Showing 129001 words to 132000 words out of 201092 words

Chapter 44 - AMRAH NAKE SO BOOK COMPLETE DOCUMENT .txt

ni to ni ma na san ki."


Ya saki dariya har da tafa hannuwa.


Dariyar suka yi su ɗin ma. Amma dai duk da haka akwai alamun ya ɗan tuna ta, ko ma dai yaya ne.


Sun jima a ɗakin Umma na masa firar Amrah, da surkulle da sokana dai yake ɗan amsa mata, wasu abubuwan kuma idan ya yi tamkar mai hankali, sai dai kuma a take sai sako shirme, wanda zai tabbatar da cewa shi ɗin mahaukaci ne ba mai hankalin ba.


Miƙewa Umma ta yi, ta ce,


"Bari in ƙoƙarta tafiya, lokacin dawowar Mallam gida ya kusa. Kar ya dawo bai same ni ba."


Mama ta ce,


"Aikam Umman Amrah babu inda za ki tafi sai kin ci abinci. Ai ina jin ma ba zai rasa ƙarisa dahuwa ba. Maryama je ki bincika."


Suka fita ɗakin a tare.


Sai da Umman Amrah ta ci abinci ta yi sallar la'asar sannan ta tafi. Da godiya suka rabu da Maryama, tana mai tsananin jin daɗin kalaman Umman Amrah, na cewa za ta rinƙa zuwa akai akai, har zuwa lokacin da zai samu lafiya ya koma asalin gidansu.


Da yamma Mama da Maryama suna zaune a falo, bayan Muhammad ma ya dawo daga Islamiyya yana ta musu zuba, wayar Mama ta ɗauki ƙara. Daga jikin chaji Muhammad ya ciro ya miƙo mata, ta duba ta ga Abba ne ke kiranta.


Da sallama ta ɗauki wayar, sai dai a maimakon ta ji Abba ya amsa sallamar, akasin haka ta samu. Cike da masifa ya ce,


"Na turo Mallam Ya'u yanzu yanzun nan ya zo ya ɗauko ku. Ku zama cikin shiri, zai kawo ku gidan Yaya Imrana ne. Ina nufin har da Maryama."


Bai jira ya gama sauraren tambayar da Mama ke masa ta lafiya? Ba, kawai ya datse wayarshi.


Cike da mamaki ta kalli Maryama, fuskarta na nuna zallar damuwa, ta ce,


"Wai mu shirya yanzu Mallam Ya'u zai zo ya tafi da mu gidan Yaya Imrana. Allah dai Ya sa lafiya."


"Ameen."


Maryama ta faɗa baki ɗaya jikinta babu ƙwari. Miƙewa ta yi babu kuzari ta nufi ɗakinta, ta ɗauko dogon hijabinta ta saka, sannan ta zauna da wayarta a hannu, tunani da fargaba sun taso ta gaba, tana son sanin haƙiƙanin dalilin wannan kiran na gaggawa da aka musu.


Bayan kamar mintina sha biyar sai ga Mallam Ya'u ya iso. Da sallama ya shigo ya sanar musu cewa su fito su tafi. Haka suka mimmiƙe jiki babu ƙwari, shi kanshi Muhammad fargabar abin da zai iya faruwa ce ta ɗarsu a zuciyarsa. Fatan samun nasara kawai yake, har suka isa gaban motar.


Muhammad ne a gaba, sai Maryama da Mama a bayan motar, bayan sun tabbatar ma mai gadi cewa ya kula da Annur da ke ciki, ba za su kulle ba gudun samuwar wata matsalar.


Da isarsu aka buɗe musu babban gate ɗin gidan. Gida ne babba mai matuƙar girma, wanda ke ƙunshe da parts kusan guda biyar.


Bayan sun faka motar ne suka firfito, dreba kawai suka bari a ciki, su kuma suka ƙarisa part ɗin kawu Imrana, da hasashen a can za su samu Abba.


A babban falon suka yi sallama. Ɗaki ne mai girma, wanda ya ƙawatu da kayan alatu. Sanyin AC duk ya gama garwaye ɗakin, ga wani irin ni'imtaccen ƙamshi da ke tashi ta kowacce kusurwa.


Tsit ɗin da suka samu a ɗakin ne ya matuƙar ƙara razana su. Ga Abba da Kawu Imrana jere bisa 3 seater, sai Deedah zaune a ƙasa, ya sunkuyar da kansa.


