Showing 45001 words to 48000 words out of 166068 words
rasa me zata ce mata don haka ta fara kwalla. Ta kama hannunta tace
‘Kiyi shiru Amira cikina ne yake ciwo ba komai.’
Ta dan share hawayen amma dai ta kasa nutsuwa.
Sun kai wajen minti talatin a haka Aishan tana ta addu’a , a hankali ciwon ya fara lafa mata. Har bacci ya fara kwasarta mararta ta kara katawa.
Ta yunkura saboda aman da ya taso mata, sai kuma taji ta jike. Ta ture Amira ta mike tana fadin
‘Kwanta Amira Ina zuwa.’
Kafin tace wani abu ta shige bandaki.
A kasa ta tsuguna tana ji jini yana bin jikinta, ta taba yin bari kafin ta haifi Abdallah don haka yanzun ma ta san abinda yake faruwa da ita. Ta kai kamar minti goma Sha biyar tana murkususu a bandakin nan, Amira tana bakin kofa tana jiranta cike da tsananin tashin hankali. Daga nan bakin kofar Amira tace
‘Anti na kirawo Mami a wayarki?’
Da kyar ta bude baki tace
‘A’a Amira bari na fito sai mu gani.’
Jimawa kadan taji gudan tayin cikin ya fado.
Ta yunkura ta mike da kyar ta karasa gaban toilet din, ta sabule dogon wandon kayan baccinta ta nade jinin da ta fitar a ciki sannan ta hau toilet din ta zauna. Mararta tana kara murdawa tana matsawa jini yana sake fita, a haka har abun ya fara lafa mata.
A hankali ta fara dawowa dai-dai, ta kirawo Amira wadda dama tana bakin kofa tace taje bandakinta ta dauko mata pad. Ta janyo abun tsarki don ta wanke jikinta tana murdawa taji babu ruwa.
‘Inna lillahi wa Inna ilaihi rajiun.’
Tabbas ta san Zahra ta hana a kunna mata ruwan kenan, dama taga ya ja baya shi yasa tace Rukayya ta kunna. Tunda tazo gidan nan bata taba murda fanfo ta ji babu ruwa ba sai yau, tana cikin wannan halin da take bukatar ruwa.
Amira ce ta katse mata tunanin ta kwankwasa kofar ta tura mata pad din. Ta dauke pad din ta yiwa Amira bayani akwai ruwa a bokitin fenti a bandakinta da kuma wani a kicin tace ta dauko mata su, in ba zata iya saukowa ba ta sami roba a kicin ta dinga debowa. Haka Amira ta kawo mata ruwan nan ta samu ta wanke jikinta ta kora toilet din ta goge sannan ta saka pad din ta dauro zanin da Amiran ta mika mata ta fito ta kwanta a jigace.
Amira ta dafata tace
‘Sannu Anti.’
Ta bude ruwan robar da ta dauko ta mika mata ta, karba ta sha kadan ta mayar mata.
‘Anti na kirawo Mami?’
‘Ki barsu Amira, da anyi asuba sai mu kirawosu. Yanzu tayar musu da hankali kawai zamuyi ba zasu iya zuwa ba kinga biyun dare ce zata yi.’
Haka suka kwanta ita da Amira, a hankali bacci ya kwashesu.
UWAR SADDIKU
Written by Sakina Yazid
(Innar su Amal)
17
Saida gari ya gama wayewa sannan Aisha ta kirawo Yaya Zainab, direbanta yana dawowa daga kai yara makaranta ta kamo hanyar gidan Aisha. Kafin ta zo Amira ta dafa musu shayi sun sha sun canza kayansu duk da basu sami ruwan wanka ba. Yaya Zainab tana zuwa suka wuce asibiti.
A can likita ya dubata aka ce cikin ya zube gaba daya don haka sai aka yi mata allura aka rubuta mata magunguna suka dawo gidan.
Suna zuwa gida Yaya Zuwaira ta karaso suka hadu.
Tana daga kwance ta cewa Yaya Zainab
‘Yaya Zee bari na sa a samo me ruwa, gidan babu ruwa.’
