Showing 165001 words to 168000 words out of 201092 words

Chapter 56 - AMRAH NAKE SO BOOK COMPLETE DOCUMENT .txt

komai na tafiyar insha Allahu sai mu dawo mu tafi da shi."


Ya miƙe. Addua da fatar alkhairi likitan ya masa, kafin Dady ya fice daga office ɗin.


Ya samu su Momy a inda ya bar su. Da sauri Momy ta tare shi cikin kuka ta ce,


"Alhaji ya kuka yi da shi?"


Bayan ya kama hannunta sun zauna ne, ya fara ƙoƙarin fahimtar da ita cewa,


"Annur ya ji sauƙi sosai, kuma da izinin Allah zai tashi da kafaɗunsa. Likitan ya ba ni shawara cewa mu fitar da shi ƙasar waje, ta yadda komai nashi zai samu daidatuwa."


"Alhaji har yanzu ban ji haƙiƙanin abin da yake damun yarona ba. Don Allah ka sanar da ni."


Gyaɗa kansa ya yi cike da tausayinta. Ya ce,


"Annur wuƙa ya luma wa cikinsa da nufin kashe kansa har lahira. Shi ne abun ya tsaya a haka, bai ƙarisa mutuwa ba..."


Bai rufe ba ki ba Momy ta zube ƙasa da ƙarfi tim! Kake ji. Da sauri Hanan da Janan suka yo kanta. Dady kuma ya hau kiran sunanta yana fifita ta da haɓar rigarsa, amma ko motsi bai ga ta yi ba. Hakan ya sa ya gwada ma Hanan nurses station cewa ta hanzarta kiran malaman jinya domin su ba ta taimakon gaggawa. Abin da ya faru ɗin kuwa kenan. Ta faɗa musu suka zo da gado aka ɗora Momy a kai, suka nufi Emergency da ita. Abun mamaki, ga gadonta ga kuma gadon Sans, haka suka jera. Shi an maƙala masa oxygen domin taimaka masa wurin numfashi. Ita kuma nurses sun hau kanta, suna ba ta agaji. Kusan minti talatin ta ɗauka sannan ta saki nannauyar ajiyar zuciya, kafin ta buɗe idonta da hawaye ya gama cika su, bayan kuma wanda ya bushe.


"Me ya sa Annur ɗina zai yi yunƙurin kashe kansa? Ina tsananin ƙaunarka, da dukkanin zuciyata. Don Allah kar ka tafi ka bar ni..."


Karaf ta ɗora idanuwanta ga Annur da ke kwance a gado. Yunƙurin tashi ta yi amma ta kasa. Wata nurse ta ce mata,


"Sister ki yi haƙuri ki kwanta. Ki kuma cire wa kanki damuwar nan. BP ɗin ki ya hau sosai, yanzu haka yana 170 ne. Don haka sai kin sauƙaƙa wa zuciyarki."


Gyaɗa kanta ta yi cikin kuka ta ce,


"Ku kira min Alhaji."


Ɗaya daga cikinsu ce ta garzaya waje ta sanar da Dady cewa patient ɗin tana son ganin shi. Da hanzari ya bi bayanta, suka shiga ɗakin tare. Ga Annur idonshi ya fara sauka, ya tausaya masa matuƙa, sannan ya juya ga Momy bayan ya isa gabanta.


"Alhaji..."


Ta faɗa cikin muryar kuka.


"Ka taimake ni ka ceto min rayuwar ɗana."


"Ba ni da ikon cetowa Suhaila. Allah ne kaɗai mai ceto. Mu namu sai dai addua kawai."


"Na san da hakan Alhaji. Amma kana da kuɗin da za ka iya kai Annur ɗina koma wacce ƙasa ce. Ba na so na rasa shi, shi kaɗai ne ɗana namiji, ina son ganin ya ajje tashi zuri'ar..."


Ta ƙarisa zancen da kuka sosai.


"Kar ki damu Suhaila. Insha Allahu in dai kuɗi na aiki, to daga kwanan yau Annur ba zai kuma yin wani a ƙasar nan ba. Da izinin Allah za a kai shi India, zai samu lafiya. Amma fa sai kin tsaida addua, kin riƙe ta tam! Saboda babu mai warkarwa face Allah maɗaukakin sarki."


Kanta ta ɗaga masa tana jin daɗi sosai. Ya ce,


"Dare ya riga da ya yi, bari in kira Islam in sanar da ita, saboda Hanan da Janan nan ya kamata su kwana, ni ɗin ma haka, saboda Annur."


