Showing 6001 words to 9000 words out of 166068 words

Chapter 3 - UWAR SADIKU COMPLT BY SAKINA YAZID.txt

11 Jul 2024

25434

shi yasa bata aiki amma duk da haka tana business daga gida inda take sayar da atamfofi da duk wata sutura ta mata.

A tsarinsa yana so ya hadesu gida daya da uwargidan sai dai ita Aishan ta gaya masa tafi so ya zama nata gidan ita kadai ko da cikin compound daya ne. Ya sanar da ita gidansa bashi da filin da zai gina mata wani a ciki amma dai ya tabbatar mata ba zai hadesu ba tunda bata so.Don haka ta saki jiki da shi sosai sunata soyayyarsu tunda shi din gwanin soyayyar ne.

Duk da ta amince da Yusuf amma bata daina kewar Mustafa ba, wasu lokutan ma sai taji kamar idan tayi aure taci amanar Mustafan. Idan taji haka sai dai tayi kukanta ta share hawayenta don ko ta gayawa ‘yanuwanta ma basa fahimtarta, so kawai suke tayi aure. Har gara ma Yaya Zuwaira da yake itace sakuwarta suna dan fahimtar juna, amma Yaya Zainab cewa take “Da kece kika mutu da yanzu yayi aure yana morewa da amaryarsa amma ke kina nan kina hana kanki bacci, addu’ar ma da kike masa ai ta isa ba sai kin cigaba da kuntatawa kanki ba.” Don haka bata ma son yin zancen da ita.
UWAR SADDIKU


Written by


Sakina Yazid
(Innar su Amal)


4

Tun kimanin shekaru shida da suka wuce ya so ya kara aure, don a lokacin har an je gaisuwa gidansu budurwar da yake nema; sadaki kawai za a kai a saka rana sai kuma aka wayi gari haka kawai maganar auren ta fita ransa. Yarinyar da yake nema bata yi masa komai ba amma haka kawai yaji ya daina sonta. Da farko ta so ta takura masa, amma sai Allah ya hadata da wani saurayi a daidai lokacin wanda ya fiye mata Yusuf din.

Matarsa daya Hajiya Zahra’u da yaransu biyar; Sadik, Yusra, Rukayya, Khadija wadda suke kira Dija sai Zulaiha mai shekaru uku wadda suke kira Ummi saboda sunan mahaifiyar Zahra’un taci.

Hajiya Zahra’u mace ce mai matukar kirki ga kyauta, duk wani abu da zai farantawa mijinta shi takeyi. Shima kuma ta samu yana da kulawa gashi yana mata yanda take so; musamman ma yanzu da Allah ya kara buda masa ya fara tara abun duniya. ‘Yan uwan Yusuf ma suna matukar kaunarta saboda yanda take musu kyauta kuma tana kulasu tana kula da mahaifiyarsu Hajiya.

Tun Yusuf yana malamin makaranta ta aureshi, suna tare ya karo karatu ya sami sauyin aiki ya koma ma’aikatar ilimi ta jiha; gashi yanzu har ya zama director. Wannan ne ya saka Hajiya Zahra’u take ji cewa ita kadai ce ta dace ta zama matarsa, don ita ta sha wahalarsa. Shi yasa ma wancan lokacin daya ya dauko maganar aure ta san yanda tayi ta kifar da zancen.

Bata yin tsafi don tana da ilimin addini gwargwado saboda haka ta san abinda zai rabata da imaninta, amma tana da malamanta irin na soro wadanda sukeyi mata aiki da ayar Allah, wani lokacin ma har su bata ruwan rubutu ko tofi wanda zata yi amfani da shi ko shi Yusuf din tayi masa amfani da shi.

Tunda taji anje gaisuwa wancan lokacin da ya fara maganar auren ta tashi ta tafi har garin Gaya, wajen wani malami da aka hadata da shi Malam Hatimu mai ‘yan makaranta. Tayi masa bayani so take kawai a sakashi ya manta da maganar auren nan ya daina son yarinyar. A nan take kuwa ya zana hatimi ya nade mata laya ya bata yace ta saka masa a karkashin katifarsa, idan dai ya kwana a kai ba zai sake maganar auren wannan yarinyar ba. Haka kuwa akayi, wannan aure dole aka barshi.