Zainab tace
‘Ko makota ai sai mu shiga a samo ko na dora miki ruwan wanka ne kafin a sami me ruwan.’
‘Kada ku shiga, ba lallai su baku ba. Bari na kirawo Umman Janan zata sa a kawo mana mai ga-ruwa.’
Aka bata wayarta ta kirawo Umman Janan wadda a bayan layinsu take gidanta da dan nisa, nan take tace zata sa mai gadinta ya taho musu da dan ga ruwa.
Sai a lokacin Aisha take gayawa su Zainab ai duk makotansu nan kusa basa kulata, duk kokarin da tayi ta shiga harkarsu sai sun tureta saboda dukansu kawayen Zahra ne. Gaba daya gidajen da suke layinsu da masu kallonsu basa shiga harkarta, itama hakan sai ya fi mata sauki saboda ta gane idan suna tare da ita za ayi amfani da su a cuceta.
Kafin wani lokaci dan ga ruwa ya kawo, sai dai kuma babu inda za a juye. Nan take Yaya Zuwaira ta tsayar da shi suka fita da direban Zainab suka siyo drums guda uku sannan aka juye ruwan. Saida aka karawa dan garuwan kudi saboda zaman jiransu da yayi, aka sallameshi a kan da yamma ya dawo ya sake kawo musu ruwan.
Nan da nan aka sa mata ruwan wanka, kafin ta fito an ajiye mata abinci ta ci ta sha magunguna ta kwanta.
Nan su Yaya Zainab suka wuni, sai da yamma tayi Zahida ta karaso da Anti Uwani tare da yara. Ana yin magriba suka tafi suka bar mata Amira da Anti Uwani.
Sai da ta huta bayan Magriba suna waya da Abban sannan ta sanar da shi bata da lafiya, tayi bari. Sosai hankalinsa ya tashi don ya sa rai da wannan haihuwar, haka ya hakura ya cigaba da yi mata addu’a a harami.
Tun daga wannan ranar sukayi alkawarin da mai ga ruwa kullum karfe bakwai ya zo ya kawo mata kura guda, don bata san me yasa ruwan baya zuwa ba idan kuma matsala ce ba aikinta bane ta kawo mai gyara.
Sati daya Anti Uwani tayi mata, ta murmure ta sami lafiya ta koma aiki sannan ta koma gidan Hajiya. A wannan zaman ne dangin Aisha suka fuskanci kadan daga cikin abubuwan da suke faruwa a gidan Aishan.
………
Kafin ya tafi aikin Hajji yayi musu bayani cewa za a kawo sa da rago, kuma ya yiwa Zahra bayani sosai a kan idan an yanka sa a bawa Aisha cinya a hada mata da cinyar rago kuma da kayan ciki.
Wajen karfe goma na safe mahauta suka zo da dabbobin, Malam Sule yana nan tunda dama shi Abban ya sa ya tsaya masa ya tabbatar mahautan sunyi aikinsu sannan ya sallamesu.
A nan a tsakar gida Zahra ta kafa kujera a gareji ta zauna, a kan idonta aka fede dabbobin nan. Mutanen da suka saba karbar na sadaka suna bakin gate Malam Sule ya ware naman sadaka da yawa ya fitar ya rabar. Ya dawo ya ware cinyar sa da kuma cinyar rago tunda zuwa lokacin Zahra ta sa an dauke bahon da aka zuba kayan ciki gaba daya an kai bayan gida inda ake wankewa kuma ba zai iya ce mata ta kawo a debarwa Aisha ba.
Ta taso daga kujerar da take zaune ta karaso inda ake fidar, ta tsaya a kusa da Malam Sule ta dubeshi shekeke tace
‘Malam Sule wannan da kake warewa kuma na menene?’
Ya dan rage tsawo cikin girmamawa ya bata amsa
‘E Hajiya dama wanda Yallabai yace a kaiwa Hajiya Karama ne, shine zan mika mata.’
Ta kara shan kunu
‘To ka barshi idan an gyara za a mika mata.’
