Showing 177001 words to 180000 words out of 201092 words
Chapter 60 - AMRAH NAKE SO BOOK COMPLETE DOCUMENT .txt
tausayi)_
Sadaukarwa ga masu cutar amosanin jini (Sickler)
Na Amrah A Mashi
(Princess Amrah)
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
7⃣1⃣
Wattpad: PrincessAmrah
***
This page is in your honour, Ummukulthum Sani. You are indeed a nice soul. I really love and cherish you. Kina cikin best 10 people da suka fi kowa ƙaunar book ɗin nan. Allahu ya bar zumunci da zaman tare. Ina ƙaunarki fisabilillah.
***
Hannunsa ya sa ya tallabo fuskar Annur yana kallonsa.
"Annur ko?"
Dr. Hamdan ɗin ya faɗa. Maryama ta ba shi amsa. Ya saki kan Annur ɗin da ya tallaba sannan ya saki murmushi.
"Akwai hasashe ɗaya da likitocin ƙwalwa ke fara yi idan za su duba mara hankali. Suna farawa da kallon cikin ƙwayar idonsa, saboda idan ka kalli idon mahaukaci sosai akwai wata ƴar birkicewa da za ka ga ya yi. To abin da ya ɗaure min kai, idanuwan wannan ɗin normal suke gaskiya. Ku dube shi da kyau."
Ya dakata daga nan.
"Annur me ya sa kake noƙewa idan na haɗa ido da kai? Kodai ba ka so in gane cewa kana a cikin hankalinka ne?"
Dukkansu da ke ɗakin suka zabura. Shiru Annur ɗin ya yi, sai dai kallo guda za ka masa ka hasasho tashin hankalin da yake a cikinsa.
"Idan ma dai ka yi haukan a baya, to lallai ka samu sauƙi sosai a yanzu kam. Annur tun yaushe ka warke?"
Nan ma dai shiru Annur ɗin ya ƙara yi.
"Ban ga amfanin pretending ɗin ba. Dukkanmu nan da muke tare babu bare, ni ne kawai baren amma kuma makusancinka, tunda na duba ka a matsayin likitanka."
Ya fasa kuka da ƙarfi Annur ɗin. Ya ɗora dukkanin hannuwansa a bisa kai, kafin a hankali ya sunkuyar da kansa yana kuka mai cike da zallar tashin hankali, da kuma shessheƙar kuka.
Su duka mamaki bai kau daga fuskokinsu ba. Maryama a ranta take jinjina kalamin likitan, ta yadda kai tsaye ya zartar da hukunci kan cewa Annur ɗin ya samu lafiya. Amma idan ya samu lafiyar me zai sa ya rinƙa acting kamar bai warke ba? Da sauri ta matsa gare shi, ta tallabo shi cikin hawaye tana rarrasarsa, hankali da ƙwaƙwalwarta sam ba su aminta cewa Annur ɗin ya warke ba. Hasashe ne dai kawai irin na likitoci, tunda dai ba ilimin gaibu gare shi ba.
A hankali ya zame daga riƙon da Maryama ta masa, sai gashi ya silalo ƙasa, tafukan hannayensa ya rufe fuskarsa da su, yana kuka bil-haƙƙi.
Bubbuga masa kafaɗa Dr. Hamdan ya hau yi.
"Ba kuka na sa ka yi ba Annur. I just want you to tell me, why are you pretending? Akwai damuwa ne?"
Sai a nan Uncle Marwan ya ce,
"Annur talk mana. Ka yi shiru ka daina kukan da kake yi kuma."
Sai a sannan ya ce,
"Haƙiƙa na ji sauƙi, tun daga ranar da na fara ganin zoben hannun Maryama..."
Cike da mamaki ta ɗago kai tana kallon shi. Mafarki take yi kawai ta riya a ranta. Saboda ba ta taɓa tsammani ba. Wai ma me yake faɗa ne?
Murmushi Dr. Hamdan ya saki.
