Showing 72001 words to 75000 words out of 166068 words

Chapter 25 - UWAR SADIKU COMPLT BY SAKINA YAZID.txt

11 Jul 2024

25387

kwana a dakin nan kuma ka gani.’

Ya nuna masa robar coke din da kwalbar maganin da ke hannunsa yace

‘Wannan fa ko suma ba a nan aka dauka ba.’

Ya mariraice

‘Ba nawa bane Abba. Balele ne ya sha ruwa a nan jiya shine ya mantasu, wallahi ban san ma menene ba kuma ba nawa bane shi yasa ban dauke ba.’

‘Sadik, Sadiku ka bi a hankali. Zan bincika idan na kamaka da wani laifi tamu ce ni da kai. Shi kuma Balelen zai zo ya sameni, gobe zai bar min gidana. Daman na san yaron nan yana shaye-shaye sai anyi magana Mommy tace ba haka bane, gobe zai bar min gidana.’

Ba tare da yayi magana ba ya fice daga dakin.


Rahama ta kalli Sadiku suka hada ido yayi mata wata gajeriyar dariya ya fada kan katifarsa ya kwanta yana dariya.

Jijjiga kai kawai tayi ta janyo kafarta ta fito daga dakin.

A falon kasa ta sami Abban, yace

‘Kada ki damu zan bincika, yaran nan sun iya karya da dabara a kan abinda suke so, zan yi maganinsu. Gobe Malam Sule zai dawo ya karbi aiki, Balele ba zai sake shigo min gida ba.’

Jijjiga kai kawai tayi ta shige kichin; duk da Balele yana kama da ‘yan shaye-shaye ta san wannan ba kayansa bane za dai a koreshi ne ba da hakkinsa ba. Har yanzu tana mamakin Sadiku, lallai yaraon yau sai a barshi.

An riga na gama assalatu har an tayar da sallar asuba, don haka ta wuce dakin baki inda a nan take kwana tare da Sumayya da Ummi. Tayi alwala ta tayar da Sallah.

Bayan ta idar da sallah ta gama azkar dinta ta dauki wayarta don taga lokaci, tana dubawa taga ashe Zahra ta kirawota wajen sai biyar. Tana da dan credit dinta don haka ta dannawa Zahran flashing. Jimawa kadan ta kirawo, bayan sun gaisa tace

‘Sadik yace min kin dauki abinda ba shi ya ajiye a dakinsa ba kin kaiwa Abbansa.’

‘Eh, dama rashin fahimta me amma ai ya yiwa Abban bayani ma shike nan.’
‘To don Allah dai ko menene yaran nan sukayi a yi hakuri a jira sai na dawo ko a yi min waya, a daina saurin hadasu da ubansu; ni na baki amanarsu in sunyi wani abu ni zaki gayawa ba wani ba.’

‘To in Sha Allahu. Babu ma abinda sukeyi muna zaune lafiya ai.’

Sukayi sallama.

Rahma ta bi wayar da kallo; wato warning Zahra take mata a kan kada ta hada Sadik da Ubansa; lallai! Da ba dan anyi abu cikin girma da arziki da ita ba ma da yau zata bar gidan nan, amma tabbas idan ta tafi ba zata sake zama a gidan nan ba. Wato kenan su yaran Zahra ba za suyi laifi; tabbas ita ta san abinda ta gani kuma shima Sadikun ya sani don haka ma har ya kirawo me kare ma sa ya tsara mata karya da gaskiya . Um!
___

Kiri-kiri Abba ya kori Balele daga aiki, sai dai ba a bashi dama ya kare kansa ba domin tabbas shi din ma yana shaye-shayen amma bai taba zuwa da abun maye gidan ba kuma bai taba zuwa gidan a buge ba. Gashi yana da in-ina don haka ma kafin yace wani abu aka yanke masa hukunci. Ya mikawa Abban mukullin mota ya fice, a ranar kuma ya dawo da Malam Sule aiki.
…………..

