Showing 30001 words to 33000 words out of 201092 words
Chapter 11 - AMRAH NAKE SO BOOK COMPLETE DOCUMENT .txt
zuwa aka bata, sannan muka nufi laboratory domin awon jini.
Bayan an gama auna mata mun fito, Annur ya ce,
"Umma bari dai na je a min wannan awon, ba dan komai ba sai dan na tabbatar, idan AS gare ni tun wuri sai na san hanyar bi domin tsayar da haihuwa, duk da dai jikina baya bani hakan."
Ajiyar zuciya na sauke,
"Haka Nake so Annur. Bari mu jiraka a can har ka dawo."
Ya tafi, mu kuma muka zauna jiransa.
Kusan awa d'aya ya da'uka sannan ya dawo, fuskarsa k'unshe da murmushi, farin ciki ya gagare b'oye kansa. Hannunshi d'aya rik'e da takarda, d'ayar kuma a cikin kansa yana wasa da sumar kansa.
Tun daga nesa yake furta,
"Umma kin gani ba, dama na fad'a miki."
Bayan mun mik'e taye na ce,
"AA gare ka ke nan?" Ni d'in kaina ina murmushi.
"AA gare ni Umma, kar'bi takardar ki gani."
Bayan na duba ne na tabbatar da maganarsa. Da gaske abin da ya fad'a. Wani irin dad'i na ji ya kewaye ilahirin zuciyata, na kalli Amrah da ita kanta da'din ne ya mamaye ta.
Da farin ciki muka isa gida, wanda sai da muka biya ta Crispy ya mana take away na abinci da lemo kafin muka isa.
***
Rayuwa ta ci gaba da tafiya, kwanaki na gudanya, muna 'kara kusanta ga Allah, har Amrah suka gama jarabawarsu duka, WAEC DA NECO d'in. Wata da'ya kacal ya rage aurenta.
A iya wannan lokacin har lefenta an kawo, akwati saiti biyu, da kaya na ji da fad'a, zan iya cewa tun da nake a rayuwata, ban ta'ba ganin kayan lefe kamar na Amrah ba.
Sadakinta naira dubu d'ari aka kawo, komai dai sai hamdala. Fatana a ko da yaushe, shi ne Allah Ya kawo farin ciki a rayuwar auren Amrah. Yanda Hajiya Suhaila ke nuna mata gata da soyayya, ina fatan d'orewar hakan har gaban abada.
Saitin kayan d'akinta da Mallam ya siya mata masu kyau, ba wasu na 'karya ba ne sosai, iya k'arfinsa ya yi, kuma a hakan ya samu rufin asiri. Komai ya yi kyau sosai.
A makuna hud'un da ya yi saura na auren Amrah, babu abin da bamu gama ha'dawa ba. Hatta da kayan abincin da za a ci lokacin aure mun gama had'awa. Kayan kitchen d'inta bakin gwargwado mun had'a mata. Dama 'yan uwana sun had'a min gudunmawa tun watan da ya gabata sun bani, da su na 'kara na mata siyayyar kayan kitchen d'in, kayan 'yan gayu, wanda na san mai rayuwar Abuja zata iya buk'ata. Dama kuma sun ce kayan kitchen ne kawai za a tafi Abuja da su, kayan d'akinta a nan Katsina zata barsu, gidansu wanda zasu ringa sauka idan sun zo. Abujan babu abin da basu zuba mata ba.
Da murna ta shigo cikin gida, bayan ta cire hijabinta ta zauna kusa da ni.
"Fuskarki ta bayyanar da farin cikin da kike ciki. Da alama an faranta miki rai."
Da murmushi ta ce,
Umma, sati mai zuwa zamu tafi Sudan, kin san na fad'a miki a can za a yi musabak'ar k'asa da za a yi. Umma ni na haye a duk fad'in ka'sar nan, ni da wani namiji da'ya ne kawai zamu wakilci Najeriya, shi zai zama na b'angaren maza, ni kuma a b'angaren mata. Shi d'in d'an jihar Gombe ne."
Cike da farin ciki na ce,
"Alhamdulillahi Ya Allah! Kai amma wannan labari ya min da'di sosai wallahi. Har na ma rasa me zan yi dan murna. Allah ubangiji Ya taimaka Ya bada sa'a. Allah Ya baku ikon d'auko ma K'asarmu lamba ta farko a wannan gasa.
