Showing 132001 words to 135000 words out of 166068 words

Chapter 45 - UWAR SADIKU COMPLT BY SAKINA YAZID.txt

11 Jul 2024

25404

iya gane hakan ba sai lokacin da yayi fushi da ke ba tare da wani dalili ba don yanzu kam kin yi abun fushi. Kawai ki gyara kuma ki bashi hakuri.'

Ta riga ta san daman haka Yaya zata ce don haka tayi shiru.

Daga baya YayaMurjan tayi mata sallama ta tafi.
__

Duk yanda yake jin haushin Zahra ya san dole yau ya ganta tunda kwananta ne. Sai da ya gama duk abinda zai yi ya ci abincin dare a gidan Aisha sannan wajen tara da rabi ya shiga gidan Zahra.

Duk yanda ya so ya kyaleta bata bashi dama ba saboda yanda ta sameshi a daki ta saka shi a gaba da kuka tana bashi hakuri. Ta bashi tausayi sannan kuma baya son ganinta a damuwa don haka da wuri ya nuna mata ya hakura. Ya dan ci abincin daren da ta dafa duk da a koshe yake. Haka suka kwana babu yabo babu fallasa.

Gari yana wayewa bayan sun gama cin abinci yara sun tafi makaranta ya daukesu ita da Yusra suka wuce asibitin.
Sai a lokacin Zahra ta sami natlsuwa da taga Saddikun, suka dan taba hira har ta tambayeshi ina motarta. Sai a lokacin ya tuna da motar inda yace mata bai sani ba sai dai ko ta tambayi Abba don wayarsa ma Abban aka bawa kuma har yanzu Abban bai bashi wayar ba. A halin da ake ciki ba zata iya maganar motar ba don lallabawa takeyi ta kankarowa kanta mutunci don haka tayi shiru.

Basu dade ba Yaya Bello ya iso ya samesu, suka gaisa da Zahran sannan ya jajanta mata jikin Saddikun. Shi da Abba suka shiga ofishin likitan, sai da suka fi minti talatin suna tattaunawa sannan suka fito; domin likitan ne ya hadasu da masu rehabilitation center din. Suna fitowa aka rubutawa Saddiku sallama.

Yusra ta taya Muhammadu suka kwaso kwanukan abinci wadanda duk na Aisha ne suka zuba a motar Malam Ali da yake jiransu, Abba ya bawa Muhammadu kudin mota yace ya wuce gida. Har ya kama hanya Yusra tace masa

‘Yaya Muhammadu kwanukan ba na gidanku bane ko a kawo daga baya.’

Yace

‘Ba na gidanmu bane na gidanku ne fa.’

Kafin suce wani abu Abba yace

‘Na Antinki ne idan kun je gida Malam Ali zai kai mata.’

Sai da Zahra tayi da gaske sannan ta danne damuwarta kada Abban ya ga sauyi a fuskarta; wato mutan gidan Bello da Aisha sun fita mahimmanci a rayuwar yaranta shi yasa ya danka musu Saddikun ya hanata ganinsa bayan babu wanda ya haifar mata yaron. Lallai!

Daga gefe guda likitan ne tsaye da Yaya Bello da Abban suna magana, bayan Saddikun ya zuba kayan hannunsa a motar Malam Ali ya karasa ya cewa Abban ya fito.
Abban ya dubeshi yace

‘Kaje ka yiwa Mommynka Sallama daga nan zamu wuce da kai makaranta ni da Yaya zamu kai ka.’

Ya amsa ya wuce wajen su Mommy din.

Tayi zaton da ita za aje taga makarantar amma Abban yace ba haka za ayi ba su wuce ita da Yusra Malam Ali ya mayar da su gida, shi da Yaya Bello zasu kai Saddikun.

Shi kanshi Abban sai da ya kula da yanda ta fusata, ta shige motar ta rufe domin Yaya Bello ma da ya taho yayi musu sallama sai hakura yayi ya tsaya wajen Abban yayinda Malam Ali yaja motar.

Abba yaja motar shi da Yaya Bellon suka nufi kan titin gwarzo road inda daga nan ne zasu kara neman kwatancen makarantar.