Kanta ta gyaɗa masa, ta ce,


"Za ka tayar mata da hankali ne a cikin daren nan. A bari har safe, sannan sai ka kira ta."


Kai ya ɗaga mata, sannan ya mata fatar samun sauƙi, ya koma waje domin gabatar da sallolin da ke bisa kanshi. Babu magrib, ga shi har an kira isha.


*


Washe gari da safe ta kama talata. Tun da sassafe Dady ya kira Dr. Islam ya sanar da ita. Sosai ta tashi hankalinta, ta shirya Abdul, tunda hutun makaranta suke dama. Ta sanar ma mijinta sannan suka wuce Nadda Specialist Hospital.


Sai bayan ta je ne Dady ya musu sallama cewa zai tafi ya fara shirye shiryen tafiya. Gida ya fara nufa, ya yi wanka sannan ya wuce ɗakin Annur, cikin kayansa yake laluben inda zai ga epassport ɗinsa. Bai gan shi ba. Hakan ya ba shi damar sake bincikar lakokinsa baki ɗaya. A nan ya ci karo da wani diary, kalar light blue, girmansa madaidaici ne. Wata zuciyarsa ce ta kitsa masa cewa ya buɗe, wata kuwa na ce mishi kar ya buɗe, sirrin yaro ne a ciki, sannan kuma ba abin da ya kawo shi ba kenan.


Har ya miyar ya ajje, kuma dai ya sake ɗaukowa, ya buɗe shafin farko.


Bama Local Government, Borno State.


Abin da ya gani kenan a head line ɗin. Bai tsaya sake karanta komai ba, kawai ya rufe sannan ya miyar. Bincika ya ci gaba da yi, a lakar ƙasa ya ci karo da epassport ɗin, ya saki ajiyar zuciya haɗe da yin hamdala.


Barin ɗakin ya yi ya koma mota, already ya ɗauko nashi epassport ɗin dama.


A cikin wannan yinin ya kammala komai. Ya so a ce a ranar za su tafi, saboda ko kaɗan bai so su ƙara kwana a Nigeria ba. Amma sai Allah bai nufa ba. Aka ce sai gobe da misalin biyar na yamma sannan jirgin nasu zai tashi.


Sai da ya musu siyayya sosai sannan ya koma asibitin.


Har komawarsa yadda ya bar Sans haka yake. Ya dai samu tabbaci cewa sauƙi ne. Sai dai zuciyarsa ta kasa aminta. Saboda yadda yake ɗin, tamkar wanda ke cikin Coma.


Bayan ya duba shi ne ya masa addua sosai, sannan ya wuce Amenity, saboda can aka miyar da Momy, tunda dai ta samu sauƙi sosai.


*


Washe gari da sassafe Dady ya gama da Dr. Safwan. Ya bashi katin da ya ce, sannan aka ba su sallama duka suka rankaya zuwa gida.


Kayanshi Annur su Hanan suka haɗa masa a wata ƴar travelling bag. Sannan suka rufo masa ɗakin nasa, suka nufo falo. A lokacin Momy ma ta gama haɗa na Dady. Daga nan suka rankaya mota, suka nufi Kano, saboda daga can ne jirgin zai tashi.


Uku da rabi na yamma ta musu a Airport ɗin Aminu Kano. Sans na a bayan motar Prado da aka kwantar da shi, mai gadinsu ya tuƙo motar sai Abba a kujerar zaman banza.


A nan suka jira har lokacin tashin jirgin yayi, can Dady ya isa ya sanar da su halin da Sans yake ciki, sai ga su da gado aka zo aka ɗora shi a kai, sannan aka kai shi cikin jirgin.


Biyar da minti goma jirgin nasu ya lula sai babban birnin Mumbai, ƙasar India.


Momy ta sha kuka, su Janan na taya ta. Hotel suka nema suka kwana, sannnan washe gari suka nufi komawa Katsina.


*


Dressing ta yi, ta saka riga da skirt na atamfa, da zira hijabinta har ƙasa. Kusa da shi ta ƙarisa, ta riƙe masa hannu cikin murmushi ta ce,


"Yah Noor ni zan tafi. Ga kalacinka nan duka na jera maka. Na zuba maka tea kar ya huce ga shi nan. Komai na zuba ka sauko ka ci. Lokaci ya ƙure min ne ba zan samu zama in karya ba. Exam ɗin ta ƙarfe takwas ce."


Bai ce komai ba face murmushin nan nasa da yake saki a kodayaushe. Ya ziro ƙafafuwansa daga bisa gadon zuwa ƙasa, sannan ya miƙe tsaye a bisa ƙafafuwansa.