Oh ni Murja! Wallahi jin abun nake tamkar a mafarki, wai 'yata da na haifa da cikina zata tafi wata K'asa gasar Al-Qur'ani mai girma, kuma wai 'Kasa baki d'aya zata wakilta.
Ke alheri ce Amrah! Ke abar alfahari ce, wacce ko wace uwa zata so samun irinta. Ke abar koyi ce Amrah, wacce ko wace macen kirki zata so zama irinki.
Allah Yana tare da ke Amrah, insha Allahu zai taimaka miki, zai baki nasara. Kuma na yi alk'awarin zan hana idanuwana bacci in kwana ina miki addu'ar samun nasara."
"Ameen Umma. A lokacin da zancen nan ya tabbata, har da hawayen farin ciki na yi. D'alibaina kansu sun taya ni farin ciki. Daga masu kukan murna sai masu hawayen farin ciki. Matan auren da nake koya ma har da wacce ta rungume ni, wai ina ma iyayena zasu bata kyaur Malama Amrah, wallahi da ta gwada min k'auna fiye da yaran da ta haifa da cikinta."
Ni d'in ma rungumarta na yi, idanuwana na kawo ruwa, ban sake ta ba, haka kuma a tsaye muke bamu zauna ba.
A haka mallam ya tarar da mu, tun bai nemi bayanin dalilin halin da muke ciki ba, na hau zayyane masa komai, ina yi ina hawaye mai had'e da dariya.
"Abin da ya dawo da ni gida ke nan, Murja. Ina wurin aiki na ji wani abokina yana saurarar radio, kamar an ce na d'aura kunnuwana a bisa bayanan, caraf kunnuwana suka jiye min sunan 'yata, a matsayin wacce zata wa'kilci K'asa baki d'aya, a musabak'ar da za a gudanar ta K'asa, a 'Kasar Sudan.
Na kasa gasgata hakan, sai da na ji muryar Malaminsu da kanshi, yana mai nuna irin farin cikinsa. A k'arshe na ji muryar jakadan musaba'ka na jiha, yana nuna tashi murnar, da d'aya daga cikin d'aliban jiharsa ce zata wakilci 'Kasa ta b'angaren mata.
Abun nan ya min dad'i kwarai da gaske. Na sake jinjina wa kaina, ke, da kuma 'yata. Tabbas samun 'ya kamar Amrah babbar sa'ar rayuwa ce.
Amrah 'yata, ba zan ta'ba gajiyawa da shi miki albarka ba. Ba zan ta'ba daina miki fatan alkhairi ba."
A haka wannan rana ta zame mana ranar farin ciki, farin cikin da na jima ban yi irinsa ba.
Shi yasa ake so ka gode wa Allah a duk halin da kake ciki. Ka karb'i duk irin yanayin da mahaliccinka Ya yi ka. Kar ka butulce maSa saboda wata jarrabta da Ya yi maka, ko ba komai ka fi wani. Idan baka da lafiya, ka gode maSa, idan ka gode maSa, sai Ya baka ta wani fannin.
Gashi dai duk wahalar da kika sha tsawon shekaru goma sha shida da watannin da na haife ki kike fama da ciwo, ciwo kuma mai matu'kar wahala, wanda babu wuya mutum zai iya kauce ma sharia, ya ji kamar shi ne aka fi tsana duk duniya. A haka muka jure, muka dage da addu'a, muka tsayanta Allah d'aya ne. A hakan da wahalar da kike, muka tarbiyyantar da ke, muka d'ora ki a bisa tafarkin kirki.
A k'arshe mun ga ribar hakan, kin zama abar alfahari gare mu, malamanki, makarantarki, jiharki, da ma 'Kasarki baki d'aya."
Annur kanshi sanda ya ji wannan labarin ya matuk'ar jin dad'i. Shi a gidajen talabijin ma ya ga sanarwar, kuma daga 'kasa aka mak'ala sunanta.
Cikin lokaci k'ank'ane magana ta gama kewaye 'Kasa. Sunan Amrah ya shiga wurare da dama wanda bata ta'ba mafarkin zata je ba, sai ga sunanta ya je. Mutane da dama suke son ganinta, suke san sanin wai wacece wannan yarinyar mai tarin baiwa, wacce ta k'etare mutane da yawa, ta zama wa'kiliyar 'Kasarta?
Ranar da zasu tafi, har Kano muka rakasu, ita da Malaminta.
