Showing 153001 words to 156000 words out of 166068 words
aka idar da sallar Magriba sannan ya wuce gidan Aishan. Kamar dazu haka ya tarar da gidan a rufe, cikin tsananin mamakin inda Aishan ta tafi ya sa mukullinsa ya bude kwadon ya shiga falon. Dakinta ya fara shiga inda ya hangi akwatunanta na saman wardrobe babu guda uku a cikinsu, ya karasa ya bude wardrobe din ya tarar ta kwashe mafi yawancin kayan sawarta. Yayi murmushi yana tunani yanzu haka ta riga shi dawowa ta hada kayanta ta koma can gidan, don haka cikin kwarin gwiwa ya fito ya nufi gidan.
Duka yaran suna zaune a falon kasa; kafin ya karasa shiga ciki Sumayya ta taso da gudu tayi masa oyoyo. Bayan ya shiga ya zauna sannan ya dubi Jummai wadda take tsaye da leda a hannunta tana jira ya dawo ta tafi gida yace
'Jummai zaki tafi ko?’
'Eh Alhaji dama jira nake ka shigo sai na tafi tunda Yayansu ma bai dawo ba tukunna.’
'To babu laifi. Aisha bata shigo bane?’
'Eh gaskiya bata zo nan ba.’
Mamakinsa ya bayyana, yayi sauri ya wayance ya sallami Jummai ta fice bayan ta yiwa yaran sallama shi kuma ya haye sama yana ta mamakin inda Aisha zata tafi harda kwashe kaya haka ba tare da ta sanar da shi ba.
Ya zauna a gefen gado ya zaro wayarsa daga aljihunsa, ba tare da bata lokaci ba ya lalubo lambar Aishan ya danna mata kira. Har aka fara kiran sallar isha'i yana nan zaune yana faman kiran wayar amma ba a dagawa, haka wayar zata kari ringing har ta katse. Cikin kosawa da damuwa ya mike ya shiga bandaki yayi alwala ya fito ya nufi masallaci yana ta tunani kala-kala; to ina Aishan ta tafi? Me ya hanata daukan wayars?
Yana daf da shiga masallacin dabara ta fado masa, don haka ya tsaya ya lalubo lambar Zahida ya kirawota. Bayan sun gaisa ya tambayeta yayarta. Nan take ta sanar da shi Aisha tana gidan Hajiya, yayi mata sallama ya ajiye wayar.
Ya mayar da wayar aljihunsa yana murmushin yake; wato Aisha gidansu ta tafi kenan saboda ba zata rike masa yara ba? To wannan wacce kalar fitna ce? Wai dama haka Aishan take ko kuwa wani ne yake zugata? To idan ma don yaranta ne ai yace ta kwasosu su dawo gidan tare? Shi dai bai taba ganin inda mutum yana da mata taki rike masa yara ba, ko da kuwa shegu ne balle yaran da aka san uwarsu. Yana nan tsaye yana mamaki ba tare da ya sami amsar tambayoyinsa ba aka tayar da Sallah, don haka ya mayar da wayar aljihunsa ya karasa masallacin ya shiga sahu cike da damuwa.
Ana idar da sallah ya koma gidan, a nan ya tarar Saddiku ya dawo don haka yayi musu sallama ya shiga mota ya nufi gidan su Aishan. Duk da bai san me zai je yayi ba amma dai yana jin gara yayiwa iyayenta bayani don yana kyauta zaton zasu goya masa baya.
UWAR SADDIKU
Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)
44
Tun a wannan daren Hajiya ta kirawo Abubakar ta sanar da shi ga Aisha a gida don haka gobe yazo da safe don a sami mafita. Suna ajiye waya ta kirawo Baffa, bayan tayi masa bayani yace to shima da safen zai zo don bai kamata a bari ta sake kwana ba ba tare an bi diddigin abun ba.
Ko da gari ya waye da yake Baffa ya saba sammako tun kafin su gama karin kumallo ya iso gidan, Anti Uwani ta zubo masa dafadukan taliya da kunun tsamiya. Ya sanar da ita ya riga ya ci abinci kafin ya fito sai kunun kawai ya debi rabin kofin ya zauna a falon yana sha yana jiran isowar Abubakar don yace ya fi so ayi a gabansa.
