Showing 75001 words to 78000 words out of 166068 words

Chapter 26 - UWAR SADIKU COMPLT BY SAKINA YAZID.txt

11 Jul 2024

25401

zan ce masa.’

Suka karasa maganganunsu kowa ya wuce gidansa.
--------

Haka kawai yake jin kansa cikin walwala, duk da azumin yayi wahala kuma gashi da la’asar da ya shaki warin nan ya galabaita; amma yanzu har ji yake kamar ma ya rage nauyi ko kuma an dauke wani abu mai nauyi da aka dade da dora masa a ka.

Cikin walwala ya sha ruwansa tare da yara, su kansu yaran har suna mamaki. Domin Yusra ita a tunaninta ma murna yake saboda saura kwana biyar Mommy ta dawo.

Tunda ta tafi yau ne kadai ya sha ruwa a falon kasa. Rahma da Jummai sai daki suka wuce bayan sun ajiye musu abincin suka barsu shi da yaransa.

Ana gama shan ruwa Mommy ta kirawo wayarsa kamar yanda ta sabarwa kanta; yana dauka ya fara yi mata korafin da kusan kullum sai yayi mata shi amma bata fasa ba.

‘Madam. Yanzu fa a nan Saudiya tarawih akeyi kuma yau daren ashirin da bakwai ai ya kamata ace kin manta damu kina can kina ibada fa, kar a ga daren lailatul kadari kina waya.’

Tace

‘Toh idan na jiku ai shine zan fi samun natsuwar ibadar ko? Ina masallacin ma fitowa nayi, da na gaisa da yara zan koma.’

Suka gaisa yana mamakin dalilin da ya sa kullum sai ta kirawosu kuma a dai-dai wannan lokacin. Ita kuwa dalilinta shine a lokacin ne kawai zata samesu gaba daya a tare kuma sannan Yusra zata karbi wayar ta shige daki tayi ta yi mata tambayoyi.
Gaba daya yaran sai da ta gaisa da su sannan daga karshe Yusra ta karbi wayar ta haye sama ta shiga dakinsu sannan suka fara magana da mommy.

Bayan ta gama bawa Mommy labarin abubuwan da suka faru a gidan tace

‘Shima Abban yau na ga sai wani jin dadi yake ko don kin kusa dawowa ne oho.’

‘Allah? Me kika ga yayi.’

‘Wallahi Mommy sai wani jin dadi yake, kinganshi can ma fa a kasa ya sha ruwa sai hira yake da kowa.’

‘Um, yanzu haka dadi kawai yake ji. Idan kin ga wani abu dai mayi magana gobe.’

Sukayi sallama ta dawo ta bawa Abban wayarsa.

Tun da suka gama waya da Yusran kuma sai ta shiga wasi-wasin dalilin da ya sa Abban yake walwala. Bata alakanta hakan da dawowarta ba ta fi dai tunanin ko yanayinsa ne haka a ranar, ta dai san ko menene babu Aisha a ciki tunda Yusra ta tabbatar mata baya shiga gidan Aishan. Haka ta cigaba da ibada tana tunanin abinda ya sa shi walwalar, don ji take kamar tayi tsuntsuwa taje ta gani.
--------

Wajen karfe tara da kwata bayan an idar da sallar tarawih Abba ya riko hannun Liman suka fito daga masallaci, suka dan matsa daga cikin mutane. Bayan sun gaisa Abba yace

‘Malam kace za muyi magana.’

‘Kwarai kuwa Alhaji Yusuf.’

Suka dan kara gyara tsayuwa, Malam liman yace

‘Wato Alhaji Yusuf wannan abun gaskiya irin suddabarun nan ne, tana iya yiwuwa anyi ne don a rabaka da ita amaryar kuma tana iya yiwuwa ma mutanen da suka zauna a gidan kafin ka zo sune suka binne. Amma yanda mukayi masa haka aka konashi to ko ma wa aka yiwa ba zai sake tasiri ba in sha Allah.’

Da tsananin mamaki a fuskarsa yace

‘Ikon Allah! Wato Malam Liman biri yayi kama da mutum.’