Bayan fasa wancan auren ne abokinsa ya bashi shawara idan ya tashi sake aure kada ya fada da wuri sai magana ta kankama, kuna shima sai ya dage da addu’a. Don haka ma tunda ya fara neman auren Aisha babu wanda ya gayawa, don har abokan nasa ma babu wanda sani.


Yayansa kawai ya gayawa wanda shine zai wuce masa gaba wajen neman auren kuma ya gaya masa bai sanarwa kowa ba don haka shima kada ya bari zancen yake wajen mata.
____

A daki ta sami Hajiya tana zaune a kan dadduma inda ta idar da sallar la’asar, ta shiga dakin da sallama ta karasa ta zauna a gaban Hajiyan bayan da ta amsa sallamarta. Hajiya ta gyara zama tace

‘To wacce sura zan biya miki da kika sakani a gaba haka kamar mai daukar karatu.’

Tayi ‘yar dariya tace

‘Kai Hajiya.’

‘To ya akayi?’

Ta dan saita fuskarta tana kokarin danne damuwar da take zuciyarta

‘Hajiya dama Yusuf ne yace zasu zo sa rana sati mai zuwa, kuma tare zasu kawo da sadaki da kayan aure duka.’

Take murmushin Hajiya ya karu

‘Kai ma sha Allahu, to ai hakan yayi. Bari Yayanki ya zo sai na sanar dashi in ya so sai ki gayawa Yusuf din ya nemeshi suyi magana ko kuma ya nemi Baffa.’

Kai kawai ta daga yayinda damuwa ta kara bayyana a fuskarta.


Hajiya ta jijjiga kai tace

‘To damuwar kuma da bacin ran na menene, ko shima Yusufan ba kya sonsa?’

Ta saka yatsanta ta goge kwallar da ta makale a kwarmin idonta, tace

‘A’a Hajiya, Yusuf bashi da wani laifi.’

Sukayi shiru na dan lokaci, Hajiya tana sauraronta don ta san zancen bai kare ba yayinda ita kuma take tunanin kalmomin da zata yi amfani da su ko Allah zai sa Hajiyan ta fahimceta. Jim kadan ta cigaba
‘Sai naga kamar idan nayi aure zan ci amanar Mustafa Hajiya, ban san ma dai me yake damuna ba Hajiya. Ga su Abdallah kuma, bana son rabuwa da su sai na ga kamar abun zai yi musu yawa; babu uba kuma ni dinma na zo na tafi wani gidan na barsu.’

Hajiya ta saka hannunta tana goge mata hawayen da yake bin kumatunta cike da tausayawa

‘Na fahimceki Aisha, tabbas idan miji ya mutu yana tafiya da rabin zuciyar matar ne kamar yanda mahaifinku yayi min. To amma hakuri shine siffar bayin Allah na gari. Baki ci amanar kowa ba idan kikayi aure, ke dai kada ki taba fasa yiwa Mustafa addu’a. Ki cire duk wata damuwa daga ranki Allah zai saka miki albarka a cikin aurenki in sha Allah.’

Ta daga kai alamar to, ta kifa kanta kan cinyar Hajiya, ita kuma ta cigaba da shafa mata kai yayinda take fadin

‘Kunyi maganar yaranki da shi ne?’

Ta dago ta karasa goge fuskarta tare da yin ajiyar zuciya, tace

‘A’a, ba muyi wata magana ba. Shi sau nawa ma ya taba yi min maganar yara? Ai bai fi sau a kirga ba. Kuma ni dama bani da niyyar tafiya da su gidan wani, a nan zan bar miki su idan dai kin yarda tunda gashi Anti Uwani zata dawo nan kin ga ta tayaki. In ya so ni sai na dinga zuwa ina dubaku tunda iyayensu suna yi musu komai kuma na san ba zamu sami matsala da su ba.’

‘Ah ni kam ai dama zan fi so ki bar min su muyi zaman mu, amma idan kina son tafiya da su ai sai kuyi maganar da shi ki ji me zai ce.’

