Showing 36001 words to 39000 words out of 201092 words

Chapter 13 - AMRAH NAKE SO BOOK COMPLETE DOCUMENT .txt

Wasu su haukace, bayan ba a haife su da hauka ba. Addu'a kawai zamu yi, Allah Ya kare mu, Ya kare zuri'armu, Ya kare al'ummar musulmai baki d'aya_.


Dont forget to vote and comment. I love you irin totally din nan.


Pinky durling💗
*RAZ 2*
[8/30, 3:37 PM] Princess Amrah✍🏻💞: *🅰MRAH NAKE SO!* ♥


(Labari mai taba zuciya, soyayya, sadaukarwa da kuma ban tausayi.)


Na Amrah A Msh
_(Princess Amrah)_
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*


_Sadaukarwa ga masu cutar amosanin jini (sickler)_


2⃣2⃣


Tun daga ranar da muka dubo Annur hankalina ya sake tashi, ga kewar Amrah, wadda a kullum take dawo min sabuwa dal. Ga kuma rashin lafiyar Annur, wadda ta gama tasar min da hankali, ta k'ara min imani, na k'ara tabbatar da cewa lallai mai rai ba a bakin komai yake ba.


Ikon Allah ya fi gaban mamaki. Babu k'arfi babu dabara face a wurin Allah ma'daukakin sarki! Shi yake juya al'amari a duk sanda Ya ga dama. Shi ne mai d'ora ciwo, Shi kuma yake bada waraka.


Duk dukiyar Alhaji Iqra Al-Hussain ta kasa sama ma d'ansa lafiya. Gashi dai babban pharmacist wanda yake sananne ne, amma ya kasa gano maganin da zai warkar da d'anshi. Ga kuma Dr. Islam, wacce take k'anwa ce ga Annur, kuma likita amma likitancinta bai tasiri ba.


Yawace yawace har wasu k'asashe aka je, daga 'karshe aka had'a su da wani babban likita, wanda b'angaren k'walwa kawai yake da ilimi, wato Dr. Aqaq Saifullah. Dr. Aqaq ya amsa sunansa wurin likitancin abin da ya samu k'wak'walwa (wanda suka karanta labarin HZ ko kuma MH zasu san shi) yana da wuya ya yi aiki ba a yi nasara ba, amma a gefen Annur kam babu ci gaba, sai ma ci baya da ake samu.


Kusan wata hud'u ke nan da rasuwar Amrah, amma zancen rasuwarta ya 'ki ficewa daga bakin al'umma. Duk ta inda ka gitta zancen rasuwarta ake.


Bayan wasu lokuta na samu labarin Annur ya warke sosai, sai dai kuma an samu matsala! Ya zama rik'ak'ken mashayi, mazinaci, mai munanan d'abi'u.


Abun haushi da takaici, har gidan su Annur na je domin mu gaisa, saboda tun da ya warke bai tab'a zuwa inda muke ba. Amma wai kai tsaye yaron nan ya wulak'anta ni.


"Ke Malama ki shafa min lafiya, ni bakya gabana."


Kawai ya ce da ni, da wani bak'in gilashi a fuskarsa, ba tare da ya zare shi ba.


Salati na yi a cikin zuciyata,


'Wata 'kila dai tab'in k'walwar nan bai sake shi ba.' Na furta a cikin zuciyata.


Sanda Hajiya Suhaila ta zo ta same mu a haka, take bani ha'kuri kan cewa wai tun sanda ya warke ya koma haka. Baki d'aya rayuwarsa ta canza, bashi da aiki sai wula'kanci, su kansu ba wani girmama su yake yi sosai ba. Kuma babbar matsalar mahaifinsa ya d'aure masa gindi, baya bari ko kad'an a fa'di laifinsa.


Cike da mamaki haka na bar gidan, zuciyata bata daina mamakin abin da ya faru ba.


A daidai k'ofar fita na sake cin karo da shi yana k'ok'arin fita hannunshi rik'e da makullin mota,


"Am...dan Allah, kar na sake ganinki a gidan nan. Ala'kar ai ta zo k'arshe tun da dai wacce ta had'a mun ta rasu. Kowa ya tsaya inda Allah Ya ajje sa. Idan ba haka ba kuma, bani da wasa..." ya zare gilashin ya kallen ido cikin ido, had'e da sakin wani mummunan murmushi.


Ban san lokacin da na ji hawaye ba. Nake tunanin wasu lokuta da suka gabata. Nake ji ina ma dai a ce mafarki nake ba gaske ba.


