Showing 87001 words to 90000 words out of 201092 words

Chapter 30 - AMRAH NAKE SO BOOK COMPLETE DOCUMENT .txt

da tarbiyyar yaranta.


"Yauwa Mamammu, a lallaɓa mana shi da kyau dan Allah. Insha Allahu zai aminc..."


"Na ma amince."


Suka jiyo muryar Abba na fitowa daga hanyar ɗakinsa, tare da ƙoƙarin isowa tsakar falon.


Murmushinsa ya faɗaɗa,


"Ba kuna magana ne a kan zuwa Maraɗi ba? Na ji komai ai. Ko ni na bada goyon baya ɗari bisa ɗari a je a taimaki bawan Allah'n. A masa duk abin da ya dace. Idan ma kuna ga kamar zama can ɗin ba zai yiu ba, za ku iya kawo shi nan, sai a nemi likitan ƙwalwa da na zuciya su duba shi, idan Allah Ya ba shi lafiya na san za mu ji komai daga gare shi. Zan bada gudummowar mota cike da mai, da kuma dreba ya kai ku har Maraɗi."


Tsalle Maryama ta buga haɗe da rungumar Abbanta, abin da ba ta saba ba. Ko a mafarki ba ta taɓa tsammanin za ta iya ma Abbanta haka ba. Sai yanzu ta yarda, ashe dai daɗi da farin cikin kan saka mutum aikata har abin da bai yi niyya ba?


"Na ji daɗi sosai Abba. Sai yanzu na ƙara tabbatar da ashe dai na tafka babban kuskure, na gudar iyayena da wata buƙata tawa. Ina sonku sosai iyayena. Wallahi na ma rasa ta ina zan fara bayyana muku murnata."


"Ta hanyar ƙara jin tsoron Allah kawai. Idan har kika kasance haka, to tabbas kin nuna mana farin cikinki na wannan lamarin, zan kuma ci gaba da yi miki addua, Allah Ya ba ku ikon taimakonsa, Ya cika muku burinku."


Komawa ta yi ga Mama, hawayen farin ciki take, wanda ba ma ta san sanda suke fitowa ba. Ji take kamar an mata bushara da gidan Aljannah.


"Thank you so much Mamana. Allah Ya miki albarka Ya raya min ke."


Dariya suke su duka a wannan lokacin, lallai ma Maryama, ji wata addua da ta ma Mama kamar wata ƴarta ta cikinta.


"Na ji to amin. A tashi a tafi kar a makara. Kamar ma na ji motsin Mallam Ya'u, da alama ya dawo daga kai Hammad Islamiyya."


Bayan ta miƙe ta share hawayenta, ɗakinta ta nufa domin sanyo hijabinta, ta kuma ɗauko jakarta. Ko kafin ta dawo sai da Jiddah ta daɗa yi musu godiya sosai, ta kuma shaida musu cewa da banda ita ne tafiyar, amma za ta ƙoƙarta sanar ma iyayenta yau, insha Allahu tare za su tafi. Ta zaɓi su tafi taren ne kawai don hankalin su Mama ya ƙara kwanciya da tafiyar.


***


Tsawon lokaci suke zaune gaban teburin likitan, tun bayan da aka ma Farouk Sardauna chest xray suke zaman jiran sakamako. Likitan na zaune da farin medical glasses a idonsa, ya mayar da hankalinshi baki ɗaya ga rubutun da yake yi.


Wani mutumi ne ya shigo bayan ya ƙwanƙwasa ƙofar an ba shi izinin shigowa. Hannuwansa riƙe suke da takarda mai faɗi, wadda hoton ƙirjin yake a ciki.


Bayan ya miƙa ta ga likita cikin girmamawa ya fita, likitan ya ɗago kanshi daga rubutun, a hankali ya zaro hoton daga cikin envelope ɗin.


Duddubawa ya hau yi, kimanin tsawon mintuna goma yana rubutu, kafin ya ce,


"Na yi mamaki. Hoton ƙirjinka lafiya lau yake, bai bayyana kowace matsala ba. Kenan dai ko kaɗan tarinka bai da nasaba da ƙirjinka, zargin da nake na pneumonia ko kaɗan ba ita ba ce. Saboda idan ita ce za ta bayyana a hoton nan. Tabbatuwar ko mura babu a ƙirjinka kenan."