Kawu Imrana ne ya amsa sallamar, haɗe da sakar musu murmushi, yana mai basu izinin ƙarisowa ciki.


A ƙasa Maryama da Muhammad suka jera, suka gaishe da kawun nasu, yayin da Mama ta zauna can nesa da su, bisa 1 seater.


"Sannunku da zuwa Hajiya."


Kawu Imrana ya ce da Mama, a lokacin da take gaishe shi.


"Yauwa Yaya. Allah dai ya sa lafiya, mun ji kiran gaggawa..."


Tun ba ta rufe bakinta ba Abba ya fara masifa,


"Ina fa lafiya. Ƙaramar yarinya kamar Maryama tana neman miyar da mu wasu shashashu, wanda ba su san abin da suke ba. Wato ita har ta yi ƙamarin da babu kunya za ta nunar da ba ta son Ahmadu ko? To wallahi ba ta isa ba! Ke ba ki isa ki baɗa mana ƙasa a idanuwa ba. Yaran yanzu sam! Ba ku san arziƙi ba."


Da hannu Kawu Imrana ya dakatar da shi, yana murmushin dattako ya ce,


"Ya isa haka Balarabe. Ba a haka ai. Ni yanzu duka ba wannan ne dalilin da ya sa na tara ku ba. So nake na ji bayani daga bakin Maryama."


Ya juya ya fuskance ta, ya ce,


"Ƴata kina son Ahmad ko bakya son shi? Ko kaɗan ba na so ki ji kunya ko kuma nauyin faɗi, feel free and tell me, babu wanda ya isa ya miki auren dole. An wuce wannan zamanin ai tunin duniya. Dama tun farko na ji daga bakin Ahmad ɗin ne, kuma shi da kanshi ya faɗa min irin shaƙuwar da take tsakaninku. Ki faɗa min gaskiya, tun daga cikin zuciyarki."


Kuka ne ya kufce ma Maryama, ta sadda kanta ƙasa, tana mai rasa dukkanin nutsuwarta. Ta ma rasa me za ta faɗa. Shin ta yaya za ta iya buɗe bakinta a gaban Kawu Imrana da kuma shi kanshi Deedah ɗin ta ce wai ba ta son shi? Abu dai da kamar wuya. Ba ma za ta taɓa iya wannan ta'asar ba. Ita ba ma ta san ta ya akai har zancen ya fito ba, cewa wai ba ta son Deedah.


Cikin kwantar da hankali Kawu ya ce,


"Ba na so ki cuci kanki ƴata. Wallahi na miki alƙawari zaɓinki za ki aura. Ƙin amincewa da auren Ahmad kuwa ba zai taɓa shafar dangantakarmu ba. Da a ce sai an yi a zo zumunci ya ɓaci, ai gwara tun wuri a tarbi abun."


Cikin ƙarfin hali take son shanye kukanta. Ta saka dukkanin hannayenta tana sharewa hawayen, sai dai kuma wasu sabbi ne ke saukowa.


Satar kallon Deedah ta yi, ta ga yadda ya baza dukkanin idanuwansa yana kallonta, yana mai son jin me za ta faɗa.


Da shessheƴa ta fara magana,


"Kawu, Abba, ku gafarce ni, ba na son a ce na zama silar ɓacin ranku. Amma wallahi ko kaɗan ban taɓa son Yaya Deedah da aure ba. Irin soyayyar da nake ma Hammad ƙanina ga shi nan, irinta nake ma Yaya Deedah. Ku yi haƙuri don Allah, amma a bar kowa da zaɓinsa."


Cikin zafin nama Abba ya taso da niyyar ya wanka mata mari, sai dai Kawu ya riga shi isa gare ta, ya san zuciyar ɗan uwanshi, ya san cewa dukan nata zai yi dama. Riƙe masa hannuwa ya yi, ya ce


"A kan me za ka dake ta? Don kawai ta faɗi ra'ayinta? Kar mu yi haka da kai Balarabe. Ko akwai wanda ya yi maka dole a sadda za ka yi aure? Babu. Haka ni ma babu wanda ya min dole. Matana uku a halin yanzu, babu wacce aka haɗa ni da ita, ko kuma aka mana auren dole. Duka auren soyayya ne. Saboda haka ƴata ma ban ga wanda zai mata dole ba. Wanda duk take so shi zan aura mata."


Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke Maryama. Tana jin wani irin daɗi a cikin zuciyarta. Damuwarta na ragewa, saboda jin kalaman Kawu. Sai dai kuma so ɗaya da ta haɗa ido da Abbanta ba ta sake marmarin kallonshi ba. Tsantsar jin haushinta da yake kawai ta iya hangowa a cikin ƙwayar idanuwansa.


"Yanzu Yaya goyon bayan wannan shashashar yarinyar za ka yi? To ni dai sam! Ba da yawuna ba. Ahmad Deedah na ce ta aura, ba kowa ba."


Murmushi ya yi Kawu. Ya dafa kafaɗar ɗan uwanshi, yana faɗin,


"Ashe dai har yanzu baƙar zuciyar nan da na san ka da ita tana nan. Sai yaushe ne za ka san ka girma Balarabe? Ka rufa wa kanka asiri ka rage wannan halin, ko kaɗan ba hanyar ɓullewa ba ce."


Gyaɗa kansa ya yi, ya ce,


"To idan ba ki auri Deedah ba uban wa za ki aura? Na ce uban waye wanda kike so?"


Bakinta kyarma yake, ta gaza furta komai, hankalinta na daɗa tashi. Kallon Mama take tana neman taimakonta, tana son jingina a jikinta ko za ta ɗan samu nutsuwa, amma ina, Mama ma harararta ta yi, tana mai tsananin jin haushinta.


Hammad ne ya riƙe mata hannun dama, yana mai ɗaga mata kai alamar ba ta ƙwarin guiwa, haɗe da sakar mata ɓoyayyen murmushi, wanda a tsakaninsu kawai za su san ya yi shi.


"Wallahi kin ji na rantse aure zan miki. Ko ki fiddo miji nan da sati biyu ko kuma in nemo duk wanda nake so in haɗa ki da shi. Wanda bai yi sharar masallaci ba ai ya yi ta kasuwa."


Tsananta duka kawai gabanta ke yi. Wani irin raɗaɗi take ji a cikin zuciyarta. Sauyi kawai take gani daga wurin Abbanta. Me ya sa zai mata haka? Shin kanta farau irin haka?


"Da ke nake magana!"


Ya zaro mata idanuwa, ya ma ƙi sauraren Kawu da ke dakatar da shi.


"Ka yi haƙuri Yaya. Amma na riga da na rantse. Wallahi aure zan mata, cikin kwanakin nan ba ma da nisa ba. Ba dai ni za ta kunyata ba? Kar ma ka yi ƙoƙarin dakatar da ni. Don Allah."


"What are you still doing Bala? Kana ɗaukar aure kamar wani abun wasa. Ta ya za ka ce aure za ka mata, babu wani binciken kirki?"


"Ita ta ja komai Yaya. Don haka ke nake sauraro. Waye shi, kuma ɗan gidan waye? Ban damu da wadata ko rashinta ba. Ke nake sauraro!"


A iya wannan lokacin kam tsoro ya gama mamaye dukkanin gaɓoɓin jikinta. Yana zagaya duk jini da jijiyoyinta.


Kallon da yake mata ne ya sa ta ƙoƙarta tattaro magana, ba tare da ta san me take faɗi ba, ta ce,


"Annur nake so!"


***


*You know what? 4k words na muku yau. The most longest page since after Sallah. Fatan kun ji daɗinshi sosai.*


*Readers, ya kuke ganin wannan al'amarin? Shin Abba ya kyauta kuwa wannan gaggawa da ya saka a auren Maryama? Zai amince da zaɓinta, duk dayake cewa Annur ɗin mahaukaci ne? Ta ya auren mahaukaci da mai lafiya zai yiwu? Idan har ya amince ɗin ma, a haka za ai aure babu danginshi ko ɗaya? Kodai za su miyarshi gida ne sannan a yi auren?*


*Amsoshin tambayoyin suna ga alƙalamin marubuciyar, sannu a hankali za ta warware mana dukkan tambayoyin.*


*Mutanena masu mutunci kuna ina? Kun ga dai na karkata na rubuto muku dogon shafi mai mutunci. Fatan kuma za ku karkata hannayenku zuwa ga ƴar tauraruwar nan domin ku kankaro min mutunci ni ma.😘😀*


*Ghosties kuma masu kama da cartoons, ku ci gaba da laɓe. Insha Allahu wayoyinku hucking za su rinƙa yi muku daga yanzu.😏*


