Showing 129001 words to 132000 words out of 166068 words
ba ko ya amsa ko bai amsa ba, ta dai san bata ji yayi magana ba sai dai da yake bata ganin fuskarsa bata san yanayin da yake ciki ba.
A tare suka shiga dakin, ya wuce ya ajiye mukullan hannunsa a kan mudubi sannan ya janyo ‘yar kujerar da take gaban mudubi ya zauna yayinda ita kuma ta zauna a gefen gado suna fuskantar juna. Tace
‘Ya jikin Saddikun? Naji kanacewa yara food poisoning ne, wanne irin abinci suka ci?’
Kallonta kawai yake a fusace wanda ita kuma take mamakin dalilin da yasa yake kallonta kamar itace tayi poisoning Saddikun. Ta dan bata rai ta kawar da kai , yace
‘Ai nima nan zuwa nayi na tambayeki abinda Saddiku yaci ya sami poisoning din?’
Mamakinta ya karu yayinda ta kara shan kunu saboda yanda ta kula yana so ne kawai ya raina mata hankali. Tace
‘Ya zaka tambayeni bayan kaine kaje wajensa?’
Yayi kwafa yace
‘Ko da yake ba ma wannan ya kamata na tambayeki ba, dazu da safe da na tambayeki Saddiku me kika ce min?’
‘Ce maka nayi ya fita, kuma ai a lokacin ya fita din ko ka ganshi ne a gidan bayan nan?’
Ya jijjiga kai saboda yanda take bashi mamaki, ya rasa yaushe Zahra ta kware a karya haka. Yace
‘Ban gashi ba, amma bari na sake tambayar watakila zaki fi ganewa. Jiya a ina Saddiku ya kwana?’
Gabanta ya fadi yayinda tayi sauri ta waske; sai a lokacin ta gane inda ya dosa. To ana maganar yau ya za ayi ya dinga tamabayarta jiya. Tana jin motsin kwayar idonsa a kan fuskarta domin ya ki ya daina kallonta wanda hakan ya saka ta kasa sukuni. Bata da wata mafita domin ta tsani yanda yake warware duk wata karya da ta yi masa ba tare da bata lokaci ba. Ta saci kallon fuskarsa suka hada ido, ta sake shan kunu sannan tace
‘Yace min zasu yi party na end of session, kuma na ga tun a secondary suke irin wannan party din shi yasa ban zata da wani abu ba. Shine yayi dare ni kuma bacci ya kwashe ni ban sanar da kai ba.’
‘Shine kika nuna min ya dawo kuma a gidan ya kwana? Ba ma wannan ba; kin zama kece uwarsa kece ubansa shi yasa kika bashi kudi kuma kika bashi izinin ya tafi party kika bashi mota yaje yayi abinda ya ga dama ba tare da ke da shi kun nemi izini na ba tunda dama kin nuna masa ni din bana son shi?’
Bata da bakin magana don haka ta sunkuyar da kai tayi shiru, so take kawai ya gama wannan hayaniyar tasa ya gaya mata abinda ya samu Saddikun da kuma halin da yake ciki.
Ya fuskanci ba zata yi magana ba. Yayi murmushin takaici yace
‘To ina yi miki murna Zahra, saura kadan ki hallaka Saddiku domin jiya da kika boyemin kika bashi kudi da mota ya tafi party zuwa sukayi suka sha miyagun kwayoyi wadanda jikinsu ba zai iya daukan wannan yawan ba. Wannan shine ya janyo su ukun suka sume aka samu aka kaisu asibiti. Tun jiya basu farfado ba har zuwa lokacin da na barosu a asibitin, sai dai mu cigaba da addu’ar Allah ya tasheshi lafiya tunda likitocin sun tabbatar ya dade yana shaye-shayen kwayoyi.’
A firgice take kallonsa da baki bude, kafin ta sami kalaman da zata gaya masa ya mike ya dauki mukullin da ya ajiye ya nufi kofar. Sai da ya kama hannun kofar ya juya ya dubeta yace
‘Kuma ban baki izinin zuwa asibitin ba, idan kuma kin ki ji to zaki sha mamaki.’