"Wasu mutanen sai su rinƙa ce ma likitocin ƙwalwa wai tamkar masu aiki da jinnu, ko kuma suna da ɓoyayyen tsafi. Alhali kuma ba haka ba ne. Karatu ne kawai mutum ya yi mai zurfi, fannin ƙwalwa kai tsaye da kuma psychology, wanda hasashenmu ke hasko mana wani abu, cikin salo da dabara muke gano gaskiyarsa. A sadda na duba Annur, ban tabbatar cewa yana a cikin hankalin nasa ba. Sai dai tun sadda na shigo, kallo ɗaya na masa na hasko cewa da hankalinsa. Saboda yanayin zamansa, dariyar yaƙe da yake saki sam! Ba irin na mahaukata ba ne. A nan duk ban gasgata ba, sai sadda na umurce shi da mu haɗa idanuwa ya noƙe, sai na ƙarisa gasgatawa. Saboda duk wanda za ka buƙaci ka haɗa ido da shi ya noƙe, lallai akwai wani ɓoyayyen al'amari a tattare da shi. Ko ga mace ma, ka nemi haɗa ido da ita ta noƙe, to cikim biyu akwai ɗaya. Kodai ba ta da gaskiya, ko kuma ta yi zurfi a ƙaunarka. To me zai sa daga haɗuwa yau ɗaya tal Annur ya noƙe ma haɗa ido da ni? Bayan nan kuma, idanuwansa normal suke, ko kaɗan babu alamun birkicewa a tattare da su. Sai ga shi hasashen nawa ya zama gaskiya. May I go?"
Ya miƙe tsaye. Alhaji Marwan ma ya miƙe fuskarsa cike da mamaki.
"Dr. Ya za a yi ka tafi daga zuwanka?"
"I've done with my job, Mr."
Ya saki murmushi.
"But Dr..."
Ya katse sa.
"Duk abin da ya yi saura iyakacinsa tsakaninku. Ba zan so jin sirrin family ba. Ku tattauna komai, ku ji dalilinsa na yin pretending ɗin. Ni zan tafi."
Ba don Uncle Marwan ya so ba ya gyaɗa kansa.
"To Dr. Ba dai za mu iya biyanka ba. Sai dai mu kamanta..."
Ya ɗaga masa hannu fuskarsa da murmushi.
"Me na muku da zan karɓi wani abu daga gare ku? Don't worry Mr. Dr. Hamdan is a very simple man. Let me go, please."
Hannu ya miƙa masa suka sake gaisawa, sannan ya taka masa har gaban motarsa, yana daɗa yi masa godiya.
Ita kam Maryama ba ma ta samu damar yi masa godiyar ba. Mamaki haɗe da al'ajabi ne lulluɓe da zuciyarta. Ta kasa ko da kallon sa ma. Yamaira da ke zaune ma mamaki ne ya hana ta tankawa. Sai famar rirrigar Yesmeen da ke barci take yi.
Bayan Alhaji Marwan ya shigo ya zauna kusa da Annur a ƙasa. Ya tallabo shi ya ɗora fuskarsa bisa cinyarsa. Yana ɗan bubbuga bayansa a hankali.
"Ka yi shiru ka ji."
"Uncle..."
Ya faɗa cikin muryar kuka. Sai Alhaji Marwan ya ƙarisa tabbatar da zancen likitan. Yadda Annur ya kira sunansa sosai ya tuno da rayuwar Annur ɗin ta baya, tun yarintarsa har zuwa girmansa.
Ya lallaɓa ya tashi zaune.
"Uncle haƙiƙa na tsinci kaina a cikin matsanancin tashin hankali, tun daga ranar da Maryama ta fara shigowa inda nake na yi tozali da zoben hannunta. Sai dai tun daga nan ciwon yakan kaɗo min, wani lokaci sai in rinƙa ji na tamkar ba ni ba, sai na tuno da wasu abubuwan, sai kuma in neme su a ƙwaƙwalwata in rasa. Na ci gaba da rayuwa a matsayin mahaukaci ne saboda in gasgata halin da nake ciki ɗin. Na farga na gan ni a gidan wasu wanda ban taɓa sanin da su ba a duniya. Ban san dalilinsu na kawo ni inda suke ba, sai dai na rinƙa jin wasu kalamai a bakinta, wanda suka tabbatar min da cewa aure za a ɗaura mana ni da ita.
A duk sadda na ji ni daidai, nakan duba ma'ajiyar Maryama, in ɗauko wannan zoben mai matuƙar daraja a gare ni, in kalla. Wani lokacin ina kuka haka nake kallonsa. Sosai nake ankara da Maryama. Na fahimci yadda take ƙaunata da zuciyarta ɗaya. Take da burin kyautata min, take son ganin dariyata.
