Showing 198001 words to 201000 words out of 201092 words
Chapter 67 - AMRAH NAKE SO BOOK COMPLETE DOCUMENT .txt
room 4.
A kwance suka same ta an rufe ta da blanket da ya aro a ɗaki na kusa da na Maryama. Cikin ruɗewa Momy ta tattaɓa jikin Maryama da aka liƙa wa drip tana barcin wahala.
"Allah sarki! Sannu Maryama. Me yake damun ta ne Annur?"
Sosa ƙeyarsa ya yi haɗe da sakin murmushi. Bin shi da kallo suka yi. Dady ya yi murmushin shi ma.
"Ah to da alama dai jika muka samu. To Allah ya raba lafiya."
Sai ma yanzu ta ƙara kallon Maryama sosai ta ga fayau ɗin da ta yi. Ta kamo hannunta ta riƙe.
"Ashe dai jika ne ke wahalar min da ƴa. To Allah ya sauƙaƙa ya rangwanta miki."
Ta ƙarisa rufe ta da blanket ɗin.
Ya sosa kansa ya ce,
"Momy to tunda kun zo bara in samu komawa gida in harhaɗo abubuwa. Ko bargon nan aro shi na yi wancan ɗakin."
Momy ta ce,
"To shi kenan. Sai ka ɗauko kafet ɗin sallah ma. Daga nan ka biyo da flask na ruwan zafi da kayan tea. Ga shi ko girki ban ƙarisa ba na baro gidan."
Dady ya ce,
"Kin dai kashe ko?"
"Na kashe."
Ta ba shi amsa.
"Ok to da kyau. Mun yi waya da Nadrah ai ta ce wai Hanan da Janan dai sun ce nan za su dawo baki ɗaya. Da suka koma ɗin nan duk sai suka ji daban. Kuma babansu ya bar su."
Annur ya ce,
"Ah to masha Allahu. Ni fa dama har zan ce ya kamata Momy ta samu mai aiki haka nan. Wai ina ma asalin waccan ɗin?"
Momy ta yi murmushi.
"Salman ya korar min da kaf masu aiki."
"Bari in je to Momy."
Ya tafi.
Da dare ɗakin ya cika da ƴan dubiya. Salman ma ya ɗauko amaryarsa Hadiza da kwanansu huɗu da aure yau. Baba da Mama ma sun zo tare da Hammad. Momy dama ba ta tafi ba tana nan. Sai ga Islam da mai gidanta sun zo Abdul-Ahad biye da su. Jiddah ma ba a bar ta a baya ba. Deedah ya kawo ta, saura sati biyu bikinsu. Suna nan sai ga Uncle Marwan ma da Yamaira wacce ƙaramin ciki ya fara bayyana a jikinta.
Kwananta biyu a asibitin aka sallame ta tare da ba su shawarwarin yadda za su kula da cikin sosai. Sannan kuma aka faɗa mata sadda za ta fara zuwa awo.
A mota shagwaɓa kawai Maryama ke sakar masa. Abu kaɗan ta kama ƙuhin kuka. Shi kuwa sai famar rarrasar ta yake yi har suka isa gida.
Cikin kwanaki biyu Maryama ta fara samun sauƙi. Annur abu kadan ya tambaye ta me ya faru? Me take so? Idan ma wurin aiki ya je to suna tare a waya, saboda ba ta koma School ba Dr. Ya ce ta bari har ta ƙara warwarewa.
Duk hidindimun bikin Jiddah babu wanda aka bar Maryama da Annur a baya. Tare suka rinƙa zuwa events ɗin ciki kuwa har da dinner. Ranar ɗaurin aure aka shafa fatiha, Jiddah ta zama amaryar Deedah, kowa ya shaida hakan. Da yamma aka ɗauki amarya aka kai ta tafkeken gidanta da ke Batagarawa lowcost, kasantuwar Deedah ya samu lecturing a jamiar Umaru Musa nan cikin garin Katsina.
Har da Maryama aka saka ango ɗaki. Ta ma amarya nasiha sosai ta mata gyare-gyaren gida, misalin goma da rabi Annur ya zo ya ɗauke ta.
Haka suka ci gaba da rainon cikinta kuma tana zuwa makaranta abin ta.
