Showing 45001 words to 48000 words out of 201092 words
Chapter 16 - AMRAH NAKE SO BOOK COMPLETE DOCUMENT .txt
Allah, ba dan ni ba..."
Ya duƙa bisa guiwayinsa, kanshi a ɗage yana kallonta, yana kallon yanda ta haɗe rai.
"Ki so ni, ba dan ni ba, ba dan munanan halaye na ba."
Yana kai wa nan ya dakata, yana binta da kallo, idanuwansa sun yi jajur, wanda kaɗan ya rage su kawo ruwa, jarumta irin tasa kawai ta hana fitowarsu.
"Ashe ma ka san kana da munanan halayen?"
Ta faɗa tana binsa da wani mugun kallo, kallo mai cike da nuna tsantsar tsana da ƙiyayya.
Shiru ya yi bai ce komai ba, sai taunar laɓɓansa da yake, yana mai takaicin halayensa, wanda ko kaɗan basu kasance na gari ba.
"Dan haka tun wuri, ka nemi wacce kake ganin zata so ka, ba wai ni ba, da har in kwanta dama ta ba zan taɓa son mutum fasiƙi irinka ba."
Runtse idanuwansa ya yi, yana mai jin ɗacin kalamanta, yana jin yanda zuciyarsa ke masa raɗaɗi, amma sai dai ba ya jin zai iya mata komai, ba ya jin baƙaƙen maganganunta zasu saka shi aikata mummunan aiki a kanta, kamar yanda yake ma duk macen da ta nemi kawo masa wargi a duniyarsa.
"Ba zan miki dole ba, saboda ba a soyayya dole. Idan ma ana yi, bana jin zan taɓa iya yi miki dole, a komai na rayuwarki.
Insha Allahu daga yau na rabu da ke, ba zan sake yi miki wata magana ta soyayya ba. Amma dan Allah ina neman wata alfarma a wurinki."
Kai ta ɗaga masa alamun ya ci gaba da maganarsa, a zuciyarta tana mai tsananin jin daɗi, da alama tarkonta zai kama kurciya.
Duka laɓɓansa ya saka a baki, ya kalli Jiddah bayan ya miƙe tsaye, ya ɗan sunkuyar da kansa ƙasa, ya ce,
"Ƙawarki nake so. Ina nufin wadda kuka zo tare."
Kasa ɓoye farin cikinta ta yi, daɗi ne ya mamaye kaf illahiri zuciyarta, ta fara ayyana abubuwa da dama a cikin zuciyarta.
"Ki taimaka min ta so ni, dan Allah."
Ya faɗa cikin wata murya mai rauni, wacce ba ko wane lokaci ba ne take bayyana, take fita daga bakinsa ba.
"Ya Noor, ba wai kana da abin ƙi ba ne a jikinka, wanda zai sa a ƙi ka. Sai dai baƙaƙen halayenka ne abun ƙi,wanda babu na tsinta a ciki. A duk halayenka babu na kirki, babu wanda mace zata ɗauka ta so ka, ta aure ka, har ta yi alfahari da kai a matsayin mijinta."
Ta koma bisa kujerar da ta sauka daga kai, ta seta idanuwanta a cikin nashi, cikin natsuwa ta ce,
"Ya Noor, me zai hana ka koma asalin Annur ɗinka? Ka koma Annur ɗin da kaf duniya take alfahari da shi? Me zai hana ka kawar da duk wannan sabbin halayen da ka ɗauko cikin ƙananan shekaru, ka koma naka na asalli na shekara da shekaru?
Wallahi matuƙar baka canza halaye ba, na tabbatar ba zaka taɓa samun matar kirki ba.
Babu macen kirkin da zata so auren mazinacin miji. Babu wacce zata so auren miji ɗan ƙwaya, wanda zai iya illatata a ko wane lokaci.
Na tabbatar Maryama ba zata ƙi ka ba, sai dai zata iya ƙin munanan halayenka. Maryama mace ce mai addini, mace ce kamila, mace ce wacce ko wane namiji zai so mallakarta a matsayin matarsa."
Shiru ta yi daga nan tana kallon reaction ɗinsa, tana jin yanda tausayinsa ke dira a cikin zuciyarta. Sai dai kuma har cikin zuciyarta bata ƙaunar Annur, bata jin zata iya son shi, ba wai dan plan ɗinsu kawai ba.
Hannunshi na dama ya cusa a cikin sumarsa, ya murza a hankali sannan ya fitar, yana mai dubanta, duban tsanaki ya ce,
"Wallahi Jiddah bana jin zan iya barin halayen nan ne, da tuni na daina su. Na riga na zama addicted da su."