Ya murza hannun kofar zai bude tayi sauri tace
‘To shi da waye a asibitin?’
Tana nufin ya gaya mata domin ta samu tayi waya taji halin da yake ciki tunda ta kula shi din ba zai yi mata bayani ba.
Cikin halin ko in kula yace
‘Shi da mutane ne. Sai da safe.’
Ya fice kafin tace wani abu ya bar mata gidan.
Take hawaye suka wanke mata fuska.
Wannan wacce irin musiba ce ? Yanzu dama da gaske ne ake gaya mata Saddiku yana shaye-shaye amma yaron nan yana musa mata? Yanzu ya zata yi? Gashi Abban ta kula wulakanci kawai yake yi mata domin yaki yayi mata cikakken bayani. Gashi bata ji ya shigo da mota ba, to ina motar tata da Saddikun ya fita da ita?
‘Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun.’
Ta fada a fili lokacin da tambayoyin suka fara yi mata yawa a ka. Anya kuwa wannan abubuwan da suke faruwa babu sa hannu a ciki? A ce Saddiku yana shaye-shaye sannan kuma gashi Abbansa ya juya mata baya yanata faman yi mata wulakanci?
Ta share hawayenta yayinda ta mike ta fice daga dakin, wayarta zata dauko ta kirawo Yaya Murja ta sanar da ita. A falo ta zauna a kan kujera ta dauki wayar tata, har ta budo lambar Yaya Murja sai kuma ta tuna cewa bata shirya sanar da Yaya Murja cewa Saddiku shaye-shaye yakeyi ba. Musamman da yake taba yiwa Yaya Murja korafin yanda mutane suke faman gaya mata cewa Saddiku yana shaye-shaye. Tun a lokacin Yaya Murja tace mata ta bincika sosai kuma ta sanar da Abbansa, har ma ta ce ta tura mata shi domin idan ta gan shi ko zata iya fuskantar wani abu a tattare dashi. Ko maganar bata yi masa ba balle ta bincikeshi don a lokacin gani take kawai kiyayya ce da hassada tasa ake mata haka. Sai daga baya ta samu ta tsara Yaya Murja.
To yanzu idan ta kirawota me zata ce mata? Nan ta ajiye wayar ta kifa kanta a kan kujerar ta sake fashewa da sabon kuka.
Haka ta kwana cikin matsananciyar damuwa; tunaninta daya hannu aka saka mata a al’amuranta take ta shiga matsala kuma ko wanene sai ta rama.
Mutum biyu take zargi; Aisha wadda dama duk itace silar rikita mata gidan aurenta wanda a baya yake cike da kwanciyar hankali da kauna, sai kuma Yaya Bello wanda sosai take zarginsa a kan al’amarin Saddiku tunda ta kula yana bakin cikin yanda yaransa basu da gata kamar yanda Abban yake kulawa da yaranta, tunda shi baya iya bawa nasa yaran gata kamar yanda Abban yake bawa nasa.
Tabbas sai ta rama; tunda daman yanzu account dinta ya fara nauyi. Sarkar Rukayya ta gwal kawai zata bayar aje a sayar shikenan da zarar Amina ta sami dama sai suje wajen malamin da ta samo musu tunda itama a halin yanzun tana da tata matsalar.
…………
Ko da gari ya waye ranar aiki ce don haka Abba ya shirya daga gidan Aisha suka fice gaba daya ba tare da ya je gidan Zahra ba. Ya riga ya san babu abinda suke bukata kuma ya yi waya da Malam Ali ya riga ya kai masa yara makaranta.
Babu yanda Aisha bata yi ba ya barta ta rakashi asibitin itama ya hanata, sai dai ta hada breakfast inda ta soya dankalin bature da sauce din kaza sannan ta zuba musu ruwan zafi a flask ta bashi ya kai musu. Yana fitowa ya sayi kayan shayi ya wuce asibitin.
Da sallama ya tura kofar dakin ya shiga.