Ranar wata laraba da yamma naƙuda ta kama Maryama. Dama Hanan da Janan sun dawo, Hanan aka kawo mata tana kwana tare da ita. Janan kuma tana gida tare da Momy. Annur ba ya gida a lokacin. A ruɗe Hanan ta ɗauki wayarta ta kira Annur ta sanar da shi halin da ake ciki. Cikin kiɗima ya ce da ita yana hanya dama. Ta harhaɗa komai kafin ya iso.
Baby wardrobe ta buɗe a ɗakin Maryama ta fiddo kaya uni-sex guda huɗu da overrole guda biyu, tunda dama duk an faɗa musu twince ne a cikin Maryama.
A kit ta haɗo da diaper da duk wani abu da za a nema. Tana gamawa Annur na isowa. Yadda ya ga halin da Maryama take ciki duk sai ya daɗa tausaya mata. Kamar ya mata kuka ya ji, ya kinkime ta ya kai mota, Hanan ma ta shiga motar suka kama hanyar asibiti.
Sai da suka isa sannan Hanan ta kira Momy ta sanar mata. Annur kuma ya kira gidan su Maryama ya faɗa.
Bayan an shiga labour room da ita su Momy suka iso. Mama ma suka iso a ruɗe suka haɗe da su Momy. Dukkansu bakin labour room ɗin suka tsaitsaya suna jiran tsammani. Annur kam tagumi ya yi da dukka hannuwansa, har hawaye na zirara daga idonshi.
Ta jima tana naƙuda, kusan awa huɗu tana abu ɗaya har duhu ya fara, sannan ta haifi namiji. A take kuma ta kama wata sabuwar naƙudar. A nan ba ta wani sha wahala sosai ba sai ga ƴa mace ta haifa.
Hamdala ta saki bayan fitowar yarinyar. Da sauri ɗaya daga cikin nurses ɗin ta fita waje. momy da Mama har rige-rigen tambayarta suke.
"Congratulations! Ta haifi twince mace da namiji yanzu za a kimtsa su duka har da uwar. Tana cikin lafiya ita da yaranta."
Annur daga nesa ya ji maganar, aikam sajdatushhukri ya yi, yana jin farin-ciki lulluɓe da zuciyarsa. Isowar Salman da Hadiza kenan su ma suna ji suka yi hamdala ga Allah.
Take suka yita kiran ƴan uwa da abokan arziƙi ana sanar da su haihuwar. A nan suka kwana, Hanan da Mama suka kwana tare da Maryama. Mama sai fama take da ita a kan ta shayar da yaran amma turo bakinta kawai take yi wai zafi. Haka dai suka yita fama har gari ya waye.
Annur ya zo da kayan kalaci da ya karɓo daga wurin Momy. Suna cikin karyawa ma aka ba su sallama. Bayan sun gama duka suka rankaya suka koma gidansu da suka koma watanni biyar da suka gabata.
A cikin kwanakin nan shida kafin suna kullum gidan cike yake da ƴan barka. Babu wanda ba ya yaba kyawun yaran. Ga su dai jarirai amma hakan bai hana kyawunsu bayyana ba. Jidda da ta zo da ƙaramin cikinta sai famar kallon yaran take yi, ba ta ma so a karɓe su.
Daren suna da dare Annur ya nemi ganawa da Maryama a part ɗinsa. Bayan ta zo ya ce,
"Uwar biyu dai."
Ta sakar masa murmushi.
"Kai kuma uban biyu."
Ya shafi fuskarta.
"Na ji dai. Dama ce miki zan yi an siyo komai da kika rubuta. Maganar sunan yaran, nake neman shawararki."
"Ban gane ba."
"Ina nufin wai sunan da za a saka musu. Miye raayinki? Tun ranar da aka haife su na so na musu huɗuba, to kuma su dama can da sunayensu, Hassan da Usaina, amma dai daga bayan nan na ji shaawar mu musu suna kawai."
Ta sakar masa murmushi.
"Macen dai na yi mata suna."
"Namijin fa?"
"Na bar maka zaɓi."
Ta ba shi amsa hannunsa riƙe da nata.
"To wane suna kika yi mata?"
Kallon cikin ƙwayar idonsa ta yi, ta ce,
"Amrah..."
