Showing 9001 words to 12000 words out of 166068 words

Chapter 4 - UWAR SADIKU COMPLT BY SAKINA YAZID.txt

11 Jul 2024

25384

kawai; kamata yayi taje gidan duk da ta san ba lallai Yaya Murja ta barta tayi yanda take so ba amma dai tana son ganinta.


Matsalarta daya bata gayawa Abban Sadik zata fita ba don da ta gaya masa zaice Sale direba ya dawo ya kaita.


Nan ta yanke shawara sauri zatayi taje ta dawo don idan ta gaya masa ya san me zata je yi gara kawai ta tafi in ya so tayi sauri ta dawo kawai.

Nan da nan ta mike, ta saka hijabi ta dau jakarta da wayarta. Har ta zo falo ta tsaya ta saka karamar jakarta a cikin hijabin ta mayar ta saki hijabinta. Ta rufo kofar falon ta nufi gate, tana daf da fita Bala megadi ya fito daga bayan gidan inda yake bawa fulawowi ruwa, yana ganinta ya karaso da gudu yana rage tsawo

‘Hajiya barka da fitowa.’

‘Yauwa Malam Bala, na shiga nan gidan Umman Haidar duk wanda yazo nemana kace ayi min waya sai na fito kawai.’

‘To Hajiya a dawo lafiya.’

Ta amsa ta wuce Malam Bala ya mayar da gate ya rufe.

Saida tayi nisa da gidan sannan ta tsaya ta hau mota, dayake shata ta dauka kai tsaye aka wuce da ita har gidan Yaya Murja.


Bayan sun gaisa da megadin da ya bude mata kofa ta wuce ta nufi cikin gidan.

Shafa’atu ce a falon wato abokiyar zaman Yaya Murja din wadda suke kira Anti Shafa; tana zaune tana bawa Arif abinci. Bayan tayi mata sannu da zuwa suka gaisa, kafin ma ta tambayeta tace

‘Umman tana samanta.’

Nan da nan kuwa ta wuce saman inda nan ne wajen Yaya Murja din wadda itace uwargida.

A falo ta sameta a kwance a kan doguwar kujera, ta kunna TV tashar Zee World yayinda take ta faman dube dube a wayarta.

Ta shiga da sallama, Yaya Murja ta amsa sallamarta yayinda ta tashi zaune. Ta karasa ta zauna kusa da ita.

‘Ikon Allah, daga ina haka babu notice ko wani wajen kika zo kika biyo.’

Yaya Murjan ta tambaya tana mamaki.

Ta danyi yake tace

‘A’a nan kawai na zo Yaya.’

Suka gaisa Yaya Murja ta tambayi lafiyar yaran. Ta dubi Zahra tace

‘Lafiya kuwa? na ga kamar da damuwa a fuskarki.’

Ta kawar da kai tana jijjiga kai, ta sake dubanta suka hada ido tace

‘Yaya wai aure Abban Sadik zai yi.’

Tayi ‘yar dariya tana tafa cinyar Zahra

‘Shine duk kika birkice haka? To ai naga ba yau ya fara maganar auren ba ko? Ai kawai sai kice Allah ya bada sa’a tunda bake za kiyi masa auren ba, tsuntsun da yaja ruwa ai shi ruwa zai doka.’

‘Yaya, shekararmu fa kusan ashirin da aure duk bai tashi kara auren ba sai yanzu? Duk yanda nake tattalinsa amma shi ba zai raga min ba? Yana wani gaya min wai mai hankali ce sosai mai ilimi, da yake ni bani da hankali.’

Dariya Murja ta sake yi

‘To meye bako a wajenki a cikin abinda yayi? Ai ki kwantar da hankalinki kawai kice Allah ya bada sa’a domin idan kika ce zakiyi wata hayaniya ma kanki zaki dorawa hawan jini. Ni ba gani ba, me ta rage min, rayuwarta takeyi ina tawa bani ma da lokacinta. Kiyita addu’a kawai tunda ko bai yi yanzu ba ma nan gaba sai ya kara.’