Muhammadu yana zaune a kan tabarmar da ya shimfida yana kokarin hada musu shayi da ragowar ruwan da ya zo da shi jiya. Ya ajiye kofunan da suke hannunsa ya tari Abban ya karbi kayan hannunsa ya ajiye. Bayan Abban ya amsa gaisuwar sa yace
‘Likitan ya zo ne Muhammadu?’
Yace
‘Bai zo ba, nurse din ce ta shigo tace yaci abinci zata dawo ta bashi magani.’
‘To ga abinci nan ka zuba muku ku ci, bari naje na sami nurse din.’
Yana fita ya sami waje ya zauna, basu dama yayi suci abinci sannan ya samu yayi magana da Saddikun kafin likitan ya shigo.
Sai da ya basu kusan awa guda sannan ya dawo dakin, lokacin sun gama cin abincin har nurse din ta bawa Sadik maganinsa. Sun gama cin abincin, Saddiku yana zaune a kan gadon yayinda Muhammadu yake zaune a kan tabarmar yana karatu. Bayan Abban ya amsa sannu da zuwansu yace
‘Kana da lecture ne yau Muhammadu?’
Yace
‘A’a, sai gobe ne zamu yi test shi yasa nake karatu. Yau ba zan shiga makaranta ba.’
‘Allah ya bada sa a.’
Ya karasa ya zauna a gefen gadon Saddikun.
Muhammadu ya dauki litattafansa ya mike yana fadin
‘Abba bari na zauna a nan waje na cigaba da karatun, idan ana nemena Ina nan.’
‘Ok to kada kayi nisa don yanzu zan tafi.'
Ya ji dadin hakan don dama so yake yayi magana da Saddikun, wanda tun bayan da ya cewa Abban Ina kwana ya sunkuyar da kai bai sake dagowa ba.
Sukayi shiru na dan lokaci babu mai magana, shi Abban yana kallon Saddikun yayinda shi kuma ya sunkuyar da kai ya kasa hada ido da Abban nasa. Jimawa kadan Abban yayi gyaran murya yace
‘Sadik me yasa kake son ka kashe kanka?’
Ya dago kai idonsa cike da kwalla, suna hada ido da Abban yace
‘Kayi hakuri Abba.’
Ya sake sunkuyar da kansa yana share hawaye.
Abban ya jijjiga kai yace
‘Likitane ya duba ka Saddiku, nurse din da ta shigo ta baka magani bata wuce sa’arka ba sai dai ko ta baka shekaru biyu zuwa uku, kalli yayanka Muhammadu yana karatu don ya zama dan jarida, ni da na haifeka public administration na karanta shi yasa kaga na kai matsayin da na kai. Amma kai Saddiku ka zabi zama dan kwaya, ka tara kayan maye ka sha ka fita daga hayyacinka shi kenan abinda kake so Saddiku.’
Cikin kuka yace
‘A’a Abba kayi hakuri.’
‘Ka daina bani hakuri Saddiku, baka yi min laifi ba. Kanka ka yiwa laifi kuma kayiwa Allah laifi. Ya baka rayuwa kuma ya baka dama ka zama abun alfahari ga al’umma amma ka zabi shaye-shaye.’
Sukayi shiru na dan lokaci, Abban yace
‘Wa ya baka kudin zuwa party?’
‘Mommy.’
‘Tun yaushe kake shan kwaya?’
Ya sunkuyar da kai yayi shiru na dan lokaci, jim kadan yace
‘Tun ina SS 2.’
‘Ka san yanzu jikinka ya saba ba zaka iya rayuwa babu kwayoyin da kake sha ba saboda ka zama addicted ko?'
Bai iya amsawa ba kai kawai ya daga don ya san hakan ne.
‘Ina son ka Saddiku, ina son kayi rayuwa a hayyacinka kaima wataran ka zama wani ka tara naka family din cikin nutsuwa. Akwai makarantar da zasu taimaka maka ka daina shan kwaya amma fa makarantar kwana ce, idan likita ya sallameka daga nan can zamu wuce. Idan Allah ya sa ka rabu da addiction din a wata shida sai ka fito ka cigaba da karatunka.’
