Showing 51001 words to 54000 words out of 201092 words

Chapter 18 - AMRAH NAKE SO BOOK COMPLETE DOCUMENT .txt

ƙafafuwansa, yana direwa bisa sasanyan tile ɗin da ke baje a farfajiyar ɗakin, da ya ji ƙawa ta ko ina, ga ƙamshi ta ko wane kwararo yana tasowa.


***


MARADI, NIJAR.


My dearest fans, how are you all? I hope evryone is doing well.


You know what? Haka kawai nake ga kaman babu nasara a tattare da wannan plan din na su Maryama, gashi kuma tana neman boye wa mahaifiyarta. Me zaku ce? Shin ya kamata 'ya ta boye wa iyayenta matsalarta, musamman ma uwa mace?


Menene zai faru a Maradi, da marubuciyar ke neman mayar da mu can?


Sai mu ci gaba da bibiyarta, na tabbatar zata warware mana komai, zamu gamsu da komai a karshe.


Thanks all. Ina yinku my fans, irin over din nan, kun sani kuwa?


Pinky durling
RAZ 2
[8/30, 3:46 PM] Princess Amrah✍🏻💞: *🅰MRAH NAKE SO!* ♥


(Labari mai taba zuciya, soyayya, sadaukarwa da kuma ban tausayi.)


Na Amrah A Msh
_(Princess Amrah)_
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*


_Sadaukarwa ga masu cutar amosanin jini (sickler)_


2⃣9⃣


A tsiyace ya taho da motarsa, wayarsa ce ta yi ƙara a karo na ba adadi, wanda yake ayyana ƙin ɗaukar wayar a cikin zuciyarsa.


Wayar na tsinkewa babu jimawa kuma ƙarar text message ya shigo, kamar kar ya buɗe kuma dai ya daure ya buɗe. Abin da ke cikin saƙon wayar ne ya matuƙar razana shi, gabansa ya daɗa dukan uku uku, yana jin yanda zuciyarsa ke tafarfasa, tana tuno masa da mahaifiyarsa.


Latsa kiran lambar da ta masa text ɗin ya yi, bai daina zura gudun ba, haka kuma bai ajje hankalinsa sosai ga tuƙin ba, saboda zafin da zuciyarsa ke masa.


"A'i, dan Allah ki hwaɗi min Mammata ta samu sauƙi, baninson jin baƙin labarin nan daga gare ki."


Cikin muryar kuka wacce ya kira da A'i ta ce,


"Shi ke nan Mahmouda, shi ke nan Allah Ya karɓi Mamma, yanzun ga ne likita ya sanar min rasuwarta, dan shi ne ma nake ta kiranka kaƙƙi ka ɗauka, shi ne niyyi maka text ɗin nan."


"Innalillahi wa ina ilaihi raji'un!"


Ya furta cike da fargaba da damuwa, bai san sanda ya saki wayar ba, gabanshi na tsananta duka, baki ɗaya hankalinsa ya gama tashi.


Giccin mutum kawai ya gani a gabansa, da iya ƙarfinsa ya take burki, ya mayar da dukkan hankalinsa ga tuƙin, amma duk da haka sai da ya bugi mutumin, da ƙarfi motar ta tsaya.


Dafe kansa ya yi yana tunanin da me zai ji? Zuciyarsa zafi kawai take masa, tashin hankalin da bai taɓa shiga ba yake jinsa a yau.


A hankali ya buɗe motar, yana kallon yanda gaban motar tasa duk ya samu matsala, da alama dai wanda ya buga ɗin ya ji jiki. Fatanshi dai Allah ya iyakantar da abun, ya sa ba mai tsawo ba ne.


A gaban matashin ya isa, yana kallon yanda matattun kayansa da suka gama jigatuwa da datti jini sai malala yake duk sun ɓaci. Babu ko alamar numfashi a tattare da shi.


Duk iya dauriyar Mahmouda sai da ruwan hawaye ya zirara daga idanuwansa, yana jin yanda duniyarsa ta sauya masa a cikin lokaci guda, ya ma rasa yanda zai yi da mutumin da ya buge ɗin.


Kafin ka ce kobo wurin ya cika da mutane, wasu na hawaye, wasu kuwa hannuwansu bibbiyu a ka, suna kallon ikon Allah.


