Showing 141001 words to 144000 words out of 166068 words
sanar da shi kada ya rufe gidan don yanzu zai dawo sannan ya fita.
Gidan Aisha ya nufa; tun ranar da akayi rasuwar rabon da ya shiga gidan nata; sai dai kawai yana ganinta a gidan Zahra. Yau ne kawai zai ce bai ganta a gidan ba.
Da sallama ya shiga falon, tana zauna a kan kujerar zaman mutum uku da waya a hannunta yayinda TV take kunne. Bayan tayi masa sannu da zuwa ya zauna, ta wuce kicin ta dauko masa ruwan sanyi. Ta zuba masa ruwan a kofi sannan ta zauna a gefensa.
Suka gaisa ta sake yi masa gaisuwa; bayan ya amsa tace
'Ya yaran?’
Cike da damuwa yace
‘Alhamdulillah. Yau ban ji ki a cikin gidan ba.’
Ta kawar da kai tana dan gatsina fuska tace
‘Kaina ne yake ta ciwo tun asuba, shi yasa tun safe da na shiga na ga basa bukatar komai na dawo na dan kwanta.’
Suka yi shiru gaba dayansu kowa da abinda yake ransa.
Ba wai ciwon kai ne ya hanata zama a gidan ba; ta dai gaji ne da yanda Yusra take yar mata da maganganu tana kokarin sai ta tsokaneta sun yi fada. Tunda Yaya Murja ta tafi Yusran ta daina raga mata sai dai idan bata shiga gidan ba, dama kuma ko da ana zaman makokin ma tana kula da yanda Yusra da Nana basa gaisheta sai dai idan ita ta yi musu gaisuwa. Don haka ma ita a yanda ta shiga yau da safen ta yanke ba zata sake shiga ba sai an kwana biyu.
Abban ne ya mika hannunsa ya shafi kumatunta yana murmushi yace
'To tunanin ya isa haka.’
Tayi ‘yar dariya ta matsa jikinsa ta zauna, ta kwantar da kanta a kan kafadarsa. Suka sake yin shiru na dan lokaci, basu jima ba Abban ya kirawo sunanta. Ta daga fuskarta daga kafadarsa ta kalleshi tana murmushi, da ya tabbatar ya sami hankalinta sai ya cigaba
'Jibi in Allah ya kai mu za ayi kwana bakwai, kuma a ranar zan koma aiki. Zan sa a gyara miki daki a can gidan zuwa next week sai ki koma. Kin ga daman saura wata uku kudin hayar gidan nan ya kare sai na basu gidansu.’
Duk da ta san zai yi wannan maganar amma sai da maganar ta shammaceta. Ta dan jijjiga kai domin ta kore damuwar da ta lullubeta, ta lalubo muryarta ta hanyar yin gyaran murya sannan ta muskuta kadan da fuskanceshi tace
'A dai dan kara lokacin ba nextweek ba don na dan kara shiryawa.’
'Babu damuwa take your time. Ai ba lallai sai kin kwashe kayanki gaba daya ba a lokaci guda. Idan aka gyara dakin; wanda shima temporary ne kinga sai ki kwashi iya kayan bukatarki a hankali a kwashe sauran. Kafin nan ma kin ga an gama gyara miki daki a saman.’
'Uhm, hakane. In sha Allah in na shirya zan maka magana.’
'Yauwa. Ki dai shirya da wuri don kin ga Goggo Binta jibi zata tafi, ba zai yiwu a bar yaran su kadai babu Babba a gida ba tunda nima ranar zan koma aiki.’
Suka dan taba hira wadda duk yawanci shi kadai yake zancensa, daga baya yayi mata sallama ya koma wajen yaran.
Yana fita ta bi bayansa ta rufe gidan ta dawo ta kintsa tayi shaf'i da witri, ta gyara zama a kan daddumar. Ta daga hannunta ta karanto ayatul kursiyyu da sauran azkar, ta bude baki zata roki Allah amman ta rasa yanda zata jera kalmominta. Sai da ta gaji da rike hannunta a sama ba tare da ta samo kalmomin ba don haka cikin damuwa ta karanto ‘Rabbi inni lima anzaltu ilaiya min khairin fakeer'.