‘Allah ko Alhaji?’

‘Kasan an dauki lokaci bana iya shiga gidan nan duk yanda zan yi, ikon Allah. To yanzu wa zai yi min haka? Kai!’

Liman ya dafa kafadar Abba yace

‘Ai ba za a iya cewa ga wanda yayi ba Alhaji, irin wannan abune wanda ake hadawa da shaidanu. Su kuma shaidanu ka san zantukansu duk karya ne. Kowa ma zai iya yi; ko a kawayen ita matar gidan idan akwai wadda take jin haushinta zata iya yi ko wani cikin manemanta wadanda ka kasa. Abun dai sai addu’a, ko a hakan ma za a iya cewa addu’a ce ta kawo dalilin da yasa aka tono abun yanzu haka da ba za a ganshi ba.’

Ya jijjiga kai

‘Hakane kam, Allah ya sauwake.’

Suka dan taba hira, daga baya Abban yayi masa sallama ya kama hanyar gida.

Yana tafe yana tunani kala-kala; wa zai yi masa wannan muguntar. Yanzu dama wannan wahalar da yake sha idan ya shiga gidan Aisha dama da hannun wani? To waye zai masa haka? Zahra? Kai ya za ayi Zahra tayi irin wannan aika-aikar? To idan ba ita ba waye zai yi haka? To ko dai a kawayen Zahran ne kamar yanda ya fada ko kuma ‘yanuwanta wadanda suke jin haushinta?

Har ya je gida bai samo amsar ba, yana kara tambayar kansa abun yana neman ya sa masa ciwon kai. Ya hakura ya bude gate ya shiga.

Babu kowa a falon kasan duk sun kwanta don haka kai tsaye ya haye sama.
A falo ya zauna ya jefa wayar a kan kujera kusa da shi.

Babu abinda yake so yanzu kamar yaje ya ga Aisha. Ya mike kamar wanda aka tsikara ya nufi dining table, ya bude kwanukan ya duba. Salad ne da kuma madarar waken suya a jug wanda Yusra ta ajiye masa. Ya zauna ya ci salad din ya sha madara sannan ya mike ya shiga daki, mintuna kadan ya fito a shirye ya kulle dakin.


Sai da ya sauko falon kasa sannan ya kirawo Rahama a waya, ta bude dakin baki wanda yake kasan ta fito.

‘Anti Rahma zan fita ne, a gidan Aisha zan kwana dauki mukulli ki kulle muku wannan kofar sai da safe zan dawo. Yaran suna bacci ban tashe su ba.’

‘To.’

Ta koma ta dauko mukullin ta fito, yana fita ta mayar da kofar ta rufe.

Karar bude kofarsa ya janyo hankalin Yusra wadda dama bata yi bacci ba.


Yana ficewa ta sauko falon lokacin Rahma ta gama kulle kofa ta juyo zata koma daki. Tace

‘Anti Rahma Abban fita yayi?’

‘Eh, haka yace gidan Antinku zai kwana.’

‘Um.’

Ta juya ta koma saman.
Itama Rahma ta shige dakin.
Tana sane da yanda tun zuwanta yake kwana a nan, amma a tunaninta kwana yake saboda yara; don haka ma yau din da yace mata can zai kwana bata yi mamaki ba don a hakan ma tana ganin yayi kokari.




UWAR SADDIKU


Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)


26

Tunda Rukayya ta zo suka hadu da Amira sai ta bar musu dakin baki, ita kuma ta koma tana kwana a dakinta ita kadai.

Tana kwance a kan gadonta Amma ba bacci takeyi ba, ta kashe fitilar dakin sai irin fitilar nan mara haske ta kan durowar ta bari a kunne. Karatun kur’ani ne yake tashi kasa-kasa a dakin wanda ta kunna a mp3 dinta take bi tana daga kwance. Kamar a mafarki ta jiyo motsin bude gate, da sauri ta tashi ta leka ta taga wadda take kallon gate din. Zuciyarta na dakan uku-uku saboda a tunaninta ko wani ne ya shigo musu gidan daga ita sai yara.