A iya inda zamu rabu, na kama hannuwanta duka biyun, na kalle ta cikin ido, na ce
"Ina miki fatan alkhairi 'yata. Ba zan tab'a daina yi miki addu'a ba. Insha Allahu nasara tana tattare da ke. Allah Ya taimaka, Ya bada sa'a. Ki kula da kanki, Amrah."
Wasu irin zafafan hawaye suka ringa kwarara daga idanuwana.
Cikin kuka take wasa da hannuwana, cikin kuka take k'irk'iro murmushi, cikin kuka take fad'in,
"Zan kula da kaina insha Allahu, Umma. Ki yafe min duk wani abu da na miki, b'oyayye da kuma bayyananne."
Zare hannu guda na yi daga cikin nata, da shi na share hawayen da ina share sa ina dambe da wani, wanda ke shirin sake fitowa.
"Baki ta'ba yi min komai ba Amrah. Banda alkhairi babu wani abu a tsakanina da ke. Idan ma akwaishi, na yafe miki."
Na sakar mata murmushi.
"Allah Ya 'kaddara saduwarmu, Umma." Ta fad'a had'e da zare hannuwanta daga nawa, ta rik'e na mahaifinta.
Tun bata furta komai ba ya ce,
"Baki ta'ba yi min komai ba 'yata. Idan ma akwai to na yafe miki. Ina mai neman gafararki, a bisa halin da muka jefa rayuwarki a ciki. Har yanzu na kasa yafe wa kaina. Har yanzu gani nake mu ne sila, mu muka jefa ki cikin wannan cutar. Ki yafe..."
Bai rufe bakinsa ba ta saka tafukan hannunta ta dafe masa bakin nasa,
"Bana son jin haka daga gare ka, Abbana. Komai na duniyar nan da zai samu mutum, to k'addararsa ce. Na sani, na kuma yarda cewa tawa k'addarar ke nan. Babu mai k'in d'aukar k'addara face butulu. Kar ka damu Abbana. Na yafe maka duniya da lahira. Na yafe maku kai da Ummana."
Cikin hawaye take murmushi.
Gaban Annur ta koma, wanda tun d'azu idonsa yake cikin nata.
Murmushi ya 'kirk'iro mata, ba tare da ya furta komai ba.
"Zan tafi Hammana. Ka yi min addu'ar samun nasara."
"Nasara na tare da ke insha Allahu, Amrah. Allah Ya taimaka, Ya bada sa'ar abin da aka je yi."
Lumshe idanuwanta ta yi, sannan ta sake bud'e su a kanshi.
"Kar ka manta da ni, Hammana. Duk rintsi duk wuya, kar ka manta da Amrah. Ni ma ba zan tab'a mantawa da kai ba."
Gyad'a mata kai ya yi, idanuwanshi cike da shauk'in soyayya,
"Idan har zan iya mantawa da ke, to tabbas zan iya mantawa da kaina. Ke ce rayuwata, Amrah. Ke ce duk wani tunanina. Na so a ce tare zamu yi tafiyar nan, sai dai kuma Allah bai nufa ba. Ni ma tafiya ta taso min, zuwa K'asar Malaysia, ina tunanin sai kamar ana gobe zaku fara zan dawo. Amma duk da haka, rayuwata tana tare da ke, zuciyata tana tare da taki. Motsinki da komai naki yana tare da nawa. Ina matu'kar k'aunarki."
Juyowa ta yi ta kalle mu, cikin jin kunya ta sunkuyar da kanta k'asa.
Saurin d'auke kallonmu muka yi daga gare su.
"Na gode k'warai Hammana. Na gode da sadaukar da rayuwarka da ka yi a kaina. Na gode da k'aunar da ka nuna min. Na gode da komai ma."
Ta fashe da kuka sosai.
"Ya isa haka to, please. Kin sani sarai, kin san yanda hawayenki yake da zafi a gare ni. Kin san yanda na tsani ganin zubar hawayenki. Kin san yanda rayuwata ta tsani ganin kin yi asarar hawayenki. Ki tafi, ga malaminki can yana ta jiranki."
"To Hammana. Allah Ya k'addara saduwarmu." Ta tafi.
Har ta isa iyakarmu da su bata daina waiwayenmu ba, bata daina hawaye ba.
Baki d'aya jikina ya yi sanyi, na rasa dalili. Duk da ina son tafiyar tata, na san ci gaba ne a gare mu baki d'aya, amma a hakan ji nake kamar ta fasa tafiyar, kamar ta dawo gare mu.