Wajen karfe takwas da kwata shima Abubakar din ya iso. Nan suka hadu a falon Hajiya da ita Hajiyan, Anti Uwani, Baffa da kuma Yaya Abubakar. Har Hajiya ta fara yiwo bayanin abinda ya kawo Aishan gidan Baffa yace
'Ai bari zakiyi Hajiya ta fito Aishatun muji daga bakinta, ta hakane idan ma bata da gaskiya da izinin Allah zan ganeta.’
Nan Anti Uwani ta mike ta shiga daki ta kirawo Aishan.
Ko Hajiya bata fito ta yiwa ina kwana ba saboda tsoron abinda zata cewa Hajiyan sai a lokacin ne ta gaisheta ta gaida su Baffa ma. Bayan ya amsa gaisuwarta yace
'Shatu ba fa na son rigima da rashin gaskiya. Me ya hadaku da mijinki har kika taho gida tun jiya, gashi ko sawunki bai biyo ba kinga da alama kenan akwai abinda kika yi masa?’
Ta sunkuyar da kai murya kasa-kasa tace
'Babu abinda nayi masa Baffa, shi yace idan na cigaba da zama zaman kaina nakeyi shine na taho.’
'Assha! Akwai abinda kika yi din kenan in ba haka ba me ya kawo wannan maganar?’
Tayi shiru tana tunanin ta inda zara fara. Jimawa kadan Yaya Abubakar yace
'Dake ake magana kina ji kin yiwa mutane shiru.’
Baffa ya daga masa hannu alamar yayi shiru, sannan ya dubi Aishan yace
'Ina sauraronki Aishatu, me ya kawo har yace miki zaman kanki kikeyi? Kuma me yasa baki bashi hakuri ba kika taho?’
Ta kasa bude bakinta don haka Anti Uwani ta karanto masa bayanin abinda Aishan ta gaya mata da ta zo. Kafin Baffan yace wani Abu Yaya Abubakar yace
'Ahaf! Ai wallahi na san akwai abinda tayi masa. Wannan shegen taurin kan nata ne ya tashi shi yasa take so ta kashe aurenta.’
Cikin muryar lallashi Baffa yace
'Aure kam ba zai mutu ba da izinin Allah, Aishatu me yasa ba zaki zauna masa da duka yaran ba? Wannan ai abu ne ma wanda ba sai kin jira ya nema ba. Haka aka saba ko rabuwar aure aka samu matar da take gidan ita take hada kan yaran ta rike, balle wadannan marayun. Kinga lada biyu zaki samu,ga ladan kula da marayu ga ladan biyayyar miji.’
Tayi gyaran murya ta korowa Baffa bayanin irin abubuwan da Yusran take yi mata tun daga farkon zamanta har zuwa maganganun data gaya mata ranar sadakar uku da kuma bangazarta da tayi a falon gidan. Tace
'Wallahi Baffa ba zata bari mu zauna lafiya da shi ba, duk wani abu da uwarta ta dinga yi min na cutarwa cigaba kawai zatayi kuma gashi nan ta fara. Shekararta kusan ashirin Baffa, ko ni na haifeta ta kai yanzu ba lallai tayi yanda nake so ba balle ta riga ta shirya cewa ni makiyarta ce. Ba wai ina tsoron abinda zata yi min bane amma ina tsoron kada ta kureni nima nace zan rama tunda yara da yawa da matan uba suke cutarwa wasu ai da akwai irin hakan a ciki don dai kawai ba za a sauraresu bane.’
Sukayi shiru gaba daya kowa da abinda yake tunani. Har Baffa ya bude baki zai yi magana Hajiya ta riga shi
'Kaji fa Baffa! Ka ga wannan ai abune wanda za a kirawo Yusufan in ya so ya tsawatarwa ‘yarsa ta bari a zauna lafiya tunda kuma ai shima yana cikin gidan.’