A fusace ta miƙe tsaye tana binsa da wani mugun kallo, kallon da ke ƙara bayyana masa irin tsanarsa da ta yi.
"To shi ke nan. Ba kuwa zaka taɓa samun ni ko ƙawata ba. Ka ga sai ka je can ka nemi wata mai irin halinka ka aura. Mu ma zamu nemi masu irin halayenmu."
Tana kaiwa nan ta fara taku, takun da ke ƙara narkar da zuciyar Annur a duk sanda yake kallonta.
Bai tsayar da ita ba, haka kuma bai bi ta ba. Sai dai ya rasa yanda zai yi, bai san ya zai yi da zuciyarsa ba. Ya rasa gane me yasa ya kasa cire Jiddah daga zuciyarsa, duk da irin wulaƙancin da take masa ba. Bai san me ya sa daga kallo ɗaya ya kamu da son Maryama ba. Bai ma san ya hakan ta kasnace ba.
Kanshi ya haɗa da guiwoyinsa, yana jin yanda kansa ke masa zafi, yake barazanar fashewa. Zuciyarsa kuwa ya ma rasa a babin da zai saka ta. Babin ƙaunar Jiddah da ya jima yana so, ko kuwa son Maryama da ya fara daga kallo ɗaya?
Farin ciki ne lulluɓe da zuciyarta, ta sani, ta san dole wani abu zai faru, ko ba yanzu ba.
Da fara'a ta shiga falon, sallama ƙunshe a bakinta.
Kallo guda Hajiya Suhaila ta mata ta ji wani irin daɗi a zuciyarta, dan da alama sun daidaita kansu ne, the way take murmushi. Ta kasa ɓoye farin cikinta.
"Kina ta jirana, ko Maryam?"
Jiddah ta faɗa bayan ta ɗauki wayarta daga kujerar da zata zauna, ta daidaita zamanta a hankali, murmsuhi bai gushe daga fuskarta ba.
"Wallahi kuwa."
Maryama ta faɗa tana kallon yanda ƙawar tata ke farin ciki.
"Afuwan, wallahi wani abokinsa ne ya haɗa ni da shi, shi ya sa na daɗe."
Tana faɗin haka tana kallon yanda fuskar Hajiya Suhaila ta sauya daga fara'ar da take zuwa wani yanayin da ba za a iya fassara irinsa ba.
"Sannunku da hutawa Momy. Bara mu fara haramar komawa, lokaci na tafiya, kuma akwai Islamiyya."
Jiddah ta faɗa bayan ta miƙe, tana fuskantar Momy, da fara'a a saman fuskarta.
"Tun yanzu zaku tafi? Gaskiya ban gode da wannan zuwan ba, 'yata. Ya kamata a fidda min rana ta musamman, Maryama ta biyo ki ku min yini guda cur."
Bayan Maryama ta miƙe ta ce,
"Insha Allahu zamu fidda rana guda mu zo, Momy. Sai dai kawai ki ganmu kwatsam."
Miƙewa ta yi Hajiya Suhaila, da murmushi ta ce,
"Ina zuwa."
Ta haura saman benen zuwa ɗakinta.
Bata jima ba sai gata ta fito, hannunta riƙe da ledoji guda biyu.
Miƙa wa Jiddah ta yi ta ce,
"Kun zo a lokacin da uwar taku bata da komai na ƴan mata. Ga wannan, turaruka ne, kowa guda ɗaya. Na gode ƙwarai da zumunci, kuma ina sauraren zuwanku yini."
Godiya sosai suka mata, sannan suka kama hanyar fita, zukatan ko waccensu da abin da take saƙawa.
Tsaye yake jikin gate, ya ɗan jingina da ɗakin mai gadi, kansa sunkuye yana kallon ƙasa.
Ganinsa da suka yi ya sa su kallon junansu, Maryama na tunanin yanda suka yi da Jiddah, da alama dai ta yi nasara, ta yanayin fuskarta kawai.
"Ku jira zan sauke ku."
Ya faɗa can ƙasa ƙasa, ba tare da ya kalli ko waccensu ba.
"Ka bar shi kawai, a napep muka zo, kuma zamu hau mu koma a kanta."
Jiddah ta faɗa, cikin halin ko in kula.
Bai saurare ta ba kawai ya nufi parking space, dama akwai makulli a jikinsa, wata farar benz kawai ya shige, ya fara ma mai gadi horn, alamun ya buɗe masa.