A haka muka kama hanyar parking lot. Muka shiga motar Annur, muka kama hanyar dawowa Katsina.
_Tabbas soyayya gaskiya ce, wacce Allah ne yake d'aura ma mutum ita, ba tare da zuciyarsa ta shawarce shi ba. Abu mafi dad'i a soyayya, shi ne ka had'u da mai sonka tsakani da Allah. Ka had'u da mai k'aunarka, wanda zai sadaukar maka da rayuwarsa. Ina rok'on Allah Ya had'a mu da masoyanmu na gaske. Allah Ya aurar da mu ga masoyanmu na gaske._
pinky durling💗
*RAZ 2*
[8/30, 3:36 PM] Princess Amrah✍🏻💞: *🅰MRAH NAKE SO!* ♥
(Labari mai taba zuciya, soyayya, sadaukarwa da kuma ban tausayi.)
Na Amrah A Msh
_(Princess Amrah)_
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
_Sadaukarwa ga masu cutar amosanin jini (sickler)_
2⃣0⃣
_Sa'kon gaisuwa ga tarin masoyan *AMRAH NAKE SO!* Kuna da yawa sosai, lissafo ku ba abu ne mai sau'ki ba. Sai dai duk inda kuke, ku sani cewa ana tare, ina yinku irin sosai d'in nan.😍_
***
Tun da muka shiga mota nake kuka, na rasa dalilin da yasa hankalina ya gaza kwanciya, damuwa da k'unci fal a cikin zuciyata.
Mallam ne yake rarrashina, amma duk da haka na gagara yin shiru, ruwan hawaye basu daina kwaranya daga idanuwana ba.
Bayan mun isa Hajiya Suhaila ta kira Annur a waya, har ya shaida mata cewa daga Kano muke, mun raka Amrah ne zasu tafi Sudan.
Wayar tasa ya bani, ta nunar min da rashin jin da'dinta sosai, a bisa rashin yi mata bankwana da Amrah ta yi. Sam! Bata ji da'din hakan ba. Kuma ko kad'an tafiyar bata zata nan kusa ba ne, bata zata cikin satin ma zasu yi tafiyar ba.
Ha'kuri kawai na bata sannan muka yi bankwana. Annur d'in ma ya bar gidan, wanda shi kanshi idan ka kalle shi zaka tabbatar yana cike da damuwa.
Ko da dare ya yi haka bacci ya gagara d'aukata, na ringa juyi, damuwa ta gama mamaye kaf ilahirin zuciyata. Yau d'in nan Amrah ta tafi, amma ji nake kamar ta yi sati bata nan.
Rayuwarta nake tausayi, mafi rinjaye a k'aunar da nake mata, ta ta'allak'a ne da tausayinta da nake, tausayin rayuwarta, tausayin yawan ciwukanta.
Tuno bankwanan da muka yi da ita kawai nake, ina tuna murmushin da take yi mai had'e da ruwan hawaye, da kuma yanda ta ringa wasa da hannuwa.
Wasa ba wasa ba, yanda na ga rana haka na ga dare. Jin kiraye kirayen sallar asuba na yi, wanda ko kad'an ban zata daren har ya kai haka ba.
Bayan gari ya waye ne Mallam ya duba wayarsa, ya ci karo da text da ta masa cewa sun sauka lafiya, yanzu haka suna masaukinsu.
Hamdala na yi a lokacin da ya bani labari. Ban san sanda na saki wani murmushi ba. Baki d'aya zuciyata na ji ta wanke, duk k'uncin da nake ciki babu shi.
"To Alhamdulillah! Sauka lafiyan dama ake buri. Zan kira ta anjima insha Allahu, gudun kar na shiga lokacinta yanzu."
Mallam ya furta shi d'in kanshi farin ciki lullub'e da fuskarsa.
A kai a kai muka ringa gaisawa da ita a waya, duk sanda zamu yi waya kuwa zan shi mata albarka, zan mata fatan alkhairi. Haka ma mahaifinta.
Ana gobe zasu fara musabak'ar Annur ya dawo, ya zo gaishe mu ne nake masa tad'inta, ta ce min za a nuna musaba'kar a tashoshi da dama, ciki kuwa har da sunnah tv, ni kuma gashi bamu da kayan kallo.
"Zan zo har nan mu kalla a waya' insha Allahu. Ai ina nan sai ranar Sunday zan tafi. Na san zasu saka live a internet."
