Showing 168001 words to 171000 words out of 201092 words

Chapter 57 - AMRAH NAKE SO BOOK COMPLETE DOCUMENT .txt

saki yana kallon ta. Umma ta ce,


"Sannu Annur. Ya ƙarfin jiki? Ka ji sauƙi ko?"


Ya ɗaga mata kai.


"To Allah ya ƙara sauƙi."


Shiru ya biyo baya.


"Zan yi fitsari."


Ya faɗa ma Maryama yana kallon ta. Kama shi ta yi ya miƙe, a haka suka isa toilet ɗin ya yi fitsari sannan ta masa alwalla suka dawo falon.


"Umma ko za ki faɗa masa maganar?"


"To Maryam."


Ta miyar da kallon ta ga Annur. Sai da ta sauke ajiyar zuciya sannan ta ce,


"Akwai wani labari da Amrah ta taɓa faɗa maka a gabana. Cewa wai tana ganin wani bawan Allah mai irin kamanninka. Za ka iya tunowa?"


Shiru ya yi yana bin ta da kallo. Ta ci gaba,


"Ka san sai na kwaɓe ta da zancen, saboda tun farko ban so ta faɗa maka ba, gudun zargi."


Nan ma dai ya yi shiru.


"A ranar da wannan abun ya faru, ka kawo ma Amrah wani zoben zinari mai matuƙar kyau, har ka ce tsarabarta ce da Kawunka ya siyo mata daga Dubai da ya je. Idan za ka iya tunawa, Amrah ba ta karɓi wannan kyautar ba, ta ce ka miyar ka ajje har sai ranar da aka ɗaura muku aure sannan ka ba ta. A lokacin sosai ka nunar da rashin jin daɗinka, ta yadda za ka kawo mata kyauta daga wurin kawunka amma ta ƙi karɓa, har ka sako ni a cikin zancen. Ka tuna?"


Bai ce komai ba, kamar yadda ta yi tsammani dama ba zai ce ɗin ba. Ta ce,


"Ni ma da kaina na goyi bayan kar ta karɓi wannan kyautar, saboda zoben ba ƙaramin zobe ba ne, irin wannan kyautar abin da ya kamata a bari har sai an yi aure sannan a yi ta. A bayyane ka nunar da rashin jin daɗinka, har ka yi fushi da Amrah, ko in ce da mu duka baki ɗaya. Ka ɗauki tsawon lokaci ba ka dawo ba, sai dai muka ji ka shiru, har a waya ba a jin ka, ashe ba ka da lafiya ne. Cikin tashin hankali muka nufi gidanku, Mahaifiyarka ke faɗa min ai kana ma asibiti an kwantar da kai, amma mu jira ita ma a lokacin za ta tafi, sai mu je tare. Tare muka tafi da ita har da Amrah, mun same ka sosai ka ji jiki. Sai a ƙarshe nake jin labari a wurin Amrah, kasantuwar ba ta ɓoye min komai, tunda ba wata ƴar uwa mace gare ta ba, kuma ba tarin ƙawaye ke gare ta ba. Dole ni kaɗai take kawo wa maganarta, kamar yadda ni ma ita nake nufa da kowacce irin matsala tawa. Take ce min wai saɓanin da kuka samu ne dalilin ciwonsa. SHI NE SILAH! Na yi mamaki sosai, ta dalilin zobe har wani abu ya gitta tsakaninku, har a ƙarshe ka kwanta asibiti? Mahaifinta ya so mu karɓi kyautar zoben, sai dai fa ni ina tsoro, tsoron danginka nake, su Islam ba su da kirki. Bai kamata mu karɓi wannan kyautar tun a lokacin ba.
Tun bayan ka ji sauƙi kuka daidaita, a nan kuma Amrah ke faɗa min wai ka miyar da zoben ga kawun naka, ka ce ya ajje maka har sai sadda aka tashi aurenka, sannan ya damƙa shi ga mai shi, wato Amrah.


Zobe dai haƙƙin Amrah ne, Annur. Amma na sadaukar da shi gare ka, ka karɓo shi daga wurin kawun naka duk sadda ka samu lafiya, ka ajje shi ko ka kayutar, duk yadda ya maka, mun bar maka."


Ta dakata daga nan, tana kallon yadda idanuwansa suka yi taf da ƙwalla.


