Showing 111001 words to 114000 words out of 201092 words
Chapter 38 - AMRAH NAKE SO BOOK COMPLETE DOCUMENT .txt
them? There's no! Don Allah ka yi haƙuri, mu taru mu dage da ambaton sunan Allah, muna sanar da shi halin da muke ciki. Mu haɗu mu ma matan can nasiha, tare da nusar da su cewa kuka babu maganin da zai mana baki ɗaya."
Wani dattijo da suka zauna a gaban mota tare ne ya ma Sans wannan maganar, cike da ƙarfafa masa guiwa.
Rage ƙarfin kukan nasa ya yi Sans. Ya dubi mutumin da idanunsa da suka kaɗa suka yi jajur. Cikin wata disasshiyar murya ya ce,
"Baba ya zan yi? Mahaifiyata na can cikin wani hali, yunwa da ƙishi har suna neman galabaitar da ita, ga shi kuma dama tana da matsananciyar ulcer. Ƙanwata ta jigatu, har tafiya ma ba ta iyawa da kanta. A cikin kunnuwana na ji harbin bindiga, wanda ya kawo ƙarshen wayar da nake yi da Abbuna. Na baro su ne cikin wani tsohon gini, da nufin in samu masu siyan wayata, ko zan sama musu wani abu su saka ma cikkunansu. Baba ga ni a nan, mota ta tsaya mana, mun rasa mafita. Ba dole na yi kuka ba?"
Kansa ya gyaɗa dattijon, sosai ya tausayawa yaron, musamman ma jin har da yarinya budurwa, yadda ƴan ta'addan suka dage tafiya da ƴan mata, abun ba a magana.
Cikin sanyin murya, mai nuna kwantar da hankali, dattijon ya ce,
"To ai ba kuka za ka yi ba, haƙuri za ka yi ka bar wa Allah lamurranSa. Ya san halin da muke ciki, kuma Shi zai fitar da mu. Idan Allah Ya sa mun samu taimako, mun samu man da zai fidda mu, na maka alƙawarin ni zan ba ka kuɗi daga aljihuna ka nemi wani abu ka siya musu, ba ma sai ka siyar da wayarka ba. Akwai kuɗi a hannuna, ni ma motar tawa lalacewa ta yi, wani aiki ya shigo da ni garin, ashe tsautsayin wahala ne ya shigo da ni."
Godiya sosai ya masa Sans. Daga nan suka ci gaba da ambaton sunan Allah, suna masu ƙanƙan da kawunansu.
Kamar an ce Dreba ya ɗaga kanshi zuwa titi, tun daga nesa ya hango wata hilux na dosowa daga cikin garin Bama. Kuma dukkan alamu sun nuna cewa ta sojoji ce. Hakan ya sa ya gaggauta sanar da sauran, suka tashi a tare suka nufi bakin titin.
Hannuwa suke ɗagawa su duka, cikin sa'a kuma hilux ɗin ta tsaya, wacce sojoji ne maƙil a cikinta, har a bodinta.
Tambayarsu suka yi abin da ke faruwa, take suka zayyane musu komai, da kuma tsawon awannin da suka ɗauka a wurin.
Babu wani tiyo wanda za su sa a zuqo mai, hakan ya sa Ogan nasu ya umurci sojojin da ke cikin motar, da su koma cikin bodi, wancan matan su shigo ciki, mazan kuma su yi skwatin a bodin. Da babu gwara ba daɗi.
Abin da ya faru ɗin kenan kuma. A haka suka ƙarisa cikin garin Maiduguri.
Suna shiga garin suka sassauka, a take dattijon nan ya ciri kuɗi masu yawa ya miƙawa Sans, ya masa fatar alkhairi sosai, tare da jaddada masa cewa sai ya bi a hankali wurin shiga garin Bama, musamman ma yanzu da dare ya yi.
Godiya ya masa Sans, sannan ya tari mai mashin, ya kai shi wata restaurant mai kyau. Abinci mai rai da lafiya ya sa aka masa take away, kusan wanda mutum goma za su ci, shi bai ma da nutsuwar cin abincin, ruwa kawai ya sha, sannan ya sai musu lemuka da yawa, ya kama hanyar tafiya.
Kai tsaye tashar mota ya dosa, inda zai samu motar Bama. Sai dai kuma a rashin sa'a, bai samu motar ba. Ga su nan jere birjik, amma duk sun ce ba za su shiga Bama a wanann lokacin ba, saboda abubuwan da suke wakana a can ɗin, duk suna da labarinsu.