Sai da ya gama shigowa gaba daya sannan ta gane shi, ta dafe kirji ta mayar da numfashi. Ta san iyakarsa kofar falo ba iya shigowa zai yi ba, ta tabe baki ta koma ta kwanta ta cigaba da bin karatunta.

Ta baza kunnuwanta tana sauraro taji fitarsa sai kuma taji motsin bude kofar falo, yana kunna fitilar falon ta hango haske ta kasan kofar. Mamaki ya cikata, a fili tace

‘Toh!’

Duk da haka dai sa rai takeyi taji fitarsa, sai kuma taji ya shiga dakinsa wanda a jikin nata dakin yake. A ranta tace yanzu haka wani abune mai mahimmanci da ake bukata yanzu ya bari a dakin shine ya daure ya shigo ya dauka.

Ta gyara kwanciyarta ta cigaba da karatunta tana mamaki.
………..

Tun daga bakin gate yake mamaki yana godewa Allah saboda kwata-kwata babu wani wari, duk wani nauyi da yake ji a kirjinsa idan ya shigo gidan yau babu. Ya karewa farfajiyar gidan kallo duk da cewa akwai duhu sai fitila guda daya dake haska wajen. Ya wuce ya nufi cikin gida.

Yana shiga falon kamshin turarenta ya doki hancinsa, tabbas yayi kewar kamshin nan da kuma mai kamshin.


Kai tsaye dakinsa ya wuce domin a tunaninsa a nan zai sameta sai dai ga mamakinsa bata ciki. Ba tare da bata lokaci ba ya fito ya nufi dakinta, tun daga bakin kofa ya jiyo sauti don haka ya tabbatar tana ciki. Yayi zaton waya takeyi don haka ya murda hannun kofar ya shiga a hankali, sai da ya bude kofar sannan ya fahimci sautin karatun kur’ani yake jiyowa.


Ya hangota a kwance a kan gado; ji yayi kamar zuciyarsa zata fito daga kirjinsa ta riga jikinsa isa inda take kwance.

Kafin ya karasa ta tashi zaune, ta kunna fitilar wayarta don ta tabbatar shine.

Yayi zaton bacci takeyi, amma da yaga ta kunna fitilar wayar sai ya dan ja baya ya kunna fitilar dakin.

Ta bishi da kallo mai cike da tambayoyi, shima kallonta yake yana murmushi a lokacin da yake karasawa inda take. Ta dan muskuta kadan ya zauna a gefen kafafunta da suke mike a kan gadon.

Ya cigaba da binta da kallo har ta dauke idonta tana kokarin tare kwallar da ta taso mata, ya dan matsa kadan ya kama hannunta. Ya kirawo sunanta kamar daga can kasan makogoronsa

‘Aisha.’

A gajarce ta bashi amsa

‘Um.’

Ya dan kara matsawa kusa da ita, so yake ya rungumeta amma ta ki motsawa. Ya kamo daya hannun nata ya rike, yayi shiru na dan lokaci yana tunanin ta inda zai fara.

Kusan wata shida kenan rabonshi da ita, fuskarta kawai da yake kallo yanzu ya tabbatar masa da cewa ya saka ta a cikin damuwa ga kuma wata rama da yaga tayi; domin rigar bacci ce a jikinta mai hannun shimi don haka yana kallon wuyanta.

Yace

‘Aisha kiyi hakuri, na san mun sha wahala amma Alhamdulillah yanzu komai ya wuce. Na sami maganin abinda yake hanani shigowa gidan nan, in sha Allah Allah ba zai bari a wani abu ya sake shiga tsakaninmu ba.’

Ta zare hannunta daga nasa ta share kwallar da ta taru a idonta, tace

‘Bari na dubo su Rukayya a dakinsu.’

Ta zare daya hannun nata ta sauko daga kan gadon, kafin yace wani abu ta fice daga dakin.

Ya juyo ya bi bayanta da kallo; sai yanzu ya kara tausayinta, tabbas ya san ya barta cikin damuwa kamar yanda shima yake cikin damuwa. Duk wanda yayi masa wannan abun tabbasa ba zai taba yafe masa ba. Ya gyara zama ya koma inda ta tashi ya zauna kamar yanda take zaune kafin ta tashi. Ya dauki wayarta ya kashe fitilar da ta bari a kunne.
…….