Ya ɗan dakata daga nan, yana fiddo iska daga cikin bakinsa. Glasses ɗin nasa ya cire, ya ci gaba da faɗin,


"Gwaje gwaje biyu ne ya kamata a maka yanzu; tuberculosis test, sai kuma a yi hoton cikinka baki ɗaya. Dole a gaggauta yinsu, matuƙar tari ya fara yin irin wannan tsananin, wanda har ake fitar da jini to lallai ya ta'azzara. Amma kar fa ku damu, insha Allahu komai zai daidaita. Gano ciwon dai ne aiki, da zarar aka gano shi, ka hau turbar magunguna, za ka ga komai ya zama tamkar ba a yi ba."


Wani irin zazzafan huci ya fiddo daga bakinsa Bobby, tausayin kansa yake. Yau kimanin watanni uku kenan yake fama da wannan mugun tarin, sai dai bai ta'azzara sosai ba sai a cikin kwanaki huɗu da suka gabata. Tun daga sannan ko barcin kirki ba ya samun yi. Da zarar barci ya ɗauke sa to sai tari ya farkar da shi. Cikakken minti talatin ba ya jerawa yana barci. Ba kuma wai ya sha naganin tari ya samu sassauci har barci ya ɗauke sa ba, sam! Ba ya masa aiki. Ya riga ya zama addicted da shan shi, ta kai ga ba ya ma saka shi barcin, sai dai kawai ya kai shi wata duniyar, mai cike da sama da ƙasa.


"Ga wannan takardar, da ita za ku je a yi gwaje gwajen. Ku tabbatar an yi su nan da ranar talata, yau Sunday gobe Easter Monday babu aiki, a nan kuma wanda zai maka ɗin ba ya nan, in short, an ɗau tsawon lokaci ma ba a yi ba a nan. Ku daure ku je a yi, idan an maka ɗin sai ku kawo min result ɗin."


Miƙewa suka yi su dukansu jiki babu ƙwari. Ko a tuberculosis ɗin aka tsaya wani babban laruri ne, mai wuyar magani. Ga shi kuma ɗaukarsa ake, babu wuya na kusa da mutum ya kwasa.


Babu wanda ya iya cewa kowa uffan. Sosai Annur yake tausayin abokinsa Bobby. Ko ba komai damuwar Farouk damuwarsa ce. Kamar yanda ta shi damuwar take ta Farouk Sardauna.


***


Tunda sassafe ta tashi ta hau shirye shiryen tafiya. Ta kira Hadiza cewa ta zama ready, nan ta minti arbain ta fito bakin titi za su ɗauke ta. Jiddah ma sun yi magana, ita za su fara ɗaukowa kafin su tafi ɗauko Hadiza.


Ko karyawa ba ta yi ba ta fito, sanye take da baƙar abaya mai adon cyan, ta yafa mayafinta, sai jaka da takalminta duka cyan colour.






Tana fitowa falon Mama ta ce,


"Maryama ba dai har tafiya ba, ba fa ki karya ba."


Cike da ɗoki ta ce,


"Ba na jin yunwa Mama. Za mu biya ta crispy mu yi take away mu tafi da shi, idan mun ji yunwa sai mu ci."


Gyaɗa kai ya yi Abba. Da murmushi a fuskarsa ya ce,


"Ke dai zakwaɗi ne kawai. Sai a yi a tafi ai. Mallam Ya'u tun ɗazu ya iso, yana zaman jiranki."


Muhammad ne ya fito daga ɗakinsa sanye da pyjamas light brown. Yana miƙa da muryar barci ya ce,


"Yaya Maryama ina za ki je?"


"Zan yi tafiya ne Hammad. Include me in your prayers, please!"


Matsowa ya yi daf da ita ya ce,


"Ina za ki je haka Yaya Maryama? Ba fa ki sanar min ba."


Harararsa ta yi cikin wasa, ta kama hannuwansa duka biyu, ta ce,


"Naughty you. Kawai dan zan yi tafiya dole sai na sanar da kai? Yaron nan fa ka raina ni ma."


"A'a fa Maryama. My boy is not a naughty boy, he's a good boy, right?"


Ya kalli Muhammad yana masa murmushi.


Kai ya ɗaga ma Abban nasa, ya ce,


"To Abba ka ce mata ta tafi da ni."


"Abba ka gani ba? Da gaske yaron nan ya raina ni fa. In banda rigima ko wanka bai yi ba sai ya ce wai a ce na tafi da shi?"


Mama ta murmusa ta ce,


"Rabu da ita yarona. Super market za mu je anjima idan ta tafi. Just let her go, wayo za mu mata."


"To Yaya Maryama a tafi. Daike iyayena suna so naaa!"


Ya ƙarisa maganar da jan ƙarshen, yana mata gwaliyo haɗe da rugawa ya ɓoye bayan Abba.