Thanks all


Pinky durling💞
RAZ 2
[9/8, 12:49 AM] Princess Amrah✍🏻💞: *🅰MRAH NAKE SO!♥*


_(Labari mai taba zuciya, soyayya, sadaukarwa da kuma ban tausayi)_




Sadaukarwa ga masu cutar amosanin jini (Sickler)


Na Amrah A Mashi
(Princess Amrah)
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*




5⃣8⃣




Wattpad: Princess Amrah


***


"Wurin Amrah nake so ku kai ni. Kullum sai na sha fama da Dadyna da Momyna kan cewa su kai ni inda Amrah, amma sai su ce da ni wai Amrah ta mutu, ba zan sake ganinta ba. Ni kuwa ta kufto na gudo ba tare da sun sani ba. Ai za ku taimaka min ko?"


Dariyar yaƙe yake, amma kuma ruwan hawaye na sauka a bisa kumcinsa. Sai famar sauke ajiyar zuciya yake.


Sosai suke mamakin wannan mahaukaci. Muryarsa da duk yanayinsa iri ɗaya ne da Sans, ba su da bambanci. To waye wannan?


Kuka ya fasa mai ƙarfi.


"Don Allah ku ma kar ku ce min Amrah ta mutu. Kar ku ce ba zan sake ganinta ba. Wallahi Amrah nake so! Ita nake ƙauna, da ita nake da burin ci gaba da rayuwata."


Ya dafe kansa, tamkar wani mai cikakken hankali.


"Ina ne gidanku, kuma su waye iyayenka?"


Sans ya yi ƙarfin halin tambayarsa, duk da mamaki da ya gama garwaye dukkan saƙon da ke cikin zuciyarsa.


"Ban sani ba ni ma. Dady da Momy su ne iyayena. Amma ban san su ba, ban san gidanmu ba."


"To kar ka damu. Za mu kai ka inda Amrah. Za ka bi mu dai ko?"


Kansa ya ɗaga da sauri, har yana cin tuntuɓen magana, ya ce,


"Zan bi ku. Ku kai ni wurin Amrah, na tabbata ita ma tana can tana jira na mu yi aure."


Mamakin abin da Sans ɗin ya faɗa ne ya wanzu a zuciyar Bobby. Ya kalli abokin nashi yana son yin magana, amma ya ɗaga masa hannu, alamar kar ya ce komai.


"Kamar yadda kuke mamaki to ni ma haka nake yi. Kamar yadda ba ku san shi ba ni ɗin ma haka ban san shi ba. Haka kawai jikina yake ba ni something will happen, alkhairi ba sharri ba. Ku duba yanayin fatarsa, alamun ya ji hutu kenan. Da kuma suturar da take jikinsa, duk da kasantuwarsa mahaukaci, amma tsadaddu ne. Don haka na yanke hukuncin mu tafi da shi. Kuma koda ma a ce ba haka ba, abu ne mai matuƙar mamaki, mutum ya haɗu da mai kamanni sak irin nashi, ko kaɗan babu bambanci. Ba na jin zan iya tafiya in bar shi, har sai na gama bincike a kansa."


Jinjina kansa ya yi Bobby. Ya ce,


"Good thinking. To amma yanzu ya za mu yi da shi? Tunda ba gida za mu nufa ba."


"Wannan mai sauƙi ne. Yax ya tafi da shi a kan mashin. Mu kuma sai mu hanzarta tafiya asibitin."


"Amma kamar da wahala fa mahaukaci ya hau mashin ba tare da mai kula da shi ba. Kuma inda na san da haka da sai in ce ya zo da napep ai. Ko kana ga babu komai?"


Sans ya ce,


"Gaskiya ka faɗa kai ma. To ko za ku tafi da motar can gida ni sai in tafi asibiti a mashin ɗin? Na ga ai ba daɗewa zan yi ba."


Bobby ya ce,


"Ƙafarka fa. Za ka iya tuƙin mashin babu matsala?"


"Babu matsala Guy. Idan ma akwai, I'll give you a call."


Bobby ya ce,


"To shi kenan abokina. Bari mu wuce."


"A kula da shi sosai Guy. A ba shi abinci ya ci. A masa duk dabarar da ta dace kafin in dawo. Idan ka ji ni shiru ka kira ni."


Da haka suka rabu, su Bobby suka juya baya domin komawa gidan gonarsu, yayin da Sans ya haye bisa mashin ya kama hanyar shiga cikin gari.


