana fatan Mommy ba zata gani ba in ya so gobe in taje makaranta sai su cinye ita da kawayenta.


Tana shigowa suka karasa hada kayan suka kwasa suka fice.

Suna fitowa falo Rukayyan ta yiwa Aisha sai da safe, har sun kusan fita daga falon Aisha tace

‘Rukayya idan kin je ki kunno min ruwa idan tankin ya cika zan bugo waya sai a kashe.’

Ta amsa suka fice.

Gida daya ne tsakanin gidan Zahra da na Aisha don haka bai sake hada ruwa ba a gidan Aisha. Sai dai kawai aka hada tankin gidan Aisha da injin jan ruwa a can gidan. Kafin ya tafi Hajji kullum da suba yake kunna ruwan tankunan su cika ya kashe daga can ko kuma da daddare idan ba a can ya kwana ba. Tun ana i gobe zai tafi ya manta bai kunna ba, ranar dazai tafi ma haka ya sake mantawa har ya tafi. Ya gayawa Sadik ya dinga kunnawa kullum, sai dai yana tafiya Sadik din ya murder wata waya ta yanda in ya kunna injin iya tankin gidansu kawai zai cika. Don haka ko da suka shiga gidan Rukayya ta kunna injin tankin gidansu ne kawai ya sake cika aka kashe.

-------

Sai wajen tara da rabi lokacin ma Amira ta fara gyangyadi a falon, suka wuce daki suka kwanta. Bayan sun shiga dakin saida ta duba ko ina ta daga katifa ta daga kafet don ta tabbatar Yusra bata binne mata wani abu ba sannan suka kwanta.

Can wajen Sha biyu da Rabi na dare fitsari ya matseta, tana tashi ta shiga bandakin da yake nan dakin tayi fitsarin ta dawo ta kwanta. Minti goma Sha biyar da kwanciyarta taji kamar ana karta wani abu a mararta, ta tashi zaune ta dafe mara ta takure a waje guda tana fitar da numfashi da kyar.

A firgice Amira ta farka, bata gani sosai saboda duhu haka ta lalubota ta tabata tana fadin

‘Anti baki da lafiya?’

Da kyar ta amsa.

Take Amira ta tashi ta lalubi fitila ta kunna, ta karaso kusa da Aishan da gudu ta dafata ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login