Bayan an sha ruwa Mommy din ta yiwo waya Yusra ta sanar da ita an dawo da Malam Sule, a lokacin ta kara shiga damuwa. Kamar dai duk wata tufka da ta taho ta bari an fara biyota da warwara. Ta zata wani direnban za a dauka amma an dawo da Malam Sule. Wannan ya kara kasa mata hankali acan Saudiya din.
__

Duk wani shirye-shiryen bikin Sallah an kammala don a yanzu saura kwana uku Sallah.

Makocin gidan Zahra wanda gidansa yake kallon gidan shine commissioner of Environment na Jihar Kano wato Alhaji Mamman Ahmad Yakasai.

Tun kafin a fara azumi gwamnatin Jiha take gangamin dashen bishiyoyi, ko ina an shuka. A yau commissioner ya ciko motar Hilux guda biyu da bishiyoyi don mutan unguwar su samu su shuka a unguwa da kuma gidajensu.


Bishiyun sun hada da na goba, gwanda, umbrella sai kuma bishiyar malmo da kuma ta madaci.

Gidan commissioner akwai masallacin a jiki wanda yawancin mutanen kan layin a nan suke khamsi salawati. Kuma da yake commissioner mutum ne mai son mutane da alkhairi in dai yana nan wajen baya rabuwa da mutane.

Nan kofar masallaci commissioner ya sa aka sauke bishiyun ga kuma matasa su kamar shida wadanda zasu shuka bishiyun.

Abba yana cikin mutane da suka fito daga masallacin daga karshe tare da liman, suna fita suka tsaya da commissioner da mutanen unguwa ana gaggaisawa.

Ya kama hannun liman yana nuna masa bishiyun yana cewa

‘Malam liman gasu fa, kaga goba da fruit kowa ya dauka a shukawa yara a cikin gidan don kaga gobar nan mai dadi ce kuma ‘yayanta manya ne sosai. Wadannan kuma da basa ‘yaya duk a shuka mana su a unguwa.’

Ya kama hannun Abba yace

‘Education! Teacher uban karatu. Ga goba nan a shukawa amarya don ina hango gidanta ko ganye babu.’

Yayi dariya suka cafke hannu

‘To sai na gayawa Uwargida in ya so tayi anti party.’

‘Kaina bisa wuyana kar kasa a mayar dani kauye, Uwargida ma a shuka mata goba harda fruit duk a hada.’

Nan liman ya sa hannu aka rarraba bishiyun, guda biyar aka warewa Abba goba biyu fruit biyu da kuma malmo wanda za a shuka a kofar gidan Aisha don gate din gidan Zahra bishiyar har guda hudu ne a wajen.

Yaran da aka taho dasu don shuka bishiyun suka fara dauka kowanne mai gida yana nuna musu gidan da zasu je su shuka masa.

Wani yarone matashi ya kwashi na gidan Abba, da hannu Abban ya nuno masa gidan Aisha yace duka a nan za a shuka domin gidan Zahra akwai bishiyar mangoro da kuma bishiyar ayaba, ga gwanda wajen bishiya hudu a jikin katanga.

Har ya juya zai wuce gaba ya rakasu sai kuma ya fasa, ya dauki waya ya kirawota. Bayan sun gaisa yace mata ga yaro nan zai shuka bishiya a cikin gidan ta bude gate.

Suna ajiye waya ya nunawa yaron gidan yace yaje za a bude masa.

Ya kwasa ya wuce ya bar Abban suna ta hirarrakinsu da mutane.
UWAR SADDIKU


Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)


25

Daidai lokacin da yaron da zai shuka bishiyar ya tsallako tare da abokin aikinsa dai-dai lokacin ta bude gate din. Suka gaisheta, bayan ta amsa ta ja baya suka wuce ciki. Har ta kama hanya zata koma ciki yaron wanda ake kira Masta yace

‘Hajiya a dai-dai ina zamu shuka, Alhaji cewa yayi a sa hudu a cikin gida biyu a waje; naga cikin gidan da dan fili ta wane gefen zamu saka?’

Ta dan karewa tsakar gidan kallo tace

‘Kusa biyu a nan gaba, biyun kuma sai ku saka a bayan gida.’