Wata budurwa ce ta taho goɗoɗo babu hijabi a jikinta, sai wani ɗan ƙaramin mayafi da ta sargafe a wuyanta. Cikakkiyar budurwa ce, mai tsawo da jiki, wacce a shekaru zata iya kai ashirin da biyar ma. Kwanon abinci ne bisa kanta, tana tafe tana rausaya, dukkan gaɓɓan jikinta suna girgiza.


Ganin dandazon mutane a bakin titi ya sa ta saki salati, bakinta a buɗe ta tsaya cak tana kallon sarautar Allah. Ita bata matsa inda suke ba, ba kuma ta tafi inda zata je ba.


Ganin an cicciɓo wanda aka kaɗe ɗin ya sa ta sakin kwanon da ke bisa kanta, ta ɗora hannunta a ka, da gudu ta ƙarisa inda suke.


"Na shiga ukuna ni Fiddou!"


Ta faɗa cike da tashin hankali, ta gagara sauke hannunta a ka.


"Me ya faru da Modu? Waye ya kaɗe sa? Wayyo niya Allah'na, Modu."


Ta sake ɓarkewa da kuka.


Ganin kamar Fiddou ta san shi ya sa Mahmouda dakatawa a gabanta, a hankali ya furta mata,


"Halan dai kin san shi ne?"


Kai ta ɗaga masa cikin kuka ta ce,


"Yanzu hakanga abincinshi ne na kawo mai. Amma idona ya gane mini wanga mugun abu. Allah de Ya sa wani abu bai samu Modu ba, wallahi rayuwata zata shiga garari matuƙar Modu ya mutu."


Cikin tausayi Mahmouda ya ce,


"Ba zai mutu ba giɗe, toho de mu tahi asibiti tare, mu hanzarta tun wani abu bai hwaru ba."


Da hanzarinta ta bi bayanshi, gaban motar ta buɗe ta zauna, yayin da aka kwantar da Modu bayan motar, sai wani ɗan unguwar mutum ɗaya a kusa da shi.


Sun yi tafiya mai ɗan nisa kafin suka isa wata asibiti wacce da alama ta kuɗi ce. Har ciki suka shiga da motar, da sauri Mahmouda ya kira nurses domin su taho da gado, a bashi taimakon gaggawa idan yana raye.


A hanzarce nurses ɗin suka taho da gadon, kafin su iso har wancan mutumin ya fiddo shi, ɗora shi kawai suka yi a kai shi da Mahmouda, sannan nurses ɗin suka tafi accident and emergency da shi.


Wani likita mai zafi ya sa aka kira Mahmouda, cikin faɗa yake shaida masa cewa ba zai karɓi Modu ba har sai ya taho da ɗan sanda.


Duk irin magiyar da Mahmouda zai ma likitan nan firfir ya ƙi yarda ya karɓe shi, a dole ya hanzarta tafiya Police station tare da wancan dattijon, ya samu ya taho da ƴan sanda mutum biyu, suka dawo asibitin.


Suna isowa wayarsa ta fara ruri, da faɗuwar gaba ya ɗauki kiran, muryar ƙanwarsa ya ji ta ce,


"Mahmouda ba zaka zo ko jana'izarta a yi da kai ba halan? Walle in dai baka zo ba mun cire ka daga sahun danginmu, mun yafe ka, tun da har ka gagara ka zo ka sallaci mahaifiyarka, dama tun ranta bai fita ba tacce a kirawo ka kui bankwana, babu irin kiran da ban yi ma ba amma kaƙƙi zuwa, daga ƙarshe ma sai kab bar ɗaukar kiran nawa, har Allah Ya karɓi rayuwarta, kuma bayan mutuwar tata ma ka ƙi zuwa. Babu komi Mahmouda, mun gode."


Kawai ta tsinke wayar da wani irin kuka.


Dafe kansa ya yi, wayar tasa ma sakinta ya yi ƙasa, yana jin yanda zuciyarsa ta masa nauyi sosai, kamar ba zata iya ɗaukar baƙin cikin da yake ƙunsa mata ba.


"Ka yi shiru giɗe, ka biya kuɗi ko ana samu a ceto rayuwar wancan bawan Allah tun bai mace ba."


Masifaffen likitan ya faɗa a karo na uku da yake ma Mahmouda magana bai ma san yana yi ba.


"Ina zan je in biya halan?"


Ya samu da ƙyar ya fiddo maganar, bayan ƴan daƙiƙu da ya yi shiru yana sauraren likitan.


"Tahi can, zaka ga hanyar Pharmacy ceniya, ka tai can ka biya kuɗɗi, zasu baka rasiɗi sai ka kawo can a cike masa katinsa, sannan ko ina duba shi."