Da hawaye na bar gidan, har na isa gida zuciyata bata daina jimamin abin da ya faru ba. Mamakin kalaman da d'an da na isa haifa da cikina ya fad'a min kawai nake.


A zuciyata har sak'e sak'e nake, wai anya dama da gaske Annur yana son Amrah? Idan har yana sonta, rashinta ba zai sa ya min haka ba. Sai dai kuma wani shashen na zuciyata yake gasgata min da soyayyar da Annur ya ma Amrah ta gaskiya ce. Nake tuna yanda ya sadaukar mata da lokacinsa tun yarintarsa har ya fara mallakar hankalinsa. Nake tuna rabawar da aka masu sanda zai tafi Cyprus. Ga kuma halin da ya shiga lokacin da ta rasu.


To me yake faruwa?


'Hauka ne bai sake sa ba.' Wata zuciyar ta bani amsa.


A haka na isa gida, baki d'aya jikina a mace yake, na rasa me ke min dad'i.


Tun daga wannan ranar ban sake zuwa gidan su Annur ba, shi d'in ma ko hanya bata tab'a kawo sa nan ba. Hajiya Suhaila ce ma wani lokaci takan zo mu gaisa, ta kawo mana abubuwan buk'ata.


Tun daga rasuwar Amrah, yau shekara biyu da watanni ke nan, duk bayan wata uku sai gwamnati ta bamu naira dubu d'ari biyu kyauta, kawai saboda abin da ya faru.


Islamiyya kuma ta ci gaba da bunk'asa, da dama malaman waccan Islamiyyar ta su Amrah sun dawo wannan, sun sadaukar da lokutansu, duk saboda abin da ya faru ga Amrah.


Wannan shi ne labarin Amrah. Yarinya ta gari, yarinya abar alfahari kuma abar koyi. Mun rasa Amrah, mun rabu da ita, Amrah ta rasu a wurin gasar karatun Al-Qur'ani mai girma."


Ta k'arisa maganar da kuka sosai, tana jin mutuwar Amrah ta dawo mata d'anya shakaf, tana jin tausayin muguwar rayuwar da Annur ya jefa kansa.


Kuka sosai Maryama ke yi, idanuwanta sun yi luhu luhu, shesshek'a take kamar wacce aka ma dukan tsiya.


Cikin kukan ya ce,


"Allah sarki! Allah sarki Amrah. Lallai kuwa na tabbata...na tabbata cewa rayuwarki babu komai a cikinta face tausayi, da kuma ababen koyi. Wayyo Allah, Amrah..." ta kuma fashewa da kuka.


"Na ta'ba jin rasuwarta tun sanda nake makaranta, a boarding School, sai dai ko kad'an ban san ita ba ce, saboda ban san sunan waccan d'in ba. Kawai dai na ji an ce wata yarinya ta rasu a wurin musaba'ka. Ashe Amrah'n da nake Islamiyyarta ce."


Ta dire maganar had'e da jan numfashi da k'arfi.


"Amma Umma bakya tunanin ko k'walwar Annur ce bata gama warkewa ba, yasa ya miki haka?"


"Maryama, lokacin da yake cikin haukan tuk'uru fa idan ya ganmu har k'ok'arin 'kwace kansa yake wai zai zo inda nake, zai zo na kai shi inda Amrarshi take. Shi yasa abun ya dad'a bani mamaki. Na kasa jin haushinsa a zuciyata, duk kuwa da irin wula'kancin da ya min."


Gya'da kai Maryama ta yi, cikin kuka ta ce,


"Na miki alk'awari zan ci gaba da kula da ke , Umma. Zan zama abar alfahari a gare ki. Zan zame miki tamkar Amrarki da kika rasa shekaru biyu da suka gabata."


Rungumar juna suka yi, ko wace cikinsu tana kuka. Sosai Umma ta ji dad'in abin da Maryama ta fad'a, tana jin a jikinta ta yi 'ya.


"Insha Allahu zan kawo Mamana har nan ku gaisa, da kuma k'anina Muhammad. Zan kuma kai ki gidanmu dan ki gani, sai a ci gaba da zumunci sosai."


Umma ta ce,


"Allah ya tabbatar da hakan, Maryama. Ki ce dai Amrah ta tafi, wata Amrar ta dawo."


Ta saki murmushi mai had'e da hawaye.