Maryama ba ta yi mamakin jin kalaman da suka fito daga bakin Umman Amrah ba. Domin kuwa dama ta riya a ranta, ta tabbatar cewa wannan zoben na Amrah ne, saboda yadda ta ga Annur ya ɗauke sa da muhimmanci. A yadda ta ƙara jin tausayin Amrah, ji ta yi ina ma Amrar za ta dawo a yanzu. Wallahi da ta mallaka mata Annur. Da ta nemi rabuwa da shi ta bar masoyan su cika burin rayuwarsu, burin zukatansu. Sai a yanzu ne take ƙara tabbatarwa, cewa Annur da Amrah ya dace. Tamkar jininsu na tafiya a tare ne.


Kansa ya ɗora bisa hannun kujera yana kuka, kuka mara sauti sai dai shessheƙarsa kawai da ake ji. A hankali Maryama ta isa gare shi, ta tallabo kanshi ta ɗora a cinyarta, ta saka hannunta na dama ta hau share masa ƙwallar, tana faɗin,


"To miye ne abun kukan kuma? Ka yi shiru, ka ji?"


Ta fuskanci Umma ta ce,


"Na matuƙar jin daɗin sirrin zoben nan Umma. Na jima ina son sanin wani abu dangane da shi, sai dai jikina ya ba ni dama ya danganci Amrah. Yanzu haka zoben yana wurina..."


Ta ba Umma labarin duk abin da ya faru. Ta ƙare da cewa,


"Kuma tun daga sadda Yah Noor ya ga wannan zoben na tabbatar da zoben ko ƙaƙa ne ma ya yi silar samuwar sauƙinsa. Tun daga ranar yake yin abubuwa na ban mamaki. Wanda har gani nake kamar ma ya warke ne. To kuma sai idan ya yi wani abun ne nake daɗa tabbatar da cewa bai warke ɗin ba, ya dai samu sauƙi sosai."


Umma ta yi hamdala ga Allah sannan ta miƙe cewa za ta tafi. Har gate Maryama ta raka ta sannan ta dawo ta same shi.


*


"To Alhamdulillah! Sauƙi ya samu sosai. Yanzu ma likitan ya bar nan, ya tabbatar min da cewa Annur ya samu sauƙi. Ya ma ba shi sallama, gobe idan Allah ya kai mu za mu dawo gida Nigeria."


Daga can ɗaya ɓangaren Momy ta sauke nannauyar ajiyar zuciya, ta ce,


"Wannan zancen ya min daɗi ƙwarai Alhaji. Allah ya ba shi lafiya ya kyauta gaba. Sannan Alhaji don Allah ka masa nasiha sosai kafin ku dawo ni ma na masa tawa."


"Abin da nake da shirin aikatawa kenan kika kira ni Suhailah. Zan mishi sosai."


"To shi kenan sai anjima. Allah ya dawo mana da ku lafiya."


"Ameen."


Ya faɗa haɗe da tsinke wayar ya fuskanci Sans da ke jingine da kan gado.


"Annur!"


Ya ɗago kansa ya kalli Dady.


"Ina so ka faɗa min tsakaninka da Allah a kan tambayar da zan yi maka."


Gabansa ne ya ji ya yi matsanancin faɗuwa. Cikin rawar murya ya ce,


"To Dady."


Dady ya ce,


"Annur me ke damun ka?"


Shiru ya yi bai ce komai ba, har ya sake jin muryar Dadyn ya ce,


"Na tabbatar da cewa kana da damuwa. Ba zai yiu ba ka da damuwar komai ba ka yi attempting kashe kanka. Don Allah ka faɗa min abin da yake damun ka. Na maka alƙawarin warware maka damuwarka, da ƙarfin mulkin Allah."


"Dady..."


Ya yi shiru sanadiyyar kukan da ya zo masa.


"Dady tabbas ina da damuwa, sai dai ba irin wacce za ta faɗu ba."


Cikin mamaki Dady ya ce,


"Annur dama akwai damuwar da ba za ta faɗu ba?"


Kai Sans ya ɗaga masa, yana mai share ƙwallarsa.


"Waye ni a gare ka?"


"Babana."


"Babanka kawai?"


Sai da ya ɗan jinjina kalmar kafin ya ce,


"Mahaifi."


"Good. To Annur idan ba ka tinkare ni da matsalarka ba waye za ka tinkara da ita ya warware maka? Me ya sa ka yi yunƙurin kashe kanka? Anya kuwa ka san hukuncin wanda ya kashe kansa?"


Da sauri Sans ya ce,


"Na sani Dady."


"Mene ne to?"


Dadyn ya tambaye sa.


"Ya mutu kafiri. Ɗan wuta ne."


