Showing 138001 words to 141000 words out of 201092 words
Chapter 47 - AMRAH NAKE SO BOOK COMPLETE DOCUMENT .txt
layar daga wuyanta. Jifa ya yi da ita, ba ta isa ƙasa ba ta tashi sama.
Kwance layar ya yi, sai ga wasu irin tsummuna a cikinta, da takardu ƙanana-ƙanana, wani irin rubutu ƙunshe a jikinsu.
Ƙwala ma wani yaro da ya zo gittawa kira ya yi. Bayan yaron ya zo ya ce,
"Shiga gidan can ka ce in ji Mallam Rabe wai a bada ashana. Ka hanzarta ka ji."
Da gudun yaron ya isa gidan, babu jimawa sai ga shi ya dawo, ya miƙa ta ga Mallam Rabe.
Ƙyasata ta ya yi a layar, take ta kama da wuta.
"Mutane babu imani. Ku kalli ku ga wannan mugunta don Allah. Yanzu ƙila wanda aka ma wannan kurciyar ya yi shekara da shekaru rabonshi da gidansu. To yau Allah ya yi, ƙarshen munahukan ya zo. Insha Allahu zai koma ga danginshi. Yau yau ɗin nan."
Da haka zaman majalisar nasu ya kasance, cike da al'ajabin wannan al'amari.
Daidai lokacin da suka cire layar kurciyar ne Maryama ta iso, suka tafi da Annur, zuwa ƙasarshi Najeriya, garinshi Katsina.
***
Zaune yake a takure, hannunsa bisa haɓa yana tunanin duniya. Sosai ya yi zurfi a tunani, har ma bai san abubuwan da suke faruwa ba.
Bubbuga shi ya ji an yi, ya zabura haɗe da shafe guntuwar ƙwallar da ta fito daga ƙwayar idonsa.
"Annur..."
Muryar Dadyn Bobby ce ta daki kunnuwanshi.
"Na'am Dady."
Ya faɗa cikin sassanyar muryarshi, wacce tun daga ranar da Farouk Sardauna ya rasu, ta koma haka. Komai nashi ya koma a nutse, tafiya ma kanta idan yana yi tamkar ƙwai ya fashe mishi a cikin cikinsa haka yake yin ta.
"So nake in tambaye ka."
Ɗora idanuwanshi ya yi a saitin fuskar Dadyn Bobby, tare da miyar mishi da dukkanin hankalinsa, don jin tambayar da za ta fito daga bakinsa ɗin.
Sai da Dadyn Bobby ya sauke ajiyar zuciya, sannan ya ce,
"Iya abubuwan da Farouk ya mallaka nake so na sani, idan kana da masaniya a kan wasu."
Shiru ya yi Sans yana nazari, kafin daga baya ya ce,
"Ehh to, na dai san akwai keke napep guda biyu da ake mishi haya da su. Sannan kuma ya zuba hannun jarinshi a Zamani Photography. Yana da Shop amma ba ta da girma sosai, ina ji ai kun san da wannan ma."
Dadyn Bobby ya share guntuwar ƙwallar da ke ƙoƙarin fito mishi, don kar Sans ya gane. Ya ce,
"Ehh tabbas na san da wannan. So nake duk wani abu da ya mallaka a siyarshi, sadaƙattul-jariyah nake so a mishi, ladar ta ci gaba da isar mishi har a kushewarshi. Tunda dai daga ni har Mamin tashi ba mu da gadonshi."
Kuka ya kufce ma Dadyn Bobby, ba tare da ya so hakan ba.
Duk da mamakin da Sans ke yawaita yi a duk sadda zai ji Dadyn ya yi makamanciyar maganar nan, hakan bai sa shi yin tambaya ba. Kewar abokinshi kawai ta ishe shi.
"Su keke napep da wurin mai photography ɗin, duka zan bar komai a hannunka. Sai ka san yadda za a yi kuɗin su fito. Ni kuma zan je wurin mai shop ɗin, zan ƙoƙarta siyen duk abubuwan da suke cikinta. Idan an tattara kuɗin duka, za a gina masallaci koda ba mai girma sosai ba. A zuba carpets da butoci, sannan zan ƙara da kuɗina a gina rijiya. Allah ya jaddada rahama ga Umar Farouk."
Ya gaggauta miƙewa ya bar wurin, gudun kar kukan nasa ya yi ƙarfi sosai, hankalin mutanen da ke wurin ya karkata gare shi.