Kai kawai ya dagawa Abban saboda yanda kuka yaci karfinsa.
Suka zauna sukayi shiru har sai da ya daina kukan, Abban yace
‘Yanzu ina ne yake maka ciwo?’
‘Babu ko ina, jikina ne kawai yake ciwo.’
Jimawa kadan Abban yayi masa sallama ya fito ya tura masa Muhammadu sanna ya wuce office zuciyarsa cike da damuwa.
Yana tausayin Saddikun sanna kuma yana ganin laifinsa ne da yayi sakaci a kan Saddikun, yana fatan Allah ya bashi ikon ceto Saddikun.
Kafin ya isa office din yayiwa Aisha waya ya sanar da ita ta dafawa Sadik abincin rana idan ta dawo daga aiki idan ta gama ta yiwa Malam Ali waya ya zo ya karba ya kai.
…………
Tun safe take jiran shigowar Abban don ta gama shirin zuwa asibiti wajen Saddiku amma har wajen karfe tara bai shigo ba. Wajen karfe tara da rabi ta sa Yusra taje ta dubo gidan Aisha ta kirawo Abban, sai dai bata dade da fita ba ta dawo ta sanar da ita babu kowa a gidan.
Zuciyarta ta kara tafasa saboda ta gaji da abinda Abban yake mata, ita da danta a hanata zuwa ta dubo shi.
Ta dauki wayarta ta shiga daki sannan ta danna masa kira, sai dai har ta gaji da kira bai amsa wayar ba. Ji take kamar ta rusa ihu saboda takaici, ta rasa ma wanda zata gayawa taji dadi. Ta zauna a gefen gadonta ta lalubo lambar Yaya Murja wadda tun jiya take kiran Zahran ita kuma ta ki dauka saboda tana kunyar abinda zata fada mata.
Tana dauka tace
‘Zahra ina kika shiga ne ? Tun dare nake faman kiranki. Yusra dai ta ce min kina nan amma me yasa ba kya daukan waya. Kin gan ni a tsaye gidan naki zan taho ko kina asibitin?’
Cikin shesshekar kuka tace
‘Ina gida. Abbansu ya hanani zuwa asibitin kuma ya ki ya gaya min me ake ciki.’
Cikin muryar lallashi tace
‘To kinga gani nan zuwa gidan yanzu.’
Ta katse wayar ta ajiye.
Wajen sha daya saura Yaya Murja ta shiga gidan, a daki ta sami Zahran ta ci kuka ta koshi. Nan ta bata labarin irin wulakancin da Abban yakeyi mata tun lokacin da aka kwantar da Saddikun a asibiti, gashi ya ma ki ya barta koda ta ji muryar Saddikun. Sai dai duk cikin bayanan da take yi bata gaya mata ainahin abinda ya sa Abban ya ke mata hakan ba.
A iya sanin Murja ta san akwai fahimtar juna tsakanin Zahra da Abban Sadik; duk da a baya bayan nan Zahran tana kokarin ta fahimtar da yayar tata cewa tunda Abban Sadik din ya auri Aisha ya canza mata.
Gaba daya dai ta kasa gane bayanin da Zahran take yi mata a halin yanzu; amma ko ma menene ya za ayi ace mace ta haifi danta kuma ace mata bashi da lafiya amma an hanata ta ganshi kuma an ki ayi mata bayanin halin da yake ciki.
Sai da ta samu Zahran ta tsagaita da kukan sannan ta zaro wayarta daga jaka ta lalubi lambar Abban Sadik din ta kirawoshi.
Cikin girmamawa da mutuntawa suka gaisa ta tambayeshi jikin Saddiku sannan ta sanar da shi tana gidansa, ta nemi yayi mata kwatancen inda Saddikun yake a asibitin tana son zuwa ta duba shi. Bai yi mata wani musu ba domin ya san dama za ayi hakan; sai dai ko da ta nemin izini zasu taho da Zahran ya sanar da ita kada su taho da ita idan ya zo zai kaita da kanshi.