‘A’a Hajiya, ba zan tafi da su ba fa, sai dai ko daga baya idan na ga da hali sai su koma can din. Amma dai yanzu suyi zamansu.’

‘To hakan yayi.’

Suka dan taba hira sannan Aishan ta fito ta shiga kicin don dafa musu abincin dare.

Tabbas Yusuf baya yawan damuwa da yaranta, watakila shi din ba mai son yara bane. Headmaster da Musbahu da suka fara zuwa wajenta a da kullum cikin yiwa yaranta tsaraba suke amma shi babu abinda ya dameshi, duk abinda ya kawo to ita ya kawowa. Har gara wancan hutun da za a koma first term ya kawo musu kyautar robobin ruwa da jakunkuna na makaranta masu kyau da tsada, amma bayan wannan ba zata iya tuna wani abu da ya hadshi da yara ba. Yana dai cewa ta gaishesu ko kuma idan ta fita da Farha ya dinga janta da hira. Ita gaba daya ma idan tana tunanin su Abdallah ji take kamar kar ta yi wani aure, bata son rabuwa da su kuma gani takeyi kamar bata yi musu adalci ba.

Ta jijjiga kai ta kawar da wannan tunanin don ta tabbatar in dai zata cigaba da irin wannan lissafin to tana dab da fasa wannan auren; ta san kuwa ba zasu daidaita da Hajiya da Baffa ba idan haka ta faru.

Ta karasa gaban cooker ta bude tukunyar ta zuba shinkafar da ta wanke ta cigaba da girkinta.
------

Sati guda da yin wannan maganar waliyyan Yusuf suka kawo sadaki da kayan auren Aisha. Gidan Baffa suka kai tunda shine ubanta, sadakinta naira dubu dari da kayan lefe da duk wasu kaya da ake kaiwa na aure haka suka hada suka kai. Sun zo da sa ranarsu suna so ayi biki sati shida, lokacin zai kama bayan karamar sallah da kwana takwas kenan shi kuma Baffa yace ayi musu hakuri a barshi sati tara. Don haka aka tashi daga taro a kan bayan sati tara za a daura auren Alhaji Yusuf Muhammad Bala da Kuma Aisha Tukur Yawale.

Bayan sun sallami baki Baffa ya cewa Yaya Abubakar idan an yi sallar isha’i yazo ya daukeshi suje su yiwa Hajiya bayanin kuma su kai mata kayan da kudin gaba daya.

……..

Tana zaune a falo tana kallon TV tare da su Abdallah wayarta tayi kara, tana dubawa taga Yusuf ne don haka ta dauki wayar ta amsa ta kara a kunnenta ta mike
tanufi daki.

Bayan sun gaisa sun dan taba hira yace

‘Baffa ya sa mana sati tara fa.’

Tace

‘Um, haka Yaya Abubakar yace min.’

‘To ai yayi ko? Kin ga kafin nan na samu na dan gyara gidan tunda kince kin fi son ki zauna gidanki da ban.’

‘Eh, gaskiya sai ya fi dadi tunda ma kace gidan jikin gidanka ne kaga ai duk muna waje daya.’
‘Hakane, sai dai zan fi son ku a gida daya amma duk da haka na hakura yanda kika ce haka za ayi. Gashi dai an ki sayar min da gidan amma sun bani haya, na ma biya na shekara biyu.’

Tayi murmushi

‘Hakan ma yayi ai.’

Suka gama hirarsu suka ajiye wayar.

Sai bayan sallar isha’i Yaya Abubakar da Baffa suka shigo gidan.


A falo Hajiya ta saukesu, bayan sun gaisa Baffa yace

‘To Alhamdulillah an kawo kudin ‘yata, kaya komai yayi Alhamdulillah kuma mun basu sati tara zuwa lokacin an gama hidimar karamar Sallah.’

Ya zaro sababbin kudin daga aljihun Babbar rigarsa ta mikawa Hajiya yana cewa

‘Ga sadakinta don haka idan sun zo auren kawai za a daura, kaya kuma suna can akwati shida gobe in sha Allah za a kawo.’