Har ta juya kuma sai ta sake tsayawa ta juyo ta nuna gefen gidan in an tafi za a zagaya dai-dai tagar dakin Abban tace

‘Ka shuka daya a nan, yanda idan ta girma zata dinga kare rana don da rana ta fito take shiga dakin nan ta taga.’

‘In sha Allah Hajiya.’

Tana wucewa suka fara aiki.

An kusa shan ruwa kuma so suke su gama kafin a sha ruwan don haka nan da nan suka fara aiki.


Suka shuka bishiyar umbrella guda daya da kuma goba guda daya a gaban gidan. Suka zagaya bayan gidan suka shuka bishiyar goba guda daya don wajen bashi da sarari sosai umbrella ba zata sami wajen budewa sosai ba.

Wajen tagar dakin Abba nan ne karshe, sai da Masta ya auna sosai tunda an ce masa ana so ta dinga kare rana, ya dan bada tazara kadan ya kara kusantar katangar tunda tagar dama bata da nisa sosai daga katangar. Yana hakawa daya yaron yana kwashe kasar.
Yana cikin hakawa ya daki roba, daya yaron yace

‘Kada fa ka fasa musu pipe Masta.’

‘Haba Baabaa, sai dai ko wata robar banza don da da dapipe a wajen nan Hajiya ba zata ce a shuka bishiyar a wajen ba.’

Ya saka hannu ya ficiko gutsuren robar, gaba daya ta taho amma sai dai ta riga ta dagargaje. Take suka kunduma ashar saboda wani wari da doyi da ya dumame wajen. Abinda yake cikin butar yayi tsalle waje daya saboda yanda aka finciko butar. Baabaa yace

‘Wannan wane irin bala’in wari ne mutumina?’

Ya goge hancinsa ya karasa kan abinda ya fita daga cikin butar, ya sa fatanyar hannunsa ta dungurin abun da yake nade a bakin kyalle yace

‘Kutumar uba, kai Baabaa ai ga warin nan.’

‘Bari na dauko ledar da muka cire sauran bishiyun mu nade a ciki kawai mu jefa a shara.’

‘Ai wallahi sai na bude bakin kyallen naga ko menene wannan, nifa ji nake kamar warin jaba ne kuma aka hada shi da wani abun da yafi jabar wari.’

Ya wuce ya nufi dauko ledar yana mita

‘Kai wallahi masta ka fiye jangwale-jangwale, daga hako abu sai kace sai ka bude. Yanzu ba zaka bari muyi mu gama aikin nan kafin a sha ruwan ba sai ka bata mana lokaci.’

Yana bude bakin kyallen yana toshe hanci kuma yana bawa Baabaa amsa

‘Ai ni na fi so mu sha ruwa a nan, Alhaji sawa zai yi a bamu dankali da kwai harda shayi, in muka tafi kuwa ka san sai da kyar ma zamu sami kunu da kosan.'

Suka saki baki gaba daya suna kallon ikon Allah, bayan ya gama cire bakin kyallen abinda yake ciki ya bayyana.

Kan jaba ne wanda gaba dayansa an rubuceshi da hatimi da wasu kalmomi sannan an tsiyaye idanuwan jabar. Bakin jabar kuma an kawo wani bakin kwado an huda sama da kasan bakin an datse kwadon, ga kuma wata laya da aka ajiye daga kan goshin jabar aka kawo allura aka soke layar a jiki.

Masta ya kalli baba, ya kara goge hancinsa yace

‘Wallahi wannan abun tsafine, ai wannan ma idan bamu fitar dashi ba gidan nan ba zai zaunu ba don ciki ma sai dai su fito su fice.’

Take Masta ya mayar da kan cikin bakin kyallen ya dauka ya nufo gate, Baabaa ya rufo masa baya.

Suna fitowa ya nufi kwalbatin da yake kofar gidan zai jefe, sai Baabaa ya dafa kafadarsa yace

‘Ka ga, mu kirawo mai gidan mu nuna masa tukunna.’

‘To kai idan fa shi yayi wa wani asirin ya binne a wajen.’

‘Shikenan asirinsa ya tonu don kaga ina jin wancan mutumin limami ne kuma da alama da iliminsa.’