Har suka isa gida Zahra ba tayi magana ba saboda yanda zuciyarta take tafasa; wato yanzu kenan Bello shine zai dinga tsarawa yaranta rayuwa saboda sun mayar da ita ‘yar iska shi da dan uwansa. Za a kai mata yaro makaranta amma bata ma isa a kaita ta ga wajen ba kenan idan wani abu ya sami Abban Bello ne kawai ya san inda Saddiku yake.

Gaskiya ba zata jure ba, wulakancin ya isa. Bata san me ta tsarewa Aisha da Bello ba suka janye mata hankalin miji, amman dole ta dauki mataki.

UWAR SADDIKU


Written by


Sakina Yazid
(Innar su Amal)


39
Sai da aka bawa su Abban Sadik takardu suka cike sannan aka nuna musu dakin Saddiku, bayan nan kuma aka yi musu bayani cewa ba zasu ziyarceshi ba sai bayan sati biyu. Babu waya a hannunsa don haka aka basu lambar wayar da za a iya kira ayi magana da shi. Mutum biyu kawai ake so wadanda sune zasu dinga ziyartar sa don haka Abba ya sa sunanshi da na Yaya Bello a kan su kadai ne za a dinga bari suna ganinsa. Sukayi masa sallama suka taho zuciyar Abban cike da damuwa yana fatan Allah ya sa kafin ya dawo Saddikun ya fara samun natsuwa.
Haka suka fito suka bar Saddikun shima yana matse hawaye yayinda kwakwalwarsa take kokarin gamsar da shi cewa iyayen nasa basu daina son sa ba.
__


Tunda aka kai Saddiku makarantar nan Zahra ta kasa nutsuwa. A da idan tana cikin damuwa Abban ne yake kwantar mata da hankali, yanzu kuma da take cikin tsananin bukatar hakan yayi burus da ita. Bai taba hanata kwananta ba amma dai babu wata hira da take shiga tsakaninsu; ita tana jin haushinsa kuma tana fushi yayinda shi yake ganin shine ya kamata yayi fushi ba ita ba. A halin yanzu ma kwata-kwata baya jin Zahra a ransa kamar yanda yake jinta a da.


Kusan kwana goma kenan da kai Saddikun amma duk ta rame tana neman fita hayyacinta saboda damuwa da rashin bacci, gashi kullum ta dan sami baccin sai ta yi mafarkin Saddikun a wani yanayi mara dadi.


Ranar asabar ce don haka yara sun tafi tahfiz, don haka ta koma dakinta ta kwanta tunda maigidan ba awajenta yake ba. Tana kwanciya bacci ya kwasheta.


Yana zaune a wani waje mai kyau da haske, shimfidun wajen farare ne tas haka ma kujerun. Yana zaune a kan kujera cikin shigar fararen kaya, sai dai abinda ya firgita ta shine yanda duk kyan wajen da kuma kyan shigar Saddikun kuka kawai yake faman yi yana matse hawaye. Magana take yi masa iya karfinta amma ko jinta bayayi, kuka yake mai ban tausayi harda shessheka.


Haka ta farka a firgice.


Irin wadannan mafarkan da takeyi su suke daga mata hankali; ta san dai kuka ba alkhairi bane to me yasa take ganin Saddiku yana kuka?


A hankali ta sauko daga kan gadon, har zata tashi sai kuma ta koma ta zauna. Ta mika hannu ta dauko wayarta a kan durowar gefen gado ta lalubo lambar Abban Saddiku ta buga masa; bayan ya dauka ta sanar da shi tana so taje gidan Yaya Murja. Ba tare da bata lokaci ba ya bata dama tunda Malam Ali yana nan.


Hijab kawai ta saka saboda bata ma da kuzarin canza kaya, ba tare da bata lokaci ba Malam Ali ya dauketa suka fice.


Ba karamin dadi taji ba lokacin da ta shiga gidan Yaya Murja ta tarar babu kowa a falon kasa; wanda falon amaryar Yaya Murja din ne. Kai tsaye ta haye sama, inda ta tarar da Yaya Murja zaune da yaranta suna hirarrakinsu. Cike da farin ciki yaran suka yi mata oyoyo, ta karasa ta zauna a kusa da yayarta. Gaba daya yaran suka matso suna gaisheta yayinda Yaya Murja ta umarci Hibba; yarinyarta ta uku wadda Yusra ta girmeta da shekara daya; ta debo ruwa ta kawowa antinta.