Tafiya ya yi inda likitan ya kwatanta masa, bayan ya biya kuɗin ya dawo medical record, ya basu reciept sannan aka cike masa katinsa. A wurin suna sai da ya tambayi Fiddou, ta ce kawai a saka masa Modu Najibou, sannan aka miƙa katin ofishin likita, aka tafi da Modu da har yanzu ko motsi baya yi.


A cikin zuciyar Mahmouda kuwa tir kawai yake da hali irin na wannan likitan, ko kaɗan bashi da kirki bare ya roƙi alfarmar tafiya wurin jana'izar mahaifiyarsa.


Ganin kaMar akwai sassauci a fuskar Ƴan sandan ya sa ya faƊa masu komai, a ƙarshe ya nemi alfarmar zai je ya halarci jana'izar mamansa da ta rasu.


Daga farko basu amince ba, sai daga baya suka tausaya masa, suka yanke hukuncin ɗaya daga cikinsu zai bi Mahmouda, idan an gama su dawo tare, har sai an ga yanda hali ya nuna ga wanda aka kaɗe ɗin.


Sefa ya zaro daga aljihunsa wanda bai ko tsaya ƙirgawa ba, a hankali ya tako har inda Fiddou take, yana kallon yanda idanuwanta ke zubda ƙwalla, wanda hakan ya tabbatar masa da cewa lallai wannan mutumin da ya banke yana da matuƙar muhimmanci a rayuwar Fiddou, musamman ma da ya ga zallar tashin hankali a cikin ƙwayar idonta.


Kuɗin ya miƙa mata, fuskarsa babu walwala ko kaɗan a tattare da ita.


"Mi zan yi da su halan?"


Ta jefo masa tambaya ba tare da ta karɓi kuɗin ba.


"Zan tai in dawo, Mammata ta rasu za a yi jana'izarta yanzu, shi ne zan tai, kuɗin ga kuma ko akwai abin da za a buƙata nashi kahin in dawo."


Jiki babu ƙwari ta ɗaga hannuwanta da take jin sun mata nauyi ƙwarai ta karɓi kuɗin, ba tare da ko kallonshi ta yi ba. Saboda a zahirin gaskiya wata irin tsanarshi take ji a zuciyarta, a ganinta kaman duk abin da ya faru da Modu SHI NE SILA, dan haka bata jin akwai sauran wani abu da zai yi ya burge ta.


"Allah Ya bashi lahiya, sai na dawo giɗe."


Bata ce masa ko uffan ba, haka kuma bata sake kallonsa ba har ya ɓace ma ganinta, ta sake fashewa da wani kukan.


Tana nan zaune a reception ta ji muryar waccan nurse ɗin tana mata magana,


"Giɗe kin taho nan kin yi zaune, mi da baki matsa inda likita ba halan? Giɗe ya tashi kuma bai san kowa ba. Gashi can likita ya gama kula da shi har ma an kai shi ɗakin maza an kwantarshi."


Tashi Fiddou ta yi a saɓule ta share hawayenta, duk irin rashin natsuwa na Fiddou amma ta koma kamar ba ita ba, tafiya ma a hankali take yinta, haka magana ma a natse kamar dai ba ita ba.


"Wane ne ɗakinsa halan giɗe?"


"Mu tai in kai ki."


Bin bayan nurse ɗin ta yi shima ɗayan ɗan sandan ya bi su, suna isa male ward ta ce,


"Ku shiga, gadon da zai kallo ku shi ne an na giɗe."


Shiga ciki suka yi bayan nurse ɗin ta tafi. Tun daga nesa ta hango shi an maƙala masa ledar jini, da alama jininsa ya fita sosai, dama kuma bata yi mamaki ba, la'akari da yanda kayanshi suka yi kace kace da jini, kamar an yanka wata dabba an goge da kayan nashi.


Da kuka ta ƙarisa zama kusa da shi, tana gyaɗa kai tana faɗin,


"Sannu Modu, sannu sannu. Wallahi laihina ne duka wanga, laihina ne da ban zo na kawo ma abinci da wuri ba, na san yunwa ce ta ishe ka ka nemi ƙetaro titi ka biɗo ni, shine wagga ta'asa ta hwaru. Allah Ya baka lahiya Modu."


A hankali ya fara buɗe idanuwan nasa, da ƙarfi ya ƙarisa buɗe su, yana tunanin a inda yake, da kuma halin da yake ciki.