Tun ba ta rufe baki ba ya jawo ta a jikinsa cike da farin-ciki.
"Sosai raayinmu ke tafiya a tare Maryama. Haka nake fatar ɗorewarmu, komai namu ya ci gaba da tafiya tare, soyayyarmu ta ci gaba da bunƙasa. Allah kuma ya raya mana yaranmu."
Ta janye jikinta daga nasa.
"Dady kar kuma a wuce gona da iri. Jego dai nake yi."
"Ba za a wuce ba uwar biyu. Ba ki tambaye ni sunan da na zaɓa wa namijin ba"
"Sai ka faɗa Dady."
Ya ɗan lumshe idanuwansa.
"Farouk na zaɓa masa. Na tabbata su Momy za su ji daɗi sosai. Kuma hakan ne kawai zan yi na kwatanta kyautatawarsu a gare mu. Allah dai ya sa ya miki."
"Ko bai min ba ya min Dady, bare ma kuma ya yi ɗin. Allah ya raya mana little Farouk da little Amrah. Allah ya albarkaci rayuwarsu."
"Amin ya Rabb. Sai ki tafi ko kar a neme ki."
Ta miƙe ta masa bankwana sannan ta tafi.
Haka sunan ya kasance cike da farin-ciki. An ci an sha, an kuma yi nishaɗi. Fiddou da Mahmouda ma ba a bar su a baya ba sai da suka zo. Aunty Saddiqa ma ta zo da yaranta. Aunty Nadrah ce kawai ba ta samu zuwa ba daga Cyprus. Yamairah ma ta zo da jinjirinta mai suna Kamal. Sunan ya tara mutane sosai. Kowa ya saka ma Farouk da Amrah albarka. Sai dare sannan aka warwatse.
*
Gyaɗa kanta ta yi cike da takaici, ta ce,
"Wai Farouk me ya sa kake da jan faɗa ne? Tun ɗazu Saddam ke kawo min ƙararka sai ka ce sharri yake yi maka. Kuma dai ga shi Amrah ta tabbatar min da kai ne ke tsokanar tasa. Ba ka jin kunya ƙaninka fa ne kuma saboda kai ya zo hutu gidan nan. Haba Farouk!"
Kunnuwansa ya kama tun kafin ya matso inda take.
"Am sorry Ammi. Ba zan ƙara ba."
Ta masa murmushi.
"Yauwa yarona. Allah ya maka albarka ka ji. Zo ka ɗaukar min Baby Hoodah in shiga toilet in dawo."
Yarinyar ƴar kimanin watanni biyar ya ɗauka. Kusan faɗuwa suka yi Maryama ta ce,
"Farouk bi min ƴa a hankali ni dai."
"To Ammi."
Ya faɗa bayan sun fita daga ɗakin.
Amrah ta yi zaune wuri guda tana duba wani littafi a hannunta. Muryar Saddam ta ji ya ce,
"Yaya Amrah me kike yi?"
Ta sakar masa murmushi.
"Saddam ina duba karatun da aka mana ne a islamiyya jiya, huruf ne. Idan na gama gwanancewa anjima sai in koya wa Farouk."
Saddam ya ce,
"Kin ji daɗinki ke kam Yaya Amrah."
"Kai ma za ka ji ai, musamman ma dai idan ka dage ka yi karatu sosai. Dady da Ammi sun sha ba mu labarin Amrah, asalin wacce aka saka min sunanta. Mace ce da ta zama abar alfahari har bayan rasuwarta. Har yau har gobe tarihinta na nan rubuce a ƙasar nan. Ina son zama kamar ita."
Farouk da ya iso kusa da su yana rirrigar Baby Hoodah ya ce,
"Ni ma ina miki fatar kasancewa kamar ta Amrah. Insha Allahu za ki zama ɗin, har ma ki zarce ta. Allah ya ba mu ikon riƙo da addininsa, ko kaɗan kar mu zama masu saɓa wa koyarwar ma'aiki SAW."
Annur da ke tsaye yana saurararsu duk sai ya ji yaran sun daɗa shiga ransa. Wayo tamkar ba ƴan shekara bakwai ba. Kansa kawai ya gyaɗa bayan ya daɗa yin godiya ga Allah da ya albarkace shi da yaran ƴan biyu, da kuma Hoodah mai sunan Momy Suhailah ƴar watanni biyar.