Bayan yaran sun gama gaisheta sannan ta fara gaisawa da Yaya Murja, a nan ta fahimci kanwar tata tana cikin damuwa don haka ta jata suka shige daki.


Suna zama a gefen gadon ta kifa kanta a kan cinyar Yaya Murja ta fashe da kuka. Bata hanata ba sai da tayi mai isarta tayi shiru don kanta, ta janyo tissue a kan durowar gefen gadon ta goge hawayen sannan Yaya Murja wadda take kallonta da mamaki tace


'Allah ya sa dai lafiya.’


Ta karasa face majinar da ta taru a hancinta ta ajiye tissue din a kasa sannan tace


'Yaya na rasa yanda zan yi da Abban Sadik, wallahi ji nake kamar an canza min shi.’


'To me kuma yayi?’


'Hmn! Yaya kin san har yanzu bai gaya min inda ya kai Saddiku ba? Gaba daya ma ko kula ni baya yi a cikin gidan harkar gabansa yake yi. Idan a kan abinda ya faru da Saddikun ne ai na bashi hakuri amma sai ya dinga faman share ni kuma ba zai gaya min inda ya kai min yaro ba, kashe ni yake so yayi tunda idan na mutu bashi da asara ya auri wata matar?’
Yaya Murja tayi murmushi ta kamo hannun Zahra ta rike a nata hannun tana kallon fuskarta a nutse, sai da suka dauki kusan minti daya a haka sannan tace


'Abinda nake so dake shine, kwata-kwata ki cire tunanin kishiyarki a ranki idan kikayi haka shine zaki iya fuskantar rayuwarki kiyi gyara a inda kike bukatar hakan. Kin ji ko?’


Ta gyada kai alamar ta fahimta, sannan Yaya Murja ta cigaba


'Abban Sadik mijinki ne kuma a halin yanzu laifi kika yi masa, ki sake kwantar da kai ki bashi hakuri. Ki sake janyo shi a jiki kamar yanda kuke da. Kuma ina son ki kwantar da hankalinki, Saddiku dansa ba zai taba cutar da shi ba don haka ki barshi ya nemawa yaronsa lafiya. Kada ki sake yi masa maganar Saddiku. Ki nuna masa duk yanda yayi da yaransa dai-dai ne, ke dai so kawai kike ku koma kamar yanda kuke a da. Ki kuma nuna masa duk wani laifi da kika yi masa da wanda kika sani da wanda baki sani ba ba zaki sake ba; domin kin san wani lokacin maza saboda mulki ba zasu gaya mana laifin ba sai dai muga sauyi a halayyarsu. Kuma kullum dare ki dinga tashi musamman ranakun da ba kwananki ba kina yin sallar dare kina addu'a, wallahi a hankali zaki ga komai ya dawo dai-dai.’


Ta gyada kai; ta sami natsuwa da wadannan kalaman duk da dai babu yanda za ayi ta cire kishiya daga lissafinta tunda ta san duk abubuwan da suke faruwa da ita sa hannu ne na kishiya. Amma dai tayi alkawarin zata gwada shawarwarin Yaya Murja.


'Shi Kuma Saddiku ki cigaba da yi masa addu'a amma don Allah ki bari a gina rayuwarsa. Kinga yaranki kamar mu suke, dukkansu mata sai shi kadai namiji. Idan ya bi hanyar lalacewa zasu taso basu da wani uba bayan ranmu. Kina kallo mu iyayenmu duka sun rasu yanzu Yaya Muhammad muke takama da shi; to da ya zama dan shaye-shaye ai da kinga bamu da sauran gata a duniya.’


Cikin sanyin murya tace


'Hakane.'


'Yauwa.'


Saida suka dauki lokaci Yaya Murja tana kwantar mata da hankali sannan da magriba ta fara kawo jiki tayi mata sallama ta kama hanya.


Duk yanda lokaci ya kure sai da ta tsaya a gidan Amina domin tana so ta samu tabbacin maganarsu tana nan ta zuwa wajen malamai.