*


Waya yake cike da ƙunci da damuwa. Jikinsa har karkarwa yake, yana faɗin,


"Inspector ban san sadda ya fita ba. Ba ni kaɗai ba, dukkan ƴan gidan ma babu wanda ya kula da fitarsa. Tun sadda ya kamu da ciwon nan yake attempting guduwa ake kama shi, daga ƙarshe ma aka fidda masa ɗaki guda haɗe da ɗaure shi, aka kuma datse ɗakin.


Ta yadda dai muke zargin fitarsa, wata ƙila ko sadda aka kai mishi abincinsa na rana ne wanda ya kai mishin ya manta bai rufe ƙofar ba. Tunda dama idan an kai mishi abincin kwance shi ake yi, har sai ya cinye sannan a koma a ɗaure shi, amma sai an datse ɗakin. To kuma bayan ya gama cin abincin ne aka tarar ba ya nan.


Inspector don Allah a taimaka mana, wallahi daga ni har mahaifiyarsa hankalinmu a tashe yake. Ba mu san inda Annur zai faɗa ba. Ba mu san a rayuwar da zai afka ma ba."


Sai a nan ya ci burki. Yana sauraron abin da inspector ɗin ke ce mishi.


"Ka cire damuwa daga ranka Pharm IA. Insha Allahu Annur zai bayyana. Za mu same shi a yau ɗin nan."


"Ina fatar hakan Inspector. Allah Ya bayyana shi. Na gode ƙwarai. Sai na ji ka."


Ya tsinke wayar daga nan, yana mai juyawa ya fuskanci Matarshi da ke ta famar kuka riris, ya ce,


"Ki yi haƙuri ki daina kuka. Da yardar Allah zai bayyana, cikin ƙoshin lafiya."


Shessheƙar kuka take, ta ce,


"Allah tabbatar mana."


Haɗe da share hawayenta, tana sharewa wani na daɗa saukowa.


Da yamman aka barbaza ƴan sanda domin neman Annur. Duk wasu tituna da ke cikin garin Katsina sai da aka watsa ƴan sanda. Daji daji haka suka rinƙa shiga. Saboda kuɗi ne masu mugun yawa Pharm IA ya tura musu.


*


Gudu yake sosai Sans, sai dai ya taka burki, a daidai isar shi wani check point, inda tun daga nesa ya hangi faskeken hoto irin nashi, sai dai ba shi ɗin ba ne.


Akwai layin motoci da mashina a gabanshi, saboda daidai junction ne. Hakan ya ba shi damar karanto rubutun da ke manne jikin hoton, cewa ana neman Annur Iqra Al-Hussein, mahaukaci ne, za a gan shi da kaya kala kaza, ya fita ne da misalin ƙarfe uku na rana.


Hasken traffic ne ya dalle rubutun, har Sans ya kai ƙarshe a karanta shi. Mamaki yake sosai, take zuciyarsa ta kitsa mishi abin da zai yi. Ba dai mahaukaci ba ne? Na san abun yi.


Ya lallaɓa ya yi kwana, ya bi one-way har sai da ya isa u-turn, sannan ya ci gaba da zura gudunshi, da nufin komawa gidan gona.


***


Cikin mamaki Abba ya kalli Maryama, bakinsa na rawa ya ce,


"Wane Annur ɗin kike magana? Kar dai ki ce min wannan mahaukacin."


Kai kawai ta ɗaga ma Abba, tana zubda hawaye sosai.


Ita kanta Mama sai da ta sha mamaki. Deedah ma kallonta yake ƙyam, yana nazartar yanayinta. Bai san komai da ke wakana game da Annur ba, kawai dai ya san cewa Annur ya zama riƙaƙƙen ɗan iska; manemin mata kuma mashayi. Amma don me Maryama za ta zaɓi wannan tuƙururun ɗan iska a matsayin abokin rayuwarta na har abada? Dama dalilin da ya sa ta taɓa tambayarsa Annur kenan? Gyaɗa kansa ya yi, yana jin ba zai iya yin shiru ba, dole ya yi magana a wannan gaɓar.


"Abba ku gafarce ni, zan ɗan yi magana."


Ya juya ya kalli Maryama, ya ce,


"Maryama ki rufawa kanki asiri, ba wai don kishi ko wani abu ba. Ba kuma ina miki buƙulun auren wanda kike so ba ne. Amma fa bai cancanke ki ba. Annur ba ya sahun mazajen da ya kamata a ce kin aura. Me ya sa? Maryam don me za ki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login