Ta sauke hannuwanta cike da damuwa da kuma saka rai cewa Allah ba zai jarrabeta da abinda ba zata iya ba. Ya za ayi ta koma wannan gidan? Ba gidan take tsoro ba amma ba zata iya zama da Yusra ba. A zamanta da Uwar Yusra; duk da sai su kusan shekara basu hadu ba; amma sharrin uwarta bai barta tayi zaman aure cikin nutsuwa ba to yanzu me zai faru idan ta fara zama da Yusra? Yarinyar da ta tare ta ido na ganin ido ta gaya mata ba zata barta ta zauna lafiya ba. Gaskiya ba zata iya zama da Yusra ba. Bata san da yaren da zata gayawa Abba cewa ba zata koma gidan ba domin abu ne da aka saba, sannan kuma bata san dalilin da zata bashi na kin komawar ba. Tabbas da ace babu Yusra da Nana to zata koma ta rike masa ragowar yaran; duk da cewa tana sane da halin ko in kula din da shi yake da nata yaran wadanda ubansu ya mutu tun kafin uwar yaransa ta mutu.
Ta san ba zai taba iya yi mata adalci ba tsakaninta da yaransa domin ta gani a gidaje da dama, duk wanda ya tashi cewa zai yi tana cutar marayu. Bata so ta zama silar raba da da uba don haka tana ganin idan aka takura ita kam sai dai ta hakura da wannan auren; tunda ma zuwa yanzu babu wata riba da zata iya nunawa tace ta ci da wannan auren. Haka ta kwanta cikin damuwa saboda abu daya ta sani ba zata iya zama da Yusra a sami zaman lafiya ba.
—-----
Washegari ranar Lahadi haka ta wuni zuciyarta babu sukuni saboda waccan maganar da take mata yawo a rai. Ta so ace ta je islamiyya da ta tambayi malamarasu ko akwai wani hadisi ko aya da zasu sa dole ta rike masa yaran da ba ita ta haifa ba, amma saboda rasuwar ta bari sai wani satin zata koma islamiyya.
Tuk kafin azahar Abban ya kirawota ya sanar da ita ta ajiye masa abincin rana don haka nan da nan ta dafa taliya da miyar kifi ta jera a table, sannan ta hada zobo ta saka a fridge.
Sai wajen karfe uku ya shigo, yana shigowa ta sa masa abincin. Sai da yaci ya koshi don kusan tunda akayi rasuwar nan bai zauna ya ci abinci ya koshi ba sai yanzu. Da aka kirawo sallar la'asar ya fita masallaci, bayan ya dawo yace mata zai yi bacci ne kada a tasheshi. Yana shirin shigewa dakin tayi gyaran murya tace
‘'Nima ina son zuwa gidan Hajiya, ko naje in ya so sai na dawo kafin magriba?’
'Eh, sai kin dawo. Lafiya Hajiyan take dai ko?’
'Lafiya kalau, na ga su Yaya Zainab ne kawai suka zo gaisuwa babu ita duk da na san gwiwarta tana ciwo amma dai munyi waya da ita. Ina so dai naje na gani.’
'To babu laifi, ki gaishe min da ita da su Abdallah.’
Ya shige dakin yayinda ita kuma ta mike ta shige nata dakin domin ta shirya.
……..
Tana shiga gidan Hajiya ta tarar da Anti Uwani da Zahida suna zaune a falo suna hira. Bayan sun gaisa ta dubi Zahida tace
'Ke kuma me kike a gidan mutane da yamman nan?’
Tayi dariya
'Ke zan tambaya, ku da kuke zaman makoki.’
'Hmmn! Ai an share makokin ma. Ina Hajiya da yaran na ji shiru?’
Anti Uwani tace
'Hajiya tana daki, inaga bata idar da azkar ba shi yasa bata fito ba. Yaran kuma Abban Afra ne ya fita dasu wai zasu je sayen kaya za ayi kaltaran menene a makaranta.’
Zahida tayi dariya tace
'Cultural day fa ake cewa Anti Uwani.'
Ta kawar da kai tace
'Oho duk daya.’