"Insha Allahu kuwa, Umma. Ni ma mu ne manya a Islamiyyarmu, mu za a fara yi ma walimar sauka nan da 'yan makwanni. Insha Allahu zan k'ara dagewa, zan jure, zan yi karatu sosai, saboda zan so zama kamar Amrah. Zan so na zama abar koyi, kamar yanda Amrah ta zama abar koyi. Zan so na yi rayuwa mai kyau, kamar yanda rayuwar Amrah ta kasance, ta bar bayanta da kyau."


Mallam ne ya shigo da sallama a bakinsa, Umma ta amsa had'e da mik'ewa ta karb'i ledar hannunsa.


"Barka da dawowa, Abba."


Maryama ta furta cikin girmamawa.


"To, Marayama ce? Sannu kin ji. Kin zo ke nan."


Da fara'a ta ce,


"Na zo, Abba. Har ma Umma ta gama bani labarin rayuwar Amrah."


Gyad"a kai Mallam ya yi cike da tausayi ya ce,


"To buri ya cika, Maryama. Yau dai kin ji abun da kika jima kina son ji daga bakin Mallam Sallau. Kin san wacece Amrah, kin ji irin gwagwarmayar da ta sha a rayuwarta. Yanzu abin da ya yi saura kawai sai ki yi koyi da Amrah, ki zama mai irin zuciyarta, wacce babu komai a cikinta face kyakkyawan kud'uri.


Ba wai dan Amrah tana 'yata ba, amma na yi imani da Allah irinta basu da yawa a wannan zamanin. Samun yarinya budurwa, mai shekaru kamar na Amrah, da tsarkakakkiyar zuciyarta zai yi wahaka.


Ina ro'kon Allah da Ya ji 'kan Amrah. Allah Ya mata rahama, Ya haskaka makwancinta.


Maryama kin ji yanda rayuwa bata da tabbas ko? Kin ji yanda mutum yake mutuwa ba tare da ciwo ba ko? Kin ji babban kuskuren da muka tafka kafin mu yi aure ko? Rashin awon genotype babbar damuwa ce, savoda baka san hakin da zaka jefa yaranka ba a gaba. Gashi dai hakan ne ya jefa Amrah a lalurin sickler, wanda ya wahalar da rayuwarta. Tun daga sanda aka gane Amrah na da sickler, bata ta'ba jera wata biyu cikakku da lafiya ba.


Wannan rayuwar abun tsoro ce, mutuwa bata alerting take zuwa, babu zato babu tsammani take riskar bawa, ta d'auke sa.


Amma da dama mutanen yanzu sun kasa zama na 'kwarai. Sun kasa jin tsoron had'uwarsu da mahaliccinsu. Munanan ayyuka 'kara yawaita kawai suke. Rashin imani da rashin tausayi k'ara ta'azzara kawai suke.


Wallahi duk wanda zai ji rayuwar Amrah, in dai zuciyarsa mai imani ce dole zai girgiza, dole zai k'ara jin tsoron Allah. Duk yanda 'karshenta ya yi kyau, amma hakan bai hana al'ummah da dama kokawa da mutuwarta ba. To ina ga wanda suka kasance suna aikata mummuna? Wanda babu kyautatawa a zamantakewarsu?


Ya Allah! Ka ji k'an Amrah, Ka ji k'an duk wanda suka rigaye mu gidan gaskiya. Idan tamu ta zo, Ka sa mu cika da imani."


Ko da ya gama wannan maganar, baki d'aya jikinsu ya 'kara yin sanyi. Ummah jin abun take kamar yanzu Amrah ta rasu. Bata san ranar da wannan rasuwar zata goge daga zuciyarta ba. Bata san sanda zata daina kukan rashin Amrah ba.


"Rashin Amrah ba wai naku ba ne ku kad'ai, Abba. Rashi ne wanda ya shafi dukkan al'ummah. Domin kuwa inda Amrah tana raye, na tabbata mutanen da zasu amfana da iliminta yawa ne da su. Mutanen da zasu k'aru da ita suna da yawa. Sai dai kuma kash! Allah'n da Ya yi ta, Shi ya ga dacewar karb'ar abarSa a daidai lokacin. "


"Haka ne Maryama. Ina ji a jikina ke alheri ce. Allah Ya miki albarka, Ya albarkaci karatunki da kuma rayuwarki gaba d'aya."


"Ameen, Umma."


Ta furta bayan ta share k'walla.


"Bara na tafi. Na hana ki aiki ko girki baki yi ba. Ga shi rana ta yi tuni."


"Babu komai ai. Sai na ji ki."


Umma ta fad'a had'e da raka ta har bakin k'ofa sannan ta dawo.