Ta kau da kai, dama ta san haka Yaya Murja zata ce domin ita din hakurinta da ban ne. Ta san ba zata sami mafita ba ta dai zo ne saboda kawai ta fada taji sanyi a ranta tunda ita take gani kamar uwarta tun bayan rasuwar iyayensu.
Ta gyara zamanta tana kokarin kawar da damuwar, Yaya Murja ta katse mata tunani

‘Idan dai namiji ne babu yanda zakiyi dashi, idan kika ce ba zai yi miki kishiya ba to kanki zaki dorawa damuwa sai yayi, ki roki Allah ya hadaki da ta gari wadda ba zata cutar da ku ba gaba daya.’

‘Hakane Yaya.’

Ta dan daki cinyarta

‘Yauwa Uwar Saddiku, ko ke fa. Bari na samo miki lemon ki kora, kina sallah kina salati babu macen da zata baki tsoro.’

Har ta mike Zahra ta riketa

‘Ai barshi kawai Yaya, wallahi ko tambaya banyi ba na fito saboda takaici.’

Ta mike kafin Murja ta zauna suka nufi kasa tare, sukayi sallama tana sake bata hakuri tare da yi mata alkawarin gobe da yamma zata zo gidan nata.

Haka ta koma gida zuciyarta a jagule; tabbas zatayi duk yanda zata yi taga an fasa auren nan idan haka bai samu ba kuma to tafi so ta zama itace kan gida sai yanda ta tsara.

Tana shiga gidan ta tarar da mai aikinta Jummai wadda dama zuwa take tana tafiya idan ta gama aikinta, don haka tare suka shige cikin gidan Jummai ta kama aikinta ita kuma Zahra’u ta haye dakinta wanda yake sama ta rufe kofa.

Tana shiga ta ajiye hijabin da jakarta a kan kujera, ta karasa ta zauna a gafen gado ta kafa tagumi. Bata jima da zaman ba kuma ta mike ta lalubo wayarta a cikin jakarta ta koma ta zauna akan gadon ta shiga laluben lambar wayar Amina; kawarta ce ta aminci wadda zata iya cewa a yanzu bata da kawar da ta kaita.


Sau daya wayar tayi kara aka dauka, bayan sun gaisa Amina tace

‘Ya nake jinki kamar kinda damuwa ne Uwar Saddiku?’

Saida ta share kwallar da take kwarmin idonta sannan ta amsa

‘Ba zaki gane ba kawata, wallahi ina cikin damuwa. Abban Sadik aure zai yi.’

Da mamaki ta amsata

‘Ikon Allah, namiji dan babansa. Yanzu ashe dama bayan waccan maganar mutumin nan ba hakura yayi ba?’

‘Wallahi ko ni ma na zata ya hakura, amma yau da safen nan yake gaya min harda wani ce min wai mai hankali ce kuma tana da ilimi.’

‘Kiji dan rainin hankali!’

‘Wallahi kuwa kawata, na ma rasa abun yi.’

‘To ai ba wani abu bane kema kin san Abban Sadiku ba zai baki matsala ba, duk da dai maza basu da tabbas. Sai ka gama shan wahalarsu da sun sami duniya su auro wata suce da ita za a more.’

‘Kawata ni kawai na fi so yanda aka fasa wancan a fasa wannan ma gaskiya, na san idan aka fasa wannan ba lallai ya kara dauko wata ba tunda kinga kullum girma yake shima.’

‘Hakane kam, to ai sai ki kirawo Mallam kiji ko zai iya taimakawa tunda shi yayi wancan aikin idan kuma ya gagareshi akwai wani malamin a garin Babura sai mu sa rana muje.’

Tayi dan murmushi a karo na farko tun lokacin da Abban Sadiku yayi mata maganar kara aure, sukayi sallama da Hajiya Amina.


Tana tsinke wayar kuma ta kirawo Malam Hatimu mai almajirai ta sanar da shi abinda take so.


Bayan Mallam ya gama jin duk bayaninta yayi gyaran murya yace

‘To Hajiya za ayi aiki, kuma in sha Allah yanzu kam babban aiki za ayi. Sai ki yi kokari zuwa gobe ki sanar damu lokacin da za a daura auren don mu san lokacin da muke da shi kada mu bata lokaci.’

Sukayi sallama da alkawarin zata kirawo shi gobe ta sanar da shi lokacin da yayi saura kafin auren.

Haka Hajiya Zahra’u Uwar Sadiku ta karasa wunin wannan ranar cikin damuwa.
……….