"Modu..."


Ta faɗa da murmushi mai haɗe da ruwan hawaye.


Murmushi shi ɗin ma sakar mata, kafin ya fara yunƙurin tashi zaune.


Miƙewa ta yi da sauri ta ce,


"A'a hwa Modu, halan baka ga baka da lahiya ba? Koma ka kwanta ka jiya? Ka natsu dan Allah dai."


Bai koma ya kwanta ɗin ba sai kallonta da yake yana murmushi irin na taɓaɓɓi , yana ɗan zaro idanuwansa.


"Walle giɗe ina hwasawa, ina hwasa kai ka inda take."


Yana jin ta faɗi haka ya koma ya kwanta, yana ɗan gyaɗa mata fuska alamar kar ta fasa, ruwan hawaye na zirara daga idanuwansa, murmushin da yake kuma bai kau ba.


"Yauwa ko kai hwa. Ka bari har likita ya gama duba ka sannan ko mi zaka yi sai ka yi abinka. Ka ga yanzu baka da lahiya ne, jininka ya fita sosai sai da aka siya wani shi ne ake ƙara ma."


Murmushin fuskarsa ya faɗaɗa, bai ɗauke kallonsa daga Fiddou ba ya ce,


"Ni bani son wannan jinin, ku bar ni da nawa wanda ke gudanya da..."


Bai ƙarisa maganar ba ta kalle shi ta ɓata fuska,


"Wai Modu me yake damunka ne? Na hwaɗi ma jininka ya hita da yawa hwa, mi da ba zaka yi shiru hakan nan ba halan?"


Shirun kuwa ya yi ganin kamar ranta ya ɓaci. Ya runtse idanuwansa alamun baccin ƙarya yake, sai kyarma idanuwan ke yi, hawaye kuma bai daina fita daga cikinsu ba.


Suna cikin haka sai ga wata nurse ɗin ta daban ta zo, hannunta riƙe da kwando mai ƙunshe da allurai da magunguna.


"Giɗe hala wanga ne Modu?"


Ta ce da Fiddou tana kallonta.


Kai kawai ta ɗaga mata.


Matsawa ta yi inda yake, tana yi tana magana,


"Hala har yanzu bai hwarka ba?"


"Ido nai biyu ai ko yanzu. Modu!"


Ta kira sunansa yanda zai ji.


Idonsa guda ɗaya kawai ya buɗe, shi ɗin ma ba duka ba, ya ɗan ƙwanyarasa a fuskar Fiddou kaɗan, sannan ya sake rufewa yana murmushi.


"Modu likita ta hwa zata baka magani. Mi da kake satar kallo na halan?"


Dariya ta so ta ɗan ƙwace wa nurse ɗin da kuma wancan ɗan sandan da ke tsaye yana kallonsu. Yanayin na su Fiddou akwai ban dariya.


Allura ta haɗa nurse ɗin kafin ta fara tunanin ta yanda zata fara, dan ta ga alamar taɓaɓɓe ne ba kansa ɗaya ba.


"Giɗe halan ya zan yi da wannan Modu?"


Ta juyo ga Fiddou tana tambayarta.


"Kuma walle Modu bashi son allura. Akwai sanda yai yi wani ciwo an sha daga da shi kahin a yi allurar nan. Amma na san yanda zan yi da shi."


Ta faɗa haɗe da mayar da kallonta ga Modu da murmushi.


"Modu ka ƙi buɗe idanuwanka ko? Walle idan baka buɗe su ba ba zan kai ka inda take ba, sai dai ko kukan jini zaka yi ka yi."


Da saurinsa ya buɗe idanuwan yana ware su a kanta, ya washe baki wanda dariyarsa kawai zaka kalla ta tabbatar maka cewa mahaukaci ne. Banda ƙazantar da ke jikin tufafinsa, da kuma sumar da ta gama mamaye kaf ilahirin fuskarsa, ta bisa kai kuwa dama ta yi tsawo har ta gaji, da alama dai ya jima bai yi aski ba.


"Mi zan yi ya yarda a yi?"


Nurse ɗin ta faɗa a tsorace, dan bata so wani abu ya same ta, kuma da alama dai baya son allurar, dan yanda ta ga yana binta da kallo ita da allurar tata, gudunta ma kar ya mammake ta.


Magana ta mata ƙasa ƙasa yanda Modu ba zai ji ba, kafin a hankali Nurse ta murmusa, ta kalli Modu ta ce,


"Kana so na kai ka wurin Amrah?"