Alk'awarin da Maryama ta mata ta fad'a wa Mallam. Shi kanshi ya ji dad'i sosai, ya kuma yarda da yarinyar d'ari bisa d'ari.


_A ko wane lokaci Allah Yana jarrabtar bawanSa, dan Ya ga shin zai haye wannan jarabawar ko kuwa ba zai haye ba? Rayuwar nan bata da tabbas. Sai muna dagewa da aikata kyakkyawa, ko zamu samu dacewa ranar gobe k'iyama. Allah Ya bamu ikon cinye jarabawoyinmu, Allah Ya sa mu yi kyakkyawan k'arshe._


*Tighten your belts, readers. This is just the beggining.*


*Annur Iqra Al-Hussain ya zaka yi haka? Ya mutuwa zata mantar da kai mutanen da suke da matuk'ar daraja a rayuwarka? Me ya sa zaka fad'a irin rayuwar da ba taka ba, wacce bata cancanta da rayuwarka ba ko kadan?*


*Shin Ina Sans yake?*


*Wannan amsoshin duka zaku same su in dai kuka ci gaba da kasancewa tare da wannan littafin.*




Pinky durling💗
*RAZ 2*
[8/30, 3:43 PM] Princess Amrah✍🏻💞: *🅰MRAH NAKE SO!* ♥


(Labari mai taba zuciya, soyayya, sadaukarwa da kuma ban tausayi.)


Na Amrah A Msh
_(Princess Amrah)_
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*


_Sadaukarwa ga masu cutar amosanin jini (sickler)_


2⃣3⃣


Gaisuwa ta musamman ga Ibrahim Lawal Zaria. Ina matu'kar jin da'din yanda kake bibiyar wannan labarin, kake bada lokacinka wurin karanta shi. Na gode kwarai da wannan kulawa. Allahu Ya bar zumunci.


***
A hanzarce Maryama ta tsayar da napep kai tsaye ta kwatanta masa Islamiyyarsu. A zuciyarta tunane tunane kawai take. Tana ji a zuciyarta ba zata ta'ba barin maganar nan ba. Zata ci gaba da bibiyar rayuwar Annur, zata ga iya gudun ruwansa. Idan ma ya yi losing memory d'insa ne zata yi duk ma yanda zata iya dan ganin tunani da hankalinsa ya dawo.


Har suka iso bakin Islamiyyar ma bata san sun iso ba, sau uku mai napep d'in ya mata magana sannan ta ji shi. Zumbur ta yi ta zaro kud'insa daga cikin jaka ta mik'a masa, sannan ta fito.


A daidai isarta bakin gate ta d'aga kanta ta kalli sunan makarantar, gabanta ne ya mummunan fad'uwa, hankalinta ya tashi. Tunani da natsuwarta duka suka fara gushewa. Sake tuno labarin Amrah take, irin gwagwarmayar da ta sha a rayuwarta kawai take tunani.


Da tafin hannunta ta share 'yar k'wallarta sannan ta 'karisa cikin makarantar.


Kamar yanda ta yi tsammmani kuma haka ne, rehearzal ne ake a tsakiyar filin makarantar da aka yi rumfa ga d'alibai zazzaune, wasu kuma daga gefen da malamai suke, alamun su ne za a ma walimar.


A hankali take takunta, ita d'in dama can mai natsuwa ce. Komai nata babu kuzari take yinsa.


Bayan ta isa filin ne ta k'arisa wurin 'yan ajinsu, tun daga nesa Jiddah ke mata murmushi, tana gwada mata wuri a kusa da ita, alamun ta je ta zauna a can d'in.


Sai da ta gaishe da malamanta sannan ta isa ta zauna, tana ma Jiddah murmushi.


"Maryama sarkin hawaye. Ke babu dalili ma ionki fitar da ruwa yake. Kar dai idanuwan nan da aka zuba miki ne kike ma hawaye."


Murmushi Maryama ta k'ir'kiro ta ce,


"Jiddah baki da dama. Ni ban ma fa san ina wani hawaye ba, amma ke har kin gani."


Jiddah ta ce,


"Maryama ke nan. Miye naki zai gagare ni ganewa yanzu? Ai da ganin fuskarki an san akwai damuwa a tattare da ke. Idanuwanki kad'ai sun isa su nunar da hakan."


Ajiyar zuciya Maryama ta sauke,


"Haka ne, Jiddah. Tabbas ina da damuwa. Ki bari har a tashi, insha Allahu zan sanar da ke komai. Kuma ke d'in ma ina da bu'katar tallafinki."