Ya samu Maryama ta fito daga toilet tana duba wasu takardu. Ji ta yi ya riƙo ta ta baya.
"Dady ba dai har ka dawo ba."
"Na dawo Ammi. Meeting muka yi da wasu baƙi. Sun ɗauke ni contract ne, zan musu wasu zane-zane tsawon watanni uku. Za su ba ni naira miliyan goma."
"Alhamdulillahi!"
Ta faɗa bayan ta rungumo shi.
"Allah ya ƙara buɗi na alkhairi Dady."
"Amin ya Allah. Salman sun dawo fa. Kin ji motsin su?"
"Ikon Allah! Wallahi ban ji ba. Kuma Hadiza ba ta kira ni ba. Allah dai ya sa sun yi nasara."
Shiru ya yi kafin ya ce,
"Ba su yi ba Maryam. Wai likitan ya ce bai ga wata matsala a tattare da duka biyun su ba. Lokacin haihuwar ne dai kawai bai yi ba. Daga can ma suka wuce saudiyya suka sake yin addua."
"Ehh Hadiza ta ce min dama Saudiyya suka wuce. To Allah dai ya kawo musu mai albarka."
"Amin. Saddam dai ya saba sosai da su Farouk."
"Wallahi fa. Ko ɗazu Jiddar ta kira ni wai ya Saddam dai ba ya mana kuka ko? Na ce da ita ko kaɗan. Don ma dai Farouk na tsokanarsa ne. Amma dai na masa nasiha insha Allahu ba zai kuma ba."
"To madalla. Fiddou ma wai ta sake haihuwa. Gama wayata da Mahmoud kenan na shigo gidan ma."
Ta zaro ido.
"Lallai Fiddou. Haihuwa ta uku fa kenan. To Allah ya raya mata su bisa sunnah."
"Ameen ya Allah. Ya ce wai ni aka yi wa takwara. Annur."
Ta ji daɗi sosai.
"Aikuwa Dady dole mu daure mu je barka sannan kuma mu koma suna. Sun yi ƙoƙari sosai wallahi."
"Allah da gaske sun yi ƙoƙari?"
Ta ɗaga kanta.
"To sai ke ma ki min ƙoƙari yanzu, ki saukar min da gajiyar nan."
Harara ta maka masa.
"Su kuma yaran da ke waje mu yi yaya da su?"
Ya taɓe bakinsa.
"Ke ni fa yara ba su isa su hana ni jin daɗi da iyalina ba. Bari ma ki ga."
Ya je ya datse ƙofar da key. Dawowa ya yi gare ta, ya ba ta peck a kumatu, sannan ya ce,
"Over to you durling."
Daga nan sai abun ya rikiɗe izuwa faranta wa juna rai. Yara na waje an haɗa su da raino, iyayensu na nan suna raya sunnah.
***

Lttle Amrah

Little Farouk and Little Amrah

little farouk and little Amrah

Little Farouk and little Amrah

Little Farouk and little Amrah

Baby Hoodah
Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!!
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah maɗaukakin sarki. Tsira da aminci su ƙara tabbata ga shugaban halitta annabi muhammadu SAW.
Karshen labarin kenan. Inda na yi daidai Allah ya ba ni ladar. Kuskuren da ke ciki Allah ya gafarta min.
Karshen labarin AMRAH NAKE SO kenan. Dogon labarin da ya ɗauke mu tsawon lokaci muna yin sa.
Fatar masoyana sun ji daɗin sa.
Saƙon jinjina ga ƙungiyar NAGARTA. Na gode ƙwarai da haɗin kai da goyon bayanku. Allah ya bar zumunci ya ƙara mana basira baki ɗaya.
A ba za ta taɓa tafiya ba sai tare da R da Z. Shi ya sa sunan ba zai tafi da R da Z ɗin nan ba sai tare da A. RAZ abin alfaharina. Mutanen ƙwarai masu matuƙar daraja a gare ni. Ina ƙaubarku da zuciya ɗaya billahi. Ba zan taɓa iya bayyana yadda kuke a cikin zuciyata ba. Amma ku sani, kulluhin rayuwata ta gama mamayewa da ƙaunarku. Allah ya bar mana zumunci har ƙarshen rayuwarmu (Rabiatu sk msh and Zara BB).