Kuka yake sosai Sans ya marairaice fuska, ya zaro duka sauran kuɗin da mutumin ya ba shi, wanda za su kai darajar naira dubu ashirin da biyar. Dubu ashirin ya fitar daga ciki, sannan ya miƙa su ga wani dreba, ya ce ya taimaka masa ga kuɗin duka, ya taimaka ya kai shi. Firfir mutumin nan ya ce ba zai je ba. Wayarsa ya zaro daga aljihu, ya haɗa da kuɗin yana kuka, ya ce ya taimaka ya kai shi. Baki ya washe mutumin, ya ƙare ma wayar kallo. Babba ce ba ƙarama ba, sosai za ta yi kuɗi idan zai siyar.
Cikin murya ƙasa ƙasa ya ce,
"Na amince zan kai ka, amma bisa ga sharaɗin a bakin gari zan ajje ka idan mun isa, ba zan shiga ciki ba."
Saurin ɗaga kansa ya yi Sans, ya ce,
"Na amince wallahi."
Haɗe da hanzarin ɗaukar ledojin abincin, ya bi bayan mutumin suka isa wurin motarsa.
Yana jin yadda abokan aikinsa ke masa magana kan cewa kar ya je, amma ina, bai ko saurare su ba ya ƙeƙashe, suka kama hanyar Bama.
***
Ruwa mai sanyi ya kora Mahmouda, yana mai tsananin jin ɗaci da raɗaɗi a cikin zuciyarsa. Me ya sa Fiddou za ta masa haka? Dama abin da ya jima yana ji ma tsoro kenan. Shi ya sa tun asali shi bai yarda da soyayya ba. Bai kuma taɓa shiga ƙanginta ba sai a yanzu.
"Mahmouda ka yi haƙuri da duk kalaman da ka ji sun fito daga bakin Fiddou ka ji? Yarinya ce. Ita har yanzu gani take kamar soyayya da mahaukaci zai yi riba a gare ta, wanda kuma sam, hakan ba mai yiuwa ba ne a gare ta. Ina so ka ci gaba daga inda ka tsaya, tunda dai duk tsiyarta ai ba za ta taɓa ci gaba da rayuwa a haka babu aure ba. Na tabbata Modu ya tahi kenan, ba zai dawo gare ta ba. Ka ba ni daga nan zuwa mako guda, zan tari kawunmu da maganar, na tabbata zai tsawatar mata, zai kuma aura maka ita, saboda ni kam har ga Allah na yarda da nutsuwarka."
Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke Mahmouda. Ya kalli ƙofar da ya ga Fiddou ta shiga, bai ko hange ta ba. Murmushin ƙarfin hali ya yi, haɗe da furta,
"Amma Yaya ba ka tunanin wani abu zai iya hwaruwa idan aka mata dole? Yanzu hwa lokaci ne da aka daina yayin auren dole, gwamma dai a bar ta ta zaɓa da kanta, gudun samun matsala."
"Kar ka damu kanka Mahmouda. Fiddou ba ita tai yi kanta ba, muna da magabata, wanda dole ne ta ji maganarsu. Don haka ka ƙyale duk wannan tunanin, tana da sauƙin kai sosai, kawai dai damuwa ce da tai yi mata yawa. Kawai dai ka ci gaba da lallaɓarta, namiji kake, ka san hanyoyi da yawa da za ka iya shawo kan mace."
"Haka ne Yaya. Allah ya taimaka mana."
"Ameen ameen Mahmouda. Ka tafi kawai, bayan sati guda ɗin sai ka dawo."
Miƙewa ya yi Mahmouda. Fuskarsa a sake ya ma Yaya da Aunty Sahiya bankwana, ya kama hanyar fita.
*
Miƙewa ta yi a bisa ƙafafuwanta, fuskarta ɗauke da murmushi, ta kalli Modu da faɗin,
"Zan je in dawo Ya Noor. Ka min addua."
Murmushi kawai ya yi ba tare da ya ce komai ba, ya bi ta da kallo har ta fice daga ɗakin.
A falo ta tarar da Mama tana kallo. Ta ce,
"Mama shiryawa zan yi yanzu, gidan su Amrah da na faɗa miki zan je nake son zuwa."
Mama ta ce,
"To madalla. Kar ki manta fa, ki sanar mata duk halin da ake ciki, wata ƙila akwai wata gudummuwa da za ta iya bayarwa wurin samun warakar Annur."
"Insha Allahu zan faɗa mata Mama."
Ta tashi ta shige ɗakinta.