Da sauri ya fizge ƙarin jinin da ake masa, ya diro daga bisa gadon, duk da ciwukan da ke jikinsa basu hana shi kuzari ba, yana kuka yana dariya da furucin,


"Dan Allah ki kai ni wurinta, wallahi *AMRAH NAKE SO!"*


How are y'all? I hope y're all fine.


How was this chapter? Kun ji ta daban ko? Ina fatan dai kuna gane maganar ta 'yan Nijar...lol😁


What do you expect? Who is that mahaukaci mai fadin AMRAH NAKE SO? I think he is the lover of Amrah, irin sosai da sosai din nan. Which Amrah? The writer of AMRAH NAKE SO? No. Her namesy from HOUSE OF NOVELS? I don't think so. To wace Amrah ce wannan? Ba dai wacce ta mutu ba ko?😳


Na hakura da jero expectations din nan nawa dai. Na bar ma marubuciyar ta warware min komai. Da haka nake son kuma masu karatu ku bar marubuciyar, ita zata bayyana maku komai.


Many regards to the readers of this book, especially those that reads and votes, not the ghosts, ehen🙄


Pinky durling
RAZ 2
[8/30, 3:47 PM] Princess Amrah✍🏻💞: *🅰MRAH NAKE SO!* ♥


(Labari mai taba zuciya, soyayya, sadaukarwa da kuma ban tausayi.)


Na Amrah A Msh
_(Princess Amrah)_
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*


_Sadaukarwa ga masu cutar amosanin jini (sickler)_


3⃣0⃣




Saurin dakatar da shi ta yi da faɗin,


"Koma ka kwanta in dai kana so na kai ka wurin Amrah. Ka kuma natsu na maka allurag ga ko kuma in hwasa."


Duk da baya son allurar amma a haka ya haƙura ya koma bisa gadon ya kwanta. Jikinsa sai karkarwa yake har ta samu da hikima ta soka masa allurar, tana yi tana faɗin,


"In dai yana son zuwa wurin masoyiyarsa Amrah to bana so ko motsi ya yi har sai na ƙare yin alluragga."


Da haka har ta samu da zare allurar daga jikinsa.


Tana gamawa kuwa ya fara ƙoƙarin saukowa daga bisa gadon, fuskarsa da murmushi yana faɗin,


"Ki kai ni wurinta. Dan Allah ki kai ni na ga Amrata."


Rasa yanda zata yi da shi ta yi. Kwandon ta ɗauka ta yi tsaye tana tunanin mafita. Jin muryar Fiddou ta yi ta ce,


"Sai ka yi bacci ka tashi sannan zata kai ka. Yanzu ka kwanta ka huta kahin a jima."


Komawar kuwa ya yi ya kwanta, yana wani irin yaƙe, haƙoransa da suka gama rinewa suka bayyana.


Gyaɗa kai kawai nurse ta yi cike da tausayi ta bar wurin. Dama allurar da ta masa har da ta bacci ta zuba a ciki. Take bacci ya ɗauke sa sai sauke ajiyar zuciya yake.


KATSINA, NIGERIA.


"Maryama, wato dai ba zaki faɗa min damuwarki ba ko? Yanzu kina ga kaman kina da wacce ta fi ni ne? Kina da wacce zaki tinkara da damuwarki wadda ta fi ni? Idan na shiga wata damuwa, zaki ji daɗi ki tambaye ni matsala ta na ƙi faɗa miki? Haba Maryama! Ya kamata fa ki san ke ba yarinya ba ce, kin wuce lokacin da zaki ringa ɓoye min damuwarki. Aikin Muhammad ne wannan ba naki ba Maryama."


Ajiyar zucuya Maryama ta sauke. Tana tunanin ta faɗa mata gaskiya ko kuwa dai kawai ta faɗa mata yanda suka yi da Jiddah? Shawara ta yanke kawai cewa kar ta faɗa mata gaskiya, saboda abin da Jiddah ta faɗa tsaf zai iya faruwa.


"Mama, na samu labarin wata baiwar Allah ne, labarin da ya matuƙar razana ni, ya zauna min a zuciya, nake jin tausayin baiwar Allah'r har cikin zuciyata."


Cikin matsuwa da son jin zancen Mama ta ce,


"Ehen, mabuƙata ne, a taimaka masu?"


"Ko kaɗan Mama, ba haka ba ne. Amrah ce..."


Ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login