Gya'da kai Jiddah ta yi, ta ce,


"Allah Ya jishe mu alkhairi to. Insha Allahu zan taimaka miki bakin k'arfina."


Daga haka suka mayar da hankalinsu ga karatun da d'aya daga cikinsu take yi.


Yanayin sab'ulewar jikin Maryama ya sa Mallam Yusuf ya ce mata kawai ta tafi gida, saboda shi a tunaninshi ma ko bata da lafiya ne. Bata musa masa ba, dan dama tana da buk'atar komawa gida ta natsu, ko zuciyarta zata samu salama.


Alk'awari ta ma Jiddah cewa da dare zata kira ta a waya, zata sanar da ita komai.


A haka suka rabu, Maryana ta kama hanyar gidansu, tun da dama babu nisa daga gidansu zuwa Islamiyyar.


K'o'karin kawar da damuwarta ta yi a daidai isarta gidan. Ta fiddo wayarta daga jika ta duba 'karfe uku ne da rabi, sannan ta mayar a cikin jikar.


Da sallamarta ta isa. Tun a parking space ta ci karo da motar cousin d'inta, mai suna Ahmad.


Murmushi ta saki lokacin da ta ji muryarsa ta amsa sallamar, ta k'arisa ciki da fad'in,


"Wata mota nake gani kamar ta Ya Deedah."


Bai ce mata komai ba sai harararta da ya yi cikin wasa, yana binta da kallo.


"To kallon kuma na menene?" Ta furta bayan ta ajiye jikarta bisa kujera.


"Sannu da gida, Mama."


"Maryama, an dawo? Amma kun tashi da wuri."


Mamar tata ta fad'a tana duba agogon bango.


"Mama bana d'an jin dad'in jikina ne, Mallam ya sallame ni."


"Subhanallahi! Me ya same ki?"
Mama ta fad'a cike da damuwa a fuskarta.


"Ciwon kai ne Mama. Ga kuma zazzab'i zazzab'i da nake ji yana sauko min."


Deedah ya ce,


"To ko lokacin tafiyar ya yi ne? Sai mu fara tanadin geron gumba."


Hijabin da ta cire ta jefa masa, ta turo bakinta tana fad'in,


"Sai ka riga ni ai."


"Yanzu dai je ki zuba abinci ki ci, sai ki sha magani."


To kawai ta fad'a ba tare da ta tashi ba.


Ganin bata da niyyar tashi ya sa Mama ta mik'e da kanta tana furta,


"Bara na zubo miki da kaina, kuma zan tasa ki gaba har sai kin cinye shi tas. Dan na san halinki ke d'in nan abinci ba damunki ya yi ba."


Bata jira ta furta komai ba kawai ta fice, had'e da nufan kitchen.


Kamar jira Maryama ke yi ta tashi, ta ce,


"Dan Allah Yaya dama akwai tambayar da nake so na maka. Seriously a cire maganan wasa."


"To ina jin ki."


Ya fad'a tare da mayar da baki d'aya hankalinsa gare ta.


"Wai ka san wani wanda ake ce ma Annur Iqrah Al-Hussain?"


Cike da mamakinsa ya zaro ido yana kallonta, bai iya furta komai ba sai dai da zarar an kalle sa za a san yana cikin mamaki.


"Tambayarka nake fa Yaya. Ka bani amsa mana."


Ta fa'da tana kallonshi.


Da k'yar ya iya furta,


"To ke Maryama me ya ha'da ki da wannan d'an iskan yaron?"


"'Dan iska?"


Ta jinjina har yanzu bata daina kallonsa ba.


"Ehh k'warai kuwa d'an iska. Wannan yaron wanda ya yi k'aurin suna wurin lalata yaran mutane? Annur na amfani da damar dukiya da suke da ita, yake yaudarar y'an mata. Wallahi Maryama zan iya ce miki, tun da nake a rayuwata ban tab'a ganin mashayin yaro kamarsa ba. Ba zan tab'a manta wata rana ba...


***
_Wasu matasa ne tafe cikin halin maye, ko wannensu ya sha ya yi tatul, tafiya suke amma kamar zasu fa'di, sai layi suke._


_Suna isowa bakin wani shago suka ci burki, ciki suka shiga har suna 'kok'arin buge kwalayen da ke jere a wurin._


_Mai tsaron shagon ya taso a tsorace yana fad'in,_


_"Me ya shigo da ku shagona? Ku fice min tun ban kira maku y'an sanda ba. Wato irinku ne masu zuwa suna kalle yanda shago yake, dan su biyo dare su yi sata ko?

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login