"Ai dai za ka iya goge ma kanka baki ko?"


Ya ɗaga mata kai.


"To ka goge sannan ka yi alwallar da na koya maka. Idan ka fito sai ka yi sallah ka karya. Insha Allahu zuwa azahar zan dawo, sai na maka wanka."


Ya sake ɗaga mata kai. Ta sakar mishi murmushi, sannan ta ɗauki jakarta da ATM card, saboda Abbah ya turo mata kuɗin zuwa makaranta, da kuma na cefane.


Ɗaga masa hannu ta yi sannan ta fice, shi kuma ya nufi ban-ɗakin don ya gabatar da brush da kuma alwalla.


Ya dawo bayan ya tabbatar da ta fita, sannan a hankali ya jawo wata ƴar drowa da ke jikin gado, inda ya ga Maryamar ta jefa karikitan da aka kawo mata daga gida, na Annur ɗin.


Wannan zoben ya gani a naɗe kamar yadda ta mishi tun waccan ranar, a hankali ya buɗe shi, ya ƙura ma zoben idanuwa. Kyam yake kallonsa, yana fitar da ruwan hawaye.


Abun mamaki sosai ke akwai a cikin lamarin nan, ta yadda mutum mahaukaci kamar Annur, kuma ya san sai Maryama ta fita, sannan ya jawo ma'ajiyarta, ya ɗauko wata ajiya da ta yi. Abin da ya kasance yana aikatawa kenan tun daga ranar da ta fara exams, kullum sai ya buɗe wannan zoben ya kalla, har ma abun ya zame masa jiki.


Ya jima a haka, kafin ya nannaɗe zoben kamar yadda yake a baya, ya miyar inda ya ɗauko sannan ya rufe drowar. Ban-ɗakin ya nufa kai tsaye, ya yi brush ɗinsa, sannan ya yi alwalla ya fito.


Sadda Maryama ta dawo ana kiran sallar azahar, da farin-ciki ya tarbe ta. Sallah suka yi sannan cikin ujila ta nufi ɗora girki, jellof ɗin macaroni.


Ta koma ta masa wanka ya shirya cikin baƙar jallabiya, sannan ita ma ta yi nata wankan, ta saka ƙananan kaya.


Knocking ta ji ana yi, daga kitchen ta fito tana tambayar waye, muryar Jiddah ta ji ya sa ta gaggauta isa bakin ƙofar ta buɗe mata.


Rungumar junansu suka yi cike da farin-ciki, sannan suka ƙarisa kan 2 seater suka zauna.


"Ƙawata amarya."


Jiddah ta faɗa tana murmushi.


"Mara kirki, ai saura kaɗan in yi fushi da ke."


"A yi min afwa, ai ga ni na zo. Ɗazu ina ta kiranki ma ba ki ɗauka ba, dama in faɗa miki zan zo yau."


Maryama ta jawo wayarta daga kan hannun kujera, ta duba, ta ce,


"Wallahi na yi exam ne yau. Dawowata gidan ma kenan, ko girki ma yanzu na ɗora shi. Kuma ban duba wayar ba."


"Wannan jarabawa dai ba ta kyauta miki ba gaskiya. Daga amarci kuma sai jarabawa?"


"To ya za a yi Jiddah. Sai haƙuri. Ai da yake ma next week zan gama insha Allah."


"To Allah ya nuna mana."


Daga nan Maryama ta koma kitchen, ta samu har girkin nata ya dahu. Sauran pepper soup ta fiddo daga fridge ta yi warming ɗinsa, sannan ta zuba ma Annur nashi daban, sai kuma ta zuba musu a tray ita da Jiddah.


A ɗakinsa ta fara kai masa da drink, sannan ta ɗauko nasu ita da Jiddah suka ci.


Bayan sun gama duka ne Jiddah ta hau labarta ma Maryama tarayyarsu da Deedah. Tun daga farko har ƙarshe ta sanar da ita, da kuma manya da suka shiga maganar.


Maryama ta yi murmushi sosai, sannan ta ce,


"Ka ji masoyan asali. Ni kam ai ba ni da labari. Kuma Hammad bai zo ba na san da na ji a bakinsa."


Duka fa jiya ne Abbanku da Dadynsa suka je wurin Abbana, suka yi magana wai next week ma za a kawo kayan saka rana. To ni dai Maryama sai nake ga kamar an yi azarɓaɓi, ba wani jimawa muka yi ba amma har a fara batun saka rana?"