Ta juya wajen Aisha tace
'Ya marayun ‘yayan naki? Kuna lafiya ko?’
‘Lafiya Alhamdulillah.’
Jimawa kadan ta mike ta shiga daki wajen Hajiya.
A zaune ta sameta a kan dadduma da kafafunta a mike, bayan sun gaisa tayi mata ya jiki suka dan taba hira sannan ta taso ta dawo falon. Bata dade da zama ba Anti Uwani ta tashi ta shige dakin da Hajiya take.
Anti Uwani tana shigewa Zahida ta taso ta dawo kusa da Aisha, tana zama Aishan ta dubeta tace
'Kin shako gulma kenan bakinki yake motsi.’
Ta zumbura baki tace
'Oh ni, wai na sake jajanta miki rasuwar yayarki.’
‘Sai dai yayarki ba ni ba.’
Sukayi shiru na dan lokaci, jimawa kadan Aishan cikin murya me dauke da damuwa tace
'Hida kin san me Abban Sadik yace?’
Ta dan zaro ido ta gyara zama tace
'Me yace?’
'Wai na tashi daga gidan da nake na koma gidan Zahra saboda yara.’
Da mamaki Zahida tace
'To da me kike tunani? Ai ko wanene ma haka zai yi tunda kinga wancan nasa ne kuma yanzu bashi da wata mata a ciki.’
'Hmm! Baki gane ba Zahida. Nifa ba zan iya zama da yaransa ba gaskiya, ba wai ina nufin dukansu ba a'a. Idan aka dauke Yusra da Nana to bani da matsala da sauran yaran. Amma ba zan iya zama da Yusra ba, ke ko gwadawa ma ba zan yi ba sai dai ayi min duk abinda za ayi Amma ba zan zauna da Yusra ba.’
Mamakin Zahida ya karu, tace
'Yusran wai zata kai shekara nawa ne da kike tsoronta har haka?’
‘Sha takwas ne idan tayi yawa sha tara. Ba wai tsoronta nake ji ba amma Zahida yarinyar nan tabbas idan ta sami dama zata iya poisoning dina na mutu. Ko bata kashe ni ba kuma ba zata taba bari mu zauna lafiya da ubanta ba, nutsuwar da yake son samu ba zai samu ba. Kinga kuma duk abinda ya faru da shi da duk masu kallo cewa za ayi ina musgunawa marayu.’
Sukayi shiru na dan lokaci, jimawa kadan Aishan ta cigaba
'Zahida kin san dai tunda na auri mutumin nan uwar Yusra bata barni na yi rayuwar aure ta shekara daya ba tare da wata matsala ba ko, to wallahi wannan yarinyar ta fi uwarta sharri. Kuma da bakinta ta tare ni ta gaya min ba zata taba bari na zauna lafiya ba muddin na tare a gidansu. To ba wai ina jin tsoron abinda zata yi bane ina jin tsoron kada ta kureni na ce zan rama don ramuwar tawa ba zatayi kyau ba, gara kawai kar a fara.’
'To yanzu ya zaki yi? Tunda dai shi ga abinda yace.’
'Ban sani ba Zahida, don ban ma gaya masa ba zan koma ba. Ce masa kawai nayi sai ma gama shiryawa, amma tabbas ba zan zauna da Yusra ba.’
'Ai kuwa akwai rigima tunda dai kin san ko sakin uwarsu yayi kece zaki rike yaran nan balle mutuwa tayi.’
Aisha ta dan zaro ido ta gatsina baki tace
'To wa ya dora min? Ai babu inda Allah yace dole sai na rike masa yaran da bani na haifa masa ba don kawai Ina aurensa. Don haka sai dai ayi duk wacce za ayi.’
Zahida ta jijjiga kai tace
'Ai kuwa akwai rigima.’
A dai-dai nan Abdul da Farha suka shigo tare da Abban Afra suna rike da ledodi. Nan suka zube kayan suna nunawa mamansu yayinda shi kuma Abban Afra ya sanar da Zahida ta gayawa Hajiya zasu tafi.