Ya fada yana nuna Abba wanda yanzu su uku suka rage a kofar gidan commissioner; shi da liman da kuma commissioner.
Masta yace

‘Kuma ka san yanzu mutane har makota suke yiwa asiri ba, rike min nan na tsallaka na kirawosu su su gani.’

Ya mikawa Masta bakin kyallen ya karba yana tofar da yawu, shi kuma ya tsallaka.

Yana zuwa dab da su ya dan rage tsawo yace

‘Yallabai akwai matsala a gidan can fa da muka je shuka bishiyar.’

Commissioner yace

‘Subhanallah, Allah ya sa dai ba wani abun kuka faso ba garin shukar.’

‘Ba mu fasa komai ba yallabai amma dai gara Alhaji ya zo ya duba.’

Ya dubi Abba yace

‘Mu karasa mu gani, Allah ya sa ba pipe suka faso ba ko suck away.’

Suka tsallako Abban yana addu’ar Allah ya sa a kofar gidan ne don baya so ya shiga gidan a gaban commissioner da liman don ba zai iya tsayawa a gidan ya dade ba.

Tun kafin su karasa tsallakowa gaba dayansu suka ji wari, haka suka daure suka karasa.


Commissioner yace

‘Meye yake wari haka ne a wajen?’

Masta yace

‘Yallabai ai abun da muka hako ne garin shuka bishiyar, shine nace gara dai shi Alhaji ya duba kafin mu yar.’

Liman yace

‘Wannan ma ai baza a yar ba sai dai ko a binne din don idan an yar ma haka zai yi ta damun mutane da wari; kana azumi wannan warin ai sai ya bugar da kai.’

Suna karasawa bakin gate din Abba ya dafe kai, ya dan tsaya kafin su kai kusa da Baabaa wanda yake rike da abun. Commissioner da yake kusa da shi yace

‘Alhaji Yusufa yaya dai, naga fa kamar tsayuwar tana neman gagararka?’

Murya kasa kasa yace

‘Warin nan sa min ciwon kai yake.’

Yanda yaga yanayinsa ya sa ya dafe shi, ya dubi liman yace

‘Malam liman duba su binne wannan abun kawai, bari mu sami wajen zama kada Alhaji Yusuf ya fadi fa ka san akwai kishin ruwa.’

Ya karasa shi da Abba, suka sami waje suka zauna a kan kwalbatin da yake gidan kusa da gidan Aishan. Shi dai Abban ya zauna ne kawai don baya son ace matsalar daga gidansa ce kuma ya tafi ya barsu, amma har nan inda ya zauna yana jin warin kuma kansa juyawa kawai yakeyi.

Su Abba suna barin wajen Baabaa ya tsuguna ya budewa liman abinda yake cikin bakin yadin. Ya tsuguna yana dubawa bayan ya toshe hancinsa.

Ya karewa abun kallo yana fadin

‘Subhanallah.’

Ya saka tsinke ya gama jujjuya kan jabar ya kare masa kallo tas, ya sa waya ya dauki hoton abun sannan ya fara karanta addu’oi yana tofawa abun. Ya tofa kul a’uzai, kulhuwallahu, ayatul kirsiyyi sannan ya tofa la haula.

Yana cikin tofawa da yake zuwa lokacin kan ya dan yiwa Abba sauki commissioner ya taso ya zo ya sami Malam liman, ya tsuguna a kusa da shi da hancinsa a rike da hannunsa yana kallon ikon Allah. Bayan liman ya gama tofin commissioner yace

‘Malam liman wannan fa?’

‘Alhaji wannan da ka gani tsafi ne, ka ga wannan bakin kwadon da wannan allurar da aka soka a goshin kan nan Allah ne kadai ya san fitnar da suke haddasawa wanda akayi wannan ta’asar domin a cuce shi.’

‘Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun.’

Ya dubi su Masta da suke tsaye a gefe yace

‘Kuma a gidan Yusuf din kuka sameshi.’

‘Eh wallahi, don ma mun dan haka ramin bishiyar da zurfi ne da ba zamu sameshi ba don an binneshi da zurfi.’