Don haka nan take ta tashi kai tsaye ta fito daga gidan ta hau motar haya ta nufi asibitin Malam. Kafin ta isa asibitin Abban ya isa don haka a farfajiyar wajen ta sameshi bayan yayi mata kwatancen wajen.
A zaune yake a kan irin kujerar nan ta dutse don haka itama Yaya Murja sai ta zauna, bayan sun sake gaisawa sukayi shiru tana jiran yace su tashi ya kaita dakin da Saddikun yake. Madadin hakan sai yace
‘Ta gaya miki abun da ya sami Saddikun?’
Cikin zakuwa tace
‘To duka bayanan nata wallahi ba ganewa nayi ba saboda tana cikin damuwa, kamar dai tace jiya da safe ya fita shine aka kirawo ta akace kamar sun ci wani abu suna asibiti. To tace kai kadai ka zo ka ganshi kuma baka bata wani bayani ba, shi yasa ma take cikin damuwa.’
Ya jijjaga kai.
Nan yayi mata bayanin ainahin abinda ya faru sannan ya kara da
‘Saboda bata son bacin ran shi tana kallo tun yana SS 2 yake shaye-shaye gashi yanzu har ya zama addicted, jiyan da ba dan Allah ya sa da kwanansu a gaba ba da sai dai mu dauki gawarsu. Yau da na fita daga nan kuma makarantarsu naje ashe ma shi ba karatun yake yi ba, tunda jarrabawar da yace mata sun gama ta bashi kudin party harda mota ya tafi an ce guda biyu kawai ya rubuta a cikin paper goma sha daya; kin ga babu maganar karatu ko.’
Kallonsa kawai take tana mamaki tana jijjiga kai, tace
‘Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun! Ita kuwa Zahra garin yaya tayi haka?’
Nan ta gaya masa yanda suka yi da Zahran a kan maganar zargin da takeyi, sannan ta sake bashi hakuri.
Nan ya tashi yayi mata jagora har dakin Saddikun, ta dai samu natsuwa yanda taga Saddikun tunda a hayyacinsa yake har hira ma suka yi kuma ya gaya mata babu inda yake masa ciwo don likitan ma yace da safe zasu sallameshi.
Bayan sun fito ne Abban yake gaya mata ya riga ya sami rehabilitation center da zai kai Saddikun, wanda a yanda ya tsara daga nan asibitin kai tsaye center din zasu wuce.
Tace hakan yayi domin itama tana so taga Saddikun ya zama mutum, sai dai ta roki Abban a kan ya taimaka ya bari Zahra ta ga Saddikun kafin a tafi da shi rehabilitation center din tunda ya ce da ita wata shida zai yi a can kuma shi kadai zai dinga zuwa yana ganinsa. Yayi mata alkawarin gobe da safe zai kawo Zahran ta ganshi inda daga nan zai daukeshi su wuce.
Sukayi sallama ta kama hanyar gida shi kuma ya koma office.
__
Kai tsaye daga asibiti gidan Zahra ta koma saboda yanda take cike da takaicin abun da Zahran tayi. Bayan ta sanar da ita Saddikun yana nan kamar ma lafiyarsa kalau sai kuma ta hau ta da fada.
Sai da tayi mai isarta sannan tace
‘Shima kansa Abban haushin ki yake ji saboda yanda kika tsaya kika bari Saddiku ya lalace kuma kika dinga hanashi yayi masa fada, shi ya sa kika ga yayi banza dake. Don haka idan ya dawo ki lallaba ki bashi hakuri tunda gaskiya dai da laifinki don shi da kansa yace ke kika bashi kudin party din. Ki samu ki bashi hakuri don gaskiya yayi fushi sosai, kuma idan an kai Saddikun rehabilitation center ki kawar da idonki a samu ya sami lafiya tunda dai kin tabbatar ubansa ba zai cutar da shi ba.’
‘Wallahi Yaya wannan wulakancin da yake yawan yi min tunzura shi matarsa take tunda da ai ba haka yake ba.’
‘Ba zamu