Cikin nutsuwa Baffan yace
'Eh da wannan. To amma fa kin ji bayaninta, kuma duk muna nan yarinyar nan ta kwashe fiye da shekara tana zaman kan nata babu miji wanda kowa ya san sihiri ne shiru kawai mukayi don a zauna lafiya. Sanna kuma ga furucin yarinyar nan wanda ana halin zaman makokin uwarta tayi. Kuma tabbas yaron da aka bawa sabulu ya dinga zuba maka a abinci don kaci idan ka bata masa rai wataran zai saka maka guba kaci ka mutu don ya huta.
‘Kin gani ko Anti Uwani! Babu wanda ya damu da rayuwata kowa kawai na yiwa miji biyayya na rike masa yara. Yarinyar nan ba zata canza ba wallahi saboda kamar karatu uwarta ta dinga biya mata kiyayyata, duk wata tsawatarwa ba zata yi mata amfani ba. A karshe kuma duk abinda ya faru da ubanta da duk masu kallo cewa za ayi nice da laifi in cutar marayu. Ba zan iya rayuwa cikin kunci ba.’
Haka Anti Uwani ta dauki lokaci tana bata hakuri tana jaddada mata ta cigaba da addu'a komai zai tafi dai-dai.
Gaba daya wunin ranar Hajiya da Anti Uwani basu kula juna ba saboda sun kasa fahimtar juna; ita Anti Uwani tana goyon bayan lallai tunda Aisha tace ba zata zauna da Yusra ba ya kamata a kyaleta tunda har ta fadi wannan matsalar don ita ta san irin wadannan mutanen basa canzawa. Yayinda ita kuma Hajiya take ganin haka akeyi don haka itama Aishan hakuri zatayi taje ta zauna.
….
Hajiya da su Farha suna zaune a falo lokacin wajen karfe tara saura aka kwankwasa kofar. Abdallah ne ya fita don ya duba, nan da nan ya dawo ya sanar da Hajiya Abban su Yusra ne. Ta bashi umarni yaje ya bude kofa ya shigo da shi falon. Kafin su shigo ita da Farha sun tattara kwanukansu Hajiya ta yafa mayafinta. Cikin girmamawa suka gaisa da Hajiya inda ta sanar dashi sakon Baffa, ya tabbatar mata da cewa da ya fita zai kirawo Abubakar ya sanar da shi gobe da safe sai su hadu a gidan Baffan. Tayi masa sallama ta shige daki bayan ta sanar da Aishan ta fito yana jiranta a falo.
Sai da ta gama gunguninta sannan Anti Uwani ta korota daga dakin ta fito. Nesa da shi ta zauna akan kujerar zaman mutum daya ba tare da ta ce masa komai ba kuma ba tare da ta kalleshi ba. Shine ya gaji da shirun yace
'Aisha shine kika taho ba tare da kin sanar da ni ba?’
Ta kalleshi ta dauke kai, tace
‘Saboda na san bai kamata nayi zaman kaina ba shi yasa na taho don su shiga maganar.’
'To ai idan dai Yusra ce kin san ba zan barta ta raina ki ba, kuma Yusra ma ai macece kamar ke ko yanzu Allah ya fito mata da miji aure za ayi mata itama ta tafi gidanta. Kinga ai an rabu lafiya ko?’
'Uhm! Ai zan koma, idan kuka gama magana da Baffa in sha Allah zan koma.’
Bai san me zai ce mata ba gashi dare yana kara yi, amma dai tunda tace zata koma idan sun gama magana da Baffa kuma baya jin zasu kasa fahimtar juna da Baffa, don haka yayi mata sallama ya tafi. Tun kafin ya isa gida ya kirawo Yaya Abubakar ya sanar da shi gobe zaizo, suka tsayar da lokaci a kan karfe sha daya da rabi su hadu a gidan Baffan. Sai da ya sanar da Yaya Bello domin tare zasu je gidan Baffan sannan ya karasa gidan.
__
Kamar kullum haka ya tashi ya tsaya a kan yaran har suka tafi tahfiz, ya zama gidan daga Saddiku sai Yusra da Jummai wanda take aiyukanta. Da yake lokacin karfe takwas ne da safe sai kawai ya koma daki ya dauki computer dinsa ya fara aiki.
