Showing 51001 words to 54000 words out of 166068 words

Chapter 18 - UWAR SADIKU COMPLT BY SAKINA YAZID.txt

11 Jul 2024

25390

Kika barta tana yawo a motar haya kuma tana sayen ruwa, saboda me?’

Maganganun nashi duka sun shammaceta don haka tayi tsamo-tsamo a wajen, ta muskuta kadan ta gyara zama. Ta gagara bashi amsa sai wani muzurai kawai da takeyi, yace

‘Ni da gidana ban isa na fadi yanda nake so ayi ba kenan saboda kin ga ina kyaleki ko Zahra? Ba kya ma tsoron koyawa yara rashin kunya kiri-kiri kike aikata abubuwan da basu dace ba a gabansu saboda tsabar wulakanci da raini…'
A fusace ta katseshi

‘Kada fa ka zageni! Ai nima sai ka tambayeni kaji ta bakina amma daga dawowa ta gaya maka karya da gaskiya ka zo kana ta fada.’

‘To a cikin abubuwan da na lissafa wanne ne karyar ai gani ina sauraronki?’

Ta muskuta ta cigaba da muzurai tana zumbura baki, gaba daya ya shammaceta. Da ta san za ayi haka da ta tanadi karyar da zata tsara masa, sai dai batayi zaton yana dawowa haka zai gane komai ba. Duk wanda yayi mata wannan munafuncin ma dole ta dauki mataki a kansa don ba zata kyale ba.

Ya gaji da jira tai magana bata yi ba don haka ya cigaba

‘To shikenan kinyi yanda kike so nima zanyi yanda nake so, yara kuma ki cigaba da koya musu rashin mutunci. Amma ki sani, kin bani mamaki don a ya da nake dake na zata ko kare na ajiye nace ki tayani kula da shi zaki yi, balle na ajiye matar aure wadda ban ce ki kula da ita ba kawai hakkinta nace a bata amma kika haye Kai saboda hadama. Fice min daga daki.’

Ta kalleshi da mamaki kwakwalwarta tana nanata mata “fice min daga daki”, yau ita Yusuf yacewa ta fice masa daga daki saboda wata amarya.


Ta tashi cikin sanyin jiki tana kallonsa tana mamaki, sai yanzu ne ma taga tsananin fushin da yake ciki. Dole ta dauki matakin a kan duk wanda yake da hannu a cikin kulla mata wannan munafurcin.

Ta fice daga dakin ta rufe masa kofar.

Tana fita hawayen da take makalewa ya kwace, haka ta barshi yana zuba har ta karasa dakinta ta shige ta turo kofar. Ta zauna a gefen gado kamar wadda aka tunkuda, ta rufe fuskarta da tafukan hannunta tana fitar da hawaye masu zafi harda shesshekar.
Wai yau ita Yusuf yake kora daga dakinsa saboda tsabar wulakanci Kuma harda ce mata hadamammiya duk don yana da wata matar. Dole ta dauki matakin a kan Yusuf da wannan matar tasa don ba a isa a zo daga baya ba a rabata da mijinta.

Haka ta karasa wunin cikin kunci, ko da yara suka dawo daga islamiyya haka tace musu bata da lafiya don haka sukayi jugum-jugum.

Ta dafa abincin dare amma ko kallon table din bai yi ba har lokacin kwanciyar bacci.


Bata yi niyyar zuwa dakinsa ba don haka a dakinta ta kwanta, sai dai duk sata irin ta bacci kasa daukarta yayi. Juyi kawai take a kan gadon, zuciyarta sai kuna takeyi saboda takaici. Ga kayan matan da ta sha duk sun hadu sun birkita ta; tun saura sati daya ya dawo aka yi mata kaza ta cinye ga tsumi galan guda wanda shima tsaf ta shanye duk don shirin dawowarsa amma ga da abinda ya dawo mata da shi.

Haka ta kwana tana juyi tana tunanin mafita don dole ta dauki mataki.
UWAR SADDIKU


Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)


19

Ko da gari ya waye haka Zahra ta tashi da idanuwanta a kumbure saboda rashin bacci, gashi ranar litinin ce don haka dole ta shirya yara zuwa makaranta. Haka ta goya Sumayya ta shiga hidima, da taimakon Yusra nan da nan suka gama.