Liman ya dubi Baabaa yace

‘Balle min kwadon nan ka zare wannan allurar, yanzu sai a kunna wuta a kona shi. Shikenan ba zai sake tasiri ba da izinin Allah.’

Nan ya fara cukucukun balle kwadon yayinda Abba ya dubi Baabaa yace

‘Koma cikin gidan ka karbo ashana a wajen matar gidan.’

Kafin ya kawo ashanar Masta ya balle kwadon ya zare allurar, nan take liman ya matsa gefe daya ya hada ‘yan karare ya jefe abun ya kunna wuta. Suka dan matsa gefe shi da commissioner suna kallon abun yana ci da wuta, yayinda ya umarci su Masta da su shiga su shuka bishiyar amma su dan matsar da ita kadan daga inda suka cire abun.

Suna nan tsaye abun yana ci da wuta Abba ya dan ji ciwon kan ya sauka har ya fara samun nutsuwa, don haka ya taso ya zo ya samesu.
‘Malam liman me ya faru ne, menene yake wannan azabar warin don Allah.’

Ya nuna masa yace

‘Gashi nan an sa masa wuta.’

‘Ikon Allah, to meye wannan din Malam Liman? Kuma a cikin gidan suka samo shi?’

‘Eh, a ciki suka samo shi mana. Amma gashi an koneshi, kaji warin ma ai ya ragu sosai kuma da zarar ya gama konewa zai bi iska shikenan. Idan muka hadu a masallaci bayan tarawih in sha Allahu zaka ji bayani; don ka ga yanzu zan karasa gida ne kafin na sake fitowa masallaci.’

‘Hakane, to babu laifi.’
Sukayi sallama gaba daya, Malam liman da commissioner suka tsallaka.


Kafin Abban ya bar wajen su Masta suka fito suka ce masa sun gama. Ya tambayesu ko a nan zasu sha ruwa suka amsa da eh, don haka yace maigadinsa zai miko musu abinci gidan commissioner din su kara.

Har zai shiga gidan kuma sai ya fasa ya kama hanyar gidan Zahra. Wannan warin da ya shaka yau ya kusa sumar da shi gashi azumin yau ya wahalar da shi, baya son ya shiga gidan ya shan wahala.
…………


Suna hanya su biyu commissioner yace

‘Wai meye wannan din Malam liman, nifa ban gane ba?’

Saida ya jinjina kai sannan yace

‘Ai wato ranka ya dade wannan abun fa tsafi ne. Gaskiya asiri ne aka yi watakila don a raba shi da matarsa da take wannan gidan ko wani abu mai kama da haka.’

Ya dan zaro ido

‘Allah Malam liman?’

‘Ai kwarai kuwa. Kaga wannan kwadon da yake bakin abun nan to duk wanda aka yiwa wannan tsafin ba zai iya bawa wani labarin abubuwan da yake ji yake gani ba balle ma a taimaka masa da wani abu na magani. Wannan allurar kuwa da aka caka ina tabbatar maka itace musabbabin wannan ciwon kan da yayi da yaji wari. Yallabai ka kalli fuskarshi kuwa lokacin da ya shaqi warin nan? Baki fa fuskarshi tayi, don ni gani nayi ma kamar shirin zurawa da gudu yakeyi sai naga ka dafe shi.'

‘Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun! Malam Liman kaji wata fitna, kai da iyalinka a shiga tsakaninki.’

‘To mutane basu tsoron Allah.’

Sukayi shiru kowa da abinda yake ransa, jimawa kadan commissioner yace

‘Ai kuwa sai ka san yanda zaka bashi labarin nan don kada yaje ya fara zargin mutane fa, kaga bamu da wani tabbas. Musamman ita daya matar tasa. Tab! Allah abun tsoro dan Adam abun tsoro.’

‘Ai in sha Allah ba zan masa bayani sosai ba, tunda kaga ko a danginsa ma ko nata ita matar wanda ke jin haushinsu zai iya yi, ko kuma manemanta wadanda ya kasa ya aurota ko ma a kawayenta; komai zai iya faruwa. Shi yasa nace ya bari sai an jima don kafin nan na tsara abinda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login