"To ka san da hakan Annur me ya sa za ka jefa kanka ga halaka da iliminka? Shin har akwai damuwar duniya da ta fi ta lahira tsanani? Haba Annur! Wane dalili zai sa kana ji kana gani ka luma wa cikinka wuƙa? Yanzu inda a ce da ka luma ɗin ka mutu, me za ka faɗa wa mahaliccinka? Za ka ce masa damuwar duniya ce ta maka yawa har ka kashe kanka?"


Gyaɗa kansa ya yi Sans.


"Ehen...to ina sauraren ka. Mece ce matsalarka?"


"Dady baki ɗaya duniyar ce ta juya min baya. Farin-ciki na ya kau. Damuwa ta tattaru ta lulluɓe min zuciya. Ƙunci ya min yawa. Na rasa yadda zan yi in samu assauci, shi ya sa na yanke hukuncin kashe kaina."


Dady ya numfasa, sannan ya ce,


"To na ji. Amma mene ne sila?"


"Dady babbar silar ce ke da nauyin faɗe. Ƙaramar kuma rasa aminina Farouk da na yi ne."


"Na san wannan na ciki Annur. Amma dai ina da buƙatar sanin babbar damuwar, komai girmanta."


Ƙara ƙarfafa kukan nasa ya yi, ya ce,


"Ka yi haƙuri ka yafe min Dady. Ni mai manyan laifuffuka ne. Amma don Allah ba don hali na ba, ka zama mai yafiya a gare ni, sannan kuma kar ka tsananta binciken koma miye. Na maka alƙawarin ba zan ƙara yunƙurin kashe kaina ba. Ina so komai daren daɗewa, wani abu ya taso game da ni kar ka guje ni Dady, kar ka juya min baya..."


Jawo shi Dady ya yi a jikinsa yana ɗan bubbuga bayansa cikin rarrashi.


"Na maka alƙawarin ba zan taɓa juya maka baya ba Annur, duk wuya duk rintsi. Kai fa ɗana ne na cikina. Ka taɓa ganin inda hannunka ya ruɓe ka yanke shi ka yar? Ka kwantar da hankalinka. Allah ya ƙara maka lafiya."


Sosai ya ji daɗi Sans. Sai dai a zuciyarsa tausayin Dady yake. Ta yadda ya yarda da shi, ya ɗauke shi matsayin ɗan da ya haifa da cikinsa, amma kuma ba hakan ba ne.


*


Cike da mamaki yake kallon ta a falon. Fuskarsa a sake ya ƙariso gabanta ya zauna. Sannu da zuwa ta masa cikin faraa.


"Ai yau mamaki kawai nake Yamairah a falo. Hala dai ke ma kin fara gajiya da zaman ɗakin ne?"


Murmushi ta sakar masa.


"Ba gajiya na fara yi ba. Yesmeen ta yi ɓarna a ɗakin ne na tura mai aiki ta gyara. An dawo lafiya?"


"Alhamdulillah. Tunda dai bakya komai kuwa tashi za ki yi mu fita?"


"Zuwa ina?"


Ta gaggauta tambayarsa. Don ita kam ba son yawan fita take ba.


"Wurin yankan kai zan kai ki."


Suka yi dariya su duka.


"Nan cikin unguwar nan ne babu nisa. Mamaki zan ba ki ne, na aurar da ɗana ba ki sani ba."


Murmushi ta yi,


"Ok bari in sako hijab."


Ta nufi ɗakinta. A lokacin har mai aikin ta gama gyaran ɗakin. Bayan ta sako hijabi ta ɗauro niƙab ɗinta kamar yadda ta saba idan za su fita. Ta ɗauko wayarta sannan ta cicciɓo Yesmeen da ta yi barci tun sadda ta gama ɓarna ta sauko ƙasa.


Cikin Corolla S suka tafi, duk da dai cewa babu nisa amma a ƙafa za a wahala sosai. Sadda suka isa gidan horn ya yi mai gadin ya leƙo ya ga ko waye. Ɗaga masa hannu ya yi alamar gaisuwa sannan ya wage masa gate ɗin gidan suka shigo da motar.


Sadda suka fito daga cikin motar har Yesmeen ta tashi. Da ƙafafuwanta ta taka suka ƙarisa ciki. Duk da Yamairah na son tambayar mijin nata ko me suka zo yi a nan? Sai ba ta furta ba. Ta zuba masa idanuwa kawai suka isa ciki.


A falo suka samu Maryama tana yankan ƙumba. Annur kuma tunda suka gama sallah sai bai fito ba. Saboda zallar damuwar labarin da Ummar Amrah ta tado masa da shi. Yana ji ne kamar komai ya dawo masa sabo.