Green ɗin atamfa ce ta saka mai zanen ganye pink. Ɗinkin riga da skirt ne da ya karɓi jikinta. Ɗaura ɗankwalinta ta yi sannan ta zira pink hijab iya guiwarta, ta shafa turaren humra, ta fito daga ɗakin hannunta riƙe da wayarta.
Ɗari biyar Mama ta bata, sannan ta mata fatar alkhairi ta fita.
A bakin ƙofa ta ci karo da Mahaifinta da kuma Yayansa, suna ƙoƙarin shigowa. Da faraa a fuskarta ta duƙa har ƙasa ta gaishe su.
"Kawu Imrana an dawo lafiya?"
Ta furta kanta sunkuye ƙasa.
"Lafiya ƙalau Maryama. Sannu kin ji. Ina ta ganin saƙunanki ta inbox duk Friday na happy Friday ai. Allah ya miki albarka."
"Ameen Kawu."
"Sai ina?"
Abba ya tambaye ta.
"Zan je gidan su Amrah ne Abba. Jiya da muka haɗu wurin sauka duk sai na ji kunya. Ban koma ba fa tun ranar farko."
Abba ya ce,
"Lallai fa ya kamata ki je kam. Ba jimawa zan yi a gidan ba Office zan koma ai da kin tafi da motar, Mallam Ya'u kuma a can Office na baro shi."
"Babu komai ai Abba. Zan hau napep."
"To Allah ya tsare. Ki gaishe su."
Miƙewa ta yi tsaye haɗe da ambatar to, sannan ta tafi.
Isar ta gidan su Amrah ta samu Umma zaune da baƙuwa a tsakar gida. Jin sallamar Maryama ya sa Umma sakin murmushi haɗe da amsa sallamar, tana mata sannu da zuwa.
"Iso daga ciki ƴata. Ga tabarma ki zauna."
Da faraa Maryama ta zauna bisa tabarmar, sannan ta gaishe su.
Amsawa suka yi su duka biyun, baƙuwar ta miƙe tsaye, tana furta za ta wuce.
"Ina zuwa Maryama. Bara na mata rakiya."
Baƴuwar ta murmusa ta ce,
"Babu komai wallahi Yaya Murja. Ki sha zamanki."
"A'a Zaliha. Mu je ko bakin ƙofa ne."
Ba ta jima ba ta dawo, tana ba Maryama haƙuri.
"Babu komai ai Umma."
Bayan ta zauna ta ce,
"Ya kika baro su Mama?"
"Lafiya ƙalau Umma. Sun ce ma a gaishe ki."
"Ina amsawa."
Daga nan shiru ya biyo baya. Miƙewa ta yi Umma, ta ce,
"Akwai kwaɗon zogale na nan kuwa da na ma Mallam ya yi saura. Bari na kawo miki."
Murmushi kawai ta yi Maryama, ta bi Umma da ido har ta ƙarisa cikin kitchen. Sosai take yabawa da kirkin matar. Tana da karamci sosai ba kaɗan ba.
Roba ce ta taho riƙe da ita a hannunta, ta rufe da wani ƙaramin plate.
A gaban Maryama ta ajjiye, da faraa ta ce,
"Ci ki ƙoshi. Idan borkonon bai miki ba sai in kawo miki ki ƙara."
Buɗewa ta yi Maryama ta fara ci, sosai kuwa ya mata daɗi, saboda dama ita ɗin maabociyar cin zogale ce.
Sai da ta ci kamar rabinsa, sannan ta yi hamdala ga Allah, ta miƙe haɗe da nufar randar gidan, ta wanke hannunta sannan ta sha ruwan ta dawo.
A rayuwar Umma, tana son ganin mutum well social, wanda ba ya da jiji da kai ko kuma ƙyamar talaka. Ko ba a faɗa mata ba ta san cewa Maryama suna da rufin asiri a gidansu, amma kuma ga shi babu ƙyama babu komai ta ci abincinsu, ta sha ruwan randarsu. Wasu halayen na Maryama sukan tuno mata da Amrarta, sosai ba kaɗan ba. Girmama na gaba da yawaita fara'a, duka haka Amrah take.
Bayan ta zauna Maryama, ta sake yi wa Umma godiya, sanan ta ɗora da faɗin,
"Umma dama akwai wata magana da nake son sanar da ke."
Gyara zamanta ta yi Umma, ta ce,
"Allah ya sa lafiya."
Murmushi ta yi Maryama, ta ce,
"Lafiya ƙalau Umma. Dama kan maganar Annur ne."
"To ina saurarenki."