Tunda ya dawo gidan daga wajen aiki take tunanin ta yanda zata tambayeshi yaushe ne auren nasa, ta kasa nutsuwa ta jeranta kalamanta yanda ba zai iya karanta damuwarta ba. Har dare yayi bata sami wannan damar ba, ya gama cin abinci sa ya zauna a falon sama yayi kallon TV daga baya kuma ya koma dakinsa.

Yana zaune a kan gadonsa ya mike kafa yana aiki a kwanfutarsa ta shiga dakin sanye da kayan baccinta, bayan ya amsa sallamarta ta karasa ta kwanta a gefensa tace

‘Har yanzu aikin bai kare ba Yallabai.’

Ya kalleta yana murmushi

‘Saura kadan Madam, in zo ne ana nemana?’
Tayi ‘yar gajeriyar dariya

‘A’a gama a hankali abunka.’

Ya mayar da hankali kan kwamfutar ya cigaba da aikinsa yayinda ta muskuta ta gyara kwanciyarta. Jimawa kadan ta kirawo sunansa

‘Abban Sadik.’

Ya kauda idonsa daga kwamfutar ya dubeta alamar yana sauraronta, don haka ta cigaba

‘Yaushe ne auren naka da kace zakayi?’

Ba tare da ya bar aikin da yakeyi ba yace

‘Da sauran lokaci gaskiya tunda kin ga bamu gama daidatawa ba tukunnu, ba zan iya sanin lokacin ba yanzu.’

‘Uhmm!’

Taji dadin hakan don ta san hakan yana nufin tana da isasshen lokacin don karasa nata shirye-shiryen.


Ya cigaba da aikinsa ita kuma tana kwance, jimawa kadan ta sake kiransa

‘Abban Sadik.’

Ya kalleta sannan ya amsa

‘Um.’

Ta gyara kwanciyarta ta tokare kanta da hannunta ta bishi da kallo ta fara magana kamar tana nazarin kalmominta

‘Don Allah me ya sa kake son kara aure? Idan akwai wani abu da kake bukata ai gara kayi min magana na gyara ko?’

Ya ajiye kwamfutar a kan durowar gefen gado ya dan matsa kusa da ita ya fara wasa da gashin kanta wanda babu kitso amma dai ta daureshi guri daya da ribbon, ya dubeta suka hada ido sannan yace

‘Babu abinda nake bukata, kuma ke ma babu abinda kikayi min. Kawai dai mun hadu da Aishan ne kuma tunda ida damar auren mace hudu ai babu laifin don nayi biyu ko? Amma kada ki damu, babu abinda zai shafi son da nakeyi miki don ni din naki ne kuma ke din tawa ce kin ji. Ki kwantar da hankalinki.’

‘Hmm! Aisha sunanta ashe.’

‘Eh.’

‘Um.’

Ta zame ta gyara kwanciyarta tana fadin

‘Bari na kwanta bacci nake ji.’

Ya cigaba da aikinsa yayinda ita kuma ta juya masa baya ta rufe ido da sunan bacci, tunani kala-kala suna ta zarya a kwakwalwarta.
UWAR SADDIKU


Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)


6

Tunda Abban Sadik ya tabbatar mata ba a kusa aurensa ba ta dan sami natsuwar, domin ta sanarwa Malam Hatimu shi kuma yayi mata alkawarin za ayi mata wani babban aiki wanda daga shi maigidanta ba zai sake aure ba har karshen rayuwarsa. Don haka ta saki ranta tana harkarta kamar bata da wata damuwa, kuma da bata ji yayi zancen kayan auren ba sai ta kara sakankancewa aikin Malam ne yake aiki.
…….

Sai bayan da ya sanar da Zahra aurensa sannan yaje gidansu ya sanar da mutanen gidan, mahaifiyarsu Hajiya Balaraba ta sawa abun albarka sosai duk da dai ta ja masa kunne a kan kada ya kuskura ya bata da uwargidansa. Ita kuwa yayarsa Yaya Saratu zancen bai yi mata dadi ba domin suna aminci sosai da Zahra’u; musamman da yake ita din mai kwadayi ce sosai ita kuma Zahra’un mai kyauta ce sosai. Inda Allah ya sawa abun ruwan sanyi don taga Yaya Bello shine gaba a wajen maganar, ta kuma san idan ta fiya rawar kai zai ci mutuncinta. Don haka itama tayi Allah ya sanya alkhairi kawai.