Maryama ta kai mata dukan wasa, ta ce,


"Ke banza ce wannan yarinyar. Mene ne abun azarɓaɓin a ciki? Insha Allahu akwai alkhairi a ciki. Mu kam a sha shagalin biki mu cashe."


Haka suka sha yinin ranar cikin nishaɗi, sai misalin shida na yamma sannan Deedah ya zo ɗaukar ta. Cikin farin-ciki suka gaisa da Maryama, tamkar babu wani abu da ya taɓa faruwa a tsakaninsu. Bai wani jima ba Jiddah ta tashi suka tafi.


Bayan wasu kwanaki


***


*Tab! Ni kaina na sha mamakin tsayin shafin nan fa. Kusan yini uku na ɗauka ina aiki a kansa. Dama na ɗaukar muku alƙawari cewa page 70 insha Allahu zan muku dogon shafi, to ga shi dai na yi a 67. Saura kuma idan kun ga guntu a 70 ku ce ban cika alƙawari ba🙄.*


*Me za ku iya cewa game da abubuwan da suka faru a cikin shafin nan?*


*Ina buƙatar comments ɗin ku sosaai, matuƙar na ga kadan, to gaskiya sai an yi kwanaki kafin a sake ji na.*


*Godiya ga masoyina duka. Ina ƙaunarku fisabilillah.*


Thanks all.


Pinky durling💞
RAZ 2
[9/22, 8:13 PM] Princess Amrah✍🏻💞: *🅰MRAH NAKE SO!♥*


_(Labari mai taɓa zuciya, soyayya, sadaukarwa da kuma ban tausayi)_




Sadaukarwa ga masu cutar amosanin jini (Sickler)


Na Amrah A Mashi
(Princess Amrah)
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*




6⃣8⃣


Wattpad: PrincessAmrah


***


A gajiye ta gama gyare-gyaren gidan, ta dawo ɗaki cikin sanyin jiki, ta hunce sannan ta ɗaura towel. Daidai ta kama hanyar shiga ban-ɗakin ne ta ji wayarta na ƙara, ta dawo ta ɗauke ta daga bisa bakin gado. Ganin wanda ke kiranta ya sa cikin hanzari ta yi recieving, sallama ƙunshe a bakinta.


"Good afternoon Doctor."


Ta faɗa cike da girmamawa, har ɗan rusunawa take alamar girmamawa.


"Kina lafiya?"


Ya faɗa cikin sakin rai.


"Lafiya ƙalau. Ya aiki?"


"Aiki muna ta fama. Ya mai jikin nan?"


"Mai jiki da sauƙi."


Ya ɗan yi shiru, kafin ya ce,


"Na kira na faɗa miki cewa ina Kano right now. Insha Allahu tomorrow I'll be on my way to Katsina."


Sassanyar ajiyar zuciya ta sauke, ta ji daɗi sosai, ta ce,


"Ok Doctor. Thank you very much. Insha Allahu gobe zan kira da yamma."


Suka yi bankwana ta kashe wayar.


Wankan ta nufa tana jin farin ciki lulluɓe da zuciyarta, har ma ba za ta iya misaltawa ba.


Bayan ta fito ta yi shafa sama-sama ta saka riga da skirt na English wears. Ta fesa turare sannan ta fita falo.


A kan doguwar kujerar ta same shi barci ya ɗauke shi, ga kuma TV a kunne. Gyaɗa kanta ta yi cikin tausayi, a bayyane ta furta,


"Ashe daga kallo barci ya ɗauke ka."


Sannan ta kashe tv ɗin. Remote ɗin AC ta ɗauka ta rage ƙarfinta saboda ɗan makurewar da ta ga ya yi. Ta jawo wayarta da ke kusa da shi ajje, ta latso kiran Jiddah.


Bayan Jiddah ta ɗauka ne suka gaisa, take ce mata,


"Matar Yaya albishirinki."


"Goro."


Jiddah ta faɗa a ɗaya ɓangaren.


"Fari ko ja?"


"Ke wuya ta da ke jan ran masifa idan za ki faɗa wa mutum abu. To dilla can fari."


"Ke kuma wuyata da ke masifa. To likitan nan da na ba ki labarinshi kwanaki. Yanzu ba da jimawar nan ba ya kira ni da kansa, yake ce min yana Kano, wai gobe idan Allah ya kai mu zai zo neman abokin nashi, sai mu haɗu da Yah Noor ɗin."