Akwai ranar da zancen Amrah ya shigo cikin hirarmu, wacce har ga Allah daga farko ban san komai ba, kamar yadda na faɗa muku cewa abin yakan kaɗo min ne. Kamar wasa zancen ya yi tsawo, sai ta rinƙa tuno min da Amrah. A take na rinƙa tunanin yarintarmu da Amrah. Ƙaunatayyar da muka yi wa junanmu. Kyautatawa da kuma soyayyarmu ta tsakani da Allah.
Soyayyar Amrah ta daɗa komawa sabuwa dal a lokacin, nake jin ina ma dai a ce Amrah za ta dawo gare ni. Ina ma a ce tafiya ce ta yi zuwa wani gari, komai daren daɗewa za ta dawo a gare ni mu ci gaba da rayuwarmu a tare.
A nan ɗin Maryama ta rinƙa kawo min kalamai masu zama zuciya, wanda duk iya taurin zuciyar mutum dole sai ta karaya. Ta nuna min zallar soyayyar da take min a baki, wacce na tabbatar da har cikin zuciyarta hakan ne. A take ta ƙoƙarta share min hawaye, ta saka ni murmushin dole, sannan ta nufi kawo mana abincin da za mu ci.
A wasu lokutan har gani nake kamar dai Maryama ta gane cewa pretending ne nake yi, ƙyale ni kawai ta yi. Sai dai kuma yadda take tausayina, jikinta ke rawa take hidima da ni, ta min wanka, ta saka ni na yi alwalla, ta saka mu yi sallah tare, abinci ta ba ni shi a baki, sai na tabbatar cewa har yanzu ba ta fahimci lafiyata lau ba.
A ranar da hankalina ya fara dawowa, Umman Amrah ta zo har gidanmu, ta tado min labarin asalin zoben Amrah. A nan ne na tabbatar hankalina ya kammala dawowa gangaar jikina. Saboda ban ƙara jin wata alamar gushewar hankali kamar a baya ba. Ita kanta Maryamar idan za ta ajje hankalinta, za ta iya gano cewa tun daga nan ibadata ta gyaru. Ta sha mamakin ganin ina alwalla daidai, sai kawai ta ɗauka cewa koya min da take yi ne ya sa komai ya daidaita. Haka sallah ma, sai ta ɗauka duk koyawarta ce ta yi tasiri, alhali kuwa hankalina ne ya dawo gangar jikina.
Hankalina bai gama tashi ba, sai da na wayi gari da tabbacin wai su Dady ba su ne iyayena ba. A lokacin da Maman Yesmeen ke bayani, ji na yi tamkar in fasa kururuwa mai tsananin ƙarfi, in yi ihun da zai jijjiga kaf ilahirin katangar gidan. Sai dai na saita zuciyata, saboda ba na son a gano na samu sauƙi, don sai na gwammacin halin haukan da nake ciki ma, a kan mugun labarin da kunnuwana suka jiye min, wai mutanen da na rayu da su ba su ba ne iyayena.
A baya na yi ɓoyon na warke ne don sanin haƙiƙanin dalilin da ya sa ba a miyar da ni gidanmu gaban iyayena ba, saboda ko ba ta fito fili ta faɗa min ba, na tabbata akwai sadda zancen zai kawo zance ta faɗa min.
Wannan shi ne gaskiyar abin da ya faru. Haƙiƙa na wamrke, na kuma samu lafiya."
Ya ƙarisa maganar da sharar ƙwallarsa.
Komai a mafarki take ganinsa. Ta kasa furta komai, kamar yadda ta kasa daina kallonsa. A wani ɓare na zuciyarta murna ce fal, abin da ta daɗe tana jira, Annur ɗinta ya warke, sai ga shi ashe ma a matsayin warkakke take tare da shi. Wani ɓaren na zuciyarta kuwa, tunani take kamar zai bar ta ne. Kamar ba zai taɓa amincewa da ita a matsayin abokiyar rayuwarsa ba. Maganar da ta ji ya yi ce ta tsamo ta daga duniyar tunanin da ta lula.