Lokacin da ya fita da motar har sun riga da sun fita su ma, hakan ya sa ya ci burki a gabansu, yana binsu da kallo su duka biyun.
Ganin kamar basu san yana yi ba ya sa ya danna horn har sau biyu, amma babu wacce ko kai ta daga ta kalle shi.
Har ya so ya yi zuciya ya ƙyale su kuma dai ya ji ba zai iya ba, ya sake danna masu wani horn ɗin, bayan ya sha gabansu.
Ɗagowa ta yi Maryama ta kalle shi, sannan ta sunkuyar da kanta ƙasa, ta ci gaba da tafiyarta.
Gyaɗa kansa ya yi, yana mai tsananin jin haushin kansa, kafin ya take motar a fusace, ya tafi ya bar su.
"Just wait a little while, zaka sha mamaki, Annur Iqra Al-Hussaein."
Jiddah ce ta yi wannan furucin, tana mai sakin murmushi, haɗe da jinjina kanta.
"Tell me something, Jiddah. Da alama haɗuwarku ta tafi yanda muke so."
Maryama ta faɗa da murmshi kwance a saman fuskarta.
"Indeed, Maryam. Komai ya kusa kasancewa yanda muke so. An kusa zuwa inda zamu ji daɗi."
Ta labarta mata kaf yanda suka yi da Annur, da halin da ya shiga ta dalilin kalamanta, da kuma ƙaunarta da ya faɗa ta lokaci guda.
Fara'a sosai Maryama ta faɗaɗa, ta ma rasa me zata ce, ta rasa yanda zata nunar da farin cikinta.
"Ban zaci abun zai zo da sauƙi haka ba, ko kaɗan. Ashe ma sauƙin hali gare shi."
Jiddah ta gyaɗa kanta ta ce,
"Waye ya faɗa miki yana da sauƙin hali? Soyayya ce kawai. Kin ma san wani abu wai?"
Kai Maryama ta gyaɗa alamar a'a.
"Ban taɓa tsammanin kallo guda zai sa Ya Noor ya so ki ba. Sai dai kuma na daina mamaki, saboda yanda ya goge da ƴan mata, yake matuƙar son mata.
Ke, mace fa ko wace iri ce in dai zai ganta sai ya ce yana so. Ina ga fa ko taɓarya aka ɗaura ma zani da riga sai gayen can ya ce yana sonta."
Ta ƙarisa maganar da dariya a fuskarta.
"Ba zan musa miki ba kam. Lallai na yarda, kin san Annur."
Maryama ma da dariya a fuskarta ta yi wannan maganar, har tana ɗaga hannunta alamun jinjina ga Jiddah.
"Yau ana ma magana? Ai dalilin da ya sa na shirya hakan ke nan. Sanin halinsa da na yi, bashi da wasa in dai ta wurin mata ne.
Ita ko Momy har ta fara jin daɗi, ta ɗauka ko daidaita kanmu ne muka yi."
Tafa hannu suka yi su biyun, a daidai tsayuwar napep a gabansu.
Bayan sun shiga suka kwatanta masa gidan su Jiddah, saboda can zasu fara zuwa ta yi shirin makaranta, sannan su tafi gidan su Maryama ita ma ta shirya.
Suna cikin napep ɗin wayar Maryama ta yi ringing. Sunan mai kiran da ta gani ne ya sa ta murmusawa, ta kalli Jiddah da murmushi sannan ta ɗaga wayar.
"Bobby."
Ta faɗa a hankali, tana sauraren abin da zai faɗa.
"Dan Allah Bobby ka ƙyale ni. Ni fa ina da wanda nake so, yake so na. Me zai hana kai ɗin ma ka nemi wacce zata so ka? Ina amfanin soyayyar maso wani wai?"
Saukar da muryarsa ya yi, ya ce,
"Ba zan taɓa daina son ki ba, kin sani. Wallahi in da a ce Allah zai haɗa ni da wannan saurayin naki, koma wanene da sai mun yi ko ni ko shi. A kan me zai nemi shiga hurumin da ba nasa ba? Rayuwarki don ni aka yi ta, dan haka ya zama dole ki so ni, ko ma ta halin ƙaƙa ne."
Yana gama faɗin haka ya tsinke wayar, ba tare da Maryama ta sani ba. Jin shiru ne ya sa ta ɗago wayar ta duba, ganin ya kashe ya sa ta sauke nannauyar ajiyar zuciya, ta mayar da wayar a cikin jaka.
"An zo wurin."
Maryama ta furta, tana kallon Jiddah, cike da farin ciki.
"Da alama plan ɗin namu ma ba wani mai tsawo ba ne. Ba da jimawa ba zamu kammala shi."