Ashnur pyar, miemie Queen, Basman mai sanyinta, Meesha, Aunty Maijidda Musa, Ummi Agoss, Asisi Fulanin birni, Zulaihat Rano, Ayshat Modu, Na gode ƙwarai da jimirin bibiyar labarin nan.
Wattpadians, ku sani cewa ina matuƙar ƙaunarku. Na ji daɗin yadda kuka bibiyi labarin nan nawa har ya zo ƙarshe. Sai kuma kun ji ni da wani insha Allah.
Masoyana:
1 teema💋
2_Kulthoum
3. Matar Sarki 🤴🏻👸🏻
4. Maryam Suleiman😍 5. Fatima Sabo
6.maman iman
7.officialmarcy
8. khairat b umar❤
9.ruqayya❣
10•√ fatima muh'd sani {sister sajeedah }💋
11. 💎Najwah💎
12.Khadeejah Musa Yahaya(budurwa)
13.Asmau Attah
14.arousal kois
15. Aysha Ummy
16.Zainab Gwandu
17.Ameena SZ
18. Safura Garba Muhammad 💞
19•Khadeejah ahmad usman(ummy)
20 Nana Hafsat
21•ummu~salmah(ummu~safwan)ut
22.hannat shagari✨
23. 🌹Hufax🌹
24. Hajara Adam
25. Smart s fawa
26. Ruqayya Sha
28 hauwy❤
29saudatu Bello Ibrhm
30Khadeeja usman sabo 💞
31 zee h
32.aysha❤
33.halima amuma(mom mk luv)
34. Lolita
35 Ummu Haidar
36. Asmau Mashee
37 Ummu Aysher
38 Meinerh
39 Fadimatu Dawaki
40. Zainab Liman Tureta.
Kuna da yawa, lissafo ku ne babban aiki. Amma ku sani cewa Amrah na alfahari da ku, matuƙar babu ku to babu Amrah. Sannunku da jimirin sharing na wannan labarin.
Yan group na RAZ NOVELLA 1&2, Khadija Candy novels, MS INDABAWA GROUP CHART, Pherty novels, Dandalin Bilkisu Bilyamin, Sahaf Novels, Stylish novels group,
Asisi Group, Queen Miemie novels Group, MH FANS Group, Mrs. Omar Group, MaryamerhAbdul Fans, House OF Novels Zauren Sadiya novels, Meesha fans group
Da duk sauran groups da nake. Na gode da soyayyarku.
Tambayoyi:
Kun ji daɗin labarin ANS?
Me ya fi birge ku a cikinsa?
Me ya fi ba ku tausayi har ya zauna a ranku?
Wane abu ne ya baƙanta muku rai har ya zauna muku a rai?
Wa kuka fi so a cikin labarin?
Wa kuka fi tsana a cikinsa?
Wa ya fi ba ku tausayi?
Wace soyayya ce kuka fi so duk cikinsa? Amrah da Annur? Fiddou da Modu? Jiddah da Deedah? Fiddou da Mahmouda? Ko kuwa ta Marnoor?
Tsakanin SHI NE SILAH da AMRAH NAKE SO wane ya fi yi muku daɗi? Me ya sa?
Kuna da saƙo zuwa ga marubuciya Amrah? Idan kuna da shi, drop your comments here.
Na gode ƙwarai masoyana. Haƙiƙa ba ni da bakin gode muku. Sai dai addua. Allah ya bar mana zumunci ya haɗa mu da alkhairi.
Sai kun ji ni a littafi na gaba mai taken GIMBIYA SA'DIYYA (Aljana ko Fatalwa?) labari mai cike da zalunci, ban tausayi, tsoro, soyayya da kuma bayyana wasu abubuwa da suke ba kowa ya san su ba.
Instagram: amrah_princess
Facebook: Amrah Auwal
Email: amratuauwal20@gmail.com
Wattpad: PrincessAmrah
Snap chart: real_amrah
Call, text, Watsapp, Imo, Telegram: 07037603276
Princess Amrah AKA Pinky durling ke muku fatar alkhairi.
An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your