Shi kanshi Sans kukan yake iya ƙarfinsa. Wannan rashin shi ne na huɗu da aka masa a rayuwarsa. Abbunshi, Aunty, ƙanwarshi Yamairah, sai kuma ga babban abokinshi, mutumin da ya kyautata mishi, ya ba shi dukkanin abin da yai rashi a baya. Ya ba shi farin ciki tamkar dama can ya san shi. Shi ma ya tafi ya bar shi. Tafiya ta har abada. Kuka ya kuma fasawa, haɗe da haɗa kanshi da guiwa, yana shessheƙa. Wani bawan Allah cikin ƴan zaman gaisuwar ne ya matso inda Sans ɗin yake, ya ce,
"Yaro ina kula da kai, tun daga ranar da Farouk ya rasu kodayaushe cikin kuka da damuwa kake. Wa ya faɗa maka kukanka zai taɓa dawowa da shi duniya? Ko ka manta cewa manzon Allah SAW ma ya yi wafati? Saboda haka dole kowa ma zai tafi. Allah maɗaukakin sarki ya ce dukkan mai rai mamaci ne. Don haka shi ma Farouk ba gaggawar tafiya ya yi ba, lokacinsa ne ya yi. Ka daina wannan kukan, ka fitar da duk wata damuwa daga cikin zuciyarka. Ka saka a ranka cewa tafiyar Farouk lokacinsa ne ya yi, duk daren daɗewa kai ma za ka bi shi. Kar ka ma ja ma kanka wannan damuwar ta jaza maka wani ciwon."
Kansa ya ɗaga Sans, ya shanye kukansa, yana faɗin,
"Na gode ƙwarai baba."
***
Zaune take a bisa sofa, tana son ta kira Jiddah sai dai kuma ba ta so ta takura mata, tunda ba haka suka yi da ita ba.
Jin ƙarar wayarta ne ya sa ta sauke ajiyar zuciya, sannan ta duba mai kiran. Sunan Jiddah ta gani ɓaro-ɓaro, hakan ya sa ta jin farin ciki ya lulluɓe zuciyarta. Tana fatan jin alkhairi a tattare da Jiddah.
Har wayar ta tsinke ma ba ta sani ba. Farin ciki kawai take. Kafin Jiddah ta sake kiranta ita ta kira. Bugu ɗaya Jiddah ta ɗauka.
"Amarya kin sha ƙamshi."
Kawai ta jiyo Jiddah ta faɗa, tana faɗaɗa dariyarta.
"Bana son iskanci fa Jiddah. Ai ke ce amaryar."
"Malama kar ki kawo min raini. Na tabbata kina nan kina jin daɗin sunan da na kira ki da shi."
Maryama ta murmusa, ta ce,
"Ashe ma jin daɗi. Ni dai ba wannan ba. Ki faɗa min abin da nake son ji daga gare ki."
"Hmm! Kuma har ki wani ce bakya so don na kira ki amarya? Na tabbata kin ji daɗi sosai."
"Jiddah."
Maryama ta faɗa.
Sosai Jiddah ta gano nufin Maryama. Ba ta cika son tsawaita abu ba. Komai ta fi son jin shi direct.
"Mun yi magana da Mama. Na mata bayanin komai dallah-dallah, tun daga farko har ƙarshe. Kuma Alhamdulillah! Ta fahimci komai, ta kuma tausaya miki.
So, a yanzu dai ta ba ni lambar wani Class mate ɗinsu, wanda yake ƙanin mahaifin Annur ne. Sunanshi Uncle Marwan. Ta tabbatar min cewa yana da kirki sosai, kuma zai fahimce mu. Ta ma ce min za ta kira ta mishi bayanin za mu zo mu same shi, sannan mu ɗin ma mu sake kiranshi. Idan mun je kar mu ɓoye masa komai, tun daga farko har ƙarshe mu sanar masa, da izinin Allah zai ba mu dukkanin taimako, zai kuma goyi bayanmu ɗari bisa ɗari."
Kamar ta yi ihun murna haka ta ji Maryama.
"I don't even know what to say. Na matuƙar jin daɗin wannan zance. Yanzu ya kenan?"
"Zan kira shi yanzu, mu ji inda yake. Sai ki gaggauta shiryawa, saboda ko Office ta kama mu same shi sai mu same shi ɗin. Mami ta ce min wai a State Inland Revenue yake aiki."
"To shi kenan Jiddah. Kin yi ƙoƙari sosai wallahi. Allah kaɗai ya san ladar da zai ba ki. Bari in je in sanar da Mama, sannan in hau shiri. Ina ji akwai mota ma ajje, da ita kawai zan zo."