Karfe bakwai da rabi Malam Sule ya juya mota yana jiransu a tsakar gidan.

Daidai lokacin Abba ya sauko bayan sun gaggaisa da yaran da kuma Malam Sule ya kunna tashi motar ya fice daga gidan. Yana fita daga gate din yaci karo da Rukayya ta fito a shirye, bayan ya amsa gaisuwar ta yace

‘Ina Antin suke ita da Amira.’

Tace

‘Basu gama shiryawa ba shine tace mu tafi.’

Yayi mata sallama ya wuce yayi parking a bakin gate din gidan Aisha, ya fito ya shiga ciki.

Amira ce a falo bayan ta gaisheshi ya shige daki inda ya sami Aisha a tsaye ta saka hijabinta ta dauko jakarta. Bayan sun gaisa yace

‘Muje na kai ku makarantar.’

Da mamaki tace

‘Kai da kanka?’

Yayi ‘yar dariya yace

‘To ya na iya, na zama direban matar Alhaji.’

Suka fito tare har bakin gate, ita da Amira suna cikin shiga motar Malam Sule ya zo wucesu da yara.

Saida Abba ya kai Amira makaranta ya dawo ya ajiye Aisha ya sanar da ita zai zo ya dauketa sai su dauko Amira in ya so sai ya kaita ta mayar da Amiran gidansu kamar yanda ta sanar masa.


Suka yi sallama ya dawo gida.

Duk da ta ajiye abincin safe amma bai ko kalli tebur din ba ya shirya ya fice ba tare da ya bi ta kanta ba.


Tunda take da shi bai taba fushi da ita har ya ki cin abincinta ba sai yau. Tsayawa kawai tayi tana kallon abincin a dinig table bayan ya fice; lallai an juya mata kan miji kuma dole ta dau mataki. Dole ta san yanda zata yi ta janyo hankalin mijinta ya dawo kanta kafin a saka shi ya koreta.

Abban bai dade da fita ba Jummai ta shigo gidan, don haka ta mikawa Jummai Sumayya tace mata ciwon kai yana damunta. Ta koma dakinta ta rufo kofa, ta zauna a gefen gado ta kafa tagumi.

Jimawa kadan ta tashi ta dauki wayarta ta fara lalube a ciki, har ta zo kan Yaya Murja sai kuma ta fasa dannan kiran. Idan dai Yaya Murja ce ta san hakuri kawai zata bata tace tayi addu’a , kuma ai kullum tana addu’a itama. Idan kuma ta kirawo Suwaiba itama hakurin zata bata don ita wannan bata ma san menene rayuwar ba.

Haka ta koma ta lalubo lambar Amina, kara daya wayar tayi aka dauka. Bayan sun gama gaisawa tace

‘Kawata ina son ganinki yanzun nan, gashi kuma ni bazan iya fitowa ba balle na zo.’

Tace

‘To nima dai gani a office amma bari mu gani watakila zan iya fitowa nan da minti ashirin haka sai na karaso gidan. Allah yasa dai lafiya.’

‘Ina fa lafiya, ke dai kawai ki hanzarta ki zo.’

Sukayi sallama suka ajiye wayar.

An dauki kamar awa daya domin har ta gaji da jiran Hajiya Amina kafin taji tsayuwar motarta a bakin gate. Cikin kankanin lokaci kuwa Jummai ta buga mata kofa ta sanar da ita isowar Aminan, nan take ta bada umarnin Aminan ta shigo ta sameta a dakin.

Tana shiga ta tura kofar ta karasa ta zauna a kusa da ita tana fadin

‘Yaya dai Uwar Sadiku? Ya zan ganki cikin duwa bayan kuma jiya maigida ya dawo? Me yake faruwa ne?’

Ta share kwallar da take kwarmin idonta tana ajiyar zuciya yayinda Aminan ta bita da kallon mamaki

‘Ni za ayiwa bura uba Aminoni? Tunda ya sauka a garin nan yake min wulakanci saboda wata banzar matarsa; wai ni Abban Sadik ya kalla yacewa hadamammiya yana wani korata daga dakinsa kamar kare.’