Da murna ta miƙe tsaye tana musu sannu da zuwa, haɗe da yi musu iso suka ƙarisa shigowa cikin falon. Sarai ta tuna da ƴar yarinyar, wannan shagwaɓaɓɓiyar ce da suka tayar a falo ranar da suka je gidan.


"Sannun ku da zuwa Uncle. Sannu Aunty."


Ta kama hannun Yesmeen. Noƙe kafaɗa ta yi haɗe da janye hannunta ta koma wurin Babanta.


Gaisawa suka yi, a zuciyarta tana jinjina kyawu irin na Yamairah. Dole ne wannan za ta zama ƴar kulle, dole kuma ta ringa saka niƙab. Saboda sadda suka shigo falon ba ta ɗage niƙabin ba har sai da ta zauna.


"Kawu ya gida?"


"Gida alhamdulillahi, Maryama. Kuka ji ni shiru ban dawo ba ko?"


Ta ɗaga kanta da faɗin


"Babu komai ai. Na tabbata uzururruka ne."


"Wallahi kuwa. Yayana ya je India ne, so kuma ina ɗan kula masa da wasu abubuwan nashi, ni ma kuma ga nawa, sai abun ya taru ya haɗe min."


"Allah sarki! Yarinya ya sunanki?"


Ta faɗa tana murmushi. Yamairah ta ce,


"Shereefa, amma Yesmeen ake kiranta da."


"Allah sarki! Sannun ku da zuwa."


Ta miƙe haɗe da nufar kitchen. Blue cocktail ta ɗoro a tray da cups guda biyu. Sai kuma bobo saboda Yesmeen. Ta kawo ta ajje a gabansu suna mata sannu. Alhaji Marwan ya ce,


"Wai ina mutumin ne?"


"Yana ɗaki kawu, tunda muka yi sallah bai fito ba. Bari in kira shi."


Ta miƙe haɗe da nufar ɗakin. Fitowa suka yi tana gaba yana biye da ita, kan Yamaira duƙe a ƙasa tana zuba wa mai gidanta lemu.


Suna isowa Yamaira na ɗago kanta. Karaf suka haɗa ido da Annur da ke ta famar yaƙe bayan ya zauna. Ido buɗe take kallonsa, har cofin hannunta na glass ya faɗi ƙasa, saboda bisa kafet ne ma ya sa bai fashe ba. Sai dai lemun ya zube, kwalbar lemun ma ta faɗi ƙasa duka ta zirare.


Da mamaki suke kallon ta su ɗin ma. Alhaji Marwan ya ce,


"Lafiya?"


Ya miyar da idonshi ga Annur da ta ƙura ma idanuwa. Shiru ya ji ba ta ce masa komai ba. Ya maimaita tambayarta amma ba ta ko san yana yi ba. Hannuwansa ya sa a daidai fuskarta ya tafa da ƙarfi, ta firgita tana nuna sa da ƴar yatsa. Hakan bai mata ba ta miƙe tsaye ta isa gabanshi. Hannunta ta sa ta tattaɓa goshinsa a hankali, tunaninta ko mafarki take. A ganinta wannan abu ne da ba zai taɓa yiuwa ba.


Miƙewar ya yi shi ma Alhaji Marwan cike da mamaki ya ƙariso inda suke.


"Yamaira me ke faruwa kike taɓa shi? Kin san shi ne? Please talk."


Kuka ta fasa mai ƙarfi. Ta rinƙa gyaɗa kanta, tana faɗin,


"Yaya Salman! Kai ne ko ba kai ba ne? Me ya dawo da kai nan? Dama kana raye?"


Da ƙarfi ta faɗi ta zube a wurin. Alhaji Marwan da Maryama suka yi kanta. Annur kam kallon mamaki kawai yake bin ta da shi.