Yanda ya gayawa Zahra haka ya gaya musu, cewa ba a saka lokacin bikin ba, domin Yaya Bello ne da abokinsa suka kai kayan kuma ya san babu wanda zai gayawa musamman matarsa wadda suke shiri da Zahra. Itama Hajiya a haka suka barta.

Tunda taji labarin wannan auren Yaya Saratu ta kasa zaune ta kasa tsaye, a tunaninta ko Zahra bata sani ba. Domin wancan karon da ya fara maganar auren Hajiya ya fara gayawa kafin ya gayawa kowa don haka kafin shi ya gayawa Zahra Yaya Saratu ce ta fara gaya mata. Hakan yana daya daga cikin abubuwan da suka kara harzuka zuciyarta a lokacin, taga lallai idan ta bari akayi auren Yusuf ya rainata; don haka ne ma ta san yanda tayi aka fasa.
Yanzu ma sauri Yaya Saratun takeyi domin ta fara kawowa Zahra labari, don haka ranar da Yusuf ya sanar musu washegari ta shirya ta taho gidan Yusuf din.

Kamar yanda ta saba haka akayi mata tarba ta mutunci, kuma da yake da safe tazo harda shayi da burodi aka ajiye mata. Saida taci ta koshi sannan Zahra ta kwashe kwanukan ta zauna a kujerar zaman mutum daya wadda take kusa da wadda Yaya Saratun ta zauna.

Zahra ta dubeta tace

‘Kin kwana biyu baki leko mu ba Yaya Saratu, ya wajen Hajiya?’

Ta gyara zama

‘Hajiya tana nan lafiya wallahi, hidimace tayi min yawa shi yasa kika ji ni shiru.’

‘Allah Sarki.’

Sukayi shiru na dan lokaci, Yaya Saratu tace

‘Sai muka ji kuma wai Abban Sadik aure zai yi.’

Dama ta riga ta san zancen da ya kawota gidan kenan amma sai ta kauda kanta tana murmushi tace

‘Ai kuwa dai, abun ya zo.’

Ta kama haba alamar mamaki sannan ta bata amsa

‘Kin san na zata mutumin nan ya fasa auren nan amma ashe ba zai hakura ba.’

‘To ya za ayi, ai babu laifi sai dai kawai muyita addu’a Allah ya bamu zaman lafiya kawai.’

Wannan magana ta Zahra ta sage gwiwar Saratu, don haka cikin sanyin jiki tace

‘Uhm, ai maza sai a barsu, kedai Uwar Sadiku Allah ya kara miki hakuri don ko ta shigo ma babu abinda zata tsinta a gidan nan. Ba zata iya gasa dake ba don ba duk mutum ba wallahi.’

‘Uhm, Yaya kenan.’

Suka cigaba da hira tana tambayarta labarin inda amaryar zata zauna inda tace mata bata sani ba. Sai can wajen sha biyu na rana sannan tayi shirin tafiya; ai kuwa Zahra ta hada mata goma ta arziki kamar yanda ta saba sannan ta kawo naira dubu biyu ta bata kudin mota.

Sukayi sallama tana ta godiya ta kama hanya.
………

Sam batayi tunanin inda amaryar zata zauna ba sai yanzu da Yaya Saratu ta tuna mata, duk da ma tana ji a jikinta ba za ayi wannan auren ba tunda Malam yace ba za ayin ba. Amma dai zata so ta san tsarin da ya tanada don tayi shirin ko ta kwana.

Wancan lokacin dai da ya fara shirin auren akwai daki a falon kasa wanda yake a kasan dakinsa, nan yace za a gyara amarya ta tare; tunda ba a kwana a ciki ajiya kawai akeyi a ciki kamar store. Yanzun ma ta san bai wuce nan din ba, amma duk da haka zata tambayeshi taji idan ya dawo daga wajen aiki.
Sai bayan la’asar Abban Sadik din ya kirawota ya sanar da ita yau ba zai dawo da wuri ba, suna da meeting da mai girma gwamna kuma sai karfe takwas da rabi ma za a fara meeting din don haka zai yi dare. Don haka ta cigaba da harkarta ta san sai wajen sha daya na dare zai dawo kuma ba zai ci abincin dare ba.