Bayan a sun gaisa da Aminan ta rakata daki ta duba Ummansu wadda take kwance sannan suka dawo falon Aminan suka zauna.


A nan suka cigaba da kulla yanda da zarar Umma ta dan ji sauki zasu kai ziyara wajen malamansu don samarwa kansu mafita a aurarrakinsu wanda a halin yanzu suke cikin wani hali.


Sai bayan sun yi sallar Magriba sannan Zahra ta fito suka kama hanyar gida da Malam Ali.


—----


A ‘yan kwanakin nan jikin Hajiya kara rikicewa kawai yakeyi, duka da cewa Yaya Bello a tsaye yake a kanta. Kusan shekaru biyar kenan tana fama da hawan jini wanda daga baya ya hade mata da diabetes. Shi yasa ma kullum Yaya Bello yake zuwa yana bata abincin da kansa don ya tabbatar ta ci abinda ya dace. Sai dai duk da haka ‘yan kwanakin nan da an samu jininta ya sauka sai kuma diabetes din ya tashi, idan kuma ya yi sauki sai jinin ya sake hawa. Haka dai suke lallabawa.


Ranar Juma'a ce don haka da wuri Abban Sadik ya tashi daga aiki. Ya je ya gaida Hajiya da safe amma duk da haka yaji yana so ya sake komawa, don haka ba tare da bata lokaci ba ya juya kan motarsa ya nufi gidan Hajiyan.


A kwance ya sameta a dakinta tana hutawa, ya shimfida dadduma a gaban gadon ya zauna. Ta rage yawan hira sosai don haka a mafi yawancin lokuta sai dai kawai su sakata a gaba su zauna. Bai dade da zama ba akayi kiran sallar Magriba, don haka ya tasheta ya rakata har kofar bandaki ta shiga ta yiwo alwala. Sai da ta zauna a kan daddumar ta inda zata yi Sallah sannan ya fito ya barta da Anisa ya nufi masallaci.


A masallacin suka hadu da Yaya Bello wanda shi kuma ya zo ne don ya duba Hajiyan ya bata abincin dare.


Tuwon alkama da miyar zogale Yaya Bello ya kawo mata; wanda shine abincin da ta fi so tun da aka hanata cin shinkafa. Anisa ce ta dauko musu plate ta kai musu daki don yau Hajiyan gaba daya ta ki fitowa falo. Haka suka saka ta a gaba ta dan ci tuwon kadan tace ta koshi, sai shayin goruba da aka hada mata ta shanye kofi guda.
Ta koma kan gadon ta kashingida ta barsu zaune suna ‘yan hirarrakinsu a tsakaninsu.


Sai da akayi sallar isha'i sannan suka yi mata sallama suka tafi suka barta da Anisa da mai aikinta kamar yanda suka saba.


………


Tun ranar da Zahra taje gidan Yaya Murja ta dawo ta aikata duk abinda yayan ta bata shawara; tunda ta fuskanci a halin yanzu bata da wata mafita da ta wuce hakan. Don haka babu laifi Abban Sadik din yana dan sauraronta duk da dai har yanzu bai ce mata komai a kan Saddiku ba.


Kwananta ne yau don haka yana dawowa daga gidan Hajiya ya tsaya a gidan Aisha yayi mata sallama sannan ya wuce gidan Zahra.


Kamar yanda suka saba karfe goma sun gama komai ya rufe gida, shi da ita ma sun yi shirin bacci.


Tana kwance idonta a rufe domin bacci ya fara daukanta yayinda shi kuma yake zaune a gefenta da computer dinsa a kan cinyarsa yana aiki. Karar wayarsa ce ta farkar da ita, ta gyara kwanciya yayinda ya kai hannu kan durowar gefen gadon ya dauki wayar. Lokaci ya fara dubawa ya ga karfe sha biyun dare har da minti goma; sai da gabansa ya fadi domin ya san ba lafiya ba tunda yaga Yaya Bello ya kirawoshi a wannan lokacin.


Yana kara wayar a kunnensa kafin yayi wata magana Yaya Bello wanda kana jin muryarsa zaka san kuka yake yace


'Yusufa Hajiya lokaci yayi, sai dai muyi hakuri.’


'Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun!’


Katse wayar kawai yayi ya ajiye computer dinsa ya mike a dai dai lokacin da itama Zahran ta tashi zaune tana tambayar abinda ya faru. Ya dubeta yana fitar da kwalla yace


'Hajiya ta rasu, yanzu zanje na gani.’


'Inna lillahi wa Inna ilaihi rajiun! Allah Sarki.'


Sukayi shiru na dan lokaci yayinda ya cigaba da kokarin saka kayansa. Ya dauki mukullin motarsa ya nufi kofa, ta mike tana fadin


'Allah yayi mata Rahama, Allah ya hada fuskokinmu a aljannah.'


'Amin.'


‘Zamu taho da safe ni da yaran.’


'Ku bari sai mun yi waya tukunna, zan turo Ali ya kai ku.’


Yayi mata sallama ya fice.


……..


Kafin gari ya waye labarin rasuwar Hajiya ya zagaya gari. Karfe tara na safe aka gama hadata aka kaita makwanci. Sai da aka dawo daga makabarta sannan Abba ya sanar da iyalansa su taho, don haka gaba dayansu suka taho. Itama Aisha saida ta biya ta dauko Amira sannan suka wuce saboda ko ba komai ta samu wadda zata debe mata kewa a gidan.


Kafin yamma gida ya cika da dangi da abokan arziki, domin Hajiya Balaraba mace ce mai mutane sosai. Allah bai bata haihuwa da yawa ba domin yara hudu kawai ta haifa, kuma da yake ita kadai ce matar mahaifinsu sai suka zama basu da ’yan uwa. Duk da haka tana da dangi da yawa, domin mahaifinta yayi aure-aure kuma ya tara yara su goma sha takwas. Lokacin da tana da jajayen sawunta yanuwanta da suke mafi yawansu mazauna Sumaila ne suna zumunci da ita sosai, sai dai daga baya bayan rasuwar mahaifinsu Yusuf din da dukiyar ta kare a hankali kowa ya janye jikinsa. Yanzu kuma da aka sami labarin rasuwarta kowa ya zo ana ta kuka ana tuna alkhairinta lokacin da tana da hali.


Duk yaranta suma sun hallara da ‘yayansu, Ummulkhairi ce kawai bata iso ba wadda a Lagos take zaune inda aure ya kaita. An riga an sanar da mijinta rasuwar wanda yayi alkawarin shi da ita zasu biyu jirgi kafin magriba zasu iso.


……..


Tun Hajiya tana da lafiyarta ta bar wasiyyaa cewa idan ta rasu kada ayi mata zaman makoki, amma saboda ‘yan uwanta wadanda suka taho daga Sumaila da kuma Ummulkhairi da yaranta su biyar wadanda sai sunyi sati biyu sannan zasu koma Lagos haka aka hakura aka yi zaman na kwana uku. Duk wanda ya tambayi Saddiku haka Yaya Bello yake cewa yana makaranta suna jarrabawa shi yasa ba a gaya masa rasuwa ba.


Ranar da aka kwana uku da safe Yaya Bello da kansa ya shiga har cikin gidan ya sanar da mata cewa bayan azahar zai sa a kawo mota za a mayar da su Sumaila. Duk yanda Yaya Saratu ta so ya bari a kai bakwai bai ma saurareta ba. Itama Ummulkhairi da taji wannan sanarwar take ta sanar da shi tana so ita da yaranta su wuce gidan Yusuf su karasa kwanakin nasu a can. Don haka ta karfin tsiya Yaya Bello ya sallami kowa aka share makoki.
Azahar nayi shima Yaya Bello ya tattara iyalansa a gaba suka koma gida tare da Najma ‘yar wajen Ummulkhairi. Iyalan Abba suka shiga mota Malam Ali ya ja suka tafi, shi kuma Abban ya dauko Ummulkhairi da yaranta wadanda zasu karasa hutunsu a gidansa. Yaya Saratu kawai suka bari a kan ita sai da yamma zata tafi sai a bar mai aikin Hajiya da kuma Innani kanwar Hajiya tare da Anisa wadanda sai daga baya zasu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login