Annur ya fad'a yana min murmushi.
Cike da jin dad'i na ce,
"Yauwa to, aiko da na ji dad'i sosai. Allah Ya nuna mana goben lafiya."
"Ameen, Umma. Bari na tafi. Idan Abba ya dawo a gaishe shi."
"Zai ji 'kwarai. A gaishe da Hajiya Suhailar. Ka mata albishir, ta tara gobe ta kalli 'yar tata."
"Zan fad'a mata, Umma."
Ya tafi.
Washe gari kuwa kusan k'arfe goma sai gashi ya zo. Malam dama ya ce ba zai fita aiki ba har sai sanda muka gama kallon musabak'ar, ko kwana nawa za a d'auka ana yinta kuwa.
Ko da ya kunna mana muna kallo, da 'Kasar Egypt aka fara. Namijin ya fara sannan macen ma ta yi.
A haka aka ringa yi, ba laifi karatu ya yi sosai, sai dai abin da ba za a rasa ba.
Har aka gama ta ranar ba a kira Najeriya ba. Haka yasa Annur ya ce zai tafi, gobe insha Allahu kafin a fara zai dawo, sai mu ci gaba da kallo.
Hakan ce kuwa ta kasance. Abun mamaki har a ranar ma ba a kira K'asarmu ba.
Sai ranar k'arshe, wacce kuma ita ce Annur zai tafi, amma a haka ya kashe tafiyar ranar, ya mayar da ita ranar litinin, dan kawai ya faranta mana rai.
Najeriya ce ta k'arshe, sai da namijin ya yi, kafin aka kira Amrah don ta yi.
Ban san sanda na mik'e ba, ganin 'yata ta doso mazaunin masu musabak'ar, cike da natsuwarta.
Wani kwali ne mai kyau aka mik'o mata, wanda a cikinsa ne ta d'auko takarda guda d'aya, ta mik'a ta ga wani wanda aka tanadar domin mik'awar kawai, shi kuma ya isar da ita ga alk'alan musabak'a.
Jan farko aka fara yi mata, a cikin suratul Bak'arah. Haka ta ringa zayyano karatunta babu kuskure, ko jar danja d'aya ba a mata ba har aka haska mata tsanwar danja, wadda ke nunar da zata dakata daga nan.
Wani jan aka mata, cikin suratul Yunus, nan ma dai haka ta ringa karatu babu kuskure ko kad'an. Daga nan sai suratul Noor. Murmushi ta saki a sanda aka jawo mata ayar farko, tana jin da'din surar, tana matuk'ar son surar, gata kuma sunan sahibinta ne.
Tun asali ta sha wahalar surar ne, sanda take hardarta har kuka ta ringa yi, saboda matuk'ar wahalar ayoyin cikinta. Amma daga sanda ta iya, sai k'aunarta da take yi.
Kamar mai bada labari haka ta ringa karatu, babu kuskure bare tangard'a a karatunta.
Cikin ja na hud'u ne aka ja mata suratul-Yaseen.
A nan kam ta dad'e tana karatun, saboda wannan shi ne ja na k'arshe da za a mata, kuma dama a kan jima kafin a dakatar da mutum. To gashi kuma dama ita ce mutum ta k'arshe a musaba'kar baki d'aya.
A daidai "kun fa yakun." Ta dire, tun bata fad'i ayar k'arshen ba ta kwanta a saman bencin, saboda irin kujerun nan ne masu had'e da teburinsu, amma na k'arshe, masu k'irar gidan sarauta.
Tana duk'ewa kuma da alama dama ta kai k'arshe, tsanwar danja aka haska mata, wacce ke nunar da ta gama karatunta ke nan.
Tun da ta duk'e bata taso ba, da dama an yi tunanin ko dan karatun da ta yi ne, saboda da wasu idan suna karatu kuka suke yi. Mu d'in ma kanmu haka muka yi zato.
Sai dai kuma abun mamaki, ta fi k'arfin minti goma a haka, ko motsi kanshi ya gagare ta.
Cike da mamaki aka nuno yanda alk'alan suke kallon kallo wa junansu, suna neman sanin dalilin duk'iyar tata.
Umurni suka yi ga d'aya daga cikin mata securities da suke gadin b'angaren da mata suke, kan ta zo ta ga ko kuka ya ci k'arfinta ne ya sa ta kasa ta shi.
Isowar kuwa ta yi inda take, kuma har a lokacin ba a daina d'aukar