Ta zaro ido tana binta da kallo, sannan tace

‘Daga dawowa Zahra? Ke kuwa me kika yi masa?’

‘Me aka gaya masa dai zaki ce?’

‘Allah kawata? Yanzu wannan matar tasa mai kama da abun tausayi ta kai ta kulla wata tsiya haka?’

Nan ta karantowa Amina abubuwan da suka faru da yanda take jin janye hankalinsa akayi daga kanta aka saka shi ya zo yana yi mata wulakanci.

Aminan tace


‘Ikon Allah, lallai kishiya bata kadan. Shi yasa wallahi ba zan taba bari Habibi ya kara aure ba sai inda karfi na ya kare. Ka rayu da mutum tun bashi da komai amma yanzu yana jin yana da bakin kiranki hadamammaiya, kai maza basu da mutunci!’

‘Ni yanzu kin san me nake so? Duk inda kudi suke dole na nemosu don kin san munyi da Malam Hatimu zai raba min su gaba daya.’

‘Hakane. To yanzu ina zaki sami kudin bayan tuntuni kike cewa baki da su, kuma kinga dai nima bani da su.’

Tashi kawai tayi ta matsa gaban wardrobe dinta ta bude, ta dauki lokaci tana lalube sannan ta mayar ta rufe. Ta dawo kusa da Aminan ta zauna tana dauke da wani dan akwati mai dauke da sarkoki.

Ta dubi Amina tana dafa akwatin sarkokin tace

‘Zan cire wasu daga cikin sarkokin nan ki kai ki sayar min, kafin a gama ciniki na dan sami kaina sai mu sa rana muje wajen Malam. Gara ayita ya kare kawai na gaji wallahi.’

Cikin walwala Amina tace

‘Yanzu kikayi magana Hajiyata, amma ki zauna yarinya kamar wannan tana ta faman kasa miki hankalin miji ai ba daraja.’

Ta bude akwatin sarkokin ta dauko zobenta guda daya na gwal babba ta mikawa Amina. Ta dauko wani karamin saiti na sarka da dan kunne mai karamin kwado ta kara mika mata tana fadin

‘Wannan ma na Yusra ne amma a hada dashi a sayar don na san wannan zoben ba zai kai dubu dari ba ma, nawa saitin kuma yayi girma da yawa. A sayar da wadannan abinda ya kama sai na cika tunda ina da wasu ‘yan kudaden.’

Ta karba tana jijjiga kai

‘Yanzu kikayi magana Uwar Saddiku, in sha Allah gobe da safe zan kaisu kasuwa. Zaki ji duk wani bayani.’

‘Shike nan, zuwa nan da kwanaki biyu zanyi kokari mu shirya don na samu muje Gaya tare, nafi so naje gani ga Malam na karanta masa abinda nake so.’

Nan suka karasa hirarrakinsu da shirin yanda za su je Gaya wajen Malam Hatimu. Kafin azahar Aminan tayi mata sallama ta tafi.
……..

Wajen karfe biyu da Rabi Malam Sule ya dawo da Yusra, Rukayya da Nana daga makaranta; ita Ummi da yake a nursery take tun sha biyu aka dawo da ita.

Suna shiga gidan suka sami Jummai a kicin, Yusra ta dubeta tace

‘Jummai ina Mommy?’

‘Tana sama, inaga dai bata jin dadi yau din nan.’

Kafin ta gama jin amsar da Jummai ta bata ta haye saman da gudu, tana shiga dakin ta zauna a gefen gadon kusa da kafar Mommy

‘Mommy har yanzu kanki bai daina ciwo ba?’

‘Um.’

Cikin kosawa ta zaro ido tana duban Mommy tace

‘Mommy kin san me na gani kuwa?’

Kai kawai ta jijjiga mata alamar a’a.

Tace

‘Mommy Abba ne fa ya kai matarshi makaranta da ita da ‘yarta, kuma yanzu ma motarsa tana kofar gidan nata na san dauko su yayi ya tsaya yin wani abun a gidan.’

