Showing 141001 words to 144000 words out of 201092 words

Chapter 48 - AMRAH NAKE SO BOOK COMPLETE DOCUMENT .txt

ɗin, har ma ya karɓi lambarshi, cewa yau ɗin nan zai kira shi, za su haɗu su yi magana.


Gidan su Jiddah suka fara zuwa. A falo suka samu Mami tana waya. Zama suka yi har ta gama.


"Da alama yaran nan nawa sun yi nasara. Saboda fara'ar da ke fuskarsu kawai ta isa ta tabbatar da hakan."


Murmushi Jiddah ta yi.


"Mami mutumin nan yana da kirki sosai. Ashe uwar gidanshi ta rasu."


Mami ta ce,


"Wallahi kuwa ta rasu Jiddah. Ai dalilin da ya sa ma nake da lambarshi kenan, sadda ta rasu dayake ba a ƙasar nan ta rasu ba, kansar jini ce ta kama ta, aka kai ta India. To dai na sa Hajiya Suhaila ta ba ni lambarshi, na kira na masa gaisuwa. Ai kusan yaransu ma duk manya ne. Suna America su ukun duka a can suke karatu. Ɗiyarshi ta biyu ai sa'ar yayarku Rabiatu ce. Ɗiyarshi ta biyu kuma sa'ar Zarah ce. Sai wanann shuwar da ya auro, ita kuma ɗiyarta ɗaya kacal, sunan ɗiyar tata Shereefa."


Gyaɗa kawunansu kawai suka yi, sannan suka hau ba ta labarin duk yadda suka yi da shi.


Sai kusan bayan la'asar sannan Maryama ta koma gida. Muhammad da Mama ta samu a falo suna hira. Muhammad na ganin ta ya ce,


"Yaya Maryama tun ɗazu nake ta fama da Mama ta ara min wayarta in kira ki ta ƙi. Ta riƙe a hannunta don ma kar in ɗauka."


"Allah sarki yarona. Ai ga ni na dawo. Mama mun je mun samu kawun na Annur, an gama komai. Har ma na haɗa shi da kawu Imrana."


Da faraa Mama ta ce,


"Kai masha Allahu! Lallai abu ya yi kyau."


Maryama ta kalli Muhammad,


"Hamnad Jiddah ta ce in gaishe ka wai."


"To ina amsawa. Ɗazu da na kai ma Yaya Annur abinci yake tambayana kina ina?"


Cike da mamaki Maryama ta zuba ma Hammad idanuwanta, ta ce,


"Annur ɗin ne ya tambaye ka ina ina?"


Kai ya ɗaga mata alamar ehh. Mama ta ce,


"Ki tabbatar da ya sha maganinshi fa. Don Hammad na aika, ban tabbatar ba ko ya sha ko bai sha ba."


Muhammad ya ce,


"Allah kuwa ya sha Mama. Shi da kanshi ma ya gwada min yadda yake sha."


Murmushi kawai Maryama ta yi sannan ta nufi ɗakin Annur ɗin. Zuciyarta sayau, sai farin ciki take yi.


*


"Alhaji Marwana ka dai ƙi shan ko ruwa ko?"


"A yi haƙuri Alhaji Imrana. Bari in sha jan ruwa to."


Murmushi suka yi su duka biyun, kafin Alhaji Marwana ya ce,


"Kar ka ji komai Alhaji Imrana. Ina mai tabbatar maka da cewa komai zai daidaita. Na ɗauko ƙafafuwana ne musamman domin na nemi auren Maryama ga ɗana Annur."


Ya karkace ya zaro kuɗi daga aljihunsa. Bandir ne na ƴan ɗari biyar, dubu hamsin kenan. Ya dire su a bisa teburin gabanshi, ya ce


"Ga wannan Alhaji Imrana. Kuɗin neman aure ne. Sadda duk kuka tsaida ranar ɗaurin aure, zan zo da kuɗin sadaki, kafin nan kun fidda ko nawa ne."


Kawu Imrana ya ce


"Yau alhamis, gobe jumua, insha Allahu rana aita gobe za a ɗaura auren Annur da Maryama. Nan da kwanaki takwas kenan. A kan sadaki naira dubu hamsin."


Da haka sukai sallama, har bakin mota kawu Imrana ya raka Alhaji Marwan, dukkaninsu suna jinjina mutunci da karamcin junansu.