Jiddah ta ce,
"To shi kenan. Sai kin zo ɗin."
Suka katse wayoyin.
Tsalle ta buga Maryama bayan ta haye bisa gado. Ba komai ya mata daɗi ba illa jin da ta yi cewa mutumin kirki ne Kawu Marwan ɗin, kuma lallai zai fahimce su.
Fita ta yi zuwa falo. Mama ba ta ciki, hakan ya sa ta nufi ɗakinta. A nan ta same ta tana duba wata takardar addua. Bayan ta yi sallama ta zauna a ƙasa, har sai da Mama ta gama ta ninke takardar adduar, ta miyar a cikin side drawer.
"Miss complain. Akwai magana a bakinki, na ga alama. Mene kuma?"
Bayan Maryama ta sunkuyar da kanta ƙasa. Ta ce,
"Mama yanzu muka gama waya da Jiddah. Ta ce min wai sun yi magana da Maminsu, har ma ta ba ta lambar wani kawun Annur. To dai wai za mu same shi, mu mishi bayanin komai. Yanzu."
Ajiyar zuciya ta sauke Mama. Ta ce,
"To shi kenan. Don Allah a kula sosai Maryam. Allah ya taimaka ya sa abun ya zo da sauki."
"Ameen Mama. Zan je in shirya."
Ta miƙe tsaye, ta fara taku har zuwa ɗakinta.
Cikin lokacin da bai wuce minti talatin ba ta gama shirinta tsaf. Jallabiya ce ta saka baƙa, mai adon silver. Ba wata kwalliya ta yi ba, powder kawai ta shafa da lip gloss, sannan ta ɗauki silver hand bag ɗinta, ta ɗauki wayarta ta fito. Sadda ta fito Mama na falo. Sallama ta mata, ta umurce ta da ta shiga ɗaki ta ɗauki dubu ɗaya ta ƙara mai a mota, sannan ta ɗauki mukullin mota, ta mata fatar alkhairi ta tafi.
Kai tsaye gidan su Jiddah ta nufa. Ta same ta ita ɗin ma ta shirya, kamar haɗin baki ta saka baƙar jallabiya, amma ita baƙi ne zalla har adonta.
Gaisawa ta yi da Mamin Jiddah. Bayan nan ta musu kyakkyawar addua, sannan suka tafi.
Dayake ya ce musu bai je Office ba yana gida, address ɗin shi da ya turo ma Jiddah ta text message suka bi, babu wahala sai ga su a cikin GRA, road K. House No. 16 ne gidan nashi, hakan ya sa suka dakata a nan, haɗe da yin horn. Babu ɓata lokaci mai gadi ya wage musu gate, kamar yadda kawu Marwan ɗin ya ce da Jiddah, idan sun iso kawai su zarto har cikin gidan.
Parking space suka dosa, motoci ne manya-manya a girke, wanda za su kai kimanin guda biyar, sai wani babban bike daga gefe.
Junansu suka kalla a lokacin da suka fito daga motar, ba su san inda za su dosa ba, saboda girman gidan. Jiddah ce ta koma wurin mai gadi ta tambaye shi ta inda za su bi su shiga gidan. Ya gwada musu ƙofar gaba, wadda za su fara cin karo da babban falon mai gidan. Sai kuma ya musu kwatancen ƙofar baya, ita kuma ita ce za ta sada su da ainahin inda iyalin gidan suke. Sai su zaɓi ta inda za su bi.
Maryama ce ta ce mafi a'ala dai su fara shiga inda iyalinshi, su gaisa sannan a musu iso zuwa ga kawu Marwan ɗin. Abin da suka yi kenan. Sun ci karo da babban tsakar gida, inda masu aiki ne jere rinkis, kowa na aikin gabanta.
Bayan sun yi sallama Jiddah ta ce,
"Don Allah ina masu gidan?"
Wani ɗaki ɗaya daga cikin masu aikin ta gwada musu. Nan ɗin suka nufa kuwa, sai ga su a wani hamshaƙin falo, wanda ya ni'imtu sosai da kayan more rayuwa. Bene ne daga can gefenshi, da alama ta nan ake bi idan za a shiga bedroom.

Babu kowa a falon, sai suka rasa ma yadda za su yi. Tunani suke, kar ma a je mai gidan ta wulaƙanta su. Saboda wannan tarin ni'ima da take cikinta, ba kowacce mace ce za ta iya tarbar mutane yadda ya kamata ba.