Ta tabe baki tana gyada kai

‘Yusra duk abinda Abbanku yayi ba zan yi mamaki ba, an riga an juyar masa da tunani sai addu’a kawai. Inaga saboda na hana Malam Sule kaita makaranta da baya nan shine yanzu yaje ya kaita don ya bani haushi.’

‘Hmn! Lallai Abba.’

Tayi kwafa tace

‘Ki barni da su duk zan yi maganinsu, da sannu zasu dawo hannunna.’

‘Gaskiya dai abun nashi yayi yawa Mommy.’

‘Kije kuci abinci kuyi shirin islamiyya kada ku makara.’

Ta sauko ta barta tana faman tunani.

Wato saboda ta hana Malam Sule ya kaita aiki shine shi ya dawo ya fara kaita, kwana biyun nan nata ne amma gaba daya a wajen Aisha yake karewa; don ta tabbatar wannan shigar da yayi gidan sai ya kaiwa Aishan kwananta. Lallai yanzu ta sake tabbatarwa da cewa Aisha bata barsa haka ba, don haka itama dole ta tashi tsaye. Kokari zata yi taga sun shirya domin bata jure fushinsa musamman da yake yana da inda zaije a debe masa kewa. Idan suka shirya sai ta fi samun natsuwar aiwatar da abubuwan da take shirin yi.
-------

Kamar kullum yauma Jummai ta gama duk wani aiki na cikin gida, ta fito tana share tsakar gida.


Can daga gefe daya akwai boys quarters mai daki biya; daki daya maigadin gidan ne Malam Sajo yake amfani da shi, daya dakin kuma kwanan nan da Sadik ya shiga SS 3 ne ya gyara saboda idan abokansa sun zo nan suke zama karatu kamar yanda yake fada.
Jummai bata share cikin dakunan, amma idan tana share tsakar gidan takan zagaya har farfajiyar boys quarters din ta share.


‘Yan kwanakin nan kullum ta zagaya sharar haka take ganin murafun kwalba kamar kwalbar magani a watse a farfajiyar wajen. Bata san na menene ba amma dai ta san Sadik lafiyarsa kalau kuma Malam Sajo ma bai ce bashi da lafiya ba; kuma koda mutum bashi da lafiya ma ai akalla ayi kwana biyar kafin a shanye kwalba guda ta magani. Amma yanzu kusan kullum sai ta share murafun nan guda uku zuwa biyar.

Haka ta tattara sharar zata kwashe sai kuma ta sa hannu ta tsince murafun kwalabar guda hudu ta rike a hannunta sannan ta kwashe sauran sharar. Ta dauki kayan shararta ta juye a kwandon sharar tsakar gidan wanda yake kusa da gate.


Bayan ta juye ta nufo wajen Malam Sajo wanda yake zaune a gefen fulawoyi yana hutawa.


Tana isowa tace

‘Malam Sajo wai ni baka da lafiya ne kwana biyun nan?’

Da mamaki ya kalleta yana dan murmushi

‘Ni kaina Jummalo? Nan da kika ganni lafiyata ras ai ko ciwon kai na manta rabon da nayi balle ace bani da lafiya. Wani ne yace miki bani da lafiya?’

‘A’a’

Ta karasa kusa da shi ta ware hannunta ta nuna masa tana fadin

‘Gani nayi ‘yan kwanakin nan kusan kullum sai na share murafun nan na kwalabar magani a wajen dakin naka, to idan ana da lafiya ai ba za a sha magani ba.’

‘A to gaskiya dai wannan ba nawa bane, nima dai kwana biyun ina ganinsu. Amma sai dai ko ki tambayi Sadiku da abokansa tunda sune ke zama a daya dakin. Ni kam ai ko bani da lafiya bana shan maganin asibiti Malama Jummai shi ya sa kika ganni gatagau nan.’

Tayi ‘yar dariya saboda yanda yake magana yana jijjiga jiki

‘Ai kuwa gaka nan.’

Ya kama haba yana sake duban murafun da har yanzu suna hannunta yana fadin

‘To amma fa gaskiya ki bincika, ko kuma kiyiwa Hajiya magana ta bincika don gaskiya matasan yanzu abun tsoro ne tunda har magungunan ma sha sukeyi masu bugarwa da wani sirab suke kiranshi ko sirap ni ban rike ba. A dai binciki Sadiku da abokansa.’