***


*Sannunmu sannunmu da jimirin karatu. Kun ga yadda sannu a hankali muka fara kai gangara ko.*


*Hirar Sans da Dady fa ta ɗan birge ni, a wani ɓangaren kuma ga tausayi. Wato dai na fahimci cewa Sans ya nadama, sai dai yana gudun ya tona asiri ne kar su kore shi daga gidansu, ya rasa tudun dafawa. Ko ya abun zai kasance duk ranar da wannan rufaffen asirin ya buɗu?*


*Su Yamaira an ga ɗan uwa an sume🤣 to idan ta farfaɗo mene zai faru?*


*Abubuwan fa akwai rikitarwa😀 amma sannu a hankali duk za a warware mana komai, tunda ga shi an fara warwarewar ma.*


*AREWA NOVELS GROUP ba na cikin group ɗin amma saƙon gaisuwa da jinjinarku ya iso gare ni. Amrah na godiya sosai. Allah ya bar zumunci.*


*Comments ɗin ku na last page sun min daɗi sosai. Ina fatar zan samu fin hakan a wannan.*


*Na gaishe ku masu mutunci. Ba laifi aikinku yana kyau, amma last page duk ƙoƙarin da na muku na dogon shafi sai ban ga an kankaro shi yadda ya dace ba. Fatar za ku gyara. Ku rabu da waƴancan masu hancin yalo da kabewar, su dama sun saba cin amana. A kyautata musu amma su yi ha'inci.🙄 ehh da ku nake. Wanda ke min laɓe a littafi.*


Thanks all.


Pinky durling💞
RAZ 2
[9/24, 6:57 AM] Princess Amrah✍🏻💞: *🅰MRAH NAKE SO!♥*


_(Labari mai taɓa zuciya, soyayya, sadaukarwa da kuma ban tausayi)_




Sadaukarwa ga masu cutar amosanin jini (Sickler)


Na Amrah A Mashi
(Princess Amrah)
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*




6⃣9⃣




Wattpad: PrincessAmrah


***


Kakkaɓe-kakkaɓen ɗakin suke su duka biyun, suna yi suna ƴan ɗage-ɗagen komai saboda su samu gyara shi yadda ya kamata. Sai da suka ƙarisa duka shara kawai ta rage Hanan ta ce ma Janan,


"Janan don Allah ko za ki taimaka ki ƙarisa sharar ɗakin nan, please? Cikina ke ɗan min ciwo wallahi."


Kallon banza ta bi Hanan ɗin da shi. Ta ce,


"Malama in kina zama mu ƙarisa aikin nan ma ki zauna. Don ƙafarki ƙafata."


Dama jikinta ya ba ta sam Janan ba za ta mata wannan alfarmar ba, saboda tun dama can Janan maƙyuyaciya ce. Sai ta ɗaure fuskarta, ta ce,


"To don Allah Janan kar ki share ɗin, tunda ke ba ki san arziƙi ba. Ciwo dai ne ya san gidan kowa."


Ta buga tsaki haɗe da barin ɗakin. Tsakin ta yi ita ma Janan, ta ce,


"Mai wayon banza. To ba zan share ɗin ba. Ni bari ma in yi bincike ko Allah zai haɗa ni da abin da raina zai so, tunda Uncle Noor akwai shi da iya ajiyar abon arziƙi."


Rawar kai gare ta dama Janan. Bambancinta da Hanan kenan. Ko sadda suka taɓa zuwa tare da Annur ɗin daga Cyprus ita Hanan ce ta gwada wa Amrah soyayya. Janan kuwa ta biye su Islam suka tsani Amrar tare.


Binciken kuwa ta hau yi, jawo wancan buɗe wancan haka ta rinƙa yi. Banda tsofaffin shisha babu abinda ta rinƙa gani, sai tarin flavors linkim. Tsaki ta rinƙa yi tana sake buɗowa, har Allah ya haɗa ta da diary ɗin Sans.


Ɗauko shi ta yi ta taɓe fuska,


"I must read this. Sai na jiyo sirrin Uncle Noor. Ƙila ma a ciki in san dalilinsa na ƙin yin aure har yanzu."


Sai kuma ta sake taɓa baki, ta ce,


"Hala ma dai labarin wannan mai sickler ɗin da ta rasu ne a ciki, don na san halinsa shi dai Amrah kawai. Ko ma dai miye I must read it."


Ta ajiye a gefe guda, sannan ta ci gaba da bincikenta. Idan handky ta gani da ya birge ta sai ta ɗauka. Tana gamawa ta harhaɗa komai yadda yake ta miyar, sannan ta tattara abubuwan da take so ɗin ta saka cikin wata farar ledar shoping da ta samu, har diary ɗin ma.


"Ai kam komai dare yau sai na karanta diary ɗin nan. Don ni ba na aikata abin da ya dace kurum, har wanda bai dace ɗin ba ma yi nake."


Ta gatsine fuska tamkar tana yi da wani ne.


Ba ta tsaya sharar ɗakin ba kawai ta fice daga ɗakin, da ledar karikitan da ta ɗauko ɗin a hannunta. Saɗaf-saɗaf ta rinƙa yi don kar a gan ta a tambayi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login