***


*My pipu, how y'all? Ya kuka ji wannan chapter ɗin? 5k words kenan na muku, har da ɗori ma. Ƴan RAZ NOVELLA 1 sai ku sakar min mara, yau dai kam kun samu yadda kuke so. Amma fa na sha aiki, sosai ba kadan ba. Wash!*


*Finally, an saka ranar aure nan da kwana takwas. Masu fitar da ashobe, ku muke jira. Lol.*


*Masu karatu me kuka hasko ga wannan matar ta Alhaji Marwana wadda aka ce ba ta taɓa haɗuwa da Sans ba? Ni dai kam na fara hango wani abu, amma bari na kame bakina har mu zo wurin sannan. Me kuke hasashe? Idan har aka samu mutum goma da suka canko daidai, lallai zan muku shafi guda gobe idan Allah ya kai mu, duk kuwa da cewa babu tsarin hakan a tattare da ni.*


*Masu mutunci ko kun san cewa saboda ku na dage rubuto wannan zungureren shafin? Ina jin daɗin yadda kuke kankaro mutunci, shi ya sa nake ƙoƙarta kankaro muku mutuncin ni ma.*


*Ƴan laɓe kuma ku ci gaba da yi, Allah na ganin ku.*




Thanks all


Pinky durling💞
RAZ 2


[9/11, 8:01 PM] Princess Amrah✍🏻💞: *🅰MRAH NAKE SO!♥*


_(Labari mai taba zuciya, soyayya, sadaukarwa da kuma ban tausayi)_




Sadaukarwa ga masu cutar amosanin jini (Sickler)


Na Amrah A Mashi
(Princess Amrah)
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*




6⃣1⃣


Wattpad: PrincessAmrah


***


Yana ganin ta ya miƙe tsaye, fuskarsa ƙunshe da faraa. Ita ɗin ma faraa ce a tata fuskar, ta ce,


"Ya Noor..."


Kafin ta ƙarisa faɗin abin da za ta faɗi, ta ji ya ce,


"Maryama yau ba ki min bankwana ba kika fita. Sai da wannan ɗan yaron ya zo ya ce da ni kin fita."


Kallonshi take sosai. Ba ƙaramin kyau ya mata ba. Pink ɗin riga ce a jikinshi mai dogon hannu. Kallo ɗaya idan mutum ya masa zai iya cewa mutum ne mai hankali. Saboda tufafin jikinsa, sabbi ne dal Maryamar ta siyo mishi.


"To koma ka zauna. Akwai albishir na musamman da zan maka."


Babu musu kuwa ya koma ya zauna ɗin. Yana bin ta da kallo.


Zaman ta yi ita ma a gefenshi, ta ce,


"Na je ne a kan maganar aurenmu ni da kai."


Dariya ya yi bayyananna, ya wangale baki dukkanin haƙoransa suka bayyana, sannan kuma ya saka tafukan hannunshi ya kare fuskar tashi.





Murmushi ta sakar mishi Maryama. Ta ce,


"Ka ma daina rufe fuskar nan Mallam. Gwara ka buɗe ta ka ba ni labarin me ka tanadar min a matsayin amaryarka?"


Shiru ya yi har yanzu yana jin kunyarta. Gyaɗa kanta ta yi, a zuciyarta tana faɗin da alama dai dama can asali Annur mutum ne mai kunya. Saboda komai ƙanƙantar abu sai ya kama rufe fuskarshi, a dole ya ji kunya.


Ɗan taunar leɓonta ta yi a hankali, ta runtse idanuwanta, tana buɗewa ta ɗauke su a kyakkyawar fuskar Annur, wadda ta ƙawatu da murmushi.


"Mun je gidan Kawu Marwan ne."


Ta faɗa, ba tare da ta ɗauke kallonta daga gare shi ba.


"Kawu?"


Ya ɗan yatsine fuska alamar tunani.


"Uncle Marwan nake nufi."


"Uncle Marwan?"


Ya faɗa idanuwanshi a buɗe.


"Ehh. Ka san shi ne?"


A bisa haɓa ya ɗora hannunshi alamun tunani. Can kuma ya ce,


"A duniyar su Amrah ne kawai na san wani Uncle Marwan."


Jinjina kanta ta yi Maryama.


"Da alama sauƙi na samuwa. Ga shi sannu a hankali idan an ambaci wasu sunayen kana tuna ka san su koma yaya ne."


Ta faɗa a bayyane.


"Barin tafi ɗakina. Wanka nake so in watsa. Anjima da dare insha Allahu zan dawo, kuma sai ka faɗa min tanadin da kake ma amaryarka."


Tana fita ta tarar da ƙawar Mama ta zo, da babbar leda a gabanta.