"A rayuwata tunda na tashi na yi wayo na san Amrah, na kamu da soyayyar Amrah, rasuwarta ta girgiza ni, ta shigar da ni wani mawuyancin hali, wanda na gagara tuna komai na rayuwata. Ban taɓa tsammanin akwai wata mace da zan so bayanta ba. Ban taɓa tunanin cewa Maryama za ta yi tasiri a cikin zuciyata ba. Ranar da na fara ganinta a cikin hankalina, ƙarfin hali da jarumta kawai suka hana na kai mata duka. Kalaman soyayya da take faɗa min, jin su nake kamar ana zuba narkakkiyar darma a cikin kunnuwana, tsabar jin haushinsu da nake yi. Ranar da ta shigo tana faɗa min an ɗaura mana aure kuwa, tamkar in rusa kuka haka na rinƙa ji. Sai dai na daure, na kai zuciyata nesa, na ci gaba da rayuwa da ita. Mamaki bai gushe min ba a ranar da Maryama ta fara shiga ban-ɗaki da ni ta yi min wanka, ta rinƙa runtse idanuwanta, amma duk da kunyar ba ta hana ta tsaftace ni ba.
Babu abin da kyautatawa ba ta sakawa. Wannan kyautatawar da ta rinƙa yi min, ita ta rinƙa siyan soyayyarta ta ƙarfi da yaji tana kai wa har a cikin zuciyata. Ita ta sa zuciyata kamuwa da ƙaunarta, duk da cewa ƙaunar Amrah na nan ba ta gushe ba. Duk da hakan nakan tuno Amrah. Nakan tuno rayuwarmu ta baya, da kuma alwashin auren junanmu da muka yi. Sai dai ina tausar zuciyata, a duk sadda na tuno da nasihun Amrah a gare ni, wanda na kasa yin amfani da su a lokacin da ta rasu, har hankalina ya gushe.
Wallahi da zuciya ɗaya na kamu da ƙaunar Maryama, nake jin ta har cikin zyciyata. Samun mace irin Maryama abu ne mai matuƙar wahala, wasu halayen nata har suna min kama da na Amrah.
Na ƙudurci rayuwa da Maryama har ƴarshen numfashina. Na yi alwashin kyautata mata, kamar yadda ta kyautata min a sadda take tunanin ba na cikin hankalina."
Duk da kukan da take yi, hakan bai hana ta sakin murmushi haɗe da ajiyar zuciya ba. Ta rinƙa bin sa da kallo, kallon mamaki. Duk da son da take masa tun da daɗewa, ba ta taɓa tsammanin duk ranar da Annur ya warke zai so ta ba. Sai ga shi wai yau Annur da kanshi, kuma a cikin hankalinsa yake furta mata kalmar so. Ina za ta saka ranta don murna?
Alhaji Marwan ya ji daɗi sosai, ya ce,
"Ni kaina har ƙarshen rayuwata ba zan taɓa daina jinjinawa yarinyar ba. Haƙiƙa yarinya ce ƴar halak, da ta amsa sunanta ƴar albarka. A cikin halin rashin hankali da kafe, ta turje kan sai ta aure ka. Ta ƙi auren ɗan uwanta da iyayenta suka zaɓa mata, kawai don ta taimaka maka.
Sannan kuma ga iyayenta da suka yi risky'n aura wa ƴarsu mahaukaci a matsayin abokin rayuwarta. Ba zan taɓa mantawa da su ba, haka kuma ba zan taɓa daina yi musu addua ba."
Annur ya jinjina kansa, yana tuno mutuncin iyayen Maryama da ya karanta a lokaci kaɗan.
"Ni yanzu abin da ban sani ba, shi wancan ɗan uwan nawa, me ya sa zai yi rayuwa a gidanmu a matsayin ni ne shi, kamar yadda na ji Maryama ta faɗa wa Yamairah jiya?"
Maryama ta ƙoƙarta tattaro magana, ta ce,
"Ni ma kaina ban sani ba, abin da na jima ina son sani kenan. Kuma abun haushi, tunda yake a gidan su ba su taɓa ganin wani bambanci a tsakaninsa da kai ba? Na jima ina tunanin nan."
Uncle Marwan ya ce,
"Allah kaɗai ya bar wa kansa sani, sai ko shi Salman ɗin. Ku haɗa da ni nan kaina, ban taɓa kawo wa raina cewa wai ba ainahin Annur ba ne. Ko kaɗan ban taɓa ganin wata alama da za ta nunar min da cewa Salman ba Annur ba ne. A ganina komai nasu ɗaya ne, basu da bambanci. Sadda su Maryama suka fara kawo min maganar, na sha mamaki sosai, har daga farko na kasa gasgatawa, sai daga baya sannan."
Yamairah ta ce,
"Suna da bambanci, sai dai kaɗan ne ba mai yawa ba."
Annur ya kalle ta.