Cikin jin daɗi Jiddah ta ce,


"Ahh! To Alhamdulillah! Abu ya yi kyau sosai wallahi. Allah ya tabbatar mana da alkhairi. Allah sa haɗuwar ta zama alkhairi."


"Ameen ya Allah, Jiddah. Na gode ƙwarai ki gaida Mami."


"Za ta ji. Ki gaishe da mara lafiyan."


Tana gama wayar tana jin knocking, ƙananan kaya ne a jikinta, hakan ya sa ta furta,


"Ina zuwa."


Sannan ta wuce ɗakinta da azama ta sako hijabi ta fito.


"Waye?"


Ta faɗa a hankali.


"Ni ce."


Muryar Umman Amrah ta daki kunnuwanta. Da hanzari ta buɗe fuskarta ƙunshe da murmushi. Tsayawa ta yi cak! Ganin Annur kwance a doguwar kujera yana barci. Cikin ɗan jin nauyi ta juyar da kanta. Fahimtar hakan da Maryama ta yi ya sa ta ce,


"Ummah mu je ɗakina."


Ta kama hannun Ummar. Suna isa ta zauna a kan sofa, tana faɗin,


"Sannu da zuwa Umma. Ya gida ya kuma Mallam? Ya gama warwarewa sosai dai ko?"


"Alhamdulillah. Ya warke sosai ma. Ya na same ku?"


"Lafiya ƙalau Umma."


Maryama ta faɗa fara'a ƙunshe a bisa fuskarta. Umma ta ce,


"Jiya ai na yi waya da Maman Hammad. Ita ke ce min wai kin faɗa mata ba ki ji daɗi ba har yanzu ban zo ba. Na ga rashin kamatuwar zuwa gidan yara ne shi ya sa ban zo ba."


"Haba dai Umma! Meye a ciki don kin zo inda nake? Nake ga kamar an zama ɗaya ai."


"Duk da haka dai Maryam ai bai kamata ba. Yanzun ma dai abin da ya sa na daure na zo saboda wani abu da na tuno game da Amrah, nake son faɗi a gaban Annur ɗin, wata ƙila ya iya tunowa da wani abu. To kuma ga shi ma na samu yana barci, ban kuma zo da nufin doguwar zama ba gaskiya."


"A'a fa Umma. Gaskiya dole ki tsaya ki ci abinci, kafin nan ma na tabbatar ya tashi daga barcin."


Murmushi Umma ta yi, ta ce,


"To zaman me zan yita yi a gidan nan Maryam?"


Maryama ba ta ko tsaya saurarar Umma ba ta wuce kitchen. Coconut rice da vegetable sauce ce ta zubo mata daban-daban ta ɗora a tray da drinks ta kawo mata. Sosai take hidima da Umma, tamkar tata mahaifiyar. Bayan ta gama duka ta dawo ta zauna, ta ce da Umma ta ci don Allah, kuma da yawa take son ta ci. Babu musu Umma ta fara cin abincin, ba ta wani ci da yawa ba ta ajje cewa ta ƙoshi. Duk yadda Maryama ta so ta ƙara amma ta ce ta ƙoshi, don haka ta kwashe kayan sannan ta gyaggyara wurin.


"Maryam tashi zan yi in tafi fa, da alama dai ba yanzu zai tashi ba. Ki ga fa har an fara kiran sallar la'asar."


"Amma dai ban ji daɗi ba Umma. Da alama dai zan kira Abba a aiko da mota in zo har gida da shi, tunda dai ya ƙi tashi daga barcin yanzu."


"Zan daure ko nan da kwana uku ne in dawo. Kar ki fitar da shi gaskiya, gudun samun matsala."


"To shi kenan Umma. Na gode ƙwarai."


Daidai Ummar ta tashi ita kuma Maryama ta jawo ledoji guda biyu, ta saka turaren touch me guda ɗaya, sai kuma freshner mai ƙamshi guda. Bayan sun fita daga ɗakin kuma ta je kitchen ta ƙarisa juye ma Umma cin-cin da dublan ɗin da suka rage a gudar ledar. Ta fito.


Da ƙyar ta samu Umma ta karɓi kyautar tata, ta buɗe ƙofa za ta fita kenan Annur ya tashi.


Juyowa suka yi a tare suka yi tozali da juna, da murmushi Maryama ta ce,


"Umma kin ga ya tashi ma."


Suka sake dawowa falon.


Bayan sun zauna, Maryama ta kalle shi da murmushi ta ce,


"Yah Noor ga Umman Amrah fa."


Ya kalli Umma. Bai ce komai ba sai murmushi da ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login