‘Nima zargin da nakeyi kenan, bari mu gani ko zan samu fuska.’

Ta koma cikin gida ta adana murafun ta cigaba da aikinta.

Har yamma abun yana ranta, tana so ta yiwa Mommy maganar amma tana tsoro don ta san yanda Mommy bata son laifin Sadiku, sannan kuma ko ta fada idan yazo yace ba haka bane babu abinda Mommy din zata yi a kai.

Sai can bayan la’asar lokacin yara sun tafi Islamiyya shi kuma Sadiku bai dawo daga makaranta ba sannan Mommy ta sauko daga sama. Har yanzu tana da sauran damuwa sai dai abun da sauki tunda zuwa yau Talata ta samu Abban yana cin abincinta; damuwarta daya yau zai koma kwanan Aisha. Duk da haka tunda akwai tanadin da takeyi wannan ba damuwa bace.

A falo ta sami Jummai a zaune a bayan kujera tana hutawa saboda babu wani aiki da zata yi.


Bayan sun gaisa ta zauna ta kunna TV, tace

‘Jummai ai sai ki fito daga bayan kujerar kiyi kallo kafin aminiyarki ta tashi daga bacci ta isheki da gwaranci.’

Ta taso ta dawo kan kafet ta zauna daga gefe tana dariya.

Tana kaunar Zahra saboda yanda take kyautata mata, matsalarta duk da ta yaranta idan ta rasa yanda zata yi haka Uwar Sadiku take wuce mata gaba ayi komai. Ba zata so taga abinda zai cutar da ita ba ko yaranta su sami matsala; duk da tana son aikinta bata son abinda zai rabata da aikin.

Ta tashi ta wuce kicin tana fadin

‘Ina zuwa Hajiya.’

Jimawa kadan ta fito da murafun maganin nan a hannunta ta tsuguna a gaban Mommy ta mika mata tana fadin

‘Hajiya kinga murafun maganin nan, a nan boys quarters na tsinto su, ‘yan kwanakin nan kuma kullum sai na gansu a shara. Na tambayi Malam Sajo yace ba nashi bane, amma fa kullum sai na gansu na share don yanzu nan haka gobe ma idan nazo shara sai na share wasu.’

Ta karba tana dubawa

‘Ikon Allah, to na waye?’

Ta sunkuyar da kai
‘To Hajiya sai dai ki binciki Sadiku tunda kinga yanzu yana shigo da abokai wajen, kuma kin san samarin zamanin nan basa raina abun maye tunda kinga har maganin ma sha sukeyi. Sai ka gama tarbiyyar naka yaron a sami bata gari su bata maka aiki.’

‘Eh, da wannan. Amma dai Sadiku ya san me yake ba zai sha wannan ba sai dai ko abokan nasa. Bari ya zo muji idan sune ma ai dole ya rabu da su kowa ya koma gidan ubansa ya dinga karatun a can.’

‘E gara kam a bincika Hajiya, yaran yanzu sai ana sa musu ido.’

Ta koma ta zauna suka cigaba da kallonsu.

Suna nan zaune Sadikun ya shigo daga makaranta, Mommy ta tsayar da shi ta nuna masa murafun tana tambayarsa a kansu. A take yace shi bai taba gani ba gaskiya sai dai idan yaran makota ne suke watsowa ta katanga.


Ta gamsu da bayaninsa don haka ta juya ta bawa Jummai murafun tana fadin

‘Kin ji ko? Ai dama na san ba shi bane don abokan nasa ma duk na san su. Zai iya yiwuwa yara ne da suke wasa da shi kin san suna yin mota da shi. Kuma idan barnar su Sayyad ta tashi zasu iya watsowa nan din. Kawai ki dinga sharewa idan kin gani.’

Ta karbi murafun tana fadin

‘To Hajiya, in sha Allahu za a dinga sharewa.’

Ta kwashe ta nufi kicin tana zullumi a ranta; domin tabbas bata jin yaran makota zasu jefo

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login