"Uhm...kanka dai ake ji yaro. Abba barin fita."


A tare Mama da Abba suka ce,


"To Allah Ya tsare hanya."


Mama ta taso ta matso inda take.


"Allah yana tare da ke, Maryam. Insha Allahu zai kare mana ku, za kuma ku yi nasara a kan wannan nannauyan aiki da kuka fara. Ki tafi cikin aminci, adduata tana tare da ke, everywhere you go. Please contact me or your father when you need any help, okay?"


Kai ta ɗaga Maryama, da murmushi a fuskarta ta ce,


"Insha Allahu. Thank you very much Mama."


Ta fita daga ɗakin.


Sai da suka fara biyawa suka ɗauki Jiddah sannan ta kira Hadiza cewa sun taho ta fito bakin titi. Ko da suka isa kuwa ta fito ɗin, su kawai take jira suka tafi.


***


Tun bayan shigarsu asibitin take rarraba idanuwa, zuciyarta ƙagare take da ganin mara lafiyan, idanuwanta na burin yin tozali da shi.


Hadiza ce gaba sai Jiddah da Maryama biye da ita a baya. Babu mai furta komai a cikinsu.


Suna isa bakin ƙofar ɗakin Modu suka ringa jiyo maganganun Fiddou da Dr. Huzaif. Masifa yake mata da iya muryarsa. Iya ɓacin rai yau ya shige shi. Dr huzaif bai kasance ɗaya daga cikin mutane masu saurin ɓacin rai ko kuma ɗaukar zafi ba, sai dai kuma yau a yanayin yanda yake faɗan ya isa ya tabbatarwa kowa cewa ransa ya hasala.


"Ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba na hwaɗi miki a gaggauta siyan maganin nan. A ƙarshe har tambayarki nai yi akwai kuɗin siyan maganin? Baƙar magana kika yi min. Kuma sai yanzu in zo ki kama ce min wai ba a samu kuɗi ba? Halan ban hwaɗi miki zuciya tai tana iya kai matakin da ba za mu so ba? Siyan magungunan nan ne kaɗai zai kawo ma giɗe sassauci, to kuma ke banda rashin kunya babu abin da kika ƙware da shi. To ni kam iyakar abin da zan iya yi kenan, magani kuma idan kin ga dama kar a siya, I did my best, and leave you the rest."


Ya kamo hanyar barin ɗakin. Kiciɓis ya yi da su Hadiza, hakan ya sa shi ɗan kauce musu, yana neman barin ɗakin.


Cikin azama Hadiza ta ce,


"Dr. Dan Allah ka yi haƙuri. In dai kuɗin magani ne ga su a siyo a ba shi. Ka ma Fiddou uzuri, wallahi ta kanta take ita ma."


"Biyo ni na rubuta miki, a gaggauta siyo masa su yanzu."


Ba ta ko bi ta kan su Maryama ba, ta bi bayan likitan kawai suka fice daga ɗakin, hankalinta a tashe.


Tun bayan shigowarsu hankalinsu yake gare shi. Zaune yake ya naɗe ƙafafuwansa kamar mai zaman tahiya. Ya fuskanci daidai ƙofa sai faman yaƙe yake. Cikin dariya ya ce,


"Na faɗa miki ki ringa ramawa. Haka kawai sai yaita miki masifa?"


Sai kuma ya yi shiru, take hawaye ya fara kwaranya daga idanuwansa.


"Halan missa kake kuka Modu? In dai dan ka ga ina yi ne to ni ma na daina, ka gani ba? Na share hawayen."


Ta ƙoƙarta yin murmushi.


Mamaki bai gushe daga fuskokin ƴan matan biyu ba. Da gaske babu bambanci tsakanin Annur da Modu. Sai dai kuma kallo ɗaya duk wani mai ƙwalwar kirki zai ma Modu ya tabbatar da cewa ya jima a cikin halin taɓin hankali. Saboda har idanuwansa sun juye, irin na mahaukata sosai. Komai nasa abun ƙyama ne; kayan jikinsa, fuskarsa, gashin kansa da komai ma.


"Ka tsaya da kukan nan ge, walle na yi shiru hwa."


Murmushi ya yi kuma, cikin wata murya kamar mai hankali ya ce,


"Amrah ta taɓa faɗa min a duk halin da na tsinci kaina na zama mai haƙuri. Ko tana raye ko ba ta raye, in rinƙa tunowa da wannan maganar, ta ce wai hakan zai sa na samu riba mai girma a rayuwa."