Ba tare da bata lokaci ba Hajiyan ta fito tare da Anti Uwani suka yi musu sallama suka tafi. Suna fita itama Aisha ta mike tana shirin tafiya, Hajiya tace
'Au dama lekomu kawai kikayi? Ba dadewa zakiyi ba.’
'Wallahi Hajiya gani nayi baki sami zuwa gaisuwa ba shine nace bari na zo na duba kafar, ko abincin dare ma ban yi ba.’
‘Ga kafa nan dai yanda kika barta. Gara kam ki tafi tunda yanzu gida ya zama ke da yara kar ki dinga lattin abinci.’
Tayi musu sallama ta fice, tana tunanin maganar Hajiya. Wato su sun ma zata ta tare da yaran ne ko me, don taga kowa maganar yaran kawai yake mata kamar yanzu itace uwarsu.
Tana shiga gidan aka fara kiran Magriba, ta leka dakin Abban ta hangoshi yana nan yana bacci. Don haka ta karasa ta tasheshi saboda magriba. Tana yin Sallah ta fada kicin, nan da nan ta tuka tuwon semovita miyar kuka wadda ta sha busasshen kifi da nama. Ta hada ta ajiye a kan table sannan ta shiga wanka.
Bayan ta gama abinda takeyi ta dawo falo ta zauna tana jiransa. Karfe tara saura ta kalli agogon, har yanzu bai shigo ba? To ko ba zai ci abincin bane? Ta sake kallon wayarta sannan ta mayar da ita ta ajiye. Bata son ta kirawoshi domin bai saba ce mata zai dawo ya saba ba, ta san ba lallai ya kwana a wajenta ba domin tunda akayi rasuwar a can yake kwana kuma bata da matsala da hakan amma dai ta kasa gane dalilin da zai sakata ta dafa abinci kuma yaki zuwa. Har ta gaji da karatun wasikar jaki bai shigo ba don haka ta zuba abincinta ta fara ci.
Ko rabin abincin bata ci ba ta jiyo motsinsa a gate, ba tare da bata lokaci ba ya shigo falon da sallama. Bayan ya amsa sannu da zuwanta ya dubeta yana murmushi yace
'An gaji da jirana ko?’
Ta yi gajeran murmushi
'Yunwa nake ji shi yasa.’
Ta fara kokarin mikewa ya dakatar da ita yayinda ya ajiye wayar hannunsa da mukullai a kan kujera ya nufi dining table yana fadin
‘Yi zamanki ki gama zan zubo abincin, nima yunwa nake ji.’
Ta cigaba da cin abincinta yayinda shima ya zubo abincin a faranti ya dawo inda take ya zauna suna ci suna hira. Bayan sun gama cin abincin ta hada kwanukan ta kwashe sannan ta kawo masa shayi, ta zauna suka cigaba da hira.
Wajen sha daya saura ta mike tana hamma tace
'Ni kam bari naje na kwanta idan zaka fita kayi min magana wallahi bacci nake ji.’
Ba tare da ya kalleta ba yace
'A nan zan kwana ai, nima yanzu zan shigo.’
Da mamaki tace
'Yaran fa?’
'Ai Goggo Binta tana nan, sai jibi ne zata tafi. Ina tunanin ma na lallabata ta kara mana ko sati ne kafin nan kin gama shiryawa tunda kin ga idan tace dole jibi zata tafi to fa ko baki shirya ba dole ki koma can din in ya so a dinga kwashe kayan a hankali.’
Tace
'Uhm! To sai ka shigo.’
Ta shige dakin ta barshi a zaune.
Haka ta karasa shiryawa cikin sanyin jiki domin idan aka ce jibi zata koma gidan Zahra to tabbas akwai rigima don ba zata koma ba. Gashi ta rasa da kalaman da zata yi masa bayanin cewa ba zata koma ba don ta san ba zai fahimceta ba; a halin yanzu ma bata jin akwai wanda zai fahimceta. A iya shekarun da tayi a rayuwa ta ga matan aure da dama wadanda yaran miji ke hanasu zaman aure wadanda ba a taba yi musu adalci, bata jin nata labarin zai babanta. Wani lokacin sai taji kamar ta koma ta fara zama da su ta gani ko zaman zai yiwu, amma zuciyarta tana tuna mata idan ta fara sai ta fi shan wahalar bari don haka gara ma kawai kada ta fara.