Har ƙasa ta duƙa ta gaisar da baƙuwar sannan ta miƙe za ta nufi ɗakinta.


"Maryama."


Mama ta kira ta. Hakan ya sa ta dawo, haɗe da durƙusawa a gaban Mama.


"Na ma Hajiya Maria maganar ashobe ne. To shi ne ta zo da su wai a zaɓa, duk da dai ƙurewar lokaci. Amma dai ai ba a yi biki haka nan ba, kuma bikin farko a gida. Takwararki ce ma ta kira ni, cewa gaskiya dole a fito da ashobe, mai halin yi ta yi. To kun ga dai wanda na fitar nan, ban san ko sun yi ba."


Laces ne guda biyu iri ɗaya, ɗaya baƙi sai ɗayan yellow, masu matuƙar kyau.





"Kin gan su nan. Duka biyun sai a bar su a matsayin ashoben ne. Kun ga duk mai raayin baƙin sai ta yi, mai raayin yin yellow kuma sai ta yi. Ya yi kyau ai ko?"


Cike da kunya Maryama ta miƙe tsaye.


"Da ke fa nake magana kika min shiru."


Susar kanta ta hau yi Maryama.


"Ni dai Mama duk wanda aka yi ɗaya ne. Wanda aka fitar zan ɗauki hoto in tura ma Jiddah."


"To ai shi kenan. Sai ki tafi."


Barin ɗakin ta yi tana mai tsananin jin kunya.


Wanka ta yi Maryama, ta saka riga da skirt na English wears, kalar ash and pink, wanda suka matuƙar hawa jikinta.


Abubuwa uku ne suka faɗo mata a rai lokaci guda. Na farko alƙawarin da ta ma Fiddou, kan cewa duk daren daɗewa za su koma gare ta, kuma Annur zai aure ta. Wani irin kishi ne ta ji ya turnuƙe zuciyarta. Ya za ta yi? Dole ta cika mata wannan alƙawarin, duk kuwa da yadda ba ta so ɗin.


Abu na biyu da ya faɗo mata a rai shi ne, ƙarshen wayarta da Bobby. Haka kawai ta samu kanta da faɗuwar gaba. Baki ɗaya hankalinta ya tashi. Tausayinsa take, duk da dai cewa a ganinta babu ko kaɗan ɗin soyayyarsa a cikin zuciyarta. Dole za ta kira shi a waya, ta ji yaya jikin nashi a yanzu?


Abu na uku kuwa Dr. Hamdan M. Ramat ne ya faɗo mata a rai. Missed calls ɗinsa da ta gani har guda biyu, wanda tashin hankali bai bar ta ta kira shi ba. To yanzu me za ta ce da shi idan ta kira shi ɗin? Dole dai ta daure ma kiranshi ɗin, ko ma ya za a yi a ƙarshe sai an yi.


Lambar Bobby ta fara ganowa. Kamar kar ta latsa kiran nashi, wata zuciyar dai ke daɗa ingiza ta a kan ta daure dai ta kira shi ɗin.


Bugawa take ta yi amma ba a ɗauka ba. Sai a kira na uku da ta yi ne Sans ya ji ringing ɗin wayar. Dubawa ya yi ya ga mai kiran, sai kuma maganar Bobby ta faɗo masa a rai. Inda yake ce masa duk sadda mutuwa ta ɗauke shi, to ya taimaka ya cika mishi burinshi, ya auri Maryama. Saboda tana da hankali sosai, kuma ya tabbata ba za ta ƙi shi ba, ko don wasiyyar da ya bar mata.


Idonshi cike taf da ƙwalla Sans ya ɗauki wayar ya kanga a kunnenshi.


Yanayin yadda ya ajje kalmar Hello kaɗai ya tabbatar mata da cewa ba Bobby ba ne wannan. Ta so ta gane muryar, duk da cewa ba da yawa sosai suka rinƙa yin waya da Sans ɗin ba, amma dai muryar ta mata kama da tashi.


"Ahmm...! Don Allah Farouk Sardauna fa?"


Sai da ya runtse idonsa sosai, yana son daurewa, amma ina, abun ya gagare shi. Dole sai da shessheƙar kukansa ta fito. Take hankalin Maryama ya tashi. Ido a buɗe ta ce,


"Farouk ɗin ba ya kusa ne? Please ka ba shi. Ka ce da shi Maryama ce."


A ruɗe take sosai. Wannan kalaman ma da ƙyar ta samu ta haɗo su.


"Ki yi haƙuri, amma Farouk ya rasu yau kwana uku kenan. Kwananshi biyu a kushewarsa."