Jiddah ta ce,
"Na tabbata wurinsa zai je yanzu. Saboda babu mutum mafi kusanci da Ya Noor kamar Bobby. Shi ya fi hallaka rayuwar Ya Noor, shi ya sa na kawo mana wannan plan ɗin."
Dunƙule hannyensu suka yi, cike da ƙaunar junansu.
To readers, how was this chapter?
Akwai masu tausayin Annur kuwa?
Akwai masu tausayin ƙangin soyayyar da ya jefa kansa a ciki?
Wai miye ribar wannan plan ɗin da Jiddah da Maryama suke ƙullawa? Zai yi tasiri kuwa? Zai gyara rayuwar Annur, ya koma asalin Annur ɗinsa?
Zaku samu amsoshin wannan tambayoyin, idan har kuka juri bibiyar Amrah. Zata warware maku zare da abawa. Har abubuwan da da dama daga cikinku na san sun manta da su, duka zan gano maku su, sannu a hankali.
Ina son ku irin sosai da sosai ɗin nan, kun san da haka kuwa? Soyayya fi sabilillah.
Pinky durling
RAZ 2
[8/30, 3:45 PM] Princess Amrah✍🏻💞: *🅰MRAH NAKE SO!* ♥
(Labari mai taba zuciya, soyayya, sadaukarwa da kuma ban tausayi.)
Na Amrah A Msh
_(Princess Amrah)_
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
_Sadaukarwa ga masu cutar amosanin jini (sickler)_
2⃣7⃣
Kamar yanda su Maryama suka yi tsammani kuwa haka abin ya kasance. Bayan Annur ya bar inda suke kai tsaye wurin Bobby ya nufa.
A fusace ya faka motar, yana jin yanda zuciyarsa ke tafarfasa, take duka da sauri da sauri.
Babu natsuwa ya iso cikin gidan su Bobby, isarsa ɗakin kuwa ko knocking babu haka ya afka ciki, babu annuri ko kaɗan a fuskarsa.
"Guy, ya dai?"
Bobby ya faɗa, yana kallon yanayin abokin nasa.
Banza da shi Annur ɗin ya yi, yana mai ƙoƙarin jawo shisha a gabanshi.
"Guy me ke damunka ne? Babu flavor a ciki ai."
Tsaki ya saki bayyananne, haɗe da ture shishar daga gabansa, yana mai dafe kansa.
Matsowa ya yi Bobby a kusa da Annur, ya dafa kafaɗarsa, yana son jin dalilin yanayin da yake ciki.
"Abokina, am in love..."
Bai ƙarisa maganar ba Bobby ya tulle da dariya, har yana riƙe cikinsa.
Da hannu ya ringa gwada sa, yana son yin magana amma dariya ta fi ƙarfinsa, da ƙyar ya iya faɗin,
"Kai ɗin? Kuma true love? It'll never be possible."
Gyaɗa kanshi ya yi Annur, ya ƙi faɗin komai, saboda takaicin Bobby da yake.
"Guy, wai da gaske kake ko da wasa? Wannan wace irin mace ce, wacce take neman jefa guy cikin tarkon ƙaunarta?"
"Wallahi..."
Bobby ya dakatar da shi.
"Ko Jiddah ce?"
"Ba Jiddah ba ce, abokina. Ta zo da wata ƙawarta ne gidanmu yanzu. Ban ma san yanda aka yi, daga kallo ɗaya na faɗa ƙaunarta ba. Lokaci ɗaya na ji ƙaunar da nake ma Jiddah, ta fara gangarowa zuwa ga ƙawar tata, wacce na ji ta ambata da Maryama. Abokina, please ka bani solution, ya zan yi ta so ni?"
Ajiyar zuciya Bobby ya sauke, cikin natsuwa ya fara ajje kalamansa,
"Guy, kai fa jarumi ne, na sani, kai ma kuma ka sani. Wace irin mace ce wacce kake ga kamar zata iya gagararka? A tunanina babu ita a duniyarta, ba a yi ta ba, ba kuma za a taɓa yinta ba. Yanzu dai bara na baka codein mai sanyi, ka sha ko zaka samu sassauci a zuciyarka. Daga nan sai mu je wurin wannan mutumin, duk ma yanda zai maka sai ya yi."
Sassanyar murmushi Annur ya ajje a saman kyakkyawar fuskarsa, yana jinjina kai alamar gamsuwa da furucin Bobby.
Deep freezer ya buɗe Bobby, ya fiddo robar coke mai sanyi ƙwarai, sannan ya rufe freezer'n, ya ƙariso gaban Annur.