Umma ta faɗa.
Bayan ta sauke ajiyar zuciya Maryama, ta ce,
"Umma abubuwa da dama sun faru bayan bari na gidan nan. Na shiga cikin rayuwar Annur sosai, na gano munana halayensa da kika faɗa min, har ma sun zarce yadda kike tunani ɗin. Sannan kuma wani katari da aka yi, ƙanwar nan tashi Dr. Islam da kike faɗa min ƴar wulakanci, yaronta Abdul tare suke da ƙanina Muhammad a makaranta, har ta silarsa ma mun ƴulla zumunci da ita. A taƙaice dai, na shiga rayuwarsa Annur tsamo tsamo, na nemi ceto shi daga halin da yake ciki, sai kuma wata matsala ta kunno kai."
Shiru ta yi daga nan, tana nazarin ta inda za ta fara sanar da Umma cewa ba shi ne real Annur ba, shi ɗin na ƙarya ne.
"Uhm, ina saurarenki Maryama."
Maryama ta ci gaba da,
"Ta hanyar wata kilakin Annur, na gano cewa ba ainahin Annur ba ne a gidansu."
Ido Umma ta ƙwalalo tana kallon Maryama. Ta ma rasa gane inda maganar tata ta dosa.
"Mun gano inda Annur ɗin Amrah yake. Cikin halin hauka muka same sa, wadda aka tabbatar mana cewa ya ɗauki kusan tsawon shekaru uku a wannan halin, a garin Maraɗi. Yanzu haka maganar da nake miki Umma, Annur na gidanmu ajje, ana ba shi kulawa."
Ta kasa gasgata maganganun Maryama, sai dai kuma tana hango tsantsar gaskiya a cikin ƙwayar idonta. Cikin muryar mamaki ta furta,
"Ta ya hakan za ta faru? Me ya sa kuma kamanninsu ɗaya babu bambanci? Kenan su ɗin ƴan biyu ne?"
"Abin da har yanzu nake tambayar kaina kenan, na kuma gaza samo amsa. Kawai dai abin da na sani ɗaya ne, shi ne basu da bambanci ko kaɗan. Bambancin kawai shi wannan cikin halin hauka yake. Kuma kullum cikin ambatar sunan Amrah yake, yana furta Amrah yake so. Amrah zai aura. A kai shi inda Amrah."
Runtse idanuwanta ta yi Umma. A hankali ta buɗe su, cikin mamaki ta ce,
"Na tabbata ba za ki min ƙarya ba Maryama. Na yarda da ke, na kuma yarda cewa wanda kika tsinto ɗin shi ne ainahin Annur, saboda ko bayan haukacewarsa kafin a ce mana ya warke, subbatunsa kullum a kan Amrah ne, yana faɗin ita yake so. Amma da mamaki. Ta ya aka yi hakan ta kasance?"
*
Ruwa da lemo Mama ta kawo ma Kawu Imrana da kuma Abba. Bayan sun gaisa ne take ce masa,
"Daɗa Alhaji tunda ka tafi sai muka ji ka shiru, kamar ma ka manta da kana da dangi a Katsina."
Murmushi ya yi bayan ya sauke glass cup daga bakinsa. Ya ce,
"Ta ya zan iya mantawa da ku? Kuna raina a kodayaushe. Aiki ne kawai ya sha gabana. Amma yanzu komai ya daidaita, na gama, na kuma dawo gida cikin iyali da dangi."
Abba ya murmusa, ya ce,
"Hakan ya fi ai. Muna ta fama da kewarka."
Sosai suke wasa da dariya da junansu, tamkar Kawu Imrana ba shi ba ne babba. A ƙarshe ya yi gyaran muryarsa, ya ce,
"Wata shawara ce na yanke da ni da zuciyata. Cewa zan haɗa yaran nan aure. Ina nufin Ahmad Deedah da kuma ƴata Maryama."
Idanuwansu buɗe cike da farin ciki suke dubar Kawu Imrana. Tun Abba bai ce komai ba Mama ta yi saurin faɗin,
"Lallai gaskiyar Hausawa ne da suka ce, abin da babba ya hango yaro ko ya hau turmi ba zai taɓa hango shi ba. Da gaske na ji daɗin wannan al'amarin sosai, na kuma tabbata akwai kyakkyawar alaƙa a tsakanin yaran, za su daidaita kansu."
Tana kaiwa nan Abba ya ce,
"Sau ɗaya wannan batun ya taɓa faɗo min a rai, sai dai kuma na bar wa cikina, sanin halin yaran yanzu, kar su watsa mana ƙasa a ido."