Sai kuma ya ci gaba da yaƙe haƙoransa.


Mutuwar tsaye kawai su Maryama suka yi.


'Amrah!?'


Su duka biyun suka jinjina a ƙasan ruhinsu.


19th Aughust 1987
BAMA, BORNO STATE.


A yi haƙuri na ji na shiru kwana biyu, abubuwa da dama suka sha kaina, kuma dai har yanzu ban gama samun ƙarfin jikina ba. Dan Allah ina barar addua'arku, Allah Ya biya mana buƙatummu na alkhairi baki ɗaya.


Yanzu za ku fara jin salon labarin yana sauyawa; za mu koma yinsa kwan-gaba kwan-baya, sai kun ajje hankalinku sosai sannan za ku fahimce shi. Fahihtarsa na ɗaya daga cikin warwaruwar labarin. Don haka ɗaure ɗamararku, the game has just started.😀


ummiieeterh jinjina da fatan alkhairi. Ƙaunarki nake fisabilillah!


Ba sai na faɗa muku me ya dace ku yi ba a yayin da kuka karanta ko wanne peji. Na san kun sani.


Pinky durling
RAZ 2
[8/30, 3:53 PM] Princess Amrah✍🏻💞: *🅰MRAH NAKE SO!♥*


_(Labari mai taba zuciya, soyayya, sadaukarwa da kuma ban tausayi)_


Sadaukarwa ga masu cutar amosanin jini (Sickler)


Na Amrah A Mashi
(Princess Amrah)
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*


4⃣4⃣


Follow me on wattpad:
PrincessAmrah


***


Kallonta yake cike da so da ƙauna, idanuwansa ƙyam a bisa fuskarta, yana jin yadda soyayyarta ke azalzalar zuciyarsa. Sosai yake tausayinta, rayuwarta, da komai nata abun tausayi ne.


"Dadyn Nadrah wannan irin kallo haka, ai sai ka sa mutum ya ƙware."


Hannunsa ya sa ya shafo fuskarta, da yatsunsa ya taɓa hancinta da murmushi shimfiɗe a bisa fuskarsa.


"Ba zan taɓa gajiyawa da daina kallon matata Suhaila ba, komanta burge ni yake; murmushinta, kallonta da komai ma. Kin ga kenan za ki shekara kina ƙwarewa in dai don ina kallonki ne."


Ya ƙarisa maganar tasa da faɗaɗa murmushin nasa.


"Yauwa, ni kam Dady akwai maganar da nake so mu yi; batun yaran nan ne, ya kamata a ce sun shiga makaranta haka nan, musamman ma Nadrah da ta fara girma, ya ci a ce ta jima da shiga makaranta."


Hannunsa na dama ya ɗora a bisa haɓar Suhaila, cikin shauƙin so ya furta,


"Na jima ina wannan tunanin, sai dai kuma abin da nake ji taɓarɓarewar karatunsu, kin ga yanzu haka maganar transfer ake mana, shi ya sa ba na son aikin federal wallahi, babu wuya sai a lalata karatun yaro, saboda yawace-yawace."


"Huh!"


Ta sauke ajiyar zuciya, ta ce,


"Duk da haka dai ai ba za mu tsaya jiran inda za a mayar da kai ba, waye ya san sadda za su ɗauke ku ɗin?"


"Gaskiya ne. Bari insha Allahu ranar Monday zan binciki makaranta mai kyau sosai, ina son gina ilimin yara sosai, babban burina shi ne yarana su ginu bisa turbar karatu, both na boko da na islama ɗin."


"Haka ne Dady. Allah Ya kai mu to."


Ta yi shiru daga nan, ta dafe ƙasan mararta da take ji yana mata ciwo sosai ba kaɗan ba.


"Suhaila ya dai?"


Ya tambaye ta bayan ya dafe mata marar tata, yana kallon cikin idonta don jin amsar da za ta ba shi.


"Babu komai Dady, kawai dai marata ce nake ji tana ɗan katsa min, amma ba sosai ba."


Ta ƙoƙarta ƙirƙiro murmushi.


"A'a Suhaila, ki faɗa min gaskiya fa, ko haihuwar ce?"


Hararar wasa ta masa, da murmushi ta ce,


"Dady akwai sauran lokaci fa, edd ɗina fa sai nan da sati biyu zai cika."


"Hmm! Suhaila kenan. Don an ce expected day of delivery ai bai zama dole a ce sai a ranar za ki haihu ba. Su ma kansu hasashe ne, ba wai sun tabbatar ba ne. Kuma za a iya haihuwa mako biyu kafin edd ɗin, ko kuma mako biyu bayan edd ɗin, babu yanda ba ta kasancewa. Don haka..."