Hajiya ta karba da fara’arta

‘Ma sha Allah, Allah ya sa ayi damu.’

‘Amin ya Allah.’

Yaya Abubakar ya amsa.
Baffa yayi gyaran murya yace

‘To yaranta fa? Ina za a barsu? Don sai an san makomarsu kafin ayiwa uwarsu aure.’

Hajiya tace

‘Eh to, duk da dai bata ce min sunyi maganar yaran ba amma dai tace min bazata tafi da su ba a nan zata bar min su.’

‘To babu laifi, Allah ya raya su yayi musu albarka. Allah ya sa albarka a cikin auren. ‘Yan uwan ubansu ma suna kokari don haka ma yaran basu da wani maraici, Allah ya saka musu da alkhairi.’

Hajiya ta amsa da Amin, sukayi sallama Baffa da Yaya Abubakar suka kama hanya.

Suna fita Hajiya ta mike ta leka dakin Aisha tana kwance a kan gado yayinda Abdallah da Farha suke kwance a gefenta suna bacci, tace

‘Ki zo Aisha ina daki.’

Ta taso ta bi bayan Hajiyan suka shiga dakin kusan lokaci guda suka zauna a gefen gadon Hajiya. Hajiya ta mika mata kudi tace

‘Ga sadakinki da kudin aurenki, gobe za a kawo kayan in sha Allah.’

Ta sunkuyar da kai kawai, saboda kunya da kuma damuwa.


Duk lokacin da aka zo wata gaba a kan maganar auren nan sai taji kamar ta fasa, amma ta san haka zata daure. Hajiya ta cigaba

‘Dama bakiyi shirin tafiya da yaranki ba ko? Baffa ne yake tambaya.’

Ta kalli Hajiya tace

‘Eh, ai na gaya miki a nan zan barsu, bamu dai yi maganarsu da shi ba amma a nan zan bar miki su.’

‘To babu damuwa, Allah ya nuna mana.’

Suka dan taba hira, Aishan ta tashi ta koma nata dakin zuciyarta cike da tunani kala-kala.


UWAR SADDIKU


Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)


5

Suna gama waya da Aisha kuma sai hankalinsa ya dawo kan uwargidansa Zahra’u, duk da dai itama Aishan ya ji ta kamar bata cikin yanayi na walwala amma dai kaf rigimar Aisha zuwa yanzu ya haddace; kuma ya iya da ita.


Yanda za ayi ya gayawa Zahra’u zai yi aure shine matsalarsa; baya jin zata bashi matsala tunda wancan lokacin ma da ya dauko auren bata bashi wata matsala; kawai dai ya san tana da kishi kuma zuwa yanzu ta kara sakankancewa ba zai taba yi mata kishiyaba tun da ya bar waccan maganar.

Tun yana office yake faman tunanin yanda zata kaya har ya dawo gidan bai samo amsa ba, haka ya shiga gidan yara suka taso sukayi masa sannu da zuwa. Ya wuce daki bayan ya amsa inda ya tarar da ita tana kwance a kan gado, bayan tayi masa sannu da zuwa cikin kulawa ta fito ta hau jera abinci a dining table.

Har suka gama cin abincin da hirarrakinsu suka kwanta bacci bai iya gaya mata ba. Don haka ma bayan an idar da sallar a asuba ya tsaya a masallaci yayi ta rakon Allah alkhairin da yake cikin auren kuma ya roki Allah a kan ya basu hakurin zama da juna. Saida ya dauki tsawon lokaci yana addu’a sannan ya fito ya koma gidan.

Ba wai tsoron Zahra’u yake ba amma dai yana son zaman lafiya da ita tunda itama yana sonta sosai. Ya santa da kishi kuma shi baya so auren nan ya zama dalilin da zai saka ta canza hali tunda ita din tana kulawa da shi sosai harma da danginsa.

Sai wajen karfe takwas da rabi na safe ya gama shirin tafiya office, ya fito a shirye ya zauna a dining table inda take jiransa suci abinci.