Ya sunkuyar da kai
‘Hajiya ai ko ni din ma sai na mi…'
Ba tare da ta bashi amsa ba ta kwalawa Hansatu kira. Nan da nan ta sheko da gudu daga bayan gida ta tsuguna
‘Hajiya gani.’
‘Kwashi wanna naman ki kirawo Sadik ya zo ya dauki wannan a kai baya zan zo nayi bayanin yanda za a gyara.’
Nan da nan kuwa ta dauki cinyar rago tayi bayan gida, kafin wani lokaci Sadik ya zagayo ya dauki cinyar san ya zagaya da ita. Ta koma ta zauna ta bar Malam Sule yana tsaye da baki a bude.
Sai da aka gama gyara naman nan tsaf ta tabbatar duk wanda ba a bayar sadaka ba an zagaya da shi bayan gida sannan ta tashi daga wajen. Malam Sule da Mai gadi suka hadu suka wanke wajen.
Tana zagayawa bayan gidan tace a hade naman gaba daya a saka mata a freezer tayi miya da shi.
………..
Tunda ya sanar da ita a gidan Zahra za a yanka sa a kawo mata nama ta san ba lallai ta samu ba. Da fari ta so tace ya bata rago a yanka mata a gidanta to amma bata so ta nuna rashin amincewa da matarsa don tana kula da tsananin yardar dake tsakaninsa da Zahran. Ya kawo mata itace da mai da duk wasu abubuwa da zata bukata na suyar.
Tunda gari ya waye ranar Sallah ita da Amira suka wanke kayan suyar suka ajiye yanda da an kawo sai su fara aiki. Abu kamar wasa har la’asar ba a kawo komai ba. Haka abun ya dinga bata dariya; wai naman sallar shi akewa wannan rowar da mugun halin.
Ta riga tayi layya a gidan Hajiya kamar yanda ta saba duk shekara, kuma dama naman yawanci ajiye mata akeyi. Don haka waya kawai tayi tace idan an soya a ajiye mata wani a danye gobe sai a kawo mata.
Cinyar sa aka kawo daga gidan ‘yanuwan babansu Abdallah don haka kawai sai Umma tace a soyawa Aisha ragonta gaba daya sai kuma a ajiye mata cinyar sa din a danye tayi miya.
Haka kuwa akayi, washegarin Sallah da yamma aka kawo naman nan a gyare aka shigar mata babu wanda ya gani.
......
Ranar kwana uku ga Sallah Nafisa; wadda ‘yar wa da kani suke da Abban Sadik; suka kawo musu ziyara ita da yaranta. Gidanta babu nisa da nan gidan nasu shi yasa duk shekara take kawo musu irin wannan ziyara.
Kamar yanda ta saba kai tsaye a gidan Zahra ta sauka, tun basu dade da zama ba Rukayya ta kwashi yaranta su uku suka tafi gidan Aisha, a can suka ci abinci suka ci nama da cake suka dawo. Suna shiga Bashar dan wajen Nafisan ya fada jikinta yana surutu
‘Ummu munci nama da yawa, Anti ta bamu abinci kuma ta bamu cake da zobo baki ji dadi ba.’
‘Um.’
Da yayi wannan maganar Zahra ta zata irin wanda ake kawowa daga makota ne, amma dai sai ta bincika don ta san ko Abba ya munafunceta.
Can da yamma Nafisa zata tafi ta dubi Mommy tace
‘Zamu tafi Mommy, idan na fita na shiga gidan Anti Aisha mu gaisa sai mu wuce.’
‘To kuje mana idan kun fito sai ku dawo nan kafin nan na hada muku kayan yara.’
Don haka suka fice suka nufi gidan Aisha tare da Rukayya, Nana da Ummi.
Wannan ne zuwan Nafisa gidan na farko wanda kafin nan duk labaran da take samu a kan Aisha na rashin mutunci ne don haka tana dari-dari ta shiga gidan. Cikin mutunci da girmamawa suka gaisa da Aishan, ta sa Rukayya ta tayata suka kawo ruwa da lemo ga kuma cake da nama. Suka dan taba hira sukayi sallama zasu tafi.