Salatin da ya ji Suhaila na yi ne ya sa ya kasa ƙarisa zancensa, cije laɓɓanta ta yi tana jin yanda ciwon ke ƙara nuƙurƙusarta, kodai haihuwar ce da gaske?


"Suhaila na faɗa miki haihuwa ce wannan, ki tashi kawai mu tafi asibiti. Nadrah! Saddiqa!"


Ya ƙwala musu kira. Nadrah ce ta yo gaba sai Saddiqa biye da ita a baya.


"Nadrah kawo hijabin Momy, asibiti za mu tafi, ba ta jin daɗi ne."


Da saurinta Nadrah ta nufi uwar ɗakar Suhaila domin ta ɗauko mata hijabin, Saddiqa kuwa tambayoyi kawai take jerowa Dadynta, cewa baby boy za a siyo musu? Baby girl? Dady a tafi da ni...


Ko saurarenta bai yi ba Dady, ya gaggauta karɓar hijabin da Nadrah ke miƙo masa, cikin kaɗuwa yake zira mata hijabin, har yana mayar da ƙasa sama, sai da Nadrah ta taimaka masa.


"Nadrah yi sauri ki ɗauko ma Saddiqa mayafi ke ma ki ɗauko na ki."


Cikin kaɗuwa ya yi wannan maganar, yana ɗaukar mukullin motarsa daga bisa tv stand, wanda yake haɗe da na gidan baki ɗaya.


Fita ya fara yi ya buɗe motar, ya wangale gate ɗin gidan sannan ya dawo ciki da sauri, ya taimaka ma Suhaila ta miƙe tsaye, hannunta dafe da mararta har yanzu ba ta saki ba. Ganin kamar dai tafiyar tata ba za ta mata daɗi ba, ya sa ya cicciɓe ta da iya ƙarfinsa, ya kai ta bayan motar ya kwantar, lokaci zuwa lokaci yana yi mata sannu.


Komawa ya yi ciki ya ɗauko kayan jarirai adadin wanda suka fara tarawa, kamar sun san cewa haihuwar za ta zo yanzu, sun siya komai, sai dai haɗa su ne wuri guda kawai Suhaila ba ta yi ba. Kwaso su ya yi da yawa ya jera a cikin riyo, ya fito daga ɗakin. Yaran ya umurta cewa su isa bakin motar, shi zai rufe gidan sannan ya fito.


A daburce yake aikata komai, dakiya kawai ya yi da bai rafka kuka ba. Dama haka yake yi a duk haihuwar da Suhaila za ta yi, sosai take shan wahala kafin ta haihu, kuma kusan a tare suke jinyar, dan ba ya zuwa ko ina har sai ta haihu.


Cikin motar ya dawo ya tada, sannu yake ta maimaita mata, sanda zai yi reverse ma sai da ya ƙura mata ido yana ƙara jin tausayin mata a zuciyarsa, lallai mata abun a tausaya musu ne, abun a ma uwa mace biyayya, shi ya sa manzon Allah SAW ya ambaci kyautatawa uwa mace har sau uku sannan ya ambaci uba namiji. Gyaɗa kansa ya yi cikin ƙarfin hali ya ƙirkiro murmushi, ganin yanda yaran ke kuka riris, mamansu da ba ta da lafiya.


"Ya isa haka Nadrah, ke fa babba ce bai kamata kina kuka ba. Ke da ya kamata ki rarrashi ƙanwarki Saddiqa amma ke ce ma za ki zama Oganniya?"


Shessheƙar kukan suke har a lokacin, sosai suke tausayawa mahaifiyarsu.


Bayan ya fitar da motar waje ya dawo ya rufe gate ɗin, a gaggauce ya koma cikin motar ya tayar suka lula sai FMC da yake aiki.


Da suka isa ba wani ɓata lokaci sosai aka yi ba, kasantuwar a can take awo, kuma shi ɗin staff ne a asibitin, yana ɗaya daga cikin manya manya a Pharmacy.


Ɗakin haihuwar aka nufa da ita, wata nurse kuma ta karɓa riyo ɗin da ke hannunsa, shi kuma ya zauna daga can nesa, kasantuwar ba a barin maza matsowa kusa da labour room ɗin.


Tagumi ya rafka da duka hannuwansa, Nadrah na daga gefensa na dama, sai Saddiqa a gefensa na hagu, ta kasa daina kukan, duk da yarintarta.


A can labour room kuwa wahala sosai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login