Daga ita sai shi a gidan domin yara duka tuni driver ya kaisu makaranta. Suna cin abincinsu suna hirarraki irin na miji da mata, duk da dai ta kula kamar wani abun yana damunsa tun jiya; jira takeyi shi ya gaya mata kafin tayi masa magana.

Bayan sun gama cin abincin ya mike ya dubeta yace

‘Idan kin gama ki zo dakin ina jiranki.’

Da murmushinta ta amsa

‘To Yallabai.’

Yana wucewa ta bi bayansa da kallo tana murmushi; ta san akwai magana a bakinsa daman wannan lokacin take jira. Cikin sauri ta daga kofin shayinta ta kurbe ta bishi dakin don haka kusan a lokaci guda suka shiga.


Kujerar mutum daya dake dakin ya zauna don haka ta zauna a gefen gado tana fuskantarsa, ta kara fadada murmushinta tace

‘Gani Yallabai, me na samu? Ka san hausawa sunce idan ka ji kira samu ne.’

Yayi wani dan gajeran murmushi ya taso ya dawo kusa da ita, ya kama hannunta na dama ya rike yana shafawa yana duban fuskarta. Suka shiru na dan lokaci sannan ya dubeta yace

‘Kanwa kika samu Zahra, aure zanyi in sha Allahu shine nake so na sanar dake.’

Tuni ta bude baki tana binsa da kallo cike da mamaki. Ya sunkuyar da kansa a hankali yayinda ta zare hannunta daga cikin nasa. Ta hadiye wani malolo da ya tokare mata makogoro tana kokarin tokare kwallar da take neman kwace mata tace

‘Aure kuma Abban Sadik?’

Ya daga kai alamar e, yana kallonta yana mata murmushi.


Suka yi shiru na dan lokaci, yaji batayi magana ba yace

‘Ai bazawara ce ma ko da yake mijin nata rasuwa yayi ya barta da yara biyu kanana. Tana da hankali kuma sosai ga ilimi na san bazaku sami matsala ba in sha Allah.’

Tayi murmushin yake tace

‘Allah ya sa, Allah ya tabbatar mana da alkhairi.’

Da sauri ya amsa

‘Amin amin.’

Ya mike da sauri tunda dama so yake ya bar gidan kafin ta saka shi a gaba da korafi. Ya matsa gaban mudubi ya dauki hularsa ya saka yanayi yana lekenta ta mudubin, ya dauki mukullan motarsa ya juyo yana fadin

‘To sai na dawo.’

‘A dawo lafiya.’

Ta fada da murya kasa-kasa tana kokarin danne damuwar da ta shiga, ya fice ya ja mata kofar dakin.

Ta bi kofar dakin da kallo tana takaici da mamaki; ashe har yanzu bata wuce kishiya a wajen Yusuf ba? Tayi zaton ma ba zai taba yi mata kishiya ba da taga shekaru shida sun shude bai kuma kwaso maganar auren ba, tayi zaton da Mallam yace mata ya dauke hankali sa daga kan maganar aure shike nan.
Hawayen da take tokarewa ya gangaro kan fuskarta, ta sa hannu ta goge. Ta cije lebe data tuno kalamansa “tana da hankali sosai, ga ilimi” lallai namiji, wai yau ita Yusuf yake gayawa zai auro mai hankali da ilimi.


Ta mike kamar wadda aka tsikara ta fice daga dakin.

Ta shiga dakinta ta turo kofa, ta jingina a jikin kofar, nan zuciyarta ta fara tuna mata rayuwarsu a baya lokacin da Yusuf din bai yi kudi haka ba; lokacin da albashinsa na wata da kyar yake kaisu kwana goma, a lokacin haka zata zauna da dadi babu dadi amma duk ya manta.

Ta fara kaiwa da kawowa tana tunanin mafita don gaskiya bata son wannan auren nasa, ta ina zata fara zama da kishiya?

Ta karasa ta zauna a gefen gado ta kafa tagumi, jimawa kadan ta mika hannu ta dauko wayarta daga kan durowar gefen gado inda take ajiye. Har ta lalubo lambar yayarta Yaya Murja zata kirawota sai kuma ta fasa ta rike wayar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login