Kawu Imrana ya ce,
"Kafin na tinkare ku da zancen sai da na yi maganar da Deedah, cikin hikima na nemin jin tsakaninsa da Maryama. Yake faɗa min yadda suke, akwai zumunci sosai a tsakaninsu. Saboda haka ba na ji ko kaɗan za su baɗa mana ƙasa a idanuwa. Addua kawai za mu musu, Allah ya sa wannan haɗin ya zama alkhairi a tsakaninmu baki ɗaya."
"Ameen ameen Yaya. Gaskiya ka yi tunani mai kyau. Tunda dai dama yana aikinsa, ai sai maganar aure kawai. Ita ɗin kuma za ta iya ci gaba da karatunta ko a gidansa."
Da haka suka miƙe, Abba ya ce zai miyar da shi gida, shi kuma daga nan zai koma Office.
Bankwana Mama ta musu, sanann ta dawo ta zauna. Tana jin farin ciki sosai lulluɓe da zuciyarta.
***
*To fa! To fa masu karatu! You see ba. Kun ga abin da yake shirin faruwa ko?😱 wai Deedah za a haɗa aure da Maryama, wacce ke da burin zame ma Annur Amrarsa da ya rasa. To ya wannan abu zai kaya? Ko Maryama za ta amince da wannan zaɓin na iyayenta? Idan ta amince ya makomar rayuwar Annur? Tirƙashi! Akwai aiki mai girma.*
*Shin akwai wani taimako da Maman Amrah za ta iya yi ma Maryama ta hanyar warwaruwar wannan ƙullin?*
*Mun dai ga halin da Sans ya shiga, a wasu shekaru da suka gabata. Shin komawar da zai yi Bama ko zai zame masa alkhairi? Iyayensa sun mutu kuwa? Wane dalili ne ya saka shi dawowa Katsina bayan kuma shi ɗin ɗan Maiduguri ne? Me ya sa halayensa baki ɗaya suka munana, har ya koma halin da yake kai a yanzu?*
*Ku ci gaba da bibiyata, sannu a hankali duk za a samu wannan amsoshin. I love y'll Fisabilillah. Kun sani ai.😀*
*Kar ku manta, sai kuna yi kuna kankaro mutunci. Yanzu kam abun ba dama, ghosts sun yi yawa. Sannunku kun ji? Babu kunya a karanta a ƙetare kyakkyawar tauraruwar nan mai daɗin dangwalawa.😁*
Thanks all
Pinky durling💞
RAZ 2
[9/1, 1:39 PM] Princess Amrah✍🏻💞: *🅰MRAH NAKE SO!♥*
_(Labari mai taba zuciya, soyayya, sadaukarwa da kuma ban tausayi)_
Sadaukarwa ga masu cutar amosanin jini (Sickler)
Na Amrah A Mashi
(Princess Amrah)
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
5⃣2⃣
Wattpad: PrincessAmrah
***
Tsaye ta miƙe bisa ƙafafuwanta. Fuskarta ba yabo ba fallasa ta fuskanci Umma da faɗin,
"Umma zan tafi. Amma don Allah ina buƙatar taimako daga gare ki."
Da fara'a Umma ta ce,
"Allah sa bai fi ƙarfina ba."
Maryama ta furzar da zazzafan iska daga bakinta, a lokaci guda kuma ta sauke ajiyar zuciya, ta ce,
"So nake ki ringa zuwa gidanmu akai-akai wurin Annur. Ina tunanin ganinki da zai ringa yi ƙila ya ringa tunowa da wasu abubuwa na Amrah, ta sanadiyyar haka har ƙwalwarsa ta dawo daidai. Da na yi tunanin na ringa kawo shi nan da kaina, sai kuma nake gudun faruwar wani abu; kar wancan Annur ɗin na ƙarya ya aikata wani mummunan abu, duk da yake dai har yanzu ba mu san taƙamai-mai yadda abun nan ya kasance ba."
Dafa kafaɗar Maryama ta yi Umma. Ta ce,
"Insha Allahu zan ringa zuwa kamar yadda kike da buƙata. Amma a ganina, me zai hana ku miyar da shi gidansu, tare da bayyana duk yadda abin ya kasance? Kamar hakan zai fi wannan ɓoye-ɓoyen ai."
Maryama ta ce,
"Zan yi hakan Umma. Sai dai lokaci bai yi ba har yanzu. Ko kaɗan ba na so Yaa Noor ya koma gidansu da hauka, saboda ba mu san