Zama suka yi bisa 2 seater, suna zaman jiran tsammani.
Wata yarinya ce suka ga ta sauko daga bisa benen, ƴar kimanin shekara biyu. Sanye take da ƴar kanti pink, gashinta an gyara shi da ƙananan ribbons su ma pink.
Har rige rigen tambayarta inda mamanta take suke, up stairs kawai ta gwada musu da hannu.
"Ki kira ta kin ji. Ki ce wai baƙi ne suka zo."
"She's sleeping."
Yarinyar ta faɗa, cikin gwarancin rashin iya magana.
Jiddah ta taɓe baki. Haushi ma yarinyar ta ba ta. Da alama irin yaran nan ne da ake ɓatawa da kilbibi ba a musu Hausa.
"Ok. Where's your father?"
Maryama ta mata wannan tambayar.
Kwakkwaɓe baki ta yi yarinyar kamar za ta yi kuka. Ita a dole sun dame ta da tambaya. Tafiyarta ta yi zuwa sama, ba tare da ta sake ce musu komai ba.
Tsoki suka saki a tare. Jiddah ta ce,
"Maryam tashi mu nufi part ɗin mai gidan, tunda dai ya san da zuwanmu."
Suka miƙe, haɗe da ficewa daga part ɗin ma baki ɗaya. Ta ƙofar gaba da mai gadin ya fara gwada musu suka nufa. Sai da suka yi knocking ya ba su izinin shiga, sannan suka cire takalmansu, suka nufi cikin falon.
Ai ƙawatuwar da ɗakin ya yi, har ma ta zarce na part ɗin matarshi. Kishingiɗe yake bisa tafkeken kafet ɗin ɗakin. Ya tsura idanuwansa a tv yana kallon news a Liberty TV.
Cike da annuri ya amsa sallanar tasu, yana faɗin
"Ku ƙariso daga ciki mana."
Ɗar-ɗar kawai suke su duka biyun. Ba su yi mamakin karamcin mutumin ba, saboda dama Mamin Jiddah ta faɗa musu, cewa yana da kirki sosai, tamkar ba mai kuɗi ba.
Har ƙasa suka duƙa suka gaishe shi, sannan ya ce da su su tashi su hau bisa kujera.
"Ayyub!"
Ya ƙwala ma wani kira. Take wani matashi ya bayyana, sanye da irin kayan kuku, har da hularshi.
"A yi serving ɗin su."
Da sauri Jiddah ta ce,
"Wallahi Baba dama an bar shi. Daga gida muke kai tsaye."
"A'a 'ya'yana, kar mu yi haka da ku. Ayyub kawo musu ko drink ne."
Da saurinshi ya bar wurin, bai jima ba sai ga shi ya turo wani keke, lemuka kala-kala jere a bisanshi, da kuma wasu irin haɗaɗɗun cups a kai.
A gabansu ya hau jerawa, yana gamawa ya tafi ya bar su.
Kaɗan suka sha drink ɗin, sannan Uncle Marwan ya ba su damar bayani. Tun daga kan zancen Amrah Maryama ta ɗauko mishi, ya san zancen sosai, saboda har ce mata ya yi ma shi ya nemo auren Amrah ɗin ma. Daga nan ta ci gaba da yi mishi bayani tiryan-tiryan, na yadda duk abubuwan suka wakana, iya wanda ta sani. A inda ta dakata, na auren dolen da ake so a mata, sai Jiddah ta ci gaba da ba shi labarin.
Sosai mutumin ya yi mamaki. Ba don daga bakin Hajiya Safiyya ya fara jin zancen ba, kuma ita ta ce mishi yaran za su zo, to da tabbas zai ƙaryata su ne. Saboda shi dai a iya saninshi, Annur ba ƴan biyu ba ne. To ta yaya za a samu mutum mai irin kamanninshi sak! Babu bambanci?
Ya yi zurfi sosai a tunani. Kuma sai wasu abubuwa suka fara faɗo mishi a rai, wanda suka fara gasgata mishi zancen na su Maryama. Tun daga sadda aka ce Annur ɗin ya warke, baki ɗaya ya rikiɗe daga mutumin kirki izuwa mutumin banza. Halayenshi kaf suka canza, daga na arziƙi zuwa na tsiya.
Dafe kansa ya yi, ya sauke nannauyar ajiyar zuciya.
"Akwai rikitarwa sosai a wannan lamarin. To amma me ya hana ku miyar da shi gaban iyayenshi, kuma ku musu bayanin komai?"