Sai wajen goma da rabi ya dawo gidan, kusan tare suka shigo da Sadik wanda wanda yake zauna a kofar gida yana hira da abokai sai da ya hango motar Abban sannan yayi sauri ya shigo gidan da gudu.

Yana shiga falon tana saukowa daga bene wanda yake cikin falon, sanye take da doguwar rigar bacci ta yafa mayafin abaya. Ta fadada murmushinta ta karasa saukowa daga benen tana fadin

‘Sannu da zuwa Abba, ashe yau da wuri zaku gama meeting din ma.’

Ya sha kunu ya amsa

‘Yauwa. Ina Sadiku?’

Ta nuna alamar mamaki a fuskarta tace

‘Um ina jin ai yana bacci ko? Bari na duba yana dakinsu ai.’

Ta nufi dakin wanda yake can gefe guda a cikin falon, kafin ta karasa yace

‘Ba wani bacci da yakeyi, yanzu ya shigo gidan da ya hango ni.’

Ta tsaya ta juyo zatayi magana, kafin ta bude baki Abban ya daga murya ya kwalawa Sadik kira, ya bude baki zai yi masa kira na biyu Sadik din ya turo kofar dakin ya fito. Ya karaso a hankali yana shafa kai yana kallon kasa kamar mara gaskiya. Kafin ya karaso Abban yace

‘Me kakeyi a waje karfe goma da rabi na dare.’

Cikin rawar murya yace

‘Eh Abba dama Sulaiman na bawa wayarsa da ya kawo aka saka masa chaji.’

‘Shi yasa kake gudu da ka hangoni ko?’

Yayi shiru ya kara sunkuyar da kai don ya san an riga an kamashi.


Abban ya cigaba

‘Na hanaka wuce karfe tara a waje amma baka ji ko? So kake mu sa kafar wando daya da kai ko Sadik?’

Da sauri yace

‘A’a Abba, kayi hakuri ba zan sake ba.’

Ya jijjiga kai yayi kwafa ya wuce ta tsakanin Zahra da Sadik din ya haye sama ya nufi dakinsa.

Zahra ta harari Sadik tace

‘Allah ya shiryeka kai dai.’

‘Mommy wallahi Suleiman na bawa wayarsa.’

‘Tafi ka kwanta ni bana son shegiyar karyar tsiya.’

Ta haye sama itama ta bi Abban dakinsa.

Sai da yayi wanka sannan ta kawo masa shayi, ya zauna a kan kujera yana kurbar shayin yana duba wasu takardu yayinda ita kuma take kwance a kan gadon tana kallonsa. Jimawa kadan ya dubeta yace

‘Ki kwanta kiyi barcinki tunda na dawo, kinga gobe da wuri ‘yan makaranta zasu tashe ki.’

Tayi murmushi tace

‘Yanzu zaka ji munshari na kuwa.’

Shima yayi dariya.


Jimawa kadan tace

‘Abban Sadik.’

Ya dago ya dubeta, ta cigaba

‘Dakin kasa za a gyarawa amaryar mu fara kwashe kayanmu ko kuwa wani dakin za ayi mata.’

Ya ajiye kofin shayin da yake hannunsa yana murmushi yace

‘Saurin me kikeyi ne? Ko har kin fi ni zumidin kanwar taki ta zo.’

Tayi murmushin yake saboda yanda taga kamar maganar ta saka shi nishadi, ta juya kai ta amsa

‘A’a! Wai saboda na fara kwashe shirgina daga dakin a hankali ba sai an tsaya a kaina ba.’

‘To ki kwantar da hankalinki ki kara baje shirginki ba nan zata zauna ba, ina dai duba wani gidan a nan kusa wanda zan saya sai ta zauna a can.’

Mamaki ya bayyana a fuskarta.

‘Au! Amma dai ba wata matsala bace ta sa za kayi hakan ba ko? Tunda ka ga nan din ma da zai ishemu kuma ni ka san bani da matsala da hakan.’

Ya ajiye kofin shayin a kan teburin gabansa bayan ya kurbe shayin sannan ya bata amsa

‘Babu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login