Wajen karfe tara saura yana nan yana aikinsa Saddiku ya shigo da sallama, bayan ya amsa sallamarsa ya nuna masa gefen gadon ya zauna. Ya mika masa kudi yace
'Abba ga wannan, dubu goma sha biyu ne yanzu Anti Jamila kawar Mommy ta kawo. Tace wai cikon kudin Mommy ne na leshi.’
Ya karba ya jiye yana fadin
'Leshi? Tun yaushe sukayi cinikin don na ga Mommyn ta dade fa bata sayar da kaya ba?’
'Ai inaga Abba kudin nan fa ya fi shekara don Mommy din da kanta ta dade tana mitar bata cika mata kudinta ba.’
Ya tabe baki
'Allah ya sauwake. Ta ma yi imani da ta kawo yanzun.’
Sukayi shiru na dan lokaci, jim kadan Saddikun yace
'Abba ina ga fa a duba wayarta musamman ta Whatsapp za a sami ragowar wadanda take bi bashi, kuma ita din ma babu mamaki wasu kawayena nata suna binta bashi.’
Ya ajiye computer dinsa a kan durowar gadon yana fadin
'Hakane. Ka san tun ranar da ta rasu da na karbi wayar na ajiye gaba daya na manta ma ban sake bi ta kanta ba. Bari yanzu ma sai na fara dubawa in sha Allah zuwa yamma sai a tattara wadanda take bi da wadanda suke binta. Akwai ma kawarta Amina ina jin itama za a samu wasu bayanan a wajenta.’
Ya mike ya matsa gaban durowarsa wadda yake ajiye litattafai a kai yayinda Saddiku ya fice daga dakin don dama wanka zai shiga a lokacin da Jamilan ta shigo kawo kudin.
Ya san inda ya ajiye wayar don haka ba tare da bata lokaci ba ya dauko ya kunna sannan ya dawo ya zauna a gefen gadon.
Chajin wayar bashi da yawa sosai amma dai yana ganin zai isheshi ya duba abinda yake son dubawa. Ya kunna data dinta ya ajiye wayar don sabbin sakonninta su gama shigowa. Bayan kamar minti biyar ya dauki wayar ya budo Whatsapp ya fara bin sakonnin da bata buda ba wadanda yawancinsu ma bayan ta rasu aka turo su. Duk sakonnin sunayen mata ne don haka duk wanda ya bude ya duba sakonnin karshe yaga hirarrakinsu ne sai ya mayar ya rufe. Wasu sakonnin kuma na groups ne don haka su tsallakesu ma ya dinga yi.
Aminoni aka saka a kan sunanta kuma yana gani ya san Amina ce don ya san Zahra tana kiranta da hakan. Ya bude sakon; maganarsu ta karshe hoton rasit me wanda Zahran ta turawa account din Amina kudi kusan dubu dari uku da sako a kasan hoton an rubuta ‘na turo kawata'.
Mamaki ya kama shi; to kudin menene wannan da Zahran ta turawa Amina har dubu dari biyu da saba'in? Ya duba sakon da yake samanshi wanda voice note ne da Zahran ta turawa Amina, ya bude ya fara sauraro kamar haka:
'Kawata na kasa hada 300k din nan amma gaskiya gara muje haka, zan turo miki abinda na hada. Na gaji da yarinyar nan wallahi, so nake duk ma yanda za ayi a datse wannan auren. Shi kanshi Abban na su so nake ya dawo hannuna kamar da don yanzu baki ga wulakancin da yake min ba.’
Ya sake shiga mamaki da damuwa a lokaci guda, ya cigaba da bin sakonnin yana budewa har dai ya fahimci cewa magana sukeyi a kan Zahra tana so a kashe aurensa da Aisha. Tafiya kawai yake yana bude sakonnin yana saurara yana yin sama. Har ya zo kan wani sakon yana budewa ya fara saurara kamar haka:
‘Kawata sai kiranki nake baki daga ba, wallahi aiki ya karye don yau ya tuna da matarsa, kin ganshi can yana ta rawar jiki ya tafi wai a can zai kwana. Ki kirani don Allah mu san abun yi.’