Kamar saukar aradu haka ta ji kalaman. Farouk ya mutu? Ta sake maimaitawa a cikin zuciyarta. Ba ta san sadda kuka ya kufce mata ba. Cikin kukan take cewa,


"Allah sarki Farouk! Ashe dai ciwon na mutuwa ne. Ashe tafiya za ka yi Farouk. Ashe ba ka zamanto daga cikin masu tsawoncin kwana ba..."


Kuka sosai take yi. Tana tuno wasu abubuwan nashi. Yadda ya nuna mata ƙauna. Ya so ta, soyayya ta tsakani da Allah. Ya nemi shiryuwa duk don saboda ƙaunar da yake mata. Ashe da gaske wasiyya ce yake ba ta a sadda suke wayarsu ta ƙarshe?


"Farouk me ya sa ka tafi? Wallahi da gaske ina ƙaunarka. Ina son ka har cikin zuciyata Farouk. Halayenka ne na ƙi, ba kai ba Farouk. Allah ya ji-ƙanka, ya haskaka makwancinka. Allah ya rahamshe ka. Allah ya gafarta maka dukkanin kura-kuranka."


Kukan da ya ci ƙarfinta ne ya sa ta ajje wayar, ba tare da ta kashe ba.


Yana jin yadda take kuka sosai. Yana jin yadda kalaman ke fita kai tsaye daga cikin zuciyarta. A take mutuwar abokinsa ta rinƙa dawo mishi sabuwa dal. Zafin rashin Farouk na daɗa ruruwa a cikin zuciyarsa. Ji yake ina ma dai a ce bai ɗauki kiran ba sadda ta kira? Da ya huta. Da ba ta tado mishi da tabon da har yanzu bai gama warkewa ba.


Da ƙyar ya samu ya katse wayar. Kuka yake sosai, jikinsa sai rawa yake. Nadama yake, nadamar munanan halayensa. Me ya sa ba su zama mutanen kirki ba? Me ya sa ba su zama wasu mutane wanda za a yi alfahari da su ba? Gyaɗa kanshi yake, yana mai istighfari a gurin Allah. Rahamar mahaliccinsa yake nema wa abokinsa. So yake ya jure, ya ci gaba da neman gafarar Allah. Amma ina, damuwa ma ba za ta taɓa barinshi ba. Kuka da zullumi ba za su taɓa barin shi yin istighfarin ba.


Wani irin zazzaɓi ya ji yana sauko mishi. Tun jiya yake jin alamunshi, yana son zuwa mishi. Sai dai bai samu damar saukar ga baki ɗaya ba sai yanzu. Abu biyu ne suka haɗe mishi, suka saka shi zazzaɓin. Na farko kukan da yake yawaita yi. Na biyu kuma kayan maye da ya kwana biyu bai sha ba, rashin shan su ne ya yi maƙasudin hakan. Drip kawai za a saka mishi ya samu sassauci.


Miƙewa ya yi jiki babu kuzari, ya saka wayar Bobby a aljihunshi, dama saboda kiran da ake mishi ne ya sa Dadyn Bobby ɗin ya sa ya ajje wayar a wurinshi. Kai tsaye chemist ya nufa, domin samun taimakon gaggawa.


Maryama kuwa kuka ta shara sosai, tamkar wacce aka ce ta yi rashin iyaye. Tausayinsa take ji. Sai yanzu take jin tsantsagwaron ƙaunar Farouk Sardauna na shiga duk wata kusurwa ta cikin zuciyarta. Ta jima zuciyarta na ba ta alamar ta kamu da ƙaunar Bobby. Sai dai take ƙaryata zuciyar tata. Sai a yanzu ne ta gasgata, yanzu da bakin alƙalami ya riga da ya bushe. Ya tafi inda ba a dawowa, har gaban abada.


Sans tunani yake shin zai aminta da wasiyyar abokin nashi ne? Ta yaya yarinyar za ta so shi, bayan kuma shi kanshi Bobby ɗin ya faɗa mishi ba wani son shi take yi sosai ba? Amma kuma yana ji a ranshi, ba zai taɓa butulce ma Farouk Sardauna ba. Zai nemi soyayyar yarinyar, matuƙar za ta so shi, to lokacin yin aurenshi ya yi. Zai sanar a gida. Amma dai sai ya fara bin address ɗin ta kamar yadda Bobby ya ba shi, sun haɗu baki da baki sun yi magana, sannan zai sanar ɗin a gida. Amma zai jira har a yi bakwai ɗin Bobby, nan da kwana huɗu kenan, sannan zai je gidan nasu. Kawai dai yau zai kira ta da dare, ya sake maka ta'aziyya, saboda yadda ya ji tana kuka sosai a lokacin da suke yin wayar.