Tana fita daga dakin hawayen da take rikewa ya kwace, fita hawaye yake daga idonta tana sharewa har ta karasa dakin baki inda Rukayya da Amira suke bacci.

Ba so take ta tashesu daga bacci ba don haka cikin sanda ta karasa kan kafet din dake tsakar dakin, ta mika hannu ta dauko filo wanda ga dukkan alamu na Amira ne ta jefo shi kasa garin bacci. Ta gyara filon ta ajiye a kan kafet din ta kwanta.

Hawayen da yake bin idonta ya cigaba da zarya babu kakkautawa; sai yanzu ya tuna da ita? Wata kusan shida? Ko jiya da za ayi shuka ta san warin da yace yana ji ne baya so ya ji shi yasa bai shigo ba ya kirawota. Me zai ce mata yanzun? Nan da ya shigo mata daki so yake ta rungumeshi shikenan ko me? To idan fa ma yanzu ta saki jiki da shi matarshi ta dawo ya koma wajenta ya kyaleta fa?

Zuciyarta ta fara harbawa da sauri yayinda hawayenta ya kara yawa; tabbas tana iya yiwuwa don matarsa bata nan ne don ta san tabbas ko ma menene ya shiga tsakaninsa itace. Idan kuwa hakane akwai yiwuwar ya zo ya hilaceta ta saki jiki da shi ana sallacewa matarsa ta dawo ya koma wajenta yace idan ya shigo nan din yana jin wari. Gaskiya a yanzu ba zata iya sakar masa kanta ba, gara ma kawai ita kada ya takura mata, ko kuma a kalla ya jira matarsa ta dawo sai a cigaba da rabon kwana. A lokacin sai ta san ba rashin matarsa ne ya kawo shi inda take ba.

Ta muskuta ta cigaba da share hawaye.

………..

Yana nan zaune yana jiran Aisha har wajen minti talatin suka shude, mamaki ya cikashi. To me take yi a dakin su Rukayyan? Ya taso ya fito daga dakin ya shiga nashi dakin bata nan, ya duba kofar falon yaga babu alamar an budeta. Wannan ya tabbatar masa da cewa dakin yaran ta shiga kenan. To me takeyi har yanzu bata fito ba?

Ya dawo falo ya kunna fitila ya zauna yana tunani; to ko dai Aisha fushi tayi dashi? Baya jin zatayi fushi tunda ai ta san ba yin kansa bane.
Ya tashi ya zo kofar dakin su Rukayyan ya tsaya ya kasa kunne ko zai ji motsinsu Bai ji komai ba, to ko dai Aisha fushi tayi da shi?


Ya Kuma kan kujera ya zauna; baya son shiga dakin yaran da wannan daren tunda su din mata ne kuma gashi harda Amira a ciki.

Haka ya gaji da zama a falon ya tashi ya koma dakin Aishan ya kwanta; sai dai da yake zuciyarsa bata da nutsuwa haka ya kasa bacci yana ta juyi.
……..

Karfe uku na dare da minti arba’in da biyar agogon dakin mai alarm ya fara kararrawa, a gefen Rukayya yake don haka cikin magagin bacci ta mika hannu ta katseshi.

A take Aisha ta tashi tunda dama ba bacci takeyi ba, ta fada bandaki ta wanko fuska ta dauro alwala sannan ta fito ta tashi yaran. Da akwai kayanta a dakin don haka ta dauki zaninta ta daura a kan kayan baccin. Saida tayi musu bayanin cewa Abban Rukayya yana nan don su san irin shigar da zasuyi kada su fito yanda suka saba da kayan bacci.

Tayi tsammanin yana falon don bata jin ya fita daga gidan, amma sai taga babu kowa, don haka kai tsaye ta fada kichin. Ta dora indomie da kuma ruwan shayi sannan ta tsaya yanka albasa.