Aisha ta tsayar da su ta shiga daki ta fito da sabbin kudi 'yan dari bibbiyu ta bawa Nafisan guda goma sannan ta bawa yaran ‘yan hamsin kowa guda biyu. Bayan ta bawa kowa harda Nana wadda ta karba a raine sai ta boye sauran a bayanta ta dubi Ummi tace
‘Bazan bawa Ummi ba bata zo min yawon Sallah ba sai yau.’
Ta matso da sauri ta kama zaninta tana fada cikin shagwaba
‘Anti na zo fa, kin gan ni ma fa.’
Sukayi dariya gaba daya ta kawo kudin ta bata. Ta sa Rukayya ta kullowa Nafisa nama a kicin, nan da nan Nana ta bita.
Suka fito da kullin naman ta bawa Nafisa sukayi godiya suka tafi.
Suna komawa gidan Zahra suka yi mata sallama suka kama hanya.
Saida ta haye sama sannan ta kwalawa Nana kira, da hanzari ta tashi ta hau saman. Ba zata tamabayi Rukayya ba domin tun tuni ta fuskanci Rukayyan ba zata gaya mata abinda take son ji ba, kuma dama tun kafin a auro Aisha ta kance Rukayya 'yar Abbanta ce domin ta fi son shi.
Sai da suka shiga kuryar daki sannan ta tambayi Nana
‘Nana wai Antin nama aka kawo mata ne da yawa take ta rabo haka?’
Ta gyara zama
‘Ai gaskiya Mommy sai dai idan rago aka yanka mata fa, kin ga naman kuwa? Manyan robobi ne fa guda biyu duka a cike da nama kuma ga karamar roba ta kayan ciki. Ina ga ma harda danye don kwanukan da aka ci abincin rana gasu nan duk kashi a kai.’
Ta dan numfasa
‘Allah Mommy. Kudin ma fa da bamu tana da su da yawa don ‘yan dari bibbiyu ma ta bawa Anti Nafisan kuma da yawa za su kai ten ko twenty. Ita ta samu sabon kudi mu kuwa da yake Abban baya nan bamu samu ba.’
‘Eh watakila sai ya dawo.’
Ta sallameta ta sauko da gudu wajen ‘yan uwanta.
Tana fita ta mike tsaye tana kaiwa da kawowa a daki; kenan Abba ya munafunceta, nan ya ce a bawa Aisha nama ashe kuma ya zagaya ya saya mata rago. Ko kuma Aishan ce ta gaya masa ba a kai nama ba shine ya sa aka kawo mata daga wani wajen? Yanzu haka kuma munafuncin Malam Sule ne, don shima ta rasa yanda zatayi da shi ne da tuni ta sa Abban ya koreshi.
Ta koma ta zauna a gefen gadon.
Ta cigaba da tunani; gashi harda sabon kudi ya bata, kenan yanzu haka kafin ya fita ya bata ko kuma daga baya ya sa aka kawo mata.
Yanzu kiri-kiri Yusuf ya koma munafiki, buya kenan yakeyi yana yiwa Aishan abubuwa wadanda ita ba zai yi mata ba. Tayi kwafa tace
‘Zai dawo ya sameni don wallahi ba zan yarda ba.’
Haka ta wuni ranar tana shirin yanda zata bullo masa idan ya dawo.
Bata son ta ga Aisha a cikin walwala, tunda dai ta kasa rabasu da Yusuf to ta fi so ta ganta cikin damuwa da takura. Idan dai farin ciki take so to taje ta nemi mijinta ta bar mata Yusuf.
------
Kamar duk Babbar Sallah ranar hudu ga Sallah a gidan Umma suke wuni, don haka ma wannan sallar duka suka hadu da yaransu.
Zainab da matar Abubakar Fauziyya suna daki waken Hajiya yayinda Aisha, Zahida da Zuwaira sune a zaune a falo yaran kuma suna ta kaiwa da kawowarsu.
Aisha ta dubi Zainab tace
‘Ya Zainab nifa mota zan saya bayan sallar nan.’