Jijjigata ya yi, sannan ya miƙa wa Annur, da murmushin jin daɗin yanayin da ya ga abokin nasa a daidai wannan lokacin.
"Thank you very much, abokina. Am proud of you, ka sani."
Ɗaga kwalbar ya yi ya kai bakinsa, bai sauke ba har sai da ya yi rabin robar, sannan ya ajje ƙasa, yana jin yanda duniyarsa ke masa daɗi, kamar ba shi ne yake cikin ɓacin rai a ƴan daƙiƙun da suka wuce ba.
Bayan kamar daƙiƙa ɗaya, ya sake ɗora robar a bakinsa, sai da ya shanye tas sannan ya sauke, yana kallon Bobby da lumsassun idanuwansa.
Minti talatin Annur ya ɗauka da shan coke ɗin, ya fara slow, yana jin daɗin yanayin nasa, wanda yake jin ba zai taɓa daina shiga irinsa ba, har sai sanda ya kwanta damarsa.
"Guy, zaka iya tashi kuwa?"
Bobby ya faɗa, bayan ya saka farar t shirt a jikinsa.
"Zan iya, ɗan taimaka min na miƙe."
Annur ya ce da Bobby, bayan ya janye daga bakin gadon da ya jingina da shi.
Taimaka masa ya yi Bobby, ya miƙe a hankali, ya ajje ƙafafuwansa ƙasa.
Makullin motarsa Bobby ya ɗauka, ya saka a aljihun wandonsa, sannan suka kama hanyar fita.
Bobby da kansa ya ja motar, sauti ya kunna, kafin ya ja motar a tsiyace suka bar wurin.
Tafiya suke sosai, suna yi suna ɗan taɓa hira, Annur na ɗan sako surkulle, saboda juyewar da ya yi, hankalinsa ya fara fita daga kansa, wai dan ma cyrup ne, a ganinsu ba ya gusar masu da hankali.
Sun yi nisa da Katsina, har sai da suka isa wani ƙaramin ƙauye mai suna Jani, hanyar Mani. Lungu da saƙo suka hau bi, har sai da suka fita daga duk gidajen da ke cikin ƙauyen. Ta cikin gonaki suka ringa bi, sai dai ga hanyar mashin da ta mota nan, da alama ana yawan bin hanyar ne.
Gaban wani gini suka ci burki, ginin jar ƙasa ne, wanda yake zagaye da wasu irin ƙayoyi, baki ɗayansa.
Faka motar Bobby ya yi, ya kashe motar, sannan ya fito ya zagaya ya buɗe wa Annur, ya kama masa hannu suka shiga gidan.
Tun daga bakin ƙofa Bobby ya fara magana,
"Boka mai ran ƙarfe, boka gagarabadau, boka mai gani har hanji, boka mai hikima da fasaha, boka gamu gare ka, ga baƙin jiya sun dawo, sun dawo da wata gagarumar buƙata."
Bobby na direwa nan sai ga wannan ƙayoyin sun fara daddarewa, suka buɗa masu hanya suka shiga ciki.
Babu mamaki ko kaɗan a saman fuskokinsu, sai ma murmushin bobby da ya faɗaɗa, suka isa bakin ɗakin, wanda shi ɗin ma zagaye yake da ƙayoyi, sai mutum ya rantse cewa kango ne, babu mai rai a cikinsa.
Wani kirarin Bobby ya ƙara yi masa, nan ma ƙayoyin suka ringa darewa suna basu hanya, har suka ƙarisa daga cikin ɗakin.
Babu kowa a ciki, sai wani tsohon gadon ƙarfe, da wata yagulalliyar katifa bisansa.
Suna zama sai ga wani irin baƙin tsoho ya ɓullo a gabansu, baki ɗaya fuskarsa ta ko ina suma ce fara tas, wacce za a iya kiranta da furfura.
Yana daidaita zamansa kuma wata ƙwarya ta ɓullo a gabansa, cike da jini a cikinta.
Bai ce masu komai ba, amma sun san abun da zasu yi. Bobby ya fara ɗaukar ƙwaryar ya sha jinin da ke ciki, sannan ya miƴa wa Annur ma ya sha, suka rage kaɗan a ciki. Shi ma bokan ɗauka ya yi ya sha, bai sauke ba sai da ya shanye jinin tas, sannan ya ajje a ƙasa. Yana ajje ta kuma ta ɓace ma ganinsu.
Kallon Annur ya yi cikin ido, ya zaro masa idanuwansa masu ban tsoro,