"Kenan dai identical twince ne mu?"
Ta ɗaga masa kai.
"Wata tawada ce ta bambanta ku, a ƙasan fuskarsa kusa da wuyansa take. Sannan kuma fuskarka ta fi ta shi walwala. A haɗuwata da kai jiya kawai na fahimci haka."
"Allah sarki! Allah mai iko! Sarki gagara-misali. Mabuwayi, mai hikima. Allah mai tsara lamurra yadda Yake so. Allah mai aikata abu ta yadda Ya so ya kasance. Mahaliccinmu mai sarrafa abu, ba tare da samun tangarɗa ko kaɗan ba.
Idan ba al'amarin Allah ba, ta yaya halittar mutum ɗaya za ta kasance ga mutum biyu?"
Uncle Marwan ya ce,
"Duk ba abin mamaki ba ne wannan. Fin biyu ma za a iya samun masu kama. Da ake haihuwar ƴan huɗu fa? Ko kwanakin nan wata mata ta haifi ƴan huɗu, kuma duk kamanninsu iri ɗaya ne."
"Haka ne Uncle...ahm..."
Ya yi shiru alamun yana so ya yi magana.
"Say it out ɗana. Akwai damuwa ne?"
"Uncle tunda dai haka abun ya kasance, ina da buƙatar komawa gida, sosai nake son ganin Dady da Momy, da kuma ganin ɗan uwana, ya faɗa min dalilinsa na yin pretending a matsayin shi ne ni."
***
Kuka take sosai, har muryarta ta disashe tsabar kukan. Duk da cikin halin da yake, shi ɗin ma tashin hankali ya gama garwaye jiki da jinin jikinsa, amma bai hana shi rarrasarta ba.
"Ba na so kina kukan nan Suhaila. Ina so ki ƙaddarta tamkar komai bai faru ba har zuwa safe, ko za ki samu ki iya runtsawa."
"Alhaji me ya sa zan yi shiru? Me ya sa zan iya runtse idanuwana da nufin yin barci bayan tashin hankalin da nake cikinsa? Ka faɗa min Alhaji, ta yaya zan iya daina kuka bayan na yi zama tare da mutumin da ba ɗana ba, tsawon shekaru da dama a matsayin ɗana?"
Ta gyaɗa kanta, hawaye sharkaf da fuskarta, duk ya gama sauka ya wanke wuyanta.
"Na sani sarai Suhaila, cewa ba abu ba ne mai sauƙi. Wannan wani gagarumin abu ne, da ba mu taɓa tsammanin faruwarsa ba. Sai dai ina so mu taru mi miƙa al'amarin ga Allah, kar hakan ya sa mu manta da ƙaddararmu, wacce duk dabararmu ba za ta taɓa nisantarmu ba."
"Alhaji..."
Ta yi shiru.
"Ki daure dai Suhaila. Ina gudun kar wannan damuwar ta jawo wata babbar damuwar."
"Alhaji gwara ma in mutu a kan wannan baƙin daren da nake a cikinsa yau. Ban taɓa tsammanin akwai ranar da rayuwa za ta birkice mana kamar haka ba. Manya-manyan abubuwa biyu sun faru a baya, amma hankalina bai tsananin tashi kamar na yau ba. Me ya sa yaron nan zai mana haka? Wane dalili zai sa ya raba mu da gudan jininmu, ya dawo a ƙarƙashin inuwarmu da zama? Alhaji ka duba fa ka ga, ashe har da shirka, ya haɗa mu da boka, don kar mu taɓa kawo wa ranmu cewa ba ɗan namu ba ne. Me ya sa rayuwa za ta min haka? Me ya sa?"
Ya jawo ta ya ɗora kanta a bisa cinyarsa. Tamkar ƙaramar yarinya haka ya rinƙa rirrigarta.
"Duk ba wannan ne abun damuwar ba yanzu, sanin haƙiƙanin inda Annur ɗinmu yake ne abin ji. Sanin halin da yake ciki, da kuma inda yake."
Ta tashi zaune.
"Alhaji shi ne kuma kake tunanin zan iya yin barci a wannan halin? Ban san halin da ɗana yake cikinsa ba. Ban san a wace rayuwa yake ba yanzu. Ban san duniyar da ya faɗa ba. Ya ce kurciya aka masa. Alhaji ko ka san cewa kurciya har ƙasar ma baki ɗaya mutum yana iya bari? Kila ma