Kwanan watan ranar da ta tura wannan sakon ya kalla ya tabbatar lallai ranar da ya koma gidan Aisha ne bayan ya dauki dogon lokaci bai je ba. Duk wani haufi da yake dashi a kan cewa Zahra tsafi tayi masa ya manta da Aisha yanzu ya kau, kuma ya tabbatar warin da ya dinga ji a gidan Aishan ma itace.
'Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun.’
Ya fada a fili yayinda ya share gumin da ya karyo masa; yana da wannan zargin a kan Zahra amma ya so ace abun ya tsaya a zargi sai dai ya makara. To me yayiwa Zahra haka har ta dinga kokarin cutar da shi da matarsa, ta sayar da imanin ta. Gashi sakonnin sun nuna har ta mutu tana da niyyar ta je ta sake yi masa wani tsafin. Ya fita daga sakon Aminan ya sake biyowa sakonnin da bai bude ba wadanda yawanci na group ne.
'Yaron Malam.'
Ya fada a fili a daidai lokacin da yazo kan sakonnin. To wanene kuma Yaron Mallam? Bai taba jin sunan ba balle yace ko a dangin Zahran ne, to wanene shi? Ya bude sakonnin wadanda sun kai kamar guda goma, na karshensu bayan kwana biyu da rasuwarta ne aka turo. Duka voice note ne don haka ya bude na karshen ya saurara kamar haka
“Hajiya Zara ina ta kiranki kwana biyu shiru. Na dawo daga tafiyar da nayi kuma na sami sa a. Don yanzu haka na shirya wani aiki da zan yi miki wannan abokiyar zaman naki sai ta bar miki gidan nan idan ba haka ba kuma zata hadu da jinya wadda ba zata warkeba; kin san kuwa namiji baya son doguwar jinya dole ya mayar da ita gidansu. Kuma shi din ma za a saka miki shi a kwalba. Sai dai kawai nace ki taho da kudi don gaskiya aikin mai tsada ne.”
‘Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun!’
Ya fada a fili yayinda ya mike kamar wanda aka tsikara; lallai Zahra ta tabbata azzaluma! To kashe Aishan take son yi kenan!
“Shi din ma za a saka miki shi a kwalba!”
Kalmar da kwakwalwarsa ta dinga maimaita masa kenan.
Tabbas da ba don Allah ya karbi rayuwar Zahra a daidai wannan lokacin ba da yanzu bai san halin da suke ciki ba shi da Aishan. Don yaji inda aka ambaci yaron Malam a hirarsu da Amina kuma yana zargin ko ba wajen yaron Malam din zasu je ba to tabbas kudin da ta turawa Amina na zuwa wajen wani matsafin ne. Ya lalubo sunan ‘yan uwanta Murja da Suwaiba ya duba hirarrakinsu, sai dai a nan bai sami wani abu da yake da alaka da zantukan da tayi da Amina ba. Ya cigaba da kaiwa da kawowa a dakin yana tunanin da mamakin yanda Zahra ta dade tana cutar dashi.
Kwankwasa masa kofar da akayi ne ya dawo da shi hayyacinsa, yace
'Shigo.'
Saddiku ne ya bude ya shigo ya dubi Abban da alamar tambaya a fuskarsa sai kuma yace
'Abba Anti Murja ce suka zo ita da Anti Suwaiba.'
Ya dafe kai yace
'Subhanallah! Ka ga na manta tun last week suka sanar min zasu zo yau din. Gani nan zuwa.’
Saddiku ya fice ya rufe masa kofa.
Ya koma ya zauna a gefen gadon ya dafe kai; gaba daya ya manta tun wancan satin Murja ta kirawoshi ta sanara da shi zasu zo ranar Lahadi su bude dakin Zahra su kwashe kayanta na sawa. Ya amsa musu don shima yana so su kwashe kayan, don shi ya ce har gadon Yaya Murja ta kwashe su sa a kasuwa sai su kawo kudin a rabawa yara shi ya yafe; fenti yake son yiwa gidan gaba daya kafin Aisha ta shiga dakin.
Ya kashe wayar cike da damuwa ya