Ta gyara zama tana murmushi
‘Haba! Ko ke fa? Tun tuni kike maganar nan amma sai wani jan kafa kike.’
‘Ba zaki gane ba Yaya Zainab. Kin san shi Yusuf da a tsarinsa yana da driver wanda ya kamata ya kaimu duk inda zamuje, amma matarsa ta hanani morar direban nan. In kika ga na hau motar nan to mai ita yana nan a gabansa ne amma yana juya baya haka zata barni da hawa motar haya.’
Zahida tace
‘Yauwa Yaya Aisha ai gara haka wallahi, ta karata da waccan motar.’
‘Hmmm! Kin san na fara yi masa maganar kwanaki yace na bari zai duba, a tunanina so yayi ya saya min to amma kinga idan ya saya min dole ya saya mata kuma inaga ko dai bashi da kudin sayen biyu ko kuma baya so ya bata motar. Su dai suka sani.’
Zainab tace
‘To ai ke da kudinki zaki saya ko?’
‘Eh, next month zan dauki adashi dubu dari uku idan na debi wasu a kudaden hayar gidana da nake tarawa na hada kamar miliyan daya da rabi na san zan sami mota mai kyau kuma kinga tunda Yaya Abubakar zan bawa ya siya min na san idan da ciko zai cika min.’
Zahida ta mika mata hannu suka tafa tana fadin
‘Baki da matsala Mrs Yusuf.’
Haka suka gama hirarrakinsu Aisha ta gama yanke shawara zata sayi mota saboda ta huta da wulakanci da Zahra take mata akan motar gidan.
………
Ya rigar ya sanar da su ranar Lahadi da sassafe zai dawo don haka duka suke ta shirin tarbarsa.
Wajen karfe bakwai na safe aka bugawa Aisha gate, Rukayya ce da kayanta niki-niki. Aishan ta dubeta bayan ta bude mata ta shigo tace
‘Rukayya ya na ganki da kaya?’
Ta sunkuyar da kai ta bata amsa
‘Mommy ce tace na taho dasu na dawo tayaki kwanan.’
‘To shiga muje ga Amira can tana bacci a dakin sai ta tayaki ki ajiye kayan ku fito muyi breakfast.’
Ta amsa ta wuce dakin, ita kuma Aisha ta koma kicin inda take aiyukanta.
Tana aiki tana dariyar Zahra; tabbas ta tabbata mai fuska biyu. Wato yana tafiya ta turo aka kirawo mata ‘yarta saboda kada ta tayata kwana, yanzu kuma da yake ya ce yau zai dawo shine har ta turota. Wato duk tsagerancinta ma akwai wanda take tsoro, sai dai tsoron Allah ne kawai bata yi. Haka tayi ta aiki tana dariya ita kadai.
Karfe shida da rabi na safe jirgin su Abba ya sauka a Nigeria. Suna sauka Malam Sule yana jiransu, a nan airport din ya sami taxi ya sa Yaya Bello don a kai shi gida kai tsaye.
Tun da suka fara shirin dawowa dama ya sanar da su a gidan Zahra zai sauka. Tayi shiri sosai na dawowarsa, an gyara gida sosai sannan ga abinci ta shirya masa funkaso da farfaesun naman Sallah ga zobo kuma sai kamshi kawai ke tashi.
Karfe takwas saura kwata motar Malam Sule ta tsaya a bakin gate din gidan Zahra, Malam Sule ya danna horn suna jiran mai gadi ya zo ya bude.
Dan ga ruwan da yake kawowa Aisha ruwa ne ya zo ya tsaya a bakin gate dinta, Abban yana hangoshi. Ya dauki dutse ya kwankwasa gate din ya dawo ya fara sauke jarkokin ruwan a wajen.
Abban ya dubi Malam Sule yace
‘Malam Sule me dan ga ruwa yake a kofar gidan can?’
‘Ah, yallabai Ina ga ai ruwa ya kawo amma ban sani ba, ko na karasa na tambayo Hajiyar?’
A dai-dai lokacin mai gadi ya zuge gate din, Abban ya