A nan su Amira suka fito suka sameta, suka tayata har indomie din ta dahu sannan ta zuba nata ita da yaran a tray Amira ta dauka ta kai musu kan kafet din falo. Shi kuma Abba ta zuba masa nashi a plate ta hada masa shayi ta dora a kan dining table.
Rukayyace ta hado musu shayi gaba daya ta ajiye sannan ta dauko musu ruwan sha ta ajiye.

Aisha ta duba agogo taga karfe hudu da kwata don haka tace da su Rukayya su fara cin abincin kafin ta taso Abban.

Tana taba kofar ya bude ido, bayan ya amsa sallamarta tace

‘Nayi serving abincin sahur, gara ka fito kaci don an kusa assalatu.’

Yana daga zaune a kan gadon yace

‘Aisha.’

Ta kalleshi suka hada ido alamar tana sauraronsa, ya cigaba yana mika mata hannunsa

‘Zo nan.’

Ta kawar da kai tace

‘Zamu makara fa, saura bai fi minti ashirin ba ayi assalatu gara ka fito kawai muci abinci.’
Kafin yace wani abu ta juya ta fice.

Ya dauki wayarsa ya duba lokaci, tabbas idan bai yi da gaske ba zai makara. Nan da nan ya kintsa ya fito falon. Tana zaune tare da su Rukayya suna cin abinci; suka hada baki suka gaisheshi bayan ya amsa ya wuce dining table ya zauna ya fara cin abincinsa.

Yana ci yana jiyo Aisha tana ta hira da yara suna dariya; tabbas ya san fushi takeyi da shi.


Ya san yana da aiki domin Aisha sarauniya ce, dole ya lallabata su shirya.

Kafin ya gama sahur sun gama ita da yaran, ta shiga dakinta ta dauko wayarta da kayan sawarta. Yana nan zaune ta wuceshi ta koma dakin yaran.

Tana shiga ita da yaran suka fara Sallah. Dama haka suke da sun gama sahur ragowar lokacin sai suyita ibadarsu har asuba tayi.

Haka ya gama cin abincinsa ya koma daki, da aka yi assalatu ya shirya ya wuce masallaci.
__

Tunda Rahma ta tabbatarwa Yusra cewa Abbansu ya tafi wajen amarya ta kasa nutsuwa, so take ta gayawa Mommy amma kuma bata da waya. Dama wayar Abban suke kiranta da ita kuma ya fita da kayarsa, shi kuma Saddiku yana bq balle ta ari tashi, ba ta so ta ari ta Rahma don kada ta zargi wani abun. Haka ta hakura ta kwanta da shawarar idan sun tashi sahur sai ta ari wayar Rahma ta kirawo Mommy din, tunda ko flashing tayi mata ta san zata kirawo.

Wajen karfe uku na dare suka tashi sahur, Yusra da Nana suka daga dakinsu. A nan falo Nana ta zauna yayinda Yusra ta wuce kichin inda ta jiyo motsin Rahma.


Bayan ta gaisheta tace

‘Anti Rahma don Allah ki bani aron wayarki na yiwa Mommy message.’

‘Tana daki ki dauka, amma don Allah ki shiga dakin a hankali kada ki tayarin da Sumayya.’

‘To Anti Rahma, ba zan tasheta ba.’

Tana daukan wayar ta haye sama ta shige dakinsu, credit din wayar ta fara dubawa taga naira dari da ashirin. Ta san ba zai isheta waya ba amma ta san zai isa ta cewa Mommy din ta kirawota.

Nan da nan ta dannan lambar Mommy ta Saudiya, ringing daya Mommy ta dauko kafin tayi magana Yusra tace

‘Mommy Yusra ce, ki kirawo ni.’

Saida gabanta ya fadi, jikinta har rawa yakeyi lokacin da take kokarin kiran lambar Rahman. To me ya faru Yusra take nemanta a wannan lokacin? Allah ya sa dai ba wani abun ne ya faru da gidan ba.

Muryar Yusra ce ta katse mata tunaninta, ta amsa gaisuwar Yusran sannan tace

‘Ya akayi Yusra?’

‘Mommy kin san jiya tun wajen sha daya na dare Abba ya fita,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login