Maryama ta ce,
"Kawu akwai damuwa ne. Babu wanda ya san manufar wancan mutumin banzan. Allah kaɗai ya san abin da ya ƙulla, kuma yake da niyyar ƙullawa a duk sadda ya ga Annur ya koma gida. Na so a ce ya samu sauƙi sosai, kafin mu miyar da shi gida. Akwai wani likitan ƙwaƙwalwa da aka haɗa ni da shi, to duk tashin hankalin nan ne ya dakatar da abun, tunda a Maiduguri yake likitan."
Shiru ya ɗan yi Uncle Marwan, kafin ya ce,
"Kuma ke ma kin yi tunani mai kyau. Yanzu yadda za a yi, ki ba ni lambar kawun naki. Insha Allahu za mu yi magana da shi, yau-yau ɗin nan ma ba gobe ba. Ni zan zama wakilin Annur, za a ɗaura muku aure a cikin kwanakin da Abbanki ya bayar."
Ya yi shiru, sannan ya ce,
"Kuma ma kun san wani abun mamaki? Tun daga sadda na auro matar nan tawa, lokacin ƙila shi wancan mugun ba zai wuce ƴan watanni da zuwa gidan ba. Nake ta bin kanshi ya zo su gaisa amma ba ya zuwa. Wancan Annur ɗin ɗana kuwa, kafin matata ta rasu kusan kodayaushe yana gidan nan. Koda ba ya ƙasar da damar ya zo to sai ya zo inda take sun gaisa. Amma ita wannan bai taɓa zuwa ba ya gaisa da ita ba. Kuma shi ba ma'abocin zama gida ba bare idan na kai ta su gaisa. Tun ina magana ma har na gaji na daina."
Jinjina kansu suka yi su duka biyun, kawunansu sunkuye a ƙasa.
"Ku saka a ranku cewa auren nan tamkar an yi shi ne. Da izinin Allah."
Da murna Maryama ta haɗa ido da shi. Zuciyarta na daɗa hauhawa da dukkanin farin ciki. Damuwarta na wucewa, tana jin yadda zaɓin Deedah da aka mata ya rikiɗe ya zame mata alkhairi. Ko ba komai idan ta zama mallakin Annur, ta zama halaliyarsa, za ta fi tsayawa ta kula da shi yadda ya kamata. Za ta ba shi dukkanin lokacinta. Za ta kula da shi, za ta tsabtatar da shi, sannan ta gwada masa irin soyayyar da mata ke gwada wa mijinta. Kasantuwarshi mahaukaci ko kaɗan ba zai sa ta ƙyamace shi ba. Duk wata kula da ta dace ta sha alwashin ba shi ita, har izuwa lokacin da zai samu lafiya. Sannan kuma ta ɗaukar wa kanta wani alƙawari, duk lokacin da Annur ya samu lafiya, ya nunar da ba ya son ta, to za ta haƙura da shi, za ta bar shi ya nemi zaɓinshi ya aura. Dama dai burinta ya samu hankali, komai nashi ya dawo daidai, kamar yadda ta yi alwashi.
"Ku ba ni lambar kawun kawai, sai ku tashi ku tafi. Kar ku ji komai, na muku alƙawarin komai zai zo yadda ya kamata, kuma babu wanda zai ji komai daga bakina, ciki kuwa har da iyalina."
Farin cikinsu bai iya ɓoyuwa ba su duka biyun, jaddada godiyarsu suka rinƙa yi, har suka ƙarisa miƙewa tsaye.
Matsawa ya yi ga drowar tv stand, ya zaro kuɗi bandir na ƴan ɗari biyu, ya miƙa musu. Ƙin karɓa suka yi, suka masa godiya.
"Kun ko san yadda na tsani na ma mutum kyauta ya ƙi karɓa? Ai ba roƙo na kuka yi ba ko. Manzon Allah SAW ya ce "La yaruddul khairu illasshaiɗan. (Babu mai miyar da alkhairi sai sheɗani.)" Saboda haka in dai ba so kuke mu ɓata ba, to ku karɓa."
Jiddah ce ta duƙa har ƙasa cikin girmamawa ta karɓa, sannan suka mishi sallama, yana mai jan Maryama cewa sarakuwarshi, cike da kunya take sakin murmushi har suka fita.
Bayan sun isa mota suka tayar, mai gadi ya buɗe musu gate. Suka tafi.
Lambar Kawu Imrana ta gano, ta rubuta mishi text cewa sun gama magana da kawun Annur