Maryama kuwa dolenta ta nemi panadol ta sha, saboda wani irin ciwo da ta ji kanta yana mata. Dukkanin jijiyoyin kan sun ƙulle, sai azabtaccen ciwo da suke sakar mata.


Ƙarar wayarta ta ji, ko kallonta ba ta yi ba, saboda ba ta da kuzarin da za ta iya ɗaukar wayar wani. Sai da aka kira har sau biyar, sannan a na shida ta duba mai kiran. Kyakkyawan tsoki ta saki da ta ga Deedah ne ke kiranta. Ta birkita wayar tana faɗin,


"Mutum sai baƙar ƙwaƙwa. An fidda min miji ma ba za ka haƙura da kirana ba."


Ƙarar shigowar text message ta ji. Ta ɗauki wayar, ta ga Deedah ne ya turo mata saƙo:


"Ban kira ki da wata manufa ba Maryam. Ni a tunanina ko auren kika yi ina da darajar da zan kira ki ki ɗauka, ashe ba haka ba ne? To dama ba wani abu ba ne, albishir na kira na miki, cewa mai neman aurenki ya zo, har an yanke magana, Jumu'a mai zuwa za a ɗaura aure."


Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke bayan ta gama karanta text ɗin. Tana jin tsananin daɗi a cikin zuciyarta. Allah sarki! Daga Kawu Imrana har Kawu Marwan ɗin ta ji soyayyyrsu ta daɗa ninkuwa a cikin zuciyarta. Dukkaninsu mutanen kirki ne, da suka san daraja da muhimmancin tausayi da soyayya.


Cikin ta huɗu a tunaninta ne ya faɗo mata a rai.


"Hadiza..."


Ta furta a bayyane.


"Ban kyauta ba, har yanzu ban sake waiwayarta ba."


*


Da dare Sans ya kira Maryama, cewa ya kira ne ya ba ta haƙuri kan kukan da ya ji ta fasa ɗazu. Ya mata nasiha sosai, kan haƙuri da ɗaukar ƙaddara. Sosai Maryama ta yi mamaki. Kamar dai ba mugun mutumin nan da ta sani abokin Bobby ba? Wanda fa yake amfani da sunan Annur, yake gidan su Annur a matsayin shi ne Annur. Kai a'a! Ina! Ƙila dai ba shi ba ne. Ƙila wani abokin na Bobby ne daban. Yaushe ya zama na ƙwarai da har ya iya yi ma wasu nasiha haka?


*


Washe gari


Da misalin ƙarfe goma na safe sai ga Alhaji Marwan ya je gidan Kawu Imrana. Dama sun yi waya cewa zai same shi a can ɗin. Yana isowa cikin gida ya kira mai gadin kan cewa ya zo ya buɗe mishi booth, akwai kayan da zai kwaso daga ciki, sannan shi kuma ya nufi part ɗin Kawu Imrana ɗin, kamar yadda ya yi jiya.


Ya same shi zaune yana shan coffee. Da faraa Kawu Imrana ya tarbe shi. Musabaha suka yi, sannan ya gwada mishi wuri cewa ya zauna.


Taya mishi coffee ɗin ya yi amma ya ce ya ƙoshi, yanzu ya gama karyawa.


A lokacin da mai gadi ya fara shigowa da kaya mamaki kawai Kawu Imrana yake yi. Bayan ya gama shigowa da duka kayan ne Alhaji Marwan ya yi gyaran murya sannan ya ce,


"To Alhaji Imrana. Wasu ƴan kayayyaki ne dai ga su nan kaɗan babu yawa. Na ga ya kamata a kawo ma amarya, kafin Allah ya ba shi angon lafiya, da kanshi sai ya siya mata. Kuma na tabbata insha Allahu su ma iyayen nashi za su mata. Na ga dai bai kamata a yi aure babu lefe ba ne, shi ya sa na sissiya, babu dai yawa."


Cike da mamaki kawu Imrana ke kallon kayan yana yaba kirki irin na Alhaji Marwan. Setin akwati ne mai guda biyar, kalar baby pink.







Murmushinsa ya faɗaɗa kawu Imrana. Ya sake ba Alhaji Marwana hannu suka yi musabaha, sannan Alhaji Marwan ɗin ya miƙe, ya ce,


"To Alhaji Imran,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login