Tana nan kwance tana karanta wasikar jaki ya shiga dakin ya sameta. Ba tare da wani bata lokaci ba ya shirya ya cimmata a kan gadon, lokacin har ta fara gyangyadi. Sai dai da yake ta san bukatar da ta kawoshi kuma ita din ma tayi kewarsa haka ta biye masa suna raba dare suna biyan bashi.
_
Tun kafin Abban ya sanar da Aisha zata koma gidan Zahra ya sanar da Jummai. Ya bata umarni a fitar da duk wasu kayan da suke dakin Saddiku ya kwashe ya kai gareji a gyara dakin don nan Aisha zata zauna kafin a gyara mata daki a sama. Nan da nan ba tare da bata lokaci da ta shiga aiki.
Tunda Rukayya taji wannan labarin ta kasa boye murnar ta, do da kanta ta dinga taya Jummai fitar da kayan dakin nan har aka gama. Yusra tana kallonsu tana kwafa musamman ya da taga Rukayyan tana ta rawar jiki.
Ranar litinin wadda tayi dai-dai da kwana shida da mutuwa ranar Abba ya umarci yara da suyi hakuri su koma makaranta. Musamman Aisha ta tashi da safe ta dafa musu abincin makaranta sannan tayiwa Abban waya ya turo Rukayya ta daukar musu. Haka ta zuzzuba musu kowa ya dauki nasa in banda Nana wadda tace ita indomie zata dafa.
Tun wuri Yusra ta dawo daga tata makarantar don haka ko da sauran yaran suka dawo wajen karfe biyu da rabi a gidan suka sameta. Bayan sun ci abinci Jummai ta taimakawa Nana, Ummi da Sumayya suka shirya suka wuce islamiyya. Basu dade da fita ba Rukayya ta shiga dakinsu na kasa inda ta sami Yusra a kashingide a kan gadonsu tana chatting a waya. Kai tsaye ta nufi wajen da ta ajiye jakar makarantar ta ta bude ta fara zaro littafanta. Yusra ta dubeta tace
'Ke bazaki islamiyyar bane?’
Ba tare da ta dubeta ba tace
'Eh, sai next week idan mun gama CA test a makarantar, yanzu ma karatu zan je nayi a gidan Anti sai dare zan dawo.’
Yusran ta tashi zaune a kan gadon a dai-dai lokacin da Rukayyan ta mayar da jakar ta rufe ta mike da litattafai a hannunta tana shirin ficewa daga dakin.
Yusran tace
'Kuma karatun ne ba zaki iya yi a nan ba duk fadin gidan nan dole sai kin je gidan da aka hanaki zuwa.’
Cikin halin ko in kula tace
'Eh, a can zan yi karatun sai dare zan dawo.’
'Lallai! Wato ke tun kafin ma Mommy ta kwana bakwai da barin duniya har kin fara karya dokokin da ta kafa miki ko, kamar daman jira kikeyi ta mutu ki koma inda ta hanaki zuwa.’
Cak ta tsaya a inda take ta juyo ta kalli Yusran yayinda idanuwanta suka cicciko da kwalla; kalaman yayar tata sun yi matukar yi mata ciwo a zuciya sai dai bata da wata amsa da zata iya bata. Ta ja hijabin jikinta ta goge kwallar da ta fado fuskarta ta juya ba tare da ta ce komai ba ta fice daga dakin. Tana fita ta tsaya a bayan kofar ta rasa me zata yi; tafiya zata yi kamar yanda tayi niyya ko kuwa ta hakura ta zauna a nan tayi karatun? Sai dai ta san idan ta zauna a gidan to da zarar Sumayya ta dawo daga islamiyya karatun ya kare. Domin a wajenta take zama kuma ko me take bukata haka Yusra zata ce taje Rukayya tayi mata.
Ta share hawayenta ta wuce tsakar gida inda ta jiyo motsin Goggo Binta da Jummai, ta sanar da su ta tafi gidan Anti Aisha sannan ta wuce cike da damuwa.